← Book details Mutun Ko Aljana Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 3 OF 14

Sashe 3

Mutun Ko Aljana Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Shiru Malam Iliyasu ya yi yana nazarin maganar yar tasa,dan tabbas shi ma ya lura da idon karen
"Tabbas ni ma naga idon karen amma kin san ba bu irin yanda Allah baya halittan abu ke dai abun da na ke so dake karki watsa da addu'a a ɗuk in da ki ke Allah yana tare da ke" Kaina na gyaɗa ina faɗin "Toh Baba in sha Allah zan yi kamar yanda ka ce " Shafa kaina Baba ya yi yana faɗin"Allah ya yi miƙi albarka".Na amsa da"Ameen" sannun na shige gida shi kuma Babana ya wuce ma sallamaci,

*Bangaren su Hanifa*

Cikin ɗak'in da Aliya take ciki ta nufa ta na zuwa ta turo kofar a hankali ta shiga ta maida kofar ta rufe hango Aliya ta yi an lulluɓe ta da farin zanin gadon asibitin,wani irin kuka ta saki da s'auri ta kara so kusa da gadon hannunta na rawa ta sa ta yaye abun da aka rufe ta da shi ido huɗu ta yi da fuskar Bastynta ga idonta dake a rufe ga kuma gefe _gefen fuskarta da ta yi jajawur saboda wahala data sha jijjigata ta shiga yi ta na kiran sunanta "Besty ! Besty!dan Allah ki tashi karki min haka.dan Allah karki tafi ki barni me ya sa ki ka ƙi yerda da shawarata Besty? Sai dana faɗa miƙi ki haƙura da Asaf amma kink'i yeɗda.gashi yanzu sun kashe min ke dan Allah ki taimaka ki tashi karki mutu yanzu muna da buririkan de ya wa daya kamata mu cika shi"Haka Hanifa ta dinga faɗa ta na yi ta na girgiza Aliya ta na kuka,ana haka ne likitan ɗazu ya turo kofar ya shigo ya sameta,

Kallon Hanifa ya yi ya ce"Haba baiwar Allah me ya sa baza ku karɓi kaddara ba ? Ya kamata ku karbi jarabawan da Allah ya aiko muku da shi hannu bibbiyu kufah muslimai ne bai kamata ku dinga yin haka ba".

Wani irin kallo Hanifa ta jefawa likata da shi,likita bai san sanda ya haÉ—iye sauran maganar da ya yi niyar yi ba,

"Karka kara cewa Bestyna ta mutu dan Bestyna ba yanzu zata mutu ba,ko yanzu zata mutu ba dai Aljana zata kashe ta ba dan haka ba ruwanka kawai ka kyaleni" ta na kaiwa nan taci gaba da kiran sunan Aliya "Aliya tashi kin ji haba Aliyata karki min haka kin ji Bestyna wannan karon cikin rarrashi ta ke magana,amma still Aliya bata tashi ba.

Tambayar kansa likita ya shiga yi akan maganar Aljana da Hanifa ta yi yanzu.'Kamar ya Aljana bazai kashe mata Besty ba?Ganin da ya yi ba bu mai basa wannan amsar ne ya sa shi watsar da maganar,"Humm saboda ta riki ce ne kawai ya sa take maganar Aljana"Kai kawai ya girgiza kana ya juya ya yi bakin kofar,

Jin karatun da Hanifa ta fara yi ne ya sa likita dakatar da tafiyan da ya yi niyar yi, ya juyo ya zuba mata ido, Ayatul kursiwu da suratul Nasi da falhagi ne ta ke karanta wa ko wanne sai data karanta kafa uƙu _uƙu sai Amanar Rasulu data fara karantashi bata ma karasa ba taji Aliya ta yi wani irin attishawa da karfi haɗe da buɗe ido Aliya na buɗe ido Hanifa ta faɗi ta suma......

Ina so naga ruwan comments dan wancan page din dana turo baku min comments 😒

Yawan comments yawan typing ✍️

Comments and share fisabilillah

*Fulanin of Jajirtattu ce ✍️*
[24/08, 23:45] Sakeena Isma'il Cameroon🥰: 💫 MUTUN 👩‍🦰KO ALJANA 👹 💫

Story and written ✍️

By: Sakeena Isma'il Cameroon
(Mom Muwadda)

__________________________________________________

Utilise ce lien pour intégrer mon groupe WhatsApp : https://chat.whatsapp.com/KN5jaKvQOu02sqXTMBtbRJ

__________________________________________________

https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v
💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
(J.W.A)
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️

__________________________________________________

*Diamond💎 Star⭐ Ladies🧝‍♀️*
*(We stand together)*
🤝🤝🤝

Paid Book ₦500

Free Page 4️⃣

Bismillahi rahmani rahim

Ba ta ma karasa ba ta ji Aliya ta yi attishawa da karfi haÉ—e da buÉ—e ido, buÉ—e idon Aliya ya ke da wuya Hanifa ta faÉ—i kasa ta suma,

Tashi zaune Aliya ta yi ta shiga kallon dakin kamar wata zararriya haka ta koma sai data karewa dakin kallon saf sannan idonta ya sauka akan na Likita sai a lokacin ta gane asibiti take baki ta buÉ—e daker ta fara magana "Doctor me ya sa meni ?" Sai a lokacin doctor ya dan motsa daga inda ya ke tsaye ya karasa kusa da gadon dan tun É—azu yake saye kusa da bakin kofa tun lokacin da ya ga Hanifa ta suma ya kasa kwakkwaran motsi dan sai a lokacin ya samu amsar tambayar da ya yi wa kansa akan maganar Aljana ta Hanifa ta yi akan Aliya.

