Sashe 14
Masarautar Gobir Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Anty Sailuba ta ɗauki masharcin da na shace mata kai ta shiga cire gashin da ya laƙe,ina ji ina gani ta jefa shi cikin gwangwani.
Su Farida suka dawo,taliya ce suka sayo mini sai hanjin ligidi na karɓe na shiga ci yayin da anty kuma ta aike su .
Haka muka yi ta samun customer har lokacin tafiya ta yayi gidan anty Hinda,ina zuwa sai na ga ta haɗe rai amma ban damu ba na shiga taya ta sayar da abincin yau ma dandanan muka sayar sai dai ko loma ɗaya ba ta bani ba.
Na yi rau-rau da ido na ce “ anty ina nawa”
“ Ni ai ba zan sake baki abinci ba,yau tun safe Kakar ki ita ta tashe ni daga bacci ta yi ta min masifa ta na zagina wai kar na sake baki abinci to wannan ma yasa na yanke shawarar sallamar ki” ta faɗa tare da ɗauko kuɗi ta miƙa mini.
Na ƙi karɓa ina bata haƙuri amma ta ƙi haƙura har gidanta na bita,muna shiga ƴarta budurwa mai sunan Sharifa ta taso cike da wulaƙanci ta na cewa “ uwar mi kika zo yi gidanmu? Dama shi talaka bai iya samun wuri ba,ɗazu don rashin mutumci kika turo mana wannan tsohuwar Kakar taki ta zo ta yi wa mutane hauka.Duk alherin da muke yi muku ba ku gani ba har da wani cewa an zuba miki guba a abinci”
Anty Hinda ta ce “ kin ga Sharifa zo ki ƙirga kuɗin nan mu ga ribar da muka samu” ta na hararena ta karɓi kuɗin da ke cikin wata roba ta koma gefe ta na ƙirgawa ta na masifa “ daga yau ni zan dinga taya uwata sayar da abinci sai ki tafi ba mu buƙata” da ta ga na ƙi gusawa ta juye kuɗin ƙasa tare da cika robar da ƙasari ta watsa min a fuska har sai na ji tsoro.Duk wannan bai ishe ta ba sai da ta wani ja ni ƙiiii ta cillo ni waje ,zuciyata ce ta soma tafasa yayin da duk illahin jikina nake jin ya ɗau zafi kamar garwashin wuta.Ni kaina ban san lokacin da na ɗauki hanyar Gulbi ba,kawai haka na ji a can ne kawai zan samu salama.Tun daga nesa da na fara hango ruwan sai nake jin kunnuwana na amsa kira, ina isa daidai gaɓarsu na yi tsaye ina kallon yadda suka soma yin zillo tuni munduwar wuyana ta fara motsi ta na ɗaukar wani haske.Ido biyu ba cikin bacci ba na soma jin tafin ƙafata na yi mini ƙaiƙayi,ko kafin ƙyaftawar ido na rikiɗe na zama Siren (sirène ) ina daga kwance gaɓar ruwa nake ƙarewa bindin nawa na kifi kallo sai motsi yake ya na fitar da haske.Kamar wata kifanya na yi tsalle na faɗa ruwan,ƙasa sosai nake nitsawa ina jin wani sanyi da daɗi na ratsa ni.
Idona buɗe suke taram haka kuma sheɗa ta daidai take babu alamun gargada irin in mutum ya shiga ruwa.Ina tsaka da yawo cikin ruwan na soma jin dariya,na juya na soma bin inda sautin ke fitowa har na iso kusan wani dutse.Wata budurwa da saurayi na gani su na wasa haɗi da hirar masoya,su ma iri na ne rabi mutum rabi kifi.Budurwar na gani na ta nufo ni ta na cewa “ waooo! Princess” ƙyafƙyaf kawai na yi da ido ina kallonta har ta iso gare ni ta na shafa goshina wanda sai a yanzu na farga akwai wani tambari a jikinsa na haske.
“ Ya aka yi kika zo wannan ƙasar? Ko wani aiki kika zo yi?” abun mamaki kasa magana na yi duk da kuwa na so buɗe baki,saurayin ne ya zo da sauri ya ja ta gefe ya na cewa “ Sarlah ya kike tsayuwa kusa da ita ko ba ki tambarin Masarautar Goma ne da ita ba?” haka suka tafi suka bar ni cike da mamaki.
Sama-sama na soma yi har na fito gaɓar ruwan ,so nake na koma gida.Sai bayan na fito ne bindin ya ɓace na dawo da ƙafafun mutane,na saki murmushi ina jin wani daɗi yayin da kuma zuciyata ta yarda ta lamunce mini tabbas ina da wata baiwa ba daidai nake da sauran mutane ba. Ina zuwa gida na ga takalmin mutane a ƙofar ɗakinmu,ban nemi izini ba na shiga.
Sai na tarar da wata mata a zaune yayin da Kaka kuma ke ta wasa da ɗiyan wuri ta na zayyano mata abubuwan da za su faru gobenta.Wato dibo Kaka take,macen ta yi godiya ta biya kuɗi irin sosai ɗin nan kafin ta fice.Na dubi Kaka wacce ke ta faman ƙirga kuɗi kamar ba ta gan ni ba,na yi gyaran murya na ce “Kaka...” ta yi saurin katse ni da “kin ga Sarah wuce ki bani wuri ban ƙaunar ganin ki,rainon ki bai yi mini rana ba sam.Ban ga amfanin zama da ke ba don haka ki kwashi inaki-inaki ki bar min gidana”
Wata irin dariya na soma wacce sama ban lura da ruwan da suka fara ɓulɓulowa daga ƙasa ba har sai da suka kawo daidai wuyana.Tsit na yi ina kallon Kaka wacce ke ta ƙoƙarin fita daga ɗakin amma ta kasa,“za ki mayar da ruwan nan ƙarƙashin ƙasa ko sai sun kashe ni ” ta faɗa a tsorace ta na riƙe bango hakan kuma sai ya ƙara bani wata dariyar amma na gimtse munduwar wuyana na lalubo na riƙe ina yi wa ruwa magana da idona,a sannu a hankali suka yi ƙasa har suka ƙwafe.
