← Book details Masarautar Gobir Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 16 OF 19

Sashe 16

Masarautar Gobir Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

“ Mama sosa mini ƙaiƙayi duk jikina ƙaiƙayi yake na shiga uku na lalace” haka take faman faɗa ,da farko Hinda ta ɗauka wasa ce sai da ta ga Sharifa na kuka har da majina sannan ta soma tayata, Sharifa ba ta samu sauƙin abun ba sai da jikinta ya bushe babu damshin ruwa.Tsabar wahala har sai ta rame,ta koma gefe ta na jan numfashi.

Hinda kuwa alwala ta yi don yin sallah nan ita ma ƙaiƙayi yayi mata wuf duk inda ke da damshin ruwa.Soshe-soshen ta yi ita ma har sai alwalar ta bushe,suka kalli juna ita da Sharifa “ ina jin tsoro Sharifa kar ace tsidagun da muka ɗauka ne”

“Shi ne mana Mama,kuma abin da na fahimta sai da ruwa suka taɓa mu ne muka ji ƙaiƙayin” Sharifa ta faɗa ,Hinda kuwa don gaskata maganar sai ta watsa ruwa a ƙafarta ai kuwa ƙaiƙayin ya sake dawowa sabo wannan karon Sharifa har sai da ta dara.

# GIDAN BILAL

Bayan sallar magrib anty Sailuba ta gama komai,an gyara ɗaki sai ƙamshi yake yayin da kuma aka jera kwanonin abinci kan table ɗinta mai kujeru huɗu.Sai da ta yi kwalliya sosai ta saka kaya masu kyau,abincina ta zuba mini kafin ta ce “ ki zauna ɗakin ki kar ki fito har sai baƙin nan sun tafi ”
Na gyaɗa kai na ce “ to anty ” fita ta yi ni kuma na zauna na soma cin abincina,sai murmushi nake yadda na ji idona na wannan zuuuu ɗin na tabbata su anty Hinda ana can cikin uƙuba.Sosai nake jin daɗin mugunta a fili na ce “ ku da yin wanka kuma sai ta Allah,kuma sai kun dawo irina kun zama ƙazamai kun yi baƙi ƙirin” sai kuma na yi shiru jin muryoyi na tashi alamun baƙin ne suka zo.
Ina jin su na zolayar anty Sailuba “ irin wannan kwalliyar matarmu ai sai ki sa mu kasa fita”
“Ina ji fa saboda matarmu ba ta son tsufa shi yasa ta ƙi barin ta haihu”
“ Ai kuwa dai in haka ne za mu kawo wata matar”

“ Allah ina son haihuwa sosai zuwa dai ne ba ta yi ba” sai yanzu kawai anty Sailuba ta yi magana.
“ Ba ki dai je neman ta ba” ɗaya daga cikinsu ya faɗa.
Bilal mijin anty Sailuba ya ce “ yanzu dai mu fara cin abinci tukuna”

Tsit falon ya ɗauka na wani lokaci kafin kuma wani irin gurnani ya ɗauki hankalina har na ji ina son leƙawa na ga su waye waɗannan baƙi.Labule na ɗan buɗe a hankali,su uku ne gami da mijin anty Sailuba su huɗu.Zaune suke su na cin abinci babu mai yin magana,amma ni kuma tambayata ita ce ‘to wannan sautin daga ina yake fitowa?’ ina shirin sauke labule daidai kuma lokacin ɗaya daga cikinsu ya ɗan tada kai tsabar tsoro har sai da na dafe zuciyata.Ido uku ne da shi,biyu irin na mutane ɗayan kuma can tsakiyar goshi ban ida shiga firgici ba sai da na ga wani abu na fitowa ta idon ya na cin abinci nan na fahimci shine ke fitar da gurnanin.
Da sauri na saki labulen ina mai tambayar kaina ,“ina kuma Bilal ya kwaso matsafan nan?” shiru na yi sai yanzu na gane wato shi yasa anty tace suka ƙi cin abincin sai ita da mijinta suka ci saboda su idonsu uku ne biyu na nan duniyar ɗayan kuma na ɓoyayyar duniya.

Tunani na soma yi mine ne dalinlinsu na abota da Bilal tabbas akwai wata a ƙasa,tunanin nawa ne ya tsaya cak jin ɗaya daga ciki ya na tambayar anty Sailuba “ni kam ku nawa ne cikin gidan nan? Ko kun samu ɗan hutu ne ?”
Ba ta kai ga basa amsa ba shi ma wani ya ce “ƙamshin Gombowa ”
“Tun shigowar mu na ji ƙazinin ɗan ƙabilar Gombo”

A karo na biyu kenan da na ji kalmar sunan Gombo ɗin nan,a hankali na ƙara buɗe labule ina leƙo cikin rashin sa'a hasken idona ya sauka a rigar ɗaya daga cikinsu,raɗam ya fito kamar fitilar nan da aka yi yayi mai hasko hoton Obama.Ɗayan ne mai face da wanda hasken idonsa ya sauka kan rigarsa ya juyo baya,muka haɗa ido da shi .........

