← Book details Masarautar Gobir Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 17 OF 19

Sashe 17

Masarautar Gobir Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Kaji muka saye manya guda uku anty Sailuba ta miƙa min su na riƙe,daga nan muka wuce wurin ƴan yaji.Mun yi tsaye ta na cinikin nawa tiyar yaji,yayin da ni kuma idona ya sauka kan yaji wanda ake kira tsidagu irin ƴan mitsimitsi ɗin nan.
“ In ɗauki guda?” na tambayi mai sayar da yajin yayi murmushi ya ce “ ɗauka mana”
Cike da masifa anty Sailuba ta ce “ mi za ki yi da tsidagu kuma?” na ce “ kawai ya burge ni ne sai na ɗauki ƙwaya gudan.Haka dai muka yi ta zaga kasuwa har muka zo wajen ƴan sayar da nama,yadda na ga mata sun yi dandazo wajen wani alhalin duk ga ma su nama nan yasa na ji ina son ganin shi ɗin kuma wace irin laya yake amfani da ita.Kamar dole haka na duƙa ina kutsawa har na shigo gaba,sai dai kafin na miƙe tsaye sai idona ya sauka kan wasu ƙafafuwan jaki a tsaye daram,a hankali na miƙe sai na ga ashe mai sayar da naman ne .Ido huɗu muka haɗa da shi da farko ya ji tsoro kafin ya soma yi min magana da ido ba wai a bakinsa ba ballantana ace mutane za su ji.
“ Mi kuma ya kawo macen Siren cikin mutane? Ko da yake ba abun mamaki ba in ka shigo kasuwa babu kalar jinsin da babu”
Ni ma ta idon na mayar masa “ wane ne kai? Ya aka yi ƙafafunka suke na jaki?”
“ Ki tambayi Anaba ita ai ta san ni ”
Anaba sunan Kaka ne,jin furicinsa yasa na kai dubana ga naman da yake sayarwa duk babu ɗaya na ƙwarai mushe ne yake sayarwa in rago ya mutu ko saniya haka zai je ya ɗauko su inda aka jefar ya gyara shi ya zo ya na sayarwa ko da kuwa ya fara lalacewa shi zai san yadda yayi ya maida shi mai kyau a idon mutane irin shine kuma sai ka ga ka ci ka faɗi rashin lafiya.
Ban ankara ba ashe har mutanen da ke zagaye da shi duk ya sallame su sai da na ji muryar anty Sailuba na cewa “ Sarah ke? Tun ɗazu fa nake yawon neman ki” sai kuma ta harari mai sayar da naman kafin ta ja hannuna mu wuce.Sai da muka yi nisa na tambaye ta “ amma anty mi yasa ba ki sayi namansa ba ? Na ga ya fi kowa arha”
Ta ja baki ta ce “ arhar ce ke kai mutane ga hallaka,ni ma na taɓa saya lokacin da abokan Bilal za su zo amma abun mamaki suka ƙi ci wai naman nan da na saka ya lalace ko ban jin warinsa.A ƙarshe dai barina suka yi da shi sai ni da Bilal muka ci daren ranar kuwa muka dinga ƴar rige-rigen shiga banɗaki” na ƙyalƙyace da dariya kafin kuma na ce “ to anty mi yasa kuka ci alhalin an faɗa muku ya lalace?”
Shiru ta yi ba ta bani amsa ba, wannan kuma yasa na lalubo amsar da kaina ‘ saboda ita da mijinta normal mutum ne!’ sai kuma zuciyata ta bada darammm ‘ to in haka ne su abokan Bilal waye ya sanar da su? Sai in kuwa su ma matsafan ne!’ duk a zuci na yi maganar har muka kai gida babu wanda ya ce komai.

Mijin anty Sailuba ya karɓi kajin ya fita waje wani ya kama masa ya yanke,ni kuwa ƙatuwar tukunya na ɗora ta ruwan zafi .Sai da suka tafasa sannan na soma fige su yayin da anty Sailuba kuma ta ɗora girkin rana ,muna aiki muna hira har muka gama.
Sai bayan mun ci abinci ne na kama mata ta tsaga cikin ta fiddo hanji ,su ma duk muka gyara su sannan ta wanke ta ɗora kan tukunya.Tafarnuwa ta miƙo min ita ma na gyara ,aikin da nake ganin mai sauƙi ne sannu-sannu sai ga shi ya ɗauki lokaci don bayan ta dafa kajin sai da ta soya su sannan ta ɗora miya bayan ta gama kuma ta tsumbula su ciki.

#GIDAN ANTY HINDA

Cike da iya yi Sharifa ta cika bokiti ta je ta yi wanka,ragowar ruwan kuma waɗanda duk sun yi farin sabulu ta kawo wa anty Hinda su ta juye cikin miya sai murna suke.
Sharifa ta ce “Mama in muka ɗora da yin haka ai hajjin bana da mu za a yi”
Ita ma Hindar ta ƙyalƙyace da dariya ta ce “ai kuwa dai musamman yanzu da na rabu da jikar bokanya ”
“Dama haushi take bani,yadda kullum cikin datti ko wanka ba ta yi”
Hinda ta ce “miƙo min ƙatuwar muciya na motso miyar nan ” muciyar ta miƙo bayan ta motsa miyar ta sa murfi ta rufe kenan ai kuwa sai ganin leda suka kuwa daga sama ta faɗo kan tukunyar miyar kwacaaaa.

