← Book details Man Of The World Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 12 OF 15

Sashe 12

Man Of The World Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Nuna juna sukayi a tare suka haÉ—a baki gurin cewa"kece? kaine?".
suka nuna juna lalubar hijab ɗinta tashigayi bazato taji ya fisgota tafaɗa faffaɗan ƙirjinsa numfashinsu na sarƙewa cikin na juna a harzuƙe yace"ke wacce irin mayyace tace da duk inda nayi sekinbini".
"kai zancewa ma mekakeyi a gidanmu Allah ya kyauta inrasa mayyar wanda zanzama setaka kaima zancewa mayena da duk inda nayi seka bini goto-goto ko kunya bakaji".
binta yashigayi da kallon mamaki gani yayi babu alamun zuwa tayi lokacin sema lura dayayi kamar anan ta kwana kallon tamfatsetsen agogon dake falon yayi yaga a lokacin seven daidai ƙuramata sexy eyes ɗinsa yayi yanamata kallon mamaki karaf idanunsu ya sargafe cikin na juna kallon kallo suka shigayi na wani lokaci bazato sejin muryar Rahama sukayi akusa dasu tace"Sweetheart barka da asuba My Aunt barka da asuba".
saurin sakinta yayi yana sosa ƙeya alamun kunya ya wani ƙara haɗe rai kamar bashine ke rungume da itaba yawani ɗauke idanunsa akanta a zuciyarsa yace"tome wannan futsarariyar yarinyar kuma takeyi a gidannan bayan anɗauramata aure jiya anyako ita nagani kuwa ba gizon data saba yimun bane kuwa to kuma meyasa Rahama takirata da Aunty har kuma take gaisheta".
ɓangaren Inteesar ko a zuciyarta tace"me wannan mara mutuncin yakeyi a gidannan iwannan lokacin kuma da jallabiya tomeyasa Rahama takirashi da Sweetheart kuma".
wata zuciyarce tabata amsa da"kika sani ko saurayinta ne".
sauke ajiyar zuciya tayi tana tinanin yadda zasu ƙare da Namijin duniya
sakejin muryar Rahama yayi tana cewa Inteesar data lula duniyar tinani"Aunty memakon nima ki tasheni infara course ɗin girki gurinki shine kikaƙi tashina ko".
taƙarasa zancenta cikin shagwaɓa saurin danne tsananin mamakin ganinsa a wannam lokacin Inteesar tayi tare da yin sansanyan murmushi cikin zazzaƙar muryata meƙara tafiya da zuwar duk wani ɗa namiji tace"sorry My Sis gani nayi bekamata na tadaki kina bacci ba saboda wasu in antadasu suna bacci suna iya tashi da ciwon kai shiyasa ban tasheki ba amma gobe insha Allahu zan tasheki kinga nima seki riƙa koyamun girkin dama nima karan bani nakeyi
"kinji wai Aunty wai na riƙa koyamiki kefa nikeson ki koyamun domin ba abinda na iya".
"toh zan koyamiki".
sosai Abdallah ke mamakin yadda Rahama take magana da Inteesar abinka da miskilin mutum seya make abunsa kamar ba mamaki yskeyi ba ya wuce ya nufi bedroom ɗin Granny da kallon mamaki Inteesar tabishi har ya ɓacewa ganinsu sauke nannauyar ajiyar zuciya tayi suka cigaba da aikinsu ita da Rahama.

