← Book details Masarautar Gobir Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 19 OF 19

Sashe 19

Masarautar Gobir Part 1 Complete Hausa Novel · about 9 min read

Ita tun farkon zuwan su Naser gidanta sam ba ta so haka ba,sai dai babu yadda ta iya saboda su ne manyan abokan mijinta duk da ba ta san su ba kafin aurensu da Bilal amma a yanzu bai da wasu bayan su.
A duk lokacin da za su kawo musu ziyara haka za ta kwana cikin kasala da mugayen mafarkai,sai dai ba ta taɓa alaƙanta hakan da su ba abu guda kawai ta riƙe shi ne addu'a sannan ta na yin sallolinta kan lokaci wannan kuma na ɗaya daga cikin turbar da Bilal ya ɗora ta don shi Ustaz ne ya na da karatu sosai saɓanin Sailuba da ko izo ɗaya ba ta da.
Yanzu bayan fitar su Musty haka kawai ta ji ta na son yin tilawar karatun da ta iya,Bilal ya sanar da ita zai wuce makarantar da yake bada karatu wannan yasa ta shiga ɗakin Sarah don ta zo ta yi kallo.Sai da ta yi alwala sannan ta soma karatun fatiha,falaqi da nasi zuwa suratul Masad.Sam ba ta raina karatun da take da haka bayan ta gama ta shiga yin addu'o'i na neman tsari da kuma neman buɗi.

A can gidan Hinda kuwa hatta salloli ba su sa sun zubar ruwa a jikinsu ba, ƙememe suka bari ta wuce su.Sai faman saƙa da warwara suke,Sharifa da ta gaji da abun ta ce “ Mama ina ga kawai mu je gidan Kaka ta bamu magani tun da dama aikinta ne bayar da magani”

Hinda ta ce “ wa ya sani ma ko ita ce ta yi mana ture? Kin ga babu inda zan je in zuwa za ki yi ban hana ki ba sai kin dawo”

Sharifa ta saka kuka ta na yi “ shikenan in na mutu sai ki huta”
“ Tashi mu tafi tun da kin fara jawo mana mutuwa” cewar Hinda ta na mai zarar mayafi, Sharifa ma haka .

Gidan Kaka suka nufa sai suka tarar da shi a rufe suka shiga bubuga shi , Sharifa ta ce “ dubi langa-langar ƙyauren nan wai shi ne ya rufu ruf ko rawa bai yi”

Hinda ta ce “ banza wa ya faɗa miki normal ƙyaure ne? To aljanu ke rufe shi ” sai kuma suka ci gaba da bugawa.

Kaka wacce ke can ɗaki ta na shagali ita da ƙawayenta bokaye da suka kawo mata ziyara ta ce “ ku na ga zan je na ga ko waye ke bugun ƙyaurena”

Ɗaya daga cikin tsoffin ta ce “ kika sani ƴar tsintuwar ki ce ta dawo” sai duk suka kwashe da dariya,Kaka ta ce “ ai na bar zama da ita,ina dalili ta min kisan gilla tsakar dare” sai kuma ta je ta buɗe gidan.
Hinda ta ce “ gafara dai Kaka,ki daɗe ki yi ƙarko akwai wata bayan ke ne mai bayar da magani ? Kai babu guda ɗaya ce rak Hajiya Kaka mai abun ban mamaki,mun zo ne a bamu magani sakamakon wata cuta da ta shafe mu”

Kaka ta basu wuri suka wuce sannan ta ƙara jan ƙyauren ta rufe,ta yi musu iso suka zauna kan tabarma.Kayan aikinta ta fidddo ta ɗora fitila aci balbal sannan ta soma wasa da ƴaƴan wuri,tsawon lokaci ta na yi kafin ta ɗago ta dube su ta ce “ duk wanda ya ce muku zai iya karye asirin nan da aka yi muku kawai yaudarar ku ce zai yi ya ci kuɗin ku,sihiri ne wanda ba a cika samunsa ba a wannan duniyar amma ku jira na kira ƙawayena mu ji mi za su ce” Kaka ta kira su kuwa,tsofi ne biyu har sun fita tsufa abin da Kakar tace su ma shi suka faɗa kafin ɗaya ta ce “ Anaba wannan ai sihirin ruwa ne ,doli ya na da alaƙa da wanda yake aiki da Mamy Water ko kuma sam wanda ba nan duniyar yake ba ” ɗayar ta cabke zancen da “ ko kuma duk duniyoyin biyu mabanbanta ya na rayuwa cikinsu ba”

