← Book details Mahaukacin So Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 9 OF 13

Sashe 9

Mahaukacin So Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

yayin da matarshi taja tsaki tana cewa "Karyar banza, idan bamu aura miki shi ba , waye me son naki ." Batula ta fita tana tare da tarin damuwa a fuskantar ta. Abincin safe suke ci , wajejen karfe 10, sakamakon yau Yaya Nasir bai fita aiki ba, kana garin an tashi da sanyi, yasa suke ta bacci abinsu. Sallamar Alaji Bashir ne yasa Mama sanya mayafi bisa kanta, lokaci guda kuma tana amsa sallamar Laila ta kalli Uncle din ta tana murmurshi "Shigo Alhaji Bashir." Mama tai maganar tare da canza wajen zama . "Assalamualaikum." "Sai yanxu kuke karyawa ke nan , an gayu." Laila tai dariya Gurin da Mama tai masa nuni da ya zauna , nan ya zauna tare da aje babbar wayarshi da mukullin motarsa "Baba ina kwana."? Laila ta fada ta na kallonshi Cikin saurin baki kamar yadda ya saba ya maida mata. "Laila lafiya kalau ." Sannan shima Nasir ya mika masa gaisuwa Yana gama amsar gaisuwar Nasir ya fara gaida Mama cikin far'a Tare da tambayar yanayin sanyi da aka fara shiga Nan Mama ta tabbatar masa komai da kowa lafiya. Sannan ya ce ."To Masha Allah haka ake so ." Shiru suka yi na wasu sakanni Sannan Alaji Bashir ya kalli Mama yana cewa. "Wato abin dake tafe dani, ba komai bane face Inna mahaifiyar babar Laila ta zo ta same ni ." Yaya Nasir da sauri ya kalli Mama, suka hada ido sannan Mama ta koma tana kallon Alaji Bashir "Ta sanar dani cewa, kai Nasir zaka bawa Laila yaro mara tarbiya , alhalin ga Mahmud can yana san ta . Kuma sannan ma kai waye a wajen Laila, bayan ni ina raye , da har zaka ba wani Laila, ba tare dana sani ba ." Yaya Nasir yaji zuciyar shi tai wani irin bugu suka hada ido da Laila Laila tai ajiyar zuciya ta mike tsaye tare da nufar dakinta "Ke Laila zo nan , ina zaki ." Alaji Bashir ya fada , sannan Laila ta dawo ta zauna Ajiyar zuciya Alaji Bashir yayi , sannan ya cigaba da cewa. "Ni bazan aurar da Laila ga wani ba , amman kasan cewa har yau bakai aure ba , sannan naga alamun Laila ma zaman gidan kake so tayi , domin ina samin labarin komai ." "Tom na baka lokaci daga yau, ka tsayarwa da Laila mijin da zamu aura mata , kuma na baka wannan damar ne domin yadda ka kula da Laila da yadda kuka shaku." Mama ta ce . "Wannan gaskiya ne , nima abin da nake so ke nan ." Alaji Bashir ya ce . "Yawwa wannan shi ne abin da ya kawo ni, domin Hasana yata kanwar Laila yanzu tana dakinta, Kuma kaima ya kamata kayi aure zuwa yanzu ." Matukar tashin hankali ya bayyana a furkar Yaya Nasir Ajiyar zuciya yayi ya kalli Alaji Bashir yana cewa. "Alaji abin da yake faruwa, har yanzu ban sami wanda zan aