← Book details Masarautar Gobir Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 18 OF 19

Sashe 18

Masarautar Gobir Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Tsit falon ya ɗauka na wani lokaci kafin kuma wani irin gurnani ya ɗauki hankalina har na ji ina son leƙawa na ga su waye waɗannan baƙi.Labule na ɗan buɗe a hankali,su uku ne gami da mijin anty Sailuba su huɗu.Zaune suke su na cin abinci babu mai yin magana,amma ni kuma tambayata ita ce ‘to wannan sautin daga ina yake fitowa?’ ina shirin sauke labule daidai kuma lokacin ɗaya daga cikinsu ya ɗan tada kai tsabar tsoro har sai da na dafe zuciyata.Ido uku ne da shi,biyu irin na mutane ɗayan kuma can tsakiyar goshi ban ida shiga firgici ba sai da na ga wani abu na fitowa ta idon ya na cin abinci nan na fahimci shine ke fitar da gurnanin.
Da sauri na saki labulen ina mai tambayar kaina ,“ina kuma Bilal ya kwaso matsafan nan?” shiru na yi sai yanzu na gane wato shi yasa anty tace suka ƙi cin abincin sai ita da mijinta suka ci saboda su idonsu uku ne biyu na nan duniyar ɗayan kuma na ɓoyayyar duniya.

Tunani na soma yi mine ne dalinlinsu na abota da Bilal tabbas akwai wata a ƙasa,tunanin nawa ne ya tsaya cak jin ɗaya daga ciki ya na tambayar anty Sailuba “ni kam ku nawa ne cikin gidan nan? Ko kun samu ɗan hutu ne ?”
Ba ta kai ga basa amsa ba shi ma wani ya ce “ƙamshin Gombowa ”
“Tun shigowar mu na ji ƙazinin ɗan ƙabilar Gombo”

A karo na biyu kenan da na ji kalmar sunan Gombo ɗin nan,a hankali na ƙara buɗe labule ina leƙo cikin rashin sa'a hasken idona ya sauka a rigar ɗaya daga cikinsu,raɗam ya fito kamar fitilar nan da aka yi yayi mai hasko hoton Obama.Ɗayan ne mai face da wanda hasken idona ya sauka kan rigarsa ya juyo baya,muka haɗa ido da shi .........

Nan na kawo ƙarshen free page duk mai son ci gaba zai biya 500 via 2670215530
ZULFAU YAHAYA Ecobank sai ki turo shaidar biya ta WhatsApp +22795045822 ko kuma katin MTN ,ƴan Nijar kuma carte moov ko airtel ta 500f.

NB:Daga lokacin da book ɗin nan ya zama complete 800 ne.

29 jully 2024

MRS SADAUKI ce 🌚
[09/09 à 10:39] MRS SADAUKI 👑M~SHURAIM🤍: ```MRS SADAUKI💫✍️```

My book is only 500 via
2670215530
ZULFAU YAHAYA Ecobank,ko kuma katin MTN na 500₦ ƴan Nijar kuma carte airtel ko Moov ta 500f sai a turo da shaidar biya ta WhatsApp +22795045822,in kin san ba ki biya kuɗin karatu ba kar ki karanta min littafi domin mallakina ne .

*FCWA ☀️*

11-12

https://chat.whatsapp.com/FMimfpwTVDDBjZmDZw2Uhs

*Inda muke turo available products din mu don ki gani, ki zaɓi wanda kike so sannan ki siya ko ki tallata kema kisami naki*🥰

*Kayan mu order muke daga ƙasashen waje, foreign ne masu kyau da quality*

*Duk abinda mukayi posting available ne, daga kin siya za'a turo miki abinki ba ɓata lokacin jira*.

08032350261

😍😍😍DAMARKUCE LOKACINKUNE MUN RAGE FARASHI SOSAI DAN KUMA KUSAMU KOMAI DA KUKA SANI ZAKU SAMESU KWASHA KWASHA ARHA GARABASA 🤝🤝🤝KUMA DUK INDA KIKE KAYANMU ZASU SAMEKU CIKIN AMINCI DA YARDAR ALLAH

Da sauri na saki labulen ina jin zuciyata na dukan uku-uku,ina nan daga tsaye dafe da saitin zuciya na ƙara jiyo amon muryar su “ zarginmu ya zama gaskiya fa mine ne abun yi?”

“ Ta fito kawai mu gane wa junanmu tun da duk bisa hanya ɗaya muke”

“Hhhh ai kuwa dai ƙila ita ma da nata plan ɗin a kansu”

Shine abin da na ji su na faɗa ,amma na yi mamakin haka a gaban sun anty Sailubar suke faɗar haka ko dai sun tashi ne? Don gusar da zargina sai na ƙara kama labule don na sake leƙawa,ina buɗe wa na yi tozali da ƙaton ido manne a jin ƙofar ɗakin nawa ban san lokacin da na fasa wani matsanancin ihu ba da ya karaɗe duk illahin gidan.Ruwa ne suka soma ɓulɓulowa su na cika gidan ga baki ɗaya hatta cikin ɗakuna.

Tuni siffata ta canza zuwa kala biyu bindin kifi ya fito min,ruwan su suka ja ni izuwa falo.

“Waooo!” suka haɗa baki su na kallona sai nitso nake ina kaɗa bindi cikin ruwan,sai wannan lokacin kuma na ankare anty Sailuba da mijinta Bilal sai bacci suke yi kamar waɗanda ba su da rai.

“ Azo ka na gani abin da nake gani?”

“Yes Musty ina gani”

“Naser kai fa?”

“Ina gani ni ma ” duk suka tsoma bakinsu a nan ne na san sunan kowa daga cikinsu.

Musty ɗin alamun ya fi su ƙarfi da surutu ya dube ni da kyau ya ce “ muna so mu san plan ɗin ki akan wannan ahalin?”

Idona na buɗe ina kallonsa waɗanda har yanzu ba su bar mugun hasken nan ba,“ku fara sanar da ni naku plan ɗin tukuna” na faɗa tare da dukan ruwa da bindina suka bada wani bacaaal.

Suka ƙara kallon juna kafin shi Musty ɗin ya ce “ ki yi mana alƙawari za ki taimake mu”
Na juya baya ina mai cewa “ tun da ba za ku faɗa ba kun ga tafiyata”

“Tsaya mana ,Musty kawai mu sanar da ita zai fi.Muna zuwa nan ne don jawo hankalin Bilal ya shigo a tsagenmu amma mun gagara yin galaba kansa,ruhinsa na da mugun ƙarfi shi da matarsa”

Na juyo ina duban Naser ya faɗa wanda na fahimci kuma duk cikinsu ya fi sauƙi don ya na da tsoro.“ Ta ya aka yi duk ƙarfin ikon ku amma suka fi ƙarfin ku?” na jefo tambayar ina kallon Naser ,sai da ya ɗan yi shiru kafin ya ce “ kin san su na da yawan addini su na salloli kan lokaci ”

Na lumshe idona ko da ya zo nan da zancensa,ina jinjina wa anty Sailuba wacce ta yi riƙo da Addini duk matsatsin aikin shago bai hana ta yin sallah muddin lokacinta yayi na fahimci hakan tun lokacin baya da nake wuni wurinta kafin na soma yi wa anty Hinda aiki.

“Na san ke ma shine dalilin da ya hana ki cin galaba kansu duk da ba mu san ke mi yasa kike bibiyar rayuwarsu ba” Azo ya faɗa ya na matso wa kusa da ni.
Wani irin zafi ne na ji gangar jikinsa na fesar wa duk da kuwa ina cikin ruwa,na ce “ ta ya aka yi ka san ina bibiyarsu?”

Yayi murmushin gefen baki ya ce “ in ba haka ba mine ne zai fito da ke daga can cikin asalinki ki zo nan? Tun daga Gombo kike sannan a yadda kike Siren kika juri zama a wajen ruwa kawai don ƙudirin ki.Faɗa mana mine ne shi?”