Abdallah na zama akan sofa Granny tafito daga toilet tana ganinshi tayi murmushi tare da zama gefan gado suna fuskantar juna tace"Mesunan Manya ba haƙuri wato amaryar taka kabiyo da sassafenan saboda rashin haƙuri irin naka yaushe rabon danaganka da sassafe se yau kamar mejiran kaɗan".
ƙara haɗe rai yayi tare da cewa"Ammih ina kwana".
"lafiya ƙlau ".
miƙewa yayi da niyyar tafiya yayinda a zuciyarsa yaketa tinanin ta yadda ze fara tambayarta kan Inteesar ƙara haɗe girar sama data ƙasa yayi tare da cewa"Ammih sabuwar ƴar aiki kikayine?".
"meka gani ".
"wata yarinya nagani a kitchen É—inki".
"ƙila takwarata ce Aishatu matarka ce ai wannan yarinya akwai tarbiyya jiya daddare muna gama cin abinci ita ta kwashe kayan ta gyara gurin gaskiya anyi sa'ar samunta komai na yarinyar nan abun birgewa ne anyako ba shuwa arab bace kuwa kai kaga kyau ko a gurin yarinyar nan kamar ita tayi kanta".
a zuciyarsa ya maimaita cewa"matata kuma".
ashe a fili yafaɗa ba'ah zuciba yana cikin maimaitawa yaji Granny tace"kwarai kuwa ɗan iya nasan yanzu zakace batayimaka ba uban sanabe todai kaji abinda mahaifinka yafaɗamaka atoh nasan yanzu zaka kusheta inkyau kake nema Aishatu kyakyawa ce ajin farko ga tarbiyya ga nutsuwa da hankali ga girmama nagaba da ita mekuma kake nema inama laifi data rufamaka asiri ta yadda kamar yadda bakasan da aurennanba haka itama batasan dashi ba dahar kake wani taɓe baki".
jin tahowar Inteesar ne yasashi taɓe baki yace"ina wani kyau yake anan gurin aba single bawani diri kamar one yazanyi tunda anliƙamun alaƙaƙai dole na haƙura na ansheta ammafa sede intemakamata amma ba ajina bace".
yaƙarasa zancensa yana sakin murmushin mugunta.

Jitayi wani iri luu jiri na É—ibarta sakamakon jin abinda Namijin duniya ke cewa dafa bango tayi sakamakon jindatayi tana niyyar yanke jiki zata faÉ—i lokaci É—aya zufa tashiga ketomata a zuciyarta tace"Innalillahi wa'innah ilaihi raji'un nashiga ukuna ni Aishatu idan naji daidai ana nufin wannan mugunne mijina meke shirin faruwa dani ne daka wannan masifar se wannan wannan wacce irin rayuwa ce ya Allah kabani ikon cinye duk jarabawar dake bibiyar rayuwata".
taƙarasa zancenta wasu hawaye ne masu zafi suka zubomata saurin sharewa tayi sakamakon jin sautin tahowar Rahama ta ƙaƙali murmushi a fuskarta jiki sanyaye tashiga cikin sanyin murya tace"salamu alaikum".
washe baki Granny tayi tare da cewa"wa'alaiki salam takwarata ashe kitchen kika shiga dasassafennan aida baki wahalar da kanki ba ga Haire ai duk zatayi komai aida kin huta".
ƙarasa zama tayi tare da yin ƙasa da kanta tayi kamar batasan dashi a gurinba taɗanyi dariya tace"ai bakomai Ammih bawata wahala sema lada dazan samu na farantawa Ammih na rai danayi".
"aikuwa dai É—iyata Allah yayimiki albarka".
"Ameen ya Allah Ammih na".
a wutsiyar ido tasaci kallonsa karaf suka haɗa ido saurin ɗauke ido tayi daga kallonsa turo ɗan ƙaramin pinky lips ɗinta tana ƙunƙunai ta juyar da fuskarta tace"ina kwana Yayah Abdallah".
shiru yayi kamar bejita ba harta fidda ran ze amsa sannan ya taɓe baki tare da cewa"lafiya ".
aninda kawai ya ce da ita kenan shigowa Rahama tayi tare da cewa"Ammih bakiji ƙanshin da falonki keyiba harna ƙagu danaci abincinnan da Aunty ta girka dakajin yadda yake ƙamshi nasan zehaɗu wallahi".
dariya Ammih tayi tare da cewa"kema hakanan zaki dena wannan banzan baccin naki na ƙaddara ki fara koya".
"ai yau ma Ammih seda nace meyasa bata tasheni ba aida munyi tare nima na koya Auntyna dan Allah gobe ki tasheni muyi tare".
taƙarasa zancenta a shagwaɓe ɗaga idonnan da Inteesar taga Namijin duniya ya taɓe baki tare da cewa"amma dai Rahama kinji kunya wallahi kirasa wadda zakiyiwa shagwaɓa se wannan ƴar abar wadda a girme kin girmeta ".
murmushi Inteesar tayi dantasan danya ƙularda ita yayi wannan maganar tace"ki kwantar da hankalinki Sis insha Allah gobe zan tasheki".
"yauwa Auntyna nagode".
fakaitar idanun mutane tayi ganin bame kallonta tayiwa Namijin duniya gwalo aiko sukayi ido huɗu dashi jinjina kai kawai yayi alamun zekamata ya miƙe yana duba agogon wayarsa yace"Granny nizan wuce Sweetheart anjuma kije ki wanken toilet".
turo baki Rahama tayi tare da yin ƙasa da murya tana ƙunƙunai tana cewa"waikai Yayah koda yaushe bazaka bari masu yima aiki suyima aikin bedroom ɗinka ba sede kasa mutum to daban dawo ba kumafa yanzu aiga matarka nan setayimaka".
ƙara haɗe rai Namijin duniya yayi kamar betaɓa dariya ba yadakamata tsawa tare cewa"kee yaushe nafara wasa dake dahar kika rainani haka to bazansa masu aikinba kenaga damar sawa".
"a'ah Malam dakata bazakazo har ɗakin kace zaka takurawa ɗiyata ba ai gaskiya tafaɗa ko ƙarya tayimaka meyasa bazakasa masu yima aiki suyima ba kokuma matarka tunda sune yazama dole suyima da dabatanan yaya kakeyi ".
"Ammih ke kikeja yara suna rainani wallahi".
yaƙarasa zancensa yana yin kwafa yafice fuuu yana fita ta sauke wata ɓoyayyar ajiyar zuciya dariya Rahama tayi tare da cewa"tofa munfa kinsawa Sweetheart baƙin ciki se Allah ya zuciya".
murmushi yaƙe kawai Inteesar ta yiwa Rahama domin hamkalinta duk baya jikinta tanacan tana tunanin rayuwar dazatayi da Abdallahnta ɗan zafin kai hira kawai sukeyi amma ita hankalinta kaf baya kan hirar tasu dariya Ammih tayi sosai tace"ai gwara daya fusata haka kurum yaro se baƙin miskilancin tsiya da faɗin ran tsiya ga matarka seka dami yarinya da mugun sa aiki idan matarshi batasan cikinsa ba wa yakeso yasani anjuma Aishatu ki shirya kije ɓangarensa ki gyaramasa".
gaban Inteesar ne yabada dammm sakamakon jin zataje gurinsa lokaci É—aya yanayinta ya canza zuwa kalar tausayi tace"Ammih da anbarshi tunda yafison na Rahama".

