← Book details Man Of The World Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 13 OF 15

Sashe 13

Man Of The World Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Dariya gabaki É—aya sukayi Ammih tace"kinibabba kinason mijinki kina kaiwa kasuwa Allah ya shiryamunku kutashi kuje ku shirya muci abinci".
"Ameen dai Amminmu toh".
cewar Rahama daketa dariya nansuka tafi suna shiga bedroom Rahama tayi sauri ta shige toilet tanaiwa Inteesar dariya tayimata wayo taɓe baki Inteesar tayi haɗe da cewa"kedai kika sani yarinya tunda dai bakwana zakiyi a toilet ɗinba aida sauƙi bawani haushi dazanji".
nan tashiga tazar dogon gashinta Rahama batawani jima tafito nan Inteesar itama tashiga batawani daɗe ba tafito ɗaure da towel kama haɓa tayi alamun mamaki ganin yadda Rahama tasha uwar kwalliya kamar wadda zata gasar kyau tasha abaya ƴar ubansu se walwali takeyi tasha stone tace"Sis irin wannan kyau haka kamar wadda zata gasar kyau ai wannan inkika fita waje seki haddass accident ɗin motoci a gari".
murmushin daya ƙaramata kyau tayi tare da cewa"kai Aunty banda sharri duk kyauna aiban kaiki ba kefa ko bakiyi kwalliyaba kyau gareki bare kinyi".
"Allah ba sharri bane gaskiya na faÉ—amiki idan nayi kyauwunki ai a kalleni".
"bawani nan kawaidai tsokanata kikeyi dan kinga kinfini shiyasa kawai kike ƙoƙarin zagina".
"wlh ba zaginki nake ba gaskiyata nake faɗamiki ƙaraso kiyi ki shirya nasan ƙila yanzu kowa ya hallara a dining mukaɗai ƙila ake jira ".
"toh ai yanzu zan shirya ni ai shirina bashi da wuya mai kawai zan shafa".
"wanne irin mai Aunty aiko dai kwalliya zan tsaramiki saboda so nike ki gigita Yayah ta yadda zeƙara faɗawa a kogin sonki ".
murmushi tayi kawai tare da cewa"Allah shiryeki Sis".
"ameen dai matar babban Yayah".
murmushin yaƙe kawai tayi domin baƙaramin faɗuwa gabanta yakeyi ba idanta tino da wai wannan mutumin me girman kan tsiyar ne mijinta tana wannan tinanin har Rahama tagama tsaramata kwalliya tana gamawa ta tsaya ƙaremata kallo tas sannan tace"amma Aunty kin haɗu tsarki ya tabbata ga Allah subhanahu wata'ala gaskiya bazaki kalli kanki a mirrior ba sekin saka kaya nayimiki rolling kinga muna gama cin abinci semu wuce shopping ɗinda Ammih tace basemun dawo ɗaki ba".
"toh nagode Sis dan Allah idan mundawo ki aramun wayarki nakirasu Besty".
"toh ai se a haÉ—o da wayarma ".
"toh".
nanta saka inner wears É—inda ta fitomata dasu sababbi masu colour É—in coffee sannan ta É—ora wata haÉ—aÉ—iyar abaya coffee wadda tasha adon stone se walwali takeyi da É—aukar ido É—auremata dogon gashinta dayasha gyara Rahama tayi da coffee É—in rebom sannan tayi rolling É—in kanta da É—ankwalin abayar lokaci É—aya ta rikiÉ—e tazama tamkar balarabiya kama hannunta Rahama tayi takaita gaban mirrior tare da cewa"Aunty kallarki kiganki".
kallon madubi Inteesar tayi taga lokaci ɗaya tacanza tayi kyau murmushin dayaƙara fito da kyawunta tayi tare da cewa"nagode Sis amma wannan kwalliyar kamar tayi yawa gakuma gashi dakika fitomun dashi dukya dameni".
"bawani yawa da kwalliyarki datayi Aunty light make-up fa nayimiki shikuma ai gashi baze rife bane shiyasa amma dan Allah karki lalata kwalliyarki mutafi nasan mu ake jira ".
"toh muje".
nan kowacce tasa plate shoe ɗinta da hand bag ɗinta kalar kayanta suka fita sunata baza ƙamshi.

