← Book details Masarautar Gobir Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 7 OF 19

Sashe 7

Masarautar Gobir Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Washegari
Masarauta ta tashi da wani firgici sakamakon wani mummunan ciwo da ya kama mai martaba,wanda aka kasa gane taƙamaimai na miye.
A rikice Yarima ya nufi palais bai ma tsaya bin ta Saffa ba wacce ke cikin mugun hali.
Sarki ya kalli Yarima sai dai babu bakin magana sakamakon wasu gunduma-gunduman ƙuraje da suka fito masa a dukan jikinsa har ma da cikin bakinsa.
Idon Yarima taf hawaye yace "Baba..."daga can bayansa Amma ta katse sa wajen cewa "kul kar ka kuskura ka sake kiransa da Baba,domin shi ɗin ba mahaifin ka ba ne.Wannan azzalumin da kake gani shi ya kashe mahaifin ka domin ya hau sarauta sai dai ka sani daga yau shikenan taka ta ƙare,kai da ganin kujerar mulki sai kuma a lahira dan yau ba sai gobe ba zan sa a mayar da can ɓangaren bayan masarauta shegen yaron ka yayi jinyar ka"Amma na faɗar haka ta zo ta janye Yarima daga gare sa ta na mai kuma cewa "taso yarona yau zan guntsura maka labarin masarautar nan mai cike da abun al'ajabi"

"Ba na so ki bari zuwa wani lokaci yanzu zan kai Sarki a duba sa,ko da ace zancen ki gaskiya ne to doli na yi biyayya ga Sarki dan ko ba komi shi ya raine ni tun ina ɗan yaro"Yarima ke faɗa kafin ya fita waje dan zaɓar masu maganin da aka kirawo dan duba Sarki.

Amma ta ƙyalƙyace da wata dariya tace "kai da tashi har abada a haka za ka ƙarasa rayuwar ka cikin datti ka na ɗoyi ka na wari,yadda ruwan ƙoramar kuffa suka ratsa gangar jikin Saffa haka ciwo zai rinƙa nuƙurƙusar ka ta ciki hhhh"Amma ta fara dariya sai kuma ta gumtse sakamakon ganin Sarki na murmushi cikin ƙarfin hali ya buɗa baki duk da ya san in yace yayi magana zai ji zafi kamar ransa zai fita amman ya gwammaci ya mayar mata da martani.

"Ba'a yabon ɗan kuturu sai ya girma da yatsun sa goma,tun kafin ki shigo wannan masarautar na san da zuwan ki da kuma ƙudirin ki.In ba ki manta ba kece mace ta wajen goma da Sarki Salis ya auro amman duk sun mutu sai ke ce kawai kika rayu,kin san dalili?"Sarki na kawowa nan yayi wata dariya wacce da ace akwai ƙaramin yaro kusa da sai ya ruga tsabar tsoro.
Shiru Amma ta yi ta na nazarin lafuzansa,tabbas ita ce ta goma cif kuma ita ɗaya ta yi rai sannan ta rayu.Jikinta ne yayi sanyi amman ta dake tace "ina jin ka miye dalilin?" Sarki ya girgiza kai maƙoshin sa na ciwo kamar ana zuba masa ruwan dalma ya daure yace "ki jira lokacin zai zo"daga nan Yarima ya shigo da wani mai bayar da magani,kallo guda malamin yayi masa yace "mugun sihiri ne aka yi masa,ba zai taɓa warwarewa ba har sai wanda ya yi sa ya bada makarin"
Prince Khalid wanda ke shigowa yace "gyara maganar kai mai bada magani,babu cutar da Allah ya sauko face sai yayi maganin ta .Kuma Allah SW ya ```«Wanunazulu minal ƙur'ani mahuwa shifaa, mun saukar da alƙur'ani ne domin ya zamo waraka a gare ku»```
In ba za ka iya ba ni ka bar ni zan yi jinyar mahaifina"
Amma wacce ita ce Ummul aba'isin cutar ta dubi Prince Khalid,wani banzar kallo ya watsa mata wanda mamaki da firgici suka bayyana ƙarara kan fuskar ta.
Mai magani ya ji haushi yayi tafiyar sa,Yarima ya kalli Prince Khalid cike da haushi yace "mi ka yi kenan?"
"Miye ruwan ka? Ina ce dai mahaifina ne ba na ka ba ko?ko kuwa ba ka ji abinda uwarka ma ciyar amana ta faɗa ma ba?"Yarima ya cakumi wuyan Prince Khalid sai kuma kogo ya juye da mujiya sakamakon bugasa da ƙasa da Prince Khalid yayi tare da hayewa bisa kan ruwan cikinsa ya na ta bugu.
Wani kullu mai ɗauke da furanni Amma ta ɗauka ta bugawa Prince Khalid a kai ya saki wata irin ƙara kafin ya faɗi a sume cikin jini .

Cikin ƙanƙanan lokaci aka kwashi tsohon sarki izuwa ɓangaren baya kamar yadda Amma ta zarta kafin a wuce da Prince Khalid asibitin masarauta.
Ɓangaren guda kuma tuni an fara bushe-bushen algaita da kiɗa ganguna,ba'a wani ɓata lokaci ba aka naɗa Yarima sarkin MASARAUTAR GOBIR.

