Sashe 2
Masarautar Gobir Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Gabansa ya sha kafin ya haɗe girar ƙasa da ta bisa yace "haba Yarima ba girman ka ba ne,ta yaya ka na shugaban gobe amman ace za ka yanke ɗanyen hukunci irin wannan?sannan sabida Allah miye laifin Marwa da za ka hukuntata ta wannan sigar?"
Kallon tsaf Yarima ya yi masa nan ya hango tsantsar son da Prince Khalid ke yiwa Marwa,cike da isa yace "wace amsa kake son na baka?ta farkon ko ta biyun?"
"Ta biyun"Prince Khalid ya bashi amsa cikin dakewa,kallon masheƙan aya ya yi masa kafin yace "ko za ka hukunta ni ne a kan mace?"kai ya girgiza yace "banda wannan ikon domin kuwa da ina da shi da ko kallonta ba zan bari ka yi ba balle har ka hukunta ta"cike da mamakin lafazinsa Yarima ya matso kusa da shi haɗi da ɗora hannun kan kafaɗarsa yace "kai haba?to ina tabbatar maka ba wai iya kallo ba har taɓata sai na yi in ya so ka haɗiye zuciya ka mutu"ya na gama faɗa ya ture Prince Khalid ya wuce ya na jin zuciyarsa na yi masa ƙuna.
Direct sashen da aka kai Marwa ya nufa,umarta masu gadin wurin ya yi da su fiddota haɗi da canza mata waje.
Cikin izzar mulki ya shigo ya na ƙare mata kallo,fara ce kyakkyawa son kowa ta na da masifar kyau mai ɗaukar hankali.
A zuci Yarima yace ‘ƙila saboda kyawunta ya ke son ta' a zahiri kuma takawa yayi kusa da ita yasa hannu zai gyara mata gashin da ya rufe rabin fuskarta,da sauri ta buge masa hannu ta na mai ja da baya ta na hararsa.
Yarima ya waro ido waje yace "iyeee!Ni kike harara da wannan ƙwala-ƙwalan idon kamar kwalshi?"kafin ta samu damar yin magana ya shaƙota tuni ta fara kakarin wahala,da sauri Yarima ya sake ta jin wani azababen zafi a kwanyarsa.
Prince Khalid ya jawo Marwa ya mannata a jikinsa murya a matuƙar ɓace yace "zan iya jure dukkanin launukan azabar da za ka min amman kar ka kuskura ka taɓa wannan domin ita ɗin rayuwata ce zan iya yin komi a kanta"ya na gama faɗar haka ya ja Marwa suka fito.
Sai da suka zo daidai sashen su sannan ya saki hannunta yace "ki shiga ki yi wanka zan kawo maki abinci sai na kai ki gun Amma"ido Marwa ta zuba masa ta na jin wani irin sonsa ya shigeta ba ta yi aune ba,ba ta san lokacin da hawaye suka shiga zubo mata ba.
Bayan hannunsa ya saka ya fara goge mata hawayen haɗi da hura mata iskar bakinsa,sai ta lumshe ido "ina son ki"muryarsa ta daki dodon kunnenta kafin ta yi magana suka ji ƙarar rufe ƙofa "gam"
Da sauri Marwa ta ruga ciki dan kuwa ta ga Saffa lokacin da take tsaye, a bisa tabarma ta tarar da ita ta na goge ƙwalla.
Marwa ta dafata tace "amadadin farin ciki mi zai kai ki zubda ƙwalla?koko ba ki ji daɗin gani na ba?" Saffa ta waske tare da aro jarumta tace "tsabar farin ciki ne yasa ni kuka" "to amman kamar fuskar ki ba ta nuna alamun farin ciki ba"cewar Marwa ta na ƙara kallon Saffa dan tantance gaskiyar lamarin.
Saffa ta haɗiye mugun kishin da take ji game da ƴar uwarta ta miƙe tsaye haɗi da cewa "eh yanayin da na ganku ke da Prince ne ya kawar min da farin cikin,sam hakan da kuka yi bai dace ba kuma ba zan ɓoye maki ba na ji haushi sosai"
Marwa ta sauke ajiyar zuciya tace "yi haƙuri ƴar uwata ni ma ban san ya haka ta faru ba amman in shaa Allah zan kiyaye" jikin Saffa duk sai yayi sanyi hakan yasa ta kwantar da murya tace "ba fa da wata niyya na faɗa ba,kawai dai ina son ki tuna matsayin ki ke baiwa ce shi kuma ɗan sarki ne"
Marwa ta saki murmurshi tace "kuma fah a hakan wai yake sona" duk da Saffa ta ji ta amman sai ta share ta ma shiga aikin gyaran ɗakin su ganin haka yasa Marwa shiga toilet bayan ta ɗauki kayan da za ta sa.
Gabanta ne ya faɗi jin muryarsa daga bisa,ta kafesa da ido ta na jin kamar ta je ta rungume sa tsabar ƙauna.
Prince Khalid ya kawar da kai jin Saffa ta ƙi amsa masa tambayar da yayi sai ma ƙure sa da ido da ta yi,ajiyar zuciya ta sauke tace "My prince !"shaye da mamaki Prince Khalid ya juyo ya na kallonta.
Marwa ta fito daga toilet sanye da wasu kaya daban,sunne kai ta yi ganin Prince Khalid a tsaye hannunsa ɗauke da kwano ga kuma Saffa ta tsare sa da kallo.
Zuciyar Marwa banda dukan uku-uku babu abinda take,a zuciya kuwa addu'a take Allah sa ba wata baƙar magana Saffa ta faɗa masa ba.
"Princesse ga abinci nan na kawo maki,ki tabbatar kin ƙoshi Amma na can na jiran zuwan ki"cewar Prince Khalid ya na sakin murmushi mai sauti haɗi da ƙarasawa inda take.
Jin hucinsa kusa da ita yasa tayi saurin ɗagowa kafin ta waiga da sauri ta kalli Saffa,uwar hararar da ta jefo mata yasa tayi saurin sunne kai idonta suna masu cika da hawaye.
"Ɗas !"hawayenta suka ɗiga a babban farcen ƙafarsa,kamar ɗigar dalma haka ya ji su ya rumtse ido da ƙarfi yayinda zuciyar
sa ta shiga girgiza jin shashekar kukan ta.
Bai san ya aka yi ba ko kuma abin da ya ja ra'ayinsa da yin haka,kawai samun kansa ya yi da kama hannunta suka fice suka bar Saffa cikin ƙunci.
Part ɗin Amma suka shigo,sanyin AC da na turaren wuta suka bugar mata hanci a doli ta ji wata irin nutsuwa ta saukar mata.
Amma wacce ke zaune ta na jan casbin da ya zame mata jiki,ta miƙe murmurshi kan fuskarta.Kafaɗun Marwa ta dafa lokaci guda suka ji wani girrr kamar lantarki amman hakan bai sa Amma janye hannuwanta daga gare ta ba.
Marwa ta ɗago kai ta kalli Amma,sai kawai tayi luuu za ta faɗi da sauri Prince Khalid ya tareta ta faɗa kan ƙirjinsa....
[06/09 à 08:18] MRS SADAUKI 👑M~SHURAIM🤍: *MASARAUTAR GOBIR*
LoVe and HoRoR StOrY
*Mallakar:* Chamsiya Laouali Rabo
(MRS SADAUKI💫✍️)
*Lambar waya:* +22795045822
*FIRST CLASS WRITER ASSOCIATIONS☀️*
Home Of Qualities And Trusted Writer's Of The Nation.
*Sadaukar wa:* Ga duk Gobirawan duniya.
_____________________
3-4
Wata irin zufa ce ke tsatsafowa daga goshin Marwa,a zahiri za ka ɗauka barci take amman a baɗini farke take mai haɗi da fitar hayyaci dan ba komi take fahimta ba.