Da wani irin saurin Kaka ta cillo ni waje ta na mai cewa “ashe duk yadda nake tunani kin wuce nan,ke annoba ce ba zan iya zama da ke ba”
Zuwa wannan lokacin na fahimci Kaka ba da wasa take ba,hakan yasa hankalina ya tashi na soma roƙonta “Kaka in kin kore ni ina zan je? Ke ce komai nawa ke kika raine ni ban san kowa ba sai ke”
“Ban haɗa komai ba da ke wallahi tsintar ki na yi da tunanin za ki yi mini amfani a gaba ki gaje ni ashe musamman da na ga ki na ɗauke da *MAITAR IDO* ashe ban san bala'in naki ya wuce nan ba sai yau na ida ganewa Mamy Water ce ke ”
Idona na zubar da ƙwalla nake kallon Kaka,tuni kuma ƙwaƙwalwata ta soma hargitse wa.Ana kiran sallar magrib haka Kaka ta jefo ni waje ni da jakar kayana ta kama gidanta ta rufe,kan dakali na zauna ina ta wasiƙar jaki har aka yi sallar isha'i.Ganin dare na ta ƙara yi na miƙe tsaye na soma tafiya,direct gidan anty Sailuba na nufa don ita ɗaya ce yanzu ta rage min wacce nake tunanin za ta zame mini bango.Da sallama na shiga gidan,tun kafin na ƙarasa nake jiyo sautin muryar mijinta Bilal ya na cewa “wallahi Sailuba ko mi za ki yi sai na ƙara aure,kuma goben nan zan je na yi wa Hajiya bayani ta samo min mata cikin danginta tun da ni ko na nema ba za ki bari ba” kai na kutsa na shiga ɗakin,anty Sailuba ta juyo ta na kallona a zuciye “uban mi kika zo yi kuma yanzu cikin dare?” ban bata amsa ba sai mijinta da na ƙure cikin ido ina mai taɓa munduwa ta ni kaina ban san dalilin yin haka ba.
“My Lub Baby wane ni na yi miki kishiya don Allah ki kwantar da hankalin ki ina mugun son ki” Bilal ya faɗa ,ni kuma na saki murmushi ashe duk anty Sailuba ta ga komai.Hannuna ta ja muka fito waje kafin ta ce “ke mine ne kika yi wa mijina? Ko ke ma bokancin kike yi kamar Kaka” na girgiza kai na ce mata “a'a ina da MAITAR IDO ne mai sarrafa abin da duk nake so,kin ga gashin Leemat ma ni ce nan na mayar da shi yanzu kuma na juye tunanin mijin ki babu ke babu kishiya” anty Sailuba ta rungume ni ba tare da tunanin wannan ɗin fa abun gudu ne,ta ce “ina na za ki je?” bayani na yi mata kan cewa Kaka ta kore ni daga gidanta sai a lokacin kuma na ji hawaye ,ta goge mini su ta na cewa “sai ki zauna gidana” sai ta ja hannuna muka koma ciki.....
Ga waɗanda suke son fara payment ƙofa a buɗe take 500 via 2670215530
ZULFAU YAHAYA Ecobank sai ki turo da shaidar biya ta WhatsApp +22795045822
[09/09 à 10:39] MRS SADAUKI 👑M~SHURAIM🤍: *MAITAR IDO*
HoRrOR story☠️
Na
© Chamsiya Laouali Rabo
#MRS SADAUKI💫✍️
*FCWA ☀️*
9-10
Ko da muka koma ciki mijinta bai falo alamun ya na can ƙurya ,anty Sailuba ta kai ni wani ɗaki ɗan madaidaici babu komai cikinsa sai dangin abinci.Ta je ta ɗauko tabarma da kuma wani ƙaton bargo ta shimfiɗa min,“ ki kwanta a nan zuwa gobe da safe in Allah ya kai mu za mu sake yin magana” kai na jinjina mata ta fice ta bar ni nan.
Na haye shimfiɗar na kwanta ina tunanin furicin Kaka wai ba ta haɗa komai da ni ba tsintata ta yi.Na juya kwanci wani sashen zuciyata kuma na hasko min wulaƙanci da Sharifa ta yi min ƴar anty Hinda.Na lumshe ido ina mai kai hannu na riƙe munduwar wuyana,‘ ko ya ake yi mutum ya je wannan duniyar da Kaka ta kai ni ? ’ na tambayi kaina a zuci abun mamaki kuwa zuciyata ce ta soma yin nauyi kamar an ɗora dutse kafin in samo amsar tambayata .Cike da jin daɗi na yi bacci wannan daren,tun da asubah anty Sailuba ta shigo ɗakina “ tashi ki yi sallah” shine abin da ta faɗa ,duk da ban taɓa yin ta ba hakan bai hana ni miƙewa ba na fito.Ƙofar falo na ga a buɗe hakan yasa na fita,banɗaki na shiga har zan hau masai sai na tuna mafarkin da na yi a jiya an nuna mini yadda zan ɗauki fansa ta wajen su anty Hinda .Na fita na samo baƙar leda sannan na koma banɗaki,a cikinta na kasaye duk abin da ke cikina sannan na miƙe ina dariya ni ɗaya.Da ido na yi wa ledar umarni ta ƙulle kanta kafin kuma na aikata can gidan anty Hinda.