Dan ba karamin tsoro ya ji ba a lokacin da ya ga Hanifa ta faÉ—i ta suma,

"Doctor ina maka magana ka yi shiru"

Aliya ta sake dafi a karo na biyu

"Sorry! ɗazu ne Mom ɗinki da wannan kawar taƙi suka kawo ki nan kamar gawa muna duba ki muka tarar kin mutu ashe ba mutuwa ki ke yi ba aikin Aljanu ne amma mai kuka masa haka har ya aikata miki wannan danyen aikin?dan na san ba karamin wahala ki ka sha ba saboda a wuyanki na gano hakan"

Doctor ya yi magana yana É—agowa,ya ga wayam bai ga komai ba juyowa ya yi ya ganta durkushe a gaban Hanifa ta na kiran sunanta"Hani! Hani na dan Allah ki tashi me ya sa meki haka ?" Shiru ba amsa, É—agowa ta yi idonta ya yi jajawur kamar karwashin wuta ta zuba su kan Likita dake saye kamar tsoko yana kallon su.

A fusa ce ta saki Hanifa ta miƙe ta tako ta karasa gaban Likita kana ta fara magana "Wai kai wana irin Likita ne?taya bestyna ya suma ba za ka taimaka mata ba?ko uniform naka na karya ne kawai?".

Sai a lokacin likita ya saƙi murmushin mai ciwo dan maganar Aliya ya dan ɓata masa rai

"Humm! Aliya ki Ke ko wa? Naji Bastyn naki na kiranki dashi.toh ba ni ne tsilar saka Bastyn ki a wannan halin da ta ke ciki ba.ke ce tsila dan haka ke ya kamata ki taimaka mata kamar yanda ita ta taimaka miki a lokacin da ki ka suma"Likita na gama fad'ar haka ya juya a fusa ce ya yi bakin kofa ga t'ausayin Hanifa dake ratsa mai zuciya yana son yi mata addu'a amma yana tsoron a bin da zai je ya dawo,

Har ya dora hannunsa samar kofar da niyar buɗewa sai ya ji ta yi magana cikin sanyin muryar"Dan Allah likita ka fahimtar dani wallahi bangane in da maganarka ta dotsa ba sam".Ba tare da Likita ya juya ba ya ce "Mu a lokacin da aka kawo ki nan muna yin bincike muka gano cewa kin mutu amma Bestynki ta ce sam baki mutu ba dan har magana nayi mata akan cewa me ya sa ba za ta d'auki jarabawan da Allah ya aiko mata dashi ba ta nuna sam ita bata yedda ba a taƙai ce dai ita ta miki addu'a cikin idon Allah ki ka farfaɗo nima da ki ka farka ba karamin mamaki na yi ba.dan haka kema yanzu ya kamata ki yi wani abu ta samu ta farfaɗo"

Hawaye Aliya ta share kana ta ce"Ni wallahi ! doctor ban iya karatu ba".

"Toh amma ai kin iya karanta suratul nasi da kuma falhagi.ko suma baki iya ba?"

"Ummm !toh shima na fara mantawa".Cikin mamaki doctor ya ke kallon Aliya dan har mamakin ya kasa ɓoyuwa akan fuskarsa

"Yanzu kina nufin shima kin manta shi?"."Eh "Aliya ta bashi amsa.

"Toh in kina sallah me ki ke karantawa"?."Wallahi ni na kwana biyu ban yi sallah ba gaskiya"Aliya ta faÉ—a ba tare da ta ji kunya faÉ—a ba.

"Hummm! Allah ya shiryeki wannan a bu
In da ki ke yi ma ai dole Aljanu su samu wajan shigarki a duk lokacin da suke so".

Ido Aliya ta zaro waje cikin tsoro da firkici Aliya take tambayar doctor.

"Doctor ! Kana nufin saboda bana sallah ne ya sa Aljanu shiga jikina ?"."Kwarai kuwa dan da ace kin rik'e addini ba bu a bin da zai sameki ko ya sameki ma ba za ki sha wahala sosai ba,ni dan Allah bani waje na duba ta"

Doctor ya yi magana haÉ—e da fara takowa ya nufi in da Hanifa ta ke kwan ce

Durkusawa ya yi gabanta hannusa biyu ya sa ya dago kanta ya gora saman cinyarsa rumtse ido ya yi ya buɗe dan tunda ya ke bai taɓa jin a bin da ya ji yau ba.bakin sa ya s'aita dai _dai kunnenta ya fara mata karatu,

Bai wani dau lokaci sosai ya na karatu ba ya ji ta fara sauke ajiyar zuciya a samar fuskarsa wani irin ya ji a lokacin da ji saukar numfashin ta a saman kunnan sa

Kara runtse ido ya yi a karo na biyu wannan karon bai buÉ—e idon sa ba, a haka ya ci gaba da karatu,

Tun lokacin da doctor ya fara karatu Aliya ya zuba masa ido bata taɓa na dama akan rashin karatun da bata yi ba sai yau, yana y'in yanda doctor ya ke karatun ba karamin burgeta ya yi ba,har ta ji da ma ita ce,

Buɗe ido ta yi a hankali ta dora a kan fuskar sa kallon sa ta ke ba bu ko kiftawa yana da kyau ba laifi duk da kuwa baƙi ne amma komai nashi mai kyau kama daga hanci har fuska,idonta ne ya sauka akan bakinsa da yake karatu kallon bakin take ba bu ko kiftawa,

Kasan cewa idon sa a rufe shi ya sa bai san cewa tana kallon shi ba.

Yana nan yana kataru ya ji a jikin sa ana kallon sa a tunanin sa ya É—'auka Aliya ce take kallon sa amma daya buÉ—e ido ya ga a she Hanifa ce
Chapter 3 · 0% Book details