Amma ta tura Jakadiya gun Saffa ta kimtsata da taimakon wasu kuyangi,sosai ta jigata shiyasa ma ba ta samu halartar taron naɗin sarautar ba.
Cike da ƙasaita irin ta sarakai ya shigo ɓangaren da Saffa take "Queen fito ki ga mijin ki cikin kayan sarauta,daga yau za mu koma sashen tsohon Sarki dan tuni an fara gyara shi"Sarki Bilal ke faɗa yayinda ya buɗe hannuwansa ya na yiwa gimbiyar tasa jawabi,cike da murna Saffa ta shiga jikinsa.A ƙasan ranta ba ta son shi amman ganin ta shiga daula yasa hankalinta ɗan kwanciya kuma ko ba komi za'a kirata da matar sarki,uwa uba za ta iya taka duk wanda ta so ciki kuwa har da Prince Khalid dan ta sha alwashi ko sau ɗaya ne sai sun haɗa shimfiɗa.

★★★DUNIYAR IFIRITU

Tuni Marwa ta saba da Maa,abu guda ke damun ta soyayyar Prince Khalid.Duk yadda ta so hakice sa daga ranta amman abu ya gagara,yanzu haka ma zaune ta ke ta na tunanin sa.
Ba ta san da zuwanta ba sai ji ta yi ta dafa kafaɗarta,ta ɗago ta kalleta gami da yin murmushin ƙarfin hali.Maa ta girgiza kai tace "ba zan hana ki tunanin Muradin Ruhin ki ba,sai dai ina son ki ɗaura ɗamara yaƙar maƙiyan ki tun kafin yaron cikin ki ya zo duniya"Marwa tace "yaron cikina?"Maa ta bata amsa da "ƙwarai kuwa,ki na da juna biyu kuma a yadda ya zo a littafin taswira namiji ne za ki haifa,wanda shine kuma zai zamanto ƙaddarar komawar ki masarautar"
Tashin hankali ya bayyana ƙarara kan fuskar Marwa ,murya a ɗan harɗe tace "Maa ta ya aka yi kika san ina da ciki kuma har da abinda zan haifa?sannan duk ba wannan ba ni gaskiya ba zan koma masarauta ba"
Murmushi kawai Maa tayi haɗi da tona ƙasa ta fiddo wani littafi wanda duk ya tsufa sosai,Marwa ta miƙa masa shi tace "ki ajiye sa gun ki,duk dare na Allah zan karanta maki page guda sannan nayi maki bayani ta yadda za ki gane"
Marwa ta karɓi littafin abun mamaki sai da zuciyarta ta motsa ga wani irin gumi da ya keto mata,Maa tace "iya wannan kawai ya isa ya tabbatar min da komawar ki masarauta domin ke ce fitilar da za ta haska ta"
Kan Marwa ya ƙulle ta tambayi Maa "fitilar masarauta kuma?"
"Ƙwaran gaske domin ke ce ke ɗauke da kabewar kan kabari ba Saffa ba"
Marwa dai sam ta kasa gane inda zancen Maa ya dosa wannan dalilin yasa ta shiga ƴar bukar su ta ajiye littafin kafin ta fito ta nufi inda ƙorama take.
Sawun tafiya ta fara ji a bayanta,da zarar ta waiga kuma sai ta ga babu kowa.Wannan ya sa tsoro wanzuwa a ranta,innuwar mutum ta gani ta na biye da ita kawai sai tayi tsaye cak ita ma innuwar ta tsaya.
"Amincin Allah ya tabbata ga ma'abociyar haƙuri"ta ji muryarsa daga bayanta,da sauri ta juyo saboda zaƙin muryar sa ya wuce misali sai dai tozali da kyakkyawar fuskarsa ya haifar mata da tsoro.
"Mutum ko aljan?"ta samu bakinta da furtawa,shi kuwa ya bata amsa da "aljan" Maa da ke bayan sa tace "Maheer kar ka firgita ta mana"yayi dariya yace "Maa tambayata ta yi ni kuma na bata amsa"
Maa tace "amsar ce ba ta dace ba dan kwanyarta ba za ta ɗauka ba"ya kuma yin murmushi yace "daga faɗin gaskiya?"
Maa ta murɗe kunnensa tace "kai dai ba ka jin magana"ya kama gun ya na mai fidda sautin "Washhh!" Marwa kuwa sai kallon sa take sosai ta shagala sai da muryar Maa ta maidota hayyacinta inda ta ke cewa "Ɗan Sarkin Aljanu ne amman shi ɗin ya kasance Musulmi ,shine malamin da zai koyar da yaron ki karatu daga zarar kin haihu"
Marwa ta murmusa ta na mai kallon Maheer,so take ta tantance shin da gaske aljanin ne ko kuwa?
Maa tace "ki gaishe sa"
"Assalamu alaikum"ta faɗa kamar wacce aka yi ma doli,Maheer ya amsa mata sallamar sannan ya ƙara da "da ace addinin Musulunci bai soke auren jinsi biyu ba da tabbas Yarima ya samu matar aure"ambatar sunan Yarima ya saka zuciyar Marwa motsawa daga tabon da ke cin ruhinta,Maa ce ta basa amsa da "da kam na tsaya maka har inda ƙarfina ya ƙare duk da dai littafin taswira ya gama tsara mata kudin ƙaddararta"
Maheer ya ɓata fuska yace "littafin tsafi har wani littafin ƙwarai ne da mutum zai yarda da shirmen sa?mu Addinin Musulunci ce mana yayi komi na Allah ne,daga gare shi mu ke kuma gare shi zamu koma sannan shi ya tsarawa kowa rayuwar da zai yi.Misali kamar gimbiya Marwa daman Allah ya ƙaddara za ta zo nan sai dai kawai ace sharrin tsafin ku ne sila"
Fuskar Maa ce ta yi baƙi ƙirin jin Maheer na sukar su amman babu yadda ta iya saboda sanin kanta ne Maheer bai taɓuwa gare su saboda ƙarfin imaninsa.
Chapter 7 · 0% Book details