Nan na kawo ƙarshen free page duk mai son ci gaba zai biya 500 via 2670215530
ZULFAU YAHAYA Ecobank sai ki turo shaidar biya ta WhatsApp +22795045822 ko kuma katin MTN ,ƴan Nijar kuma carte moov ko airtel ta 500f.

NB:Daga lokacin da book ɗin nan ya zama complete 800 ne.

29 jully 2024

MRS SADAUKI ce 🌚
[09/09 à 10:39] MRS SADAUKI 👑M~SHURAIM🤍: *MAITAR IDO*

HoRrOR story☠️

Na
© Chamsiya Laouali Rabo
#MRS SADAUKI💫✍️

*FCWA ☀️*

9-10

Ko da muka koma ciki mijinta bai falo alamun ya na can ƙurya ,anty Sailuba ta kai ni wani ɗaki ɗan madaidaici babu komai cikinsa sai dangin abinci.Ta je ta ɗauko tabarma da kuma wani ƙaton bargo ta shimfiɗa min,“ ki kwanta a nan zuwa gobe da safe in Allah ya kai mu za mu sake yin magana” kai na jinjina mata ta fice ta bar ni nan.

Na haye shimfiɗar na kwanta ina tunanin furicin Kaka wai ba ta haɗa komai da ni ba tsintata ta yi.Na juya kwanci wani sashen zuciyata kuma na hasko min wulaƙanci da Sharifa ta yi min ƴar anty Hinda.Na lumshe ido ina mai kai hannu na riƙe munduwar wuyana,‘ ko ya ake yi mutum ya je wannan duniyar da Kaka ta kai ni ? ’ na tambayi kaina a zuci abun mamaki kuwa zuciyata ce ta soma yin nauyi kamar an ɗora dutse kafin in samo amsar tambayata .Cike da jin daɗi na yi bacci wannan daren,tun da asubah anty Sailuba ta shigo ɗakina “ tashi ki yi sallah” shine abin da ta faɗa ,duk da ban taɓa yin ta ba hakan bai hana ni miƙewa ba na fito.Ƙofar falo na ga a buɗe hakan yasa na fita,banɗaki na shiga har zan hau masai sai na tuna mafarkin da na yi a jiya an nuna mini yadda zan ɗauki fansa ta wajen su anty Hinda .Na fita na samo baƙar leda sannan na koma banɗaki,a cikinta na kasaye duk abin da ke cikina sannan na miƙe ina dariya ni ɗaya.Da ido na yi wa ledar umarni ta ƙulle kanta kafin kuma na aikata can gidan anty Hinda.

Na fito na wanke jikina na koma ɗakina,gari na wayewa anty Sailuba ta sake shigowa tare da samun wuri ta zauna.
Ta ɗan ja ajiyar zuciya kafin ta ce “ da farko dai ina yi miki godiya game da abin da kika yi min jiya,na biyu kuma abin da zan ce miki babu kyau cutar da mutane ki bari”

“ Shikenan ya bar zancen auren?” ita ce tambayar da na yi mata.
Ta ce “ eh ya bari sai kuma ya ɓullo da wata matsalar wai za mu tashi daga nan mu koma can gidan da ɗan uwansa ya gina kin san nan haya muke”
Na ce “ to ai hakan ba matsala ba ce kin ga kuɗin da yake biya na haya sai ku yi wani abu da su”
Ta girgiza kai ta ce “ uwar mijina ƴar masifa ce ta bugawa a jarida,kuma kin ga ita ma a can take.Yanzu dai mu bar maganar nan zo ki yi mini wanki ki share gida da kuma wanke-wanke kin san halin Bilal shi ma wani sa'in bai da mutumci shi yasa kawai na ce masa ƴar aiki na ɗauke ki”
Tashi na yi tsaye na ce “ babu matsala anty in dai zan zauna a nan ko ƴar aikin sai na zama” tulin kayanta da na mijinta na wanke ,na yi shara na yi wanke-wanke a ƙarshe na je na yi wanka sannan ta zuba mini waina da miya sosai na ci na ƙoshi.“ Ki shirya za mu je kasuwa abokan Bilal yau a nan za su ci abincin dare”
Na ce “ kenan yau ba za mu buɗe shago ba?”
“ Eh gaskiya tun da kaji za mu sayo sai kuma mun yi gyaran su”

Da muka fito za mu tafiya kasuwa ta ƙofar gidan anty Hinda muka wuce,tun daga nesa na hango ledar kashin da na yi tanadi ta na nan tsaye kamar haure jira kawai take lokacin da na ƙa'ide ta faɗi ƙasa.Na yi murmushin mugunta har na matsu ƙarfe sha biyu ta yi,da muka shiga kasuwa kuwa na yi ta gamuwa da abubuwan mamaki waɗanda normal mutane ba su iya gani.Yawancin ƴan kasuwa duk su na da layar da za ta jawo musu customer su sayi kayansu ba tare da sanin ita fa wannan layar ta na ɗauke ne da aljanu su ne kesa mutane sayen kaya ko ba su shirya ba,wani abun ma bai da amfani sai ka je gida ka yi ta tunanin mi yasa ma ka saye shi da ka bar kuɗin ka.
Chapter 16 · 0% Book details