Ɓangaren Namijin duniya ko yana gama rai ɓace ya isa part ɗinsa yana shiga falonsa ya zube kan kujera tare da sauke wani nannauyar ajiyar zuciya harya lunshe idanunsa yaji verbrating ɗin wayarsa tsaki yayi tare da duba mekiran yakara a kunne tare da yin shiru daga ɗaya ɓangaren Ahmad yace"mutumina inaka shigane inata kiranka baka ɗauka ba".
wani guntun tsaki yayi tare da cewa"wannan yarinyar ce taɓatamun rai wai kamata za'ayiwa auren dole batare danasani ba kuma Abbih ya rasa yarinyar daze auremun se fitsarrar yarinyar nan mara tarbiyya".
"aure kuma My Man wacce yarinya kenan".
"wacce yarinyace banda Inteesar take kowa oho mata".
a zabure Ahmad yace"wacce Inteesar kake nufi badai ta office É—inka ba".
"itaman".
wani farinciki ne ya lulluɓe Ahmad yashiga godiya ga Allah nunawa Abdallah yayi yana tayashi alhini daga ƙarshe yacemasa zasu shigo shida Adam daddare nan sukayi sallama Ahmad ba abinda yakeyi se murna tsaki Abdallah yayi tare da miƙewa yashiga bedroom ɗinsa ya ɗaura towel yashiga bathroom dan watsa ruwa bewani jimaba yafito towel ƙarami yana tsane kwantacciyar sumar kansa hand drayer ya jona yashiga busar da gashin yashiga gyarashi da mayamayan gyaran gashinsa lokaci ɗaya suma taɗau sheƙi
yana gamawa yayi shafa ys shirya cikin wata haɗaɗiyar black arman suit yasaka komai baƙi yafeshe jikinsa turarukansa masu daɗin ƙamshi ya gyara jikinsa tsaf ko ina yaɗau gayu cikin takun ƙasaita ya nufi ɓangaren Granny dan amsa kiran Abbih.

Yana isa falon Granny ya nufi dining dan yagasu Ammih nacan cikin girmamawa ya gaidasu Mummy suka amsa tashi Meemah tayi daga kujerar datake zaune takoma kusa data Abdallah shiko ɗan gogan yi yayi kamar besan tazauna kusa dashi ba ya maze ta ƙasan ido yashiga kallon kowa na gurin yaga Rahama amma beganta ba kai hannu yayi ya tsiyayi ruwa a glass cup yakai bakinsa a zuciyarsa yace"ko ina kuma wannan fitsararriyar yarinyar tashiga oho".
yana cikin wannan zancen zucin yaji ƙamshin wani daddaɗan turare ya daki hancinsa saurin maida glass ɗinsa yayi a idonsa ya kalli direction ɗin dayaji wannan ƙamshin tozali yayi da Inteesar dataci uban gayu kamar ka saceta ka gudu dan kyau hannunta riƙe da wani babban ball tari yashigayi!!!!!!!!!

Votes and Comments

_*Daga Alƙalamun ƴar Mutanen Gwarzo.*_

# Real eeshow

_*Paidbook,Amount Nml grp 300,Vip 800,pc 1k, Account Detail 2411022356 Aisha Umar Ibrahim Zenith Bank, or Vtu mtn or airtel ga Æ´an Niger kuma zaku turo da katin Airtel na daidai kuÉ—in da kikeson shiga aiko da shedar biyanka/biyanki ta wannan number 08108362334.*_

Book 2

5️⃣7️⃣➡️5️⃣8️⃣

Saurin shanye ruwa dake hannunsa yayi yayinda yake binta da idanu ta cikin baƙin glass ɗinsa kamar wanda yaga sabuwar halitta har ta aje ball ɗin dake hannunta kallon chairs ɗin gurin tayi taga ɗaya ce kawai ta rage wadda ke facing ɗin Abdallah jiki a suluɓe ta nufi kujerar yayinda kanta ke ƙasa gabanta ke tsananin faɗuwa saboda jin idanunshi na yawo a jikinta ta zauna tare da sauke wata boyayyar a jiyar zuciya kanta a ƙasa tace"sannunku da hutawa kuyi haƙuri nabarku kuna jirana".
murmushi Ammih tayi yayinda takejin wata ƙaunar Inteesar dake ƙara ninkuwa a zuciyarta tace"bakomai daughter ke za'aiwa sannu irin wa'innan abinci haka Allah dai yayi albarka ɗiyata kema Allah yabaki masu yimiki".
murmushi tayi tare da yin ƙasa da kanta alamun kunya tace"ameen".
taɓe baki Namijin duniya yayi tare da
# Real eeshow