Salati Ammih tayi ta sanar da ubangiji gami da tafa hannayenta duka biyub tace"yau ninaga ja'irar yarinya ni Indo ana ƙoƙarin kwatarmata ƴanci tanaiwa mutane shashanci amma gaskiya albasa batayi halin ruwa ba anyako sunanki Aisha ba Sarai ba kuwa ƴar nan domin nidai a iya sanina dame suna Aisha jaruma ce batada tsoro keko daka cewa kije ɓangaren mijinki duk kinbi kintashi hankalinki kamar wadda akace taje gurin mutuwarta hadda wani marairaice murya Ammih kibarshi tunda yafison na Rahama".
taƙarasa zancenta tana kwaikwayon muryar Inteesar ganin yadda taƙara ruɗewa ne yasa Ammih kamo hannunta Granny tayi ta zaunar da ita gefanta ta kama hannunta tace"karki bani kunyaman takwara ta kizama jaruma kidena jin tsoronsa mijinkine a tafin hannunki yake duk wani hura hanci dakikaga yanayi yadena baki tsoro ki tsaya ki natsu ki gyara mijinki aida ba haka yakeba kinada damar da zaki canzashi daga wannan murɗaɗen halin nasa yadawo normal kefa macece kiyi amfani da kisisinarmu ta ƴaƴa mata ki canzamanashi kinji ɗiyata nasan abu ne me matuƙar wahala amma ki daure nasan zaki iya kinji ɗiyata watarana se labari kiyimun alƙawarin zakiyimun wannan aikin danasaki Aishatu domin rabonda muga haƙuri Abdallah a waje da sunan dariya tun kafin mahaifiyarshi ta rasu dan Allah ki temakeni ki dawomasa da walwalarsa kamar da yazama mutum kamar kowa dan Allah ƴata".
jiki a sanyaye Inteesar tace"insha Allah Ammih zanyi iya bakin ƙoƙarina".
murmushi Ammih tayi tare da cewa"nagode É—iyata Allah yayimiki albarka yabaku zaman lafiya da zuri'ah tagari kuje ku shirya saboda Abbih É—inku yace idan angama cin abinci akwai meeting.
ƙasa Inteesar tayi alamun jin kunya a zuciyarta ta amsa da Ameen dukan wasa Ammih takaiwa Inteesar saurin gocewa Inteesar tayi tana dariya .
Chapter 12 · 0% Book details