Duk suka yi baya a tsorace su na zaro ido ganin kashi duk ya ɓata murfin tukunyar .
Cike da ƙyanƙyami Hinda ta ɗauke murfin ta je ta wanke shi,Sharifa kuwa cewa ta yi “Allah ma dai yayi sa'a ba a ciki ya faɗa ba”
“Ɗauko muzubi ku juye min miyata Allah kaɗai ya san abin da za a jefo min kuma nan gaba” cewar Hinda , Sharifa ta ɗauko ta dinga kwashe miyar dama ta dafu.

Ita ma Hinda wankan ta yi kafin su ɗora abincin kan baro,almajiri ya tura masu shi inda suke sayarwa .Sharifa an ci wuyar kwalliya,mutane ne suka fara zuwa su na saye kamar kullum sai da Hinda ta buɗe baki ta na zage-zage “ ƴan hassada ƴan baƙin ciki,to sai ku je ku sake biyan wasu kuɗin wannan aikin bai yi ba.Ni za a yi wa turen aljanu daga ganin kasuwata ta bunƙasa”
Customer ɗinta kuwa har da masu shigar mata,kafin kuma wurin yayi tsit babu wanda ya ƙara saya ga abinci jibge har bayan sallar Asar sai ƴar kallon-kallon suke ita da Sharifa.
“ Na fa ji tsoro kar aje dai ɗin sun ƙara tafiya sun kai wasu kuɗin wurin Malam,dubi shiru babu masu saya”
Sharifa ta turo baki ta ce “ ai ke ce da masifar tsiya tun da kin ga abun bai yi aiki ba ai sai ki yi shiru da bakin ki”
“ Ƙirga kuɗin mu ga nawa aka samu” cewar Hinda . Sharifa ta ɗauki robar kuɗi,yaji ta gani tsidagu babu wani tunani ta ɗauke shi ta jefar kuɗin ta ƙirga ta na turo baki gaba saboda ko icce ba za su saya ba.Ta miƙa wa Hinda “ tsidagun mine ne kuma za ki aje min cikin kuɗi?” Hinda ta tambaya ta na mai ɗauka ita ma ta jefar a ƙasa.
Sharifa ta ce “ na fa jefar da shi”
“Ƙafafuwa gare shi ballantana ya sake tsalle ya shiga?”
“Allah Mama na cire”
“Kin ga tashi mu je gida kin ga duk wasu masu sayar da abinci sun sayar sai mu”
“To wannan ɗin ya za mu yi da shi?”
“Ko almajirai sai na rabawa ”
Abincin suka mayar a baro suna gaba almajiri na bin su a baya har suka isa gida, Sharifa ta cika bokiti ta je ta yi wanka tun a cikin banɗaki ta ƙurma uban ihu ta na kiran Hinda .
“ Ke lafiyar ki? Ko ƙadangaren ne yau ma ya sake faɗo miki?” Hinda ta tambaya, Sharifa ba ta amsa ba sai fitowa ta yi da ɗaurin ƙirji ta na soshe-soshe.

“ Mama sosa mini ƙaiƙayi duk jikina ƙaiƙayi yake na shiga uku na lalace” haka take faman faɗa ,da farko Hinda ta ɗauka wasa ce sai da ta ga Sharifa na kuka har da majina sannan ta soma tayata, Sharifa ba ta samu sauƙin abun ba sai da jikinta ya bushe babu damshin ruwa.Tsabar wahala har sai ta rame,ta koma gefe ta na jan numfashi.

Hinda kuwa alwala ta yi don yin sallah nan ita ma ƙaiƙayi yayi mata wuf duk inda ke da damshin ruwa.Soshe-soshen ta yi ita ma har sai alwalar ta bushe,suka kalli juna ita da Sharifa “ ina jin tsoro Sharifa kar ace tsidagun da muka ɗauka ne”

“Shi ne mana Mama,kuma abin da na fahimta sai da ruwa suka taɓa mu ne muka ji ƙaiƙayin” Sharifa ta faɗa ,Hinda kuwa don gaskata maganar sai ta watsa ruwa a ƙafarta ai kuwa ƙaiƙayin ya sake dawowa sabo wannan karon Sharifa har sai da ta dara.

# GIDAN BILAL

Bayan sallar magrib anty Sailuba ta gama komai,an gyara ɗaki sai ƙamshi yake yayin da kuma aka jera kwanonin abinci kan table ɗinta mai kujeru huɗu.Sai da ta yi kwalliya sosai ta saka kaya masu kyau,abincina ta zuba mini kafin ta ce “ ki zauna ɗakin ki kar ki fito har sai baƙin nan sun tafi ”
Na gyaɗa kai na ce “ to anty ” fita ta yi ni kuma na zauna na soma cin abincina,sai murmushi nake yadda na ji idona na wannan zuuuu ɗin na tabbata su anty Hinda ana can cikin uƙuba.Sosai nake jin daɗin mugunta a fili na ce “ ku da yin wanka kuma sai ta Allah,kuma sai kun dawo irina kun zama ƙazamai kun yi baƙi ƙirin” sai kuma na yi shiru jin muryoyi na tashi alamun baƙin ne suka zo.
Ina jin su na zolayar anty Sailuba “ irin wannan kwalliyar matarmu ai sai ki sa mu kasa fita”
“Ina ji fa saboda matarmu ba ta son tsufa shi yasa ta ƙi barin ta haihu”
“ Ai kuwa dai in haka ne za mu kawo wata matar”

“ Allah ina son haihuwa sosai zuwa dai ne ba ta yi ba” sai yanzu kawai anty Sailuba ta yi magana.
“ Ba ki dai je neman ta ba” ɗaya daga cikinsu ya faɗa.
Bilal mijin anty Sailuba ya ce “ yanzu dai mu fara cin abinci tukuna”
Chapter 17 · 0% Book details