← Book details Man Of The World Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 3 OF 15

Sashe 3

Man Of The World Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

A gigice Muhseen ya ɗago jin furucin abokinsa murya na rawa yace"anyako Zaid kana cikin hankalinka kuwa Jameelah fa ƙanwar Inteesar wanne irin mummunan abu kake ƙoƙarin aikatawa haka".
duƙawa Zaid yayi a gaban Muhseen kamar wanda zeyi kuka yace"niko nasan menake cewa Muhseen zancen gaskiya bazan kwari zuciyata ba na tilastata kan abunda bataso ba dan Allah ina roƙonka daka tayani neman mafita domin idan na rasa Jameelah wallahi zan iya samun babbar matsala Inteesar kuma dan Allah kazo muje nabata haƙuri domin gaskiya yanzu bana ra'ayinta……".
cikin tsananin ɓacin rai Muhseen ya bugamasa tsawa tare da dakatar dashi da hannu yace"nagaji da jin wa'innan miyagun kalaman naka marasa daɗi kuma bari kaji infaɗamaka karka indai seda sa hannuna zaka samu Jameelah wallahi bazaka taɓa samunta kuma daka ranar daka aikata wannan mummunan aikin da kake ƙoƙarinyi karka ƙara nuna kasanni domin ni bazan iya rayuwa da mutum butulu irinka ba mayaudari wanda besan abinda kemasa ciwoba mezaki da ragowar maza yarinyar daba abinda tasani sebin maza".
a zafafe Zaid yaci kwalar Muhseen yana huci idanunsa sun rine se uban huci yake yace"kai waye da zaka riƙa faɗan munanan kalamai akan farincikina to bari kaji infaɗamaka abinda bakasani ba kan Jameelah a shirye nake dana ɓata da uban kowa dan haka iname gargaɗinka da indai kanaso mushirya dakai kaso abinda nake so ".
fizge jikinsa yayi daga riƙon da Zaid yayimasa cikin ɓacin rai Muhseen yace"ni ba kowa bane face abokinka meson ganin cigabanka amma tunda kace zaka iya ɓatawa da uban kowa kasani daka yau bani bakai kowa ya kama gabansa ko a hanya kaganni karka ƙara nuna kasanni ka manta dani a babin tarihin rayuwarka banza butulu kawai".
a harzuƙe Zaid yace"seme ninamafi son haka sarkin takura kawai kai kaje ka aureta man shine zan tabbatar dakai ba butulu bane ɗan sa ido kawai rayuwarka ko tawa".
nan Muhseen yafice rai ɓace tsaki Zaid yayi yacigaba da shafarshi yana gama saka kaya wayarsa dake kan gado tashiga ringing zama yayi a gefan kan gadon tare da jawo wayar hakan yayi daidai da katsewar kiran buɗe wayar yayi yashiga cal log dan duba waye mekiran wani kiran yaƙara shigowa baƙuwar number ya gani har ze jefar da wayar yafasa ya ɗaga tare da karata a kunnensa daga ɗaya ɓangaren Jameelah naji anɗaga tasaki doguwar ajiyar zuciya tare da cewa"Yah Zaid ina yini".
jin muryarta ne yasashi lumshe idonsa haɗe da buɗe lokaci ɗaya yace"lafiya ƙlau dawa nake magana".
yaƙarasa faɗi tare dason ƙara tabbatarwa dakansa ba gizon data saba yimasa bane murmushi Jameelah tayi me sauti wanda yaƙara narkar dashi a duniyar ƙaunarta taƙara narkar da murya tace"au Yayana baka ganeni bane ƙanwarka ce Jameelah".
"a'aahhh kice Malama ce".
"eh Yayah nice ya gida dasu Ummah".
"lafiya ƙlau ƙanwata ya dalibanki".
"Alhamdulillah ai se anjuma zasu zo Yayah".
"ok masha Allah Malama Jameelah yaushe nima za'ah fara koyamun karatun nima".
dammm ƙirjinta ya buga sakamakon jin ze ƙureta dakyar ta aro jarumta tace"haba Yayah aiku manyanmu ne kune masu koyamana mukuma mu koyawa na ƙasa damu".
"a'aaah ƙanwata kice dai bazaki koyamunba dai".
"zan koyamaka man amma ba yanzu ba dama kira nayi naji ya lafiyar Yayana".
"aiko naji daɗi ƙanwata idan da kina free baki da wa'inda zaki koyawa karatu anjuma danazo kin rakani unguwa".
"kaji Yayah meze hanani rakaka aiko sunzo nabasu haƙuri na tafi raka babban Yayana inmun dawo na koyamusu kazo kawai na rakaka baka da wata matsala".
"nagode ƙanwata da kulawarki gareni idan kin shirya kiyimun flashing senazo na ɗaukeki mutafi".
"bakomai Yayah ka taho yanzu mutafi a shirye nike nanda 8pm ma dawo".
"toh gani nan zuwa".
"yauwa".
nanya kashe tare da ɗaura wayar a ƙirjinsa ya rungume yanajin ƙaunarta naƙara nunkuwa miƙawa yayi yaje bakin mirrior yaƙara turare a jikinsa tare da saka hula matching ɗin kayansa ta ɗauki wayarsa da car key ɗinsa ya nufi down stairs.

