← Book details Man Of The World Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 7 OF 15

Sashe 7

Man Of The World Part 2 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Zaune Hauwah tashigo tasamu Inteesar baki ta buÉ—e da alamun mamaki tace"au yanzu nan Besty har yanzu baki tashi kinshiga wankanba kenan Æ´an É—aurin aure har sunfara taruwa ko sokike anguna suzo hotuna aga baki shiryaba ko wani abunke damunki ne".
"Besty yau narasa meke damuna tunda na tashi gabana ke faɗuwa a jikina inajin kamar wani abunke ƙoƙarin faruwa dani mara daɗi".
"kinsandai banaso kina ɓata ranki a banza nasandai duk wannan sanyin da jikinki keyi be wuce na rashin wayarku da mijinki ba kuma wallahi banajin Uncle Zaid zeƙi kiranki haka kurum nasan hidima ce tayimasa yawa shiyasa kidena damun kanki dan Allah insha Allahu ba abinda zefaru dake se alkhairi oh ni Hauwa'uh Besty kinfitsare idonki ko kunyata bakyaji hardamun kuka waikan bakiji mijinki inaga kuma anhaɗe anzama ɗaya ai se addu'ah sede mu rife idanunmu ".
murmushi da iyakarsa fatar baki Inteesar tayi tare da cewa"Allah ba haka bane Besty kawai dai yau tunda na tashi gabana ke faÉ—uwa".
"naji dai kitashi ki shirya ki yawaita addu'ah ko wani abunne zesameki sekiga abun yazo da sauƙi".
"tom Bestyna ammafa zanyi missing É—inki".
taƙarasa zancenta murya na rawa hawaye na ƙoƙarin zubomata saurin juyar da fuska Hauwah tayi domin itama Hauwahn hawaye ne ya zubomata tayi saurin sharewa takama Inteesar seda takaita har bakin ƙofar toilet taga shigarta sannan takoma ta zube kan gado tashiga kukan rabuwa da aminiyartata seda tayi me isarta sannan ta buɗe kayan lefan Inteesar ta ɗakkomata wani dakakken les brown me tsadar gaske da mayafinsa da danƙareren gwal ɗin da aka sako a lefan da takalmi da jaka black tana fito wanka tashirya baƙaramin kyau tayiba Hafsat tayimata simple make up sosai tayi kyau kayan sunyi mugun amsar jikinta kamar angwadata hotuna Hauwah tashiga yimata nan sukaita hotunansu.

Abbih da Abban Zaid suna zaune a gurin ɗaurin aure Zaid yazo ya zube gabansu hawaye shaɓe-shaɓe ya haɗa hannuwa a gaban Abbansa alamun roƙo yace"dan Allah Abbah ka fahimceni wallahi inason Jameelah bazan iya rayuwa bataba".
murya a kausashe Abbah yace"ka mutu inkana iyawa sakarai kawai tashi kabani guri".
yaƙarasa zancensa rai ɓace yana nunamasa hanya dakatar dashi Abbih yayi ta hanyar cewa"subahanallahi ya yaro yana roƙonka kaƙi saurarensa wanne irin abune Abubakar seka tsaya ka fuskanci matsalarsa asamu solution ".
harar Zaid Alhaji Abubakar yayi tare da cewa"rankashidaɗe ka rabu dashi wannan sakarci yake ƙoƙarin tsiromun dashi wanda nikuma bazan lamunci hakanba".
"menene ke faruwa kuma wacece Jameelah kuma ko amarya ce".
"ƙanwar amaryar ce".
"bangane ba".
nan Alhaji Abubakar ya labartawa uban gidansa duk yadda sukayi da Zaid da safe sauke numfashi Abbih yayi tare da buɗar baki zeyi magana kenan sukaji muryar Abbansu Inteesar yace"aida Inteesar da Jameelah duk ɗayane Allah yasa haka shine mafi alkhairi nabashi Jameelah duniya da lahira itakuma Inteesar ɗin Allah yazaɓamata mafi alkhairi a gareta Alhaji kabarshi ya auri zaɓin ransa yanzu andena auren dole ga matama bare ga namiji".
"kwarai kuwa a ɗaura da Jameelah kawai itakuma Allah ya zaɓamata miji nagari".
cewar Abbih haÉ—a baki sukayi gurin cewa"Ameen ya Allah".
harar Zaid Abbansa yayi cikin ɓacin rai tare da cewa"hankalinka ya kwanta ka nunawa duniya ban isa dakaiba" .
"haba Abubakar kamar bakasan illar auren dole ba abarshi ya auri wadda yakeso".
"toh Allah yasa haka shine mafi alkhairi".
"Ameen ".
suka amsa gabaki É—aya nan suka isa cikin mutane aka fara gabatar da É—aurin aure kamar yadda addini ya tanaza nan aka É—aura auren Jameelah da Zaid É—aurin auren daya girgiza kowa na gurin akan sadaki dubu hamsin bayan angama É—aurin auren ne jama'ah suka shiga É—auro alwala domin gabatar da sallar juma'ah .