_*Paidbook,Amount Nml grp 300,Vip 800,pc 1k, Account Detail 2411022356 Aisha Umar Ibrahim Zenith Bank, or Vtu mtn or airtel ga Æ´an Niger kuma zaku turo da katin Airtel na daidai kuÉ—in da kikeson shiga aiko da shedar biyanka/biyanki ta wannan number 08108362334.*_

Book 2

5️⃣7️⃣➡️5️⃣8️⃣

Saurin shanye ruwan dake hannunsa yayi yayinda yake binta da idanu ta cikin baƙin glass ɗinsa kamar wanda yaga sabuwar halitta har ta aje ball ɗin dake hannunta kallon chairs ɗin gurin tayi taga gabaki ɗaya da mutane kai saura guda ɗaya ce kawaita rage wadda ke facing ɗin Abdallah jiki a suluɓe ta nufi kujerar yayinda ƙirjinta ke dukan tara-tara kanta a ƙasa gabanta na tsananin faɗuwa saboda jin idanunshi na yawo a jikinta batason yakuma tsiromata da wani salon masifar tashi ta zauna ganin bemata wata muguntar bane yasata sakin wata ɓoyayyar ajiyar kanta a ƙasa tace"sannunku da hutawa kuyi haƙuri nabarku kunata jirana".
murmushi Ammih tayi yayinda takejin wata sabuwar ƙaunar Inteesar na ƙara ninkuwa a zuciyarta tace"bakomai daughter ke za'aiwa sannu irin wannan abinci haka Allah dai yayimuku albarka ɗiyata kema Allah yabaki masu yimiki".
murmushi tayi tare da yin ƙasa da kanta alamun jin kunya tace"ameen".
taɓe baki Namijin duniya yayi tare da yin magana a ƙasan maƙoshinsa ta yarda ba wanda zeji se ita yace " a haka kamar wata mutuniyar kirki hadda wani ƙasa dakai kamar gaske nanko ba abinda ke cikinta se ƴar banzar rashin kunya kamar kuɗin cizo".
karaf sukayi ido huÉ—u da Inteesar kashemata ido É—aya yayi tare da sakin wani shu'umin murmushi ya É—agamata gira alamar yadai saurin É—auke kanta tayi daka gareshi dankar wani yagansu.

Karaf akan idon Meemah waddata tashi cikin yauƙi zatayi serving ɗinsu tinani tashiga yi itako a ina tasan wannan fuskar ganin tashiga tinani ne yasa Abbih cewa"Daughter ƙarasa ladanki mana kiyi serving ɗinmu".
cikin girmamawa ta miƙe tare da cewa"toh Abbih".
nanta shiga serving ɗin kowa cike da nutsuwa gefe guda kuma ba abinda Meemah keyi se aikin kallon Inteesar tana son tino inda tasanta a haka takoma ta zauna har Inteesar tagama serving ɗinsu tana tinani nan kowa yafara cin abincinsa cikin kwanciyar hankali a zabure ta miƙe tare da cewa"bura uba kece..........?".
ta faɗa tare da nuna Inteesar dake ƙoƙarin kai spoon ɗin shayi bakinta kowa na gurin ne yajuya yana kallon Inteesar saurin maida spoon ɗinta tayi tare da shiga dube-dube alamun nema wanda Meemah ta nuna gani tayi kowa na gurin na kallonta saurin yin ƙasa da kanta tayi gabanta na dukan tara-tara domin tin shigowarta tagane Meemah sarai a zuciyarta tashiga addu'ar Allah yasa karta faɗi inda ta taɓa ganinta domin batason kowa yasan ta taɓa ganin Namijin duniya.

Tana cikin wannan zancen zucin taji muryar Abbih yace"A uzubillahi mina shaÉ—anirrajim anan gidan ake kutuntuma wannan ashar É—in sekace gidan maguzawa".
saurin zungurarta Mummy tayi ta ƙasan dining ba tare da angansu ba tayimata alamun a cikin mutane suke ganin tayi shiru ne tana jifan Inteesar da wani kallon ƙasƙanci ne yasa Mummy yin gyaran murya cikin ƙissa tace"nifa banson shashanci kinsanta ne?".
"wallahi da naÉ—auka wata Æ´ar class É—inmu ce da mukayi karatu a England Zainab se yanzu nagane ashe ba ita bace amma ko suna tsananin kama sorry fa".
taƙarasa zancenta tana mai jifan Inteesar da wani kallon wulaƙanci murmushin gefan baki Abdallah yayi domin shima yagane inda Meemah ta taɓa ganin Inteesar.
Chapter 13 · 0% Book details