← Book details Man Of The World Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 2 OF 15

Sashe 2

Man Of The World Part 2 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Tana fita ta hangeshi tsaye shida babban amininsa Muhseen sun haɗe cikin ƙananun kaya sunyi matuƙar amsar jikinsu sunyi sharr dasu cikin nutsuwa take tafiya kamar wadda take tausayin ƙasa tsaki Zaid yayi ya shige cikin motarsa cikin masifa yace"baza ka taho mutafi koko haifarmu tayi da seta gama isarta zata fito kamar wata uwarmu nina ƙiji jinin baƙin wulaƙanci ko wani abun mukazo nema gurinta da zata rainamana hankali sannan tabamu".
"anya ko Zaid hankalinka É—aya Inteenka cefa".
a zafafe yace" koma wacece da Allah Malam ka taho mutafi inbazaka shigoba ni zan wuce".
"to Invitation É—inda zamu batafa".
"nafasa ko dolene satayi gayyar kashigo mutafi".
ganin Muhseen bashi da niyyar shiga ne yasa yiwa motar key ya tafi a guje tare da bulamusu uwar ƙura mamakine yakama Muhseen a zuciyarsa yace "anya ba wani abun Inteesar tayiwa Zaid ba kuwa domin naga kwana biyunnan koson inyimasa maganarta bayayi wanda da har so yake ayimasa zancenta gaskiya da abinda yake faruwa bara inji tabakinta koma meke akwai zanji".
jiki a sanyaye taƙaraso gurin nunawa tayi kamar bataji duk abinda ke faruwa ba a tsakaninsu ba cikin girmamawa tace"ina yini Yah Muhseen".
sakarmata murmushi yayi haɗe da cewa"amarya bakya laifi kokin kashe ɗan masu gida lafiya ƙlau".
murmushin yaƙe kawai tayimasa haɗe da cewa"hmm haka dai kace Yah Muhseen amma ni ai bankai ba".
"harma kin wuce domin ninasan halin kayana mekika yiwa abokinane naga yaƙi tsayawa".
"hmm wallahi ba abinda nayimasa ".
"tino dai domin hakanan baze riƙa jin haushinki ba daliliba".
shiru tayi secan tace"wallahi nidai a iya sanina ba abinda nayimasa".
"ok zan tambayeshi inji dama zuwa mukayi mu tambayeki events nawa zaki sekuma iv ɗin ɗaurin aure da zamu baki yaƙi tsayawa ".
baƙaramun sanyi jikinta yayiba sakamakon jin abubuwan dataji Zaid na faɗa akanta ta girgiza kai haɗe da cewa"ba abinda zanyi Yah Muhseen ".
waro ido Muhseen yayi hakan dayayi seda yabawa Inteesar dariya yakama baki yace"haba ƙanwata baki isa ba kinko san yadda muka daɗe muna jiran wannan ranar ta bikin Zaid kuwa da zakice haka ".
"a'ah wannan dole mutumina yariƙa jin haushinki walkahi ace biki kamar na Zaid ba'ayi komai ba sekace bikin bazawara to bazeyiwu ba dole ki faɗi abunda za'ayi inke bazakiyi ba mu zamu haɗa dakanmu".
"toh nidai Yah Muhseen walimah kawai zanyi sauran kuma nabarmaka komai a hannunka duk abinda kace haka za'ai".
"ok yanzu kika yi magana zan tsara komai insha Allahu".
"tom ".
"yauwa gobe zan dawo tunda kinga jibi za'ah fara biki gobe zamuzo mu kawomuku kuɗin ƙunshi koma dai meke akwai zamuyi waya ina Tweeny ɗin taki".
murmushi tayi tace"tana gida inkirata ne".
"a'ah kibarta nakirata a waya muji schedule É—in ita data tsara".
"toh ".
nan yayimata sallama yana mamakin canzawar aminin nasa lokaci É—aya shiga gida tayi shikuma ya wuce.