Abbih na alola yaji wasu maza biyu dake kusa dashi suna alola ɗaya yace"gaskiya ba'ah yiwa Inteesar adalciba daka gani kuma nasan sharrin Uwar Gwarama ne domin matar nan ba Allah a zuciyarta ba abinda bazata iyaba waƙilama gurin bokanta taje ya asircemata angonnan domin a kwanakin baya nazo wucewa naji ta tari angonnan tanata sukar Inteesar wai karya sake ya auri ragowar wani ita dake gwano beyajin warin jikinsa kaf faɗin unguwarnan ba wanda besan Jameelah ba akan bin maza a kamata da wannan akamata da wancan aiko inaji angonnan yacemata shi Inteesar ce tayimasa ba Jameelah ba kaga dake duniya ba gaskiya sun juyar masa da hankali ya aureta yarannan da uwarsu suna zama haƙuri a rayuwarsu harfa iƙirari takeyi da indai tana numfashi ko zata rasa zanin ɗaurawa bazata bari ƴaƴan Aminah suyi aure gidan da zasu huta ba ya Allah ka kawowa wannan bayi naka mafita cikin gaggawa".
"Ameen ya Allah insha Allahu itakuma seta kwashi kashinta a hannu tsinanniya kawai shiyasa ƴaƴanta duk bana zaɓa duk wanda yace tukunyar wani bazata tafasa ba shi tashi ko ɗumi bazatayi ba gata ga duniyar nan".
murmushi Abbih yayi kawai ya nufi cikin masallaci yana zama ya turawa Ammih test bajima da turawa ba takira tare da cewa"hakan yayi indai hakan baze haifar da matsala ba".
"babu komai insha Allah Ammih ".
"toh Allah yayimaka Albarka".
"Ameen".
nan ya kashe yana sakin murmushi yasamu liman sukayi magana sannan aka tada sallah ana idarwa liman ya tsaida mutane dake ƙoƙarin fita cikin laudspeaker yace"jama'ah kuɗan dakata munada wani ɗaurin auren".
kallon-kallo mutane suka shigayi nan su ƙannan Abbih suka iso da goro da alawa aka shiga rabawa jama'ah se mamaki sukeyi aka ɗaura auren Inteesar da Abdallah akan sadaki kujerar makkah guda huɗu kabbara ƴan masallaci suka shigayi mutane se murna sukeyi.

Zaune take a gefan gado tana yiwa ɗiyar Aunty Badi'ah wasa ta miƙawa Hauwah ita ta miƙe dan gyara ɗaurin zane sukaji muryar wani maroƙi yace!!!!!!!!!