Furicin nan ya haskawa Kaka fitila har ta fahimci tabbas aikin Sarah ne,ta gyara zama ta ce “ Hinda mu ga kuɗin da ke gare ki zan yi miki aikin nan don yanzu na fahimci tushensa ”
Ba tare da wani tunani ba Hinda ta kwance kuɗin da ke ɗaure da ga haɓar zanenta ta bai wa Kaka,ƙawayenta suka shiga tambayarta “ wai mi za ki yi? Anaba kar ki jefa kan ki cikin masifa aljanun ruwa ƙarfi ne da su sun fi waɗanda muke aiki ƙarfin iko”

Kaka ta ce “ babu wani nan ku dai ku jira ni yanzu na dawo” ta faɗa tare da ɗaukar wata ƙwarya ta fice,ba ta zarce ko ina ba sai gaɓar ruwa.Ƙwarya ta aje gabanta sannan ta soma wasu suratai daga ƙarshe ta jefa kuɗi cikin ruwan,canɓallll sautin faɗawar kuɗin ta fito kamar ƙyaftawar ido kuwa ruwan suka fara tashi sama su na hargowa kafin wata murya ta soma yi wa Kaka magana “ faɗa mana mi kike da buƙata?”

“ Magani domin warkar da wasu”

“Ai kin san da cewa komai ya na da farashi ko?”
“Na sani a bani maganin” Kaka ta faɗa ba tare da ta tsaya tambayar mine ne farashin ba,ƴar ƙwaryar da ta ajiye ce ta soma cika da ruwa tsulululu har sai da ta cika tab kafin Kogin ya bar motsi.Cike da murna Anaba ta ɗauki ƙwaryar ta koma gida,da kanta ta yi wa su Hinda wanka abun mamaki kuwa sam ba su ji ƙaiƙayi ba.
“Mun gode sosai Kaka Anaba haƙiƙa ke shararriya ce kuma gwana wurin warkar da cuta” Hinda ta faɗa kafin ta ja hannun Sharifa su koma gida.Sai a lokacin suka samu suka yi sallah,da suka zo kwanciya bacci suka kasa saboda uban zafin da suka ji sai zufa suke .Wanka suka yi,Sharifa ta kunna masu fanka a haka suka samu suka yi bacci,sai dai abu kamar wasa sai gumi ya jiƙa shimfiɗar tasu.Da farko Hinda ce ta soma tashi ta sake yin wani wankan kafin sharifa ita ma ta yi,sam ba su kawo komai a kansu ba kawai sun ɗauka yanayin garin ne ya ɗau zafi.

SARAH

Da tunanin Mamana na samu bacci ya ɗauke ni,ko minti biyu ban yi ba tsinci kaina can ƙarƙashin ruwa ina wasa da su cike da nishaɗi.A inda nake ƴan mata ne kewaye da ni su na min taɓi kowacce da bindinta na kifi ga dogon gashi sannan fuskokinsu masu kyau ne farare tas saɓanin ni da ke baƙa ƙirin.Na tsaya da wasa da ruwan na ce “ ya aka yi dukkan ku farare ne amma ni kuma baƙa ?”

Wata murya ta namiji ce ta bani amsa “ saboda ke Mamarki kika ɗauko” da gudu na ga ƴan matan na tserewa su na cewa “ ga sarki nan ! Ga sarki nan!”
Na juyo muna kallon juna da wani kyakkyawan namiji zai kai a ƙalla shekara arba'in da biyar,kansa ɗauke da kambun sarauta na zinari haka ma daidai damatsansa an yi masu ado da wani ƙaton awarwaron zinari.Wuyansa kuwa sarƙar Munduwa ce irin tawa sai dai tasa ta fi tawa girma ,ya zo kusa da ni ya jawo ni ya na shafar gashina idonsa ne suka ɗau wani haske ya dinga juya su ya na umarta gashina ya ƙara tsayi sai gashi kuwa gashin nawa ya zama dogo har bisa gadon baya .Sosai na ji daɗi,cikin murna na ce “ wane ne kai?”
“Ni ne Babanki Sarah ” ya bani amsa tare da ɗora min wata gyanɗama a baki ya ce “ sha! Ruwan ƙarfin iko!” ban musa ba na soma sha,shi kuma ya na shafar gashina ya na mai ci gaba da cewa “ barkar da ranar zagayowar haihuwar ki” sai ya cire kambun sarautar kansa ya ɗora min .