A falo yasamu Mum ɗinsa da Yasmeen zaune suna hira cikin girmamawa yaƙarasa inda suke ya langwaɓar da kansa tare da cew"Mum sannu da hutawa".
"yauwa Son ina zuwa haka naga kasha uwar kwalliya kamar wanda zashi gasar kyau kodai gurin É—iyae tawa zaka".
sosa ƙeya yayi alamun kunya tare da cewa "eh Mum can zani".
"ok idan kaje kace ina gaisheta".
"zataji".
Yasmeen da kanta ke cinyar Mum ce tace"Yayah wai wanne event Aunty zatayine naga guri na ƙurewa har yau bamu sani ba".
dammm ƙirjinsa ya buga yawun bakinsa ya ƙafe lokaci ɗaya a zuciyarsa yace"bazan sanar daku gaskiyar al'amari ba domin nasan halin Mum zata iya yimun wani abun".
yana cikin zancen zuci yaji muryar Mum tace"kayi shiru saboda tanaso tashiga cikinsu ne ayo komai da ita".
wata dabara ce tafaɗomasa yasaki murmushi yace"Mum nima na tambayeta mezatayi tace wai ita batason ayi bidi'ah a bikinta batason komai wai idan akayi bidi'ah a biki befiye albarka ba na rasa yadda zanyi da ita dana dameta da maganarma harda yimun kuka nikuma banason abinda zeriƙa ɓatamata rai shiyasa na haƙura nima".

Murmushi Mum tayi a zuciyarta tana ƙara godewa Allah daya bata kamilar suruka a fili kuma tace"aiko daughter bata isaba dole ayi ko kamune duk salahancinta kuwa ina za'ayi biki sulungudi kamar na mutuwa".
"wlh kuwa Mum kinji Auntynnan tawani kwafsa mana data bari ansha shagali aida ba haka ba nifa harta ɓatamun rai ".
murmushi Mum tayi tace"da gaskiyarta gaskiya yarinyar nan tanada hankali shiyasa nake ƙara godewa Allah dayayimun kyautarta a matsayin suruka samun irinta a wannan zamanin se an tons kariƙa dakyau Zaid domin yarinyar bata da laifi insha Allahu zan kula da ita tamkar Yasmeen ka gaisheta kace nace dole ayi kamu".
"zataji Mum sena dawo".
"toh seka dawo Allah ya tsare".
"Ameen ".
nanya fita yabar Mum da Yasmeen sunata yabon Inteesar.

Direct unguwar su Inteesar ya nufa ya tsaya daka ɗan nesa da gidansu yayi parking yayi hakan yayi daidai da fitowar Hauwah zata shiga gidansu Inteesar daga nesa ta hangi kamar motar Zaid mamakine yakamata ganin ya tsaya nesa da gida shiga gida tayi cikin sauri Jameelah dake raɓe a zaure tana ganin wucewar Hauwah cikin sauru ta fice ta nufi inda yayi parking tashiga yaja suka ɗauki hanyar oasis.