Votes and Comments

_*Daga Alƙalamun ƴar Mutanen Gwarzo.*_

# Real eeshow

_*Paidbook ,Amount Nml grp 300,Vip 800, pc 1k, Account Detail 2411022356 Aisha Umar Ibrahim Zenith Bank, or Vtu mtn or airtel ga Æ´an Niger kuma zaku turo da katin Airtel na daidai kuÉ—in da kikeson shiga aiko da shedar biyanka/biyanki ta wannan number 08108362334.*_

Book 2

4️⃣9️⃣➡️5️⃣0️⃣

" Masha Allah a yau mun sheda ɗaurin auren Inteesar da Abdallahi bangon sukari kowa ya raɓu dakai seya lasa namiji ɗaya tamkar da dubu lakadan ba ajalanba Zaidu da Jameelah akan sadaki dubu hamsin lakadan ba ajalanba munawa angwaye da amare fatan zaman lafiya Allah yabada zuri'ah ɗayyiba".
jikake luu ta faÉ—i a sume cikin tsananin tashin hsnkali gabaki É—aya su Hauwah sukayi anta a ruÉ—e jijigata Hauwah tashiga yi tana kuka tana cewa"Bestyna ki tashi karki mutu kibarni nima bazan iya rayuwa ba".
tana kuka tana sambatu tana jijjiga Inteesar dako alamar numfashi babu a tare da ita cikin saurin Aunty Badi'ah ta nufi gurin pridge ɗinsu Hauwah ta ɗakko pure water me sanyi ta fasa tashiga yayyafawa Inteesar a jiki jan wani numfashi tayi me ƙarfi tare da miƙewa zaune ta fashe da wani marayan kuka tana cewa"Hauwah menayiwa Zaid dana cancanci irin wannan tozarcin daga garesa meye aibuna danya nuna yana sona na karɓesa ko inada wani aibune dase daka baya yaga nakasuna ya tsaneni meyasa zezo gareni danya jefani cikin wani hali menayimasa daya yaudareni a lokacin danake da buƙatarsa meyasa a rayuwata ni bani da sa'ah ne ya Allah ka ɗauki rayuwata na huta da wannan baƙar rayuwar da nike ciki meyasa Abbana zemun haka ya auramun wani can da bansanshiba abarni da abinda ke damuna man nasan tunda na rasa Zaid na rasa duk wani farinciki nawa dama zan mutu yanzu dana huta da
wannan masifar da nike ciki".
taƙarasa zancenta tana fashewa da wani marayan kuka meban tausayi cikin kuka Hauwah tace"Insha Allah Besty bazaki mutu yanzu ba sekinyi rayuwa me farinciki a rayuwarki Zaid kuma insha Allahu Allah seya sakamiki abinda yayimiki tsinanne mara imani bara naje gunsa ashe shiyasa yaketa faman yimana ƴan wulaƙance wulaƙancensa ashe da gadar daya taka wai a ina yasamu yarinyar daya aura ɗin kuma ya sunanta".
jin muryar Khadijah sukayi dake shigowa tace"Jameelah da kika fifita kikaita zagina akanta itace ta auri Zaid aikinga yanzu ta nunamiki baki da hankali ta auri muradin zuciyarki".
"what Jameelah kuma".
cewar Hauwah tana zaro ido tana kallon Khadijah samun guri Khadijah tayi ta zauna tare da cewa"eyi munada wata Jameelah ne bayan ta gidanmu itace ta aureshi aidama shi wanda ya nunamaka tun farko baya ƙaunarka to karka sake ka yarda dashi daka baya dan yazo ya nunamaka yana ƙaunarka to ƙarya yakeyi to kinga ashe datazo tayi kwance-kwance akan tadena duk abinda takemana harda kukanta akan mu yafemata ashe da plan ɗin data shirya shiyasa a lokacin nayita nunamiki kikaƙi fahimtata ke a tunaninki ƙinta nike duk abinda nakeyi inayinsa ne saboda farincikinki amma kikaƙi fahimtata harda dena yimun magana tokinga ai tayi maganinki cikin ruwan sanyi".
a zabure Hauwah tayi waje tana waje ta iske Zaid da abokansa sunata hotuna da Jameelah da ƙawayenta cikin annashuwa kamar ba abinda yafaru kallonsu tashigayi ɗaya bayan ɗaya taga ba Muhseen wani tuƙuƙin baƙin cikin Zaid ne ya tunƙure Hauwah tayi gurinsu rai ɓace.
Chapter 7 · 0% Book details