Zaune yake akan haɗaɗiyar kujera system nakan cinyarsa yana operating ɗinta tashigo ɗakin ko ba'ah faɗaba yasan ba wanda ze shigo masa kai tsaye se Sweetheart ɗinsa da gudu taƙaraso inda yike tare da yin hugging ɗinsa ta baya tace"I miss you Ya Abdallah".
sauke system É—in dake kan cinyarsa yayi tare da cewa"miss you too dear ina zaki kika sha wannan wankan haka kamar wadda zata gasar kyau".
yaƙarasa faɗa yana jan kumatunta kyalkyalewa tayi da dariya tare da cewa"shan ice cream zaka kaimu sannam inaso inyo shopping ɗin wasu abubuwa".
murmushin daya ƙara yimasa kyau yayi hakan yasa Meemah dake tsaye tana kallonsu ƙara narkewa a duniyar ƙaunarshi yace"menene wasu abubuwa kiyi list kibada su Abubakar su siyomiki man Sweetheart kinga kingaji da yawa ki huta".
cikin shagwaɓa tace"Allah Allah ni bangaji ba ka shirya ka kaimu yaushe rabona da ƙasar please Bro".
jamata kumatu yayi tare da cewa"toh shagwaɓatuna bara na shirya muje kizauna a falo kijirani".
yaƙarasa zancensa tare da kallon bakin ƙofa Meemah yagani tsaye ta shagala da kallonsa ɗaure fuska yayi kamar be taɓa dariya ba tsallen murna Rahma tayi tare da cewa"seka fito Bro dan Allah fito da wuri domin so nike mu zagaye garin Abuja".
"toh ".
nanta miƙe cikin farinciki suna haɗa ido da Meemah yajefeta da wani kallo tafice ba tare data shiryaba.

Cikin wata dakakkiyar gizna yafito brown se ɗaukar ido take baƙaramun amsar jikinsa shadda tayi ba abinka da cikakken namiji me jini a jika daɗan sassarfa yake sakkowa daga stair zaune yasamu su Mummy suna hira Rahma naganin sakkowarsa ta miƙe zumbur tare da cewa"tashi mutafi Sis ga Yayah nan".
mumrmushi Mummy tayi tare da cewa"toh Æ´ar gidan Yayah se tafiya ko to adawo lfy".
"Allah yasa Mum".
cewar Meemah murmushin gefan baki yayi tare da cewa"Mum semun dawo".
"toh adawo lfy kardai ayi dare".
"insha Allah ".
yafaÉ—a yana tafiya nansuka tafi.

Tsaye suke a gurin jeweleries suna dudubawa juyamusu baya yayi yana waya yana katse wayar ya juya yana bin jeweleries É—in gurin da ido sexy eyes É—insa ne ya sauka kan!!!!!!!

*Wannan littafin na kuɗine inbaki biyaba dan Allah karki karantamun inkuma kinbiya dan Allah karki fitarmun mu riƙe amanar juna Sighn and udate by Real eeshow MAN OF THE WORLD*

Votes and comments

_*Daga Alƙalamun ƴar Mutanen Gwarzo.*_# Real eeshow

_*Paidbook ,Amount Nml grp 300,Vip 800, pc 1k, Account Detail 2411022356 Aisha Umar Ibrahim Zenith Bank, or Vtu mtn or airtel ga Æ´an Niger kuma zaku turo da katin Airtel na daidai kuÉ—in da kikeson shiga aiko da shedar biyanka/biyanki ta wannan number 08108362334.*_