“Sarah? Sarah keeee!” muryar anty Sailuba ta tashe ni daga bacci,a hankali na ware idona sai na ga ɗakin da duhu.
“Ƙwan lantarkin ɗakin ki ya ƙone sai an saka sabo ,tashi dai ki yi sallah lokaci yayi” sai kuma ta fice.

Zaune na yi kan shimfiɗa mafarkin da na yi ya na dawo min,ina nan zaune sai na ga ɗakin ya cika da wani mugun haske kuma .Ban yi wani dogon tunani ba na fahimci daga inda hasken ke fitowa,na kai hannu na laluba kaina .Wani irin taushi da santsi ne suka ziyarce ni,wato gashina ya zama dogo irin na turawa hatta Kambu sarautar da na gani a mafarki ga shi a hannuna.Juyasa na soma yi kafin na soma shafarsa,ƙaton jan dutsen da ke tsakiya ya fitar da wani farin haske hakan ya bayyana mini kyakkyawar baƙar fuskata.A karon farko da na fara ƙarewa kaina kallo,ina da doguwar fuska mai siririn hanci idona sun so su yi shige da na mage,gashin girata da na idona su na da yawa sosai yanzu kuma ga wani ƙarin adon wato gashin kaina ya koma mai yawa.Shafar shi na soma yi ina jin tsantsar farin ciki tare da tambayar kaina ‘ shin gaske mafarki ne na yi ko kuwa rayuwar zahiri ce na je can ɗin a gaske?’ banda amsa,kawai sai na je na ɓoye Kambu sarautar cikin kayana tuni kuma haskensa ya ɗauke yayin da kuma na lantarki ya dawo.

Gashina na harɗe wuri guda da abun ɗaurewar da ni kaina ban san inda na same shi ba,sai kuma na laulaye gashin yayi tudu kamar na sa a cuci maza sannan na ɗaura kallabi.
Fita na yi na je na yi fitsari tare da wanke jiki na dawo na kwanta,sai dai sam na kasa komawa bacci har rana ta fito wantsar na fita na yi shara na wanke kwanuka a ƙarshe kuma na yi wanka na zo na canza kaya .
Sai na tsurawa Kambun ido ina kallo ina murmushi tuna wai mahaifina ya bani shi,

“ Ke lafiyar ki?” na ji muryar anty Sailuba.Da sauri na rufe kayan na ce “ babu komai ina kwana anty?”
“Lafiya lau,ungo ga makullin shago ki je ki share shi ki goge komai sannan a cika manyan bokitan ruwa yadda ba mu yi aiki ba jiya ai na san yau aiki sai mun ture wa buzu naɗi wasu ma har sun fara kirana ”
Makullin na karɓa,har zan fita ta ce “zo ki karɓi kuɗin da za ki ci abincin kari,don mayun jiya duka suka cinye komai mtswww” ta ja tsuki.
Na dube ta da kyau na ce “kenan kin san Mayu ne su?”
Yadda ta tsure ni da ido yasa na yi saurin canza tambayar “ina nufin kenan Mayu ne?”
“Hum! Ungo dai ban iya surutun ki da kika iya ba” kuɗin na karɓa na fice,maimakon na je shagon a'a sai na wuce gidan anty Hinda don ina son ganin yadda suka kwana tun a hanya nake tuntsira dariya har na isa....

Littafin kuɗi ne Hajiya domin samunsa tun daga farkonsa har zuwa ƙarshensa ki yi payment ɗin 500 via 2670215530
ZULFAU YAHAYA Ecobank sai ki turo da shaidar biya ta WhatsApp +22795045822 Ni kuma sai na saka ki paid group inda nake posting.
Chapter 19 · 0% Book details