Samun Inteesar tayi ta fito daga wanka se ƙamshi ketashi sakamakon anfara yimata gyara cikin girmamawa tace"Ummih sannu da hutawa".
"yauwa Hauwah".
"Inteesar kunyi waya da Uncle Zaid ne naga motarsa a É—an nesa da gidannan".
"a'ah mekika gani ".
"motarsa nagani aÉ—an nesa da gidannan ".
"ko ɗaya wataƙila gurin Abbah yazo zasuyi wata maganar".
"ƙila kuwa".
nan suka cigaba da hirarsu batare da zargin komai ba.

Suna isa Oasis yana gama parking cikin shaukin so yace"ƙanwata bara na buɗemiki saboda banaso kina aikin wahala".
"kaji Yayah daka barshi ma na buÉ—e aiki ni nake aikin abincin gidanmu gabaki É—aya".
"eh dai kidaibari na buÉ—emiki".
"toh".
nan ya fita ya zaga ya buɗemata suka fito suka nufi cikin gurin ɓangaren Namijin duniya ma baƙaramin siyayya yayiwa su Rahama ba shikuma yasamu seat ya zauna yasa sukayi oder duk abinda sukeso aka kawomusu bayan sun gama cine yabawa Rahama atm card ɗinsa aka ciri kuɗin abubuwan da suka siya yayi gaba suna binsa a baya necklace ɗin dake hannunsa ce ta faɗi ya duƙa da niyyar ɗakkowa kafin yakai ƙasa Zaid ya rigasa!!!!!!!!!

*Kuyi haƙuri Sisters bani da lafiya se yau na samu sauƙi dan Allah ku sakani a addu'o'inku .*

Votes and Comments

_*Daga Alƙalamun ƴar Mutanen Gwarzo.*_# Real eeshow

_*Paidbook ,Amount Nml grp 300,Vip 800, pc 1k, Account Detail 2411022356 Aisha Umar Ibrahim Zenith Bank, or Vtu mtn or airtel ga Æ´an Niger kuma zaku turo da katin Airtel na daidai kuÉ—in da kikeson shiga aiko da shedar biyanka/biyanki ta wannan number 08108362334.*_

Book 2

4️⃣1️⃣➡️4️⃣2️⃣

Yana É—agowa da niyyar basa sukayi ido huÉ—u da Namijin duniya kallon-kallo suka shiga yi yayinda Namijin duniya ke jifansa da kallon tuguma cikin inda-inda Zaid yace"Ina yini Yah Abdallah".
"lafiya ".
yana gama faɗin haka ya miƙa hannu ya anshi necklace ɗin hannun Zaid ta gefan ido ya kalli wadda ke gefan Zaid a zuciyarsa yace"kenan yaudarata yakeyi".
rasa me basa amsa ne yasashi fara tafiya yana mamakin abinda idanunsa suka ganemasa lokaci ɗaya yaji wani abu na tasomasa daga zuciyarsa se huci yakeyi yayinda yakejin haushin kowa direct gurin da yayi parking ɗin motarsa yashiga tare da jingina da jikin seat yanajin zuciyarsa na mugun tafarfasa a zuciyarsa yace"meyasa zeyimata haka seda yarinya ta aminta dashi shine ze zage yariƙa cin amanarta aiko yazama dole na ɗauki babban mataki akansa ".
wata zuciyarce tace"tokai meye naka na damuwa da yarinyar da bata ganin darajarka yaje yayita yaudararta matsalarsu".
wata zuciyar ce tace"yazama dole ka kula da rayuwarta tunda a ƙarƙashinka take kaje kawai ka faɗamata koda zata gwasaleka shine kawai mafita".
jin shigowar su Rahama ne yasashi buɗe rinannun idanunsa da yaketa ƙoƙarin ɓoye damuwarsa yashiga yiwa motar key dafa kafaɗarsa Rahama tayi tare da cewa"Yayah meyasa naga gabaki ɗays mood ɗinka ya canza daka haɗuwa da Yah Zaid lafiya".
ba tare daya kalleta ba yace"bakomai sweetheart muje nakaiku gida inada wani mahimmin aiki a office ".
"toh mutafi tare man Yayah".
"a'ah bari na kira Salisu driver yazo yamaidaku gida".
"toh".
nan yayi dialing number Salis yayimasa kwatancen ta hanyar da zasu haɗu yabada su ya nufi office ɗinsa cike da zaƙuwar son yaganta.
Chapter 3 · 0% Book details