Prince Khalid ya goge mata zufa a karo na ba adadi,kafin ya dubi mahaifiyar ta sa yace "Amma kin ga fah kamar idonta sun juye babu baƙi sai fari" cikin son kwantar masa da hankali Amma tace "barci ne take,dayawan mutane za ka same su a ido buɗe kamar ita dai a yanzu"
Prince Khalid ya sauke gwabron numfashi ya na jin mamakin faɗuwar Marwa har yanzu bai fita daga zuciyarsa ba.
```Gefen fuskarta ya shafa ya na wangale mata bakinsa mai ɗauke da haure ƙwaya ɗaya tal,halshensa ya ziro mai kama da maciji ya saka sa kunnenta ya na zuba mata yawunsa,ido ta rumtse jin wata irin azaba na ɗigar mata a kunne ya na shigewa cikin kwanyar ta.Ihu ta fara yi amman alamu sun nuna sam babu mai jin ta dan kuwa Prince Khalid da ke tsaye kanta bai nuna alamar ya fahimci halin da ta ke ba balle kuma wasu jama'a da ke waje.Tsawon lokaci kafin ya zare halshensa daga cikin kunnenta wanda kuma ya yi daidai da ɓacewar hallitar,atishawa ta yi kafin ta miƙe zaune.```
"Kin tashi?"ita ce tambayar da Prince Khalid ya yi mata,kai kawai ta gyaɗa ta na jin wuyanta ya ƙage ga wani irin sarawa da ɗaya-wajen kanta ke yi mata.
Amma ta yi murmurshi tace "Barka da zuwa Princesse" da sauri Marwa ta dafe kai jin muryar ta ruɓayan gida biyu inda ta ji wata tace ```"ki fita daga harakar Prince Khalid"``` kai ta ɗago ta dubi Amma wacce a zahiri murmurshi ne kan fuskarta amman a wajen Marwa wata fuska ta ke gani kamar dodanniya.
Da sauri ta sunne kai zuciyarta na halbawa,Prince Khalid ne yace "Amma ina ga surukar nan ta ki har yanzu ba ta warware daga sumen da ta yi ba"
'Suma?'Marwa ta maimaita kalmar cikin ranta,cinkayo muryar Amma tayi ta na cewa "ƙila turaren nan da na saka ne ya juya mata kai,ka san kwanaki ma haka ya sumar da jakadiya" Prince Khalid ya kai dubansa ga Marwa wacce ta sunne kai sannan yace "ya kamata ki bar kunna sa kar ya zo ya hana surukar shigowa nan sashen"
Da sauri Amma tace "wane shigowa kuma?ai ta shigo kenan daga yau nan sashen za ta ci gaba da zama"cike da firgici Marwa ta ɗago ta kalli Amma,wata uwar harara ta aika mata babu shiri ta mayar da kanta yadda yake wato ƙasa.
Ɓangaren Yarima kuwa ba ƙaramin jin zafin bugun da Prince Khalid ya yi masa,dauriya ya aro ya fice.
Direct sashensa ya nufa,zarya ya fara yi ya na tunanin mafita dan sam bai so Sarki ya san da maganar.
Wani murmurshin mugunta yayi bayan ya hango hanyar ɓullewa ta har abada wacce zai yanke farin cikin Prince Khalid ga baki ɗaya.
Toilet ya shiga yayi wanka,kayan shan iska ya saka bayan ya fito kafin ya ɗauki waya ya kira wata lamba "a kawo min ita"kawai ya faɗa bayan an ɗaga kiran.
Babu jimawa jakadiya ta shigo yayin da a bayanta matar mutumen nan ce wanda Yarima ya yi masu Shari'a.
"Ranka shi daɗe ga ta nan na kawo,an yi komi kamar yadda ka buƙata fatan komi yayi yadda kake so?"Jakadiya ta tambaya ta na wani yin ƙasa da kai kamar tantabarar da hauka ya kama.