Book 2

3️⃣9️⃣➡️4️⃣0️⃣

Wasu diamond necklace se ɗaukar ido suke guda biyu iri ɗaya baƙarmun kyau suka yimasa ba hakan yasashi kai hannu ya ɗakkosu jin muryar Rahmah yayi tace"wow Yayah ya akai idanunka ya hangomaka wannan haɗaɗen necklace ɗin ba tare damu mungashi ba".
"baku da ido ".
"hhh kaji Yayah bani dan Allah".
satar kallon Meemah yayi ta gefan ido yaga yadda ta tsaresu da ido tanata zabga smiling murmushin gefan baki yayi tare da cewa"gashi".
ansa tayi tare da cewa"wannan ta hannunka fa ".
yana lumshe sexy eyes ɗinsa kyakyawar fuskarta yagani lokacin daya kamata tana ma hotonsa kiss sake tinowa yayi da lallausan lips ɗinta daya yiwa kiss batare daya sani ba murmushi ya suɓucemasa bazato yana duniyar tinani yaji karaɗin muryar Rahama tace"gaskiyane Yayah niko zanso inga Auntyntinnan tawa me sa'ah haka datayi wuff da zuciyar ɗan uwana lokaci ɗaya haka naga ka mutu akanta haka amma ko wacece me sa'ah ce zanso ganinta dan nasan ɗan uwana bazeyi zaɓen tumun dare ba nifa harna ƙagu danaga photonta dannasan ba baya bace Yayah meye sunanta ".
murmushin dabe shirya yinsa bane ya suɓucemasa ya shafa yalwataccen sajensa tare da satar kallon Meemah daketa faman doka murmushi a tinaninta ita yake nufi murmushin gefan baki yayi haɗe da cewa"ina ruwanki zata bayyana nanda lokaci ƙalilan kedai kullum ki wanke ido domin nasan kema zaki yaba da ita 100%".

Wani farin cikine ya lulluɓe zuciyar Meemah a zuciyarta tace"ashe dama shima yana sona yaketa jamun aji yana nunamun kamar bayasona nifa dama nasan yana sona domin duk wani namiji me lafiya ya ga irin shigar da nikeyi dole hankalinsa ya tashi aiko yanzu zan fara nunamaka zallar ƙauna ashe dama bason wannan kucakar yarinyar yakeba kenan dole inzo inzage gurin nunamaka zallar ƙaunar da nike maka".
jitayi Rahama ta taɓata tare da cewa"yadai Sis tunɗazu naketa magana kinyi shiru koke bakyason kiga matar da Yah Abdallah ya mutu akanta ne".
"inaso inganta man Sis".
riƙe ɗaya sarƙar yayi a hannunsa ba tara daya saka cikin kayan siyayyarba suka nufi gurin biyan kuɗi suka biya suka nufi hanyar oasis.

Ɗaure yafito da towel a ƙugunsa hannunsa kuma ƙaramin towel yana sharce gashin kansa ta mirrior ya ga abokinnasa kama haɓa yayi alamun mamaki yace"mutumin shine zaka ƙaraso koka taɓani".
harara Muhseen ya maka masa tare da cewa"yanzu ai seka koma tunda nima bakason ganina".
"nina isa ince banason ganinka".
"harma kayi yawa tunda ka iya tozartani a idon duniya muje gurin yarinyar nan domin bata invitation shine sekace wanda ze bar gari kashiga zazzaga ruwan masifa ta inda kake shiga batanan kake fita ba kafin ta ƙaraso kabar gurin aini a tinani ko wani abun tayimaka bekamata koni na sani ba seka hukuntata iya kaida ita shine so na haƙiƙa bakazo kana tozartata a gaban kowa ba idan ni kayi a gabana ai wani be kamata kayi a gabansa ba domin su magauta haka suke so yarinyar nan ko mara haƙuri ce bekamata kayimata haka ballema ita bameson fitina bace dan Allah abokina abinda nakeso dakai koda wani abun tayimaka kariƙa bari daga kai se ita seka nunamata abinda tayi ba daidai bane seta gyara ba tare da wanima yaji abinda kuke cikiba".
zama Zaid yayi kan kujerar gaban dressing mirrior tare da cewa"zancen gaskiya ba abinda yarinyar nan tayimun abokina kawai lokaci ɗaya naji na tsaneta koson ganinta banayi kai datake matsowa bakaji wani shegen wari na fita daka jikinta ba kamar jaɓa zahirin gaskiya kuma banajin zan iya rayuwa da ita domin se yanzu nagane ba ajina bace Jameelah ce daidai da class ɗina".
Chapter 2 · 0% Book details