Ban da lokacin tunani ,na kuma fahimci ko masu ganin abin da normal mutane ba su gane ba komai ne suke da sanaya a kai ba.Ba don haka ba tabbas da za su fahimci ban zo nan da niyyar cutar da su anty Sailuba ba,amma don kar su raina mini fiƙirata sai kawai na ce musu “ yanzu dai kawai mu zama ƙawaye daga baya duk za mu tattauna akan abin da ya shafi duniyarmu,tun ɗazu kun saka bayin Allahn nan bacci ya kamata ku tashe su haka”

Azo yayi wata dariya ya na mai cewa “ da alamu fa Siren tausayin su kike”
Na girgiza kai na ce “ ko ɗaya,kawai ban so su zargi wani abu ne”

“Kuma kin yi gaskiya komawar ki ɗakin ki”

“Kafin nan ta janye ruwan nan da ta cika mana ɗaki da su”

Murmushi na yi ina mai kai hannu ina taɓa Munduwar wuyana haɗi da kallon ruwan da ido ina basu umarnin su koma,a haka na shige ɗakina ni ma tuni ruwan kuma sun ƙwafe tsab .Na kwanta kan shimfiɗata ina kallon rufin ɗakin ina cewa “ karo na biyu kenan da na ji sunan Gombo,shin ina ne ? Wace ƙabila ce?” ban ida rufe bakina ba kafin wani girgije ya danno kai tamkar shine rufin ɗakin.Munduwar wuna ta soma zuƙo girgijen nan a hankali ya soma tarwatsewa na zamar haske mai kamar mai sai kuma ya shiga radadowa ina fasa ƙirjina ya na shiga “ Mamaaa!” na furta da ƙarfi saboda amon muryarta da ya cika mini kunnuwa ,yayin da kuma hoton siffarta wacce take flou ta bayyana gare ni ga wani Baby a hannunta kafin ta aje shi tsakiyar daji ta ce “ sunan ki Sarah !”

Hawaye suka zubo mini kan kumatuna,na samu abu na farko daga cikin tarihina wato jefar da ni mahaifiyata ta yi sai dai ban san dalilinta na yin haka ba.
Daga can falo ina jin su Musty na yi wa su anty Sailuba sallama,babu jimawa kuwa ta shigo ɗakin ta na mai kiran sunana “ Sarah taso ki yi kallo baƙin sun tafi” na girgiza mata kai saboda ba na cikin yanayi,“ fushi kika yi don na hana ki fitowa?”

Kai na girgiza tare da tashi na zo na rungume ta da ƙarfin tsiya ina mai cewa “ anty Sailuba ina son ganin Mahaifiyata,ina jin kewarta.Ina son jin soyayyar nan da ke tsakanin uwa da ƴa amma ni wurin Kaka Anaba na taso wacce babu alaƙar jini ko ɗaya a tsakanin mu”

Anty Sailuba ta riƙe ni ta na cewa “ haba Sarah kar ki sa na yi kuka mana,kin ga dama yanzu haka ina cikin wani yanayi.Sannan wa ya faɗa miki Kaka ba jininki ba ce,ƙila ta faɗi haka ne don ta hora ki ”
Na sake ta na ɗan ja baya ina mai girgiza kai na ce “ a'a gaskiya ta faɗa don yau ɗin nan aka nuna min lokacin da Mamana ta jefar da ni a cikin jeji”
Anty Sailuba ta jefo min wani kallo “ don Allah kar ki sa na fara jin tsoron ki,wa ya sanar da ke to?”
Shiru na yi don ni kaina ban san ya ko wane ne ba.
“ Kin ga sai da safe bari na je na yi karatu ” har ta kai bakin ƙofa na tsayar da ita ta hanyar kiran sunanta,ta juyo na ce mata “ ki ƙara dagewa da addu'a haka ma mijinki” ba ta ce komai ba ta fice.

Sailuba
Chapter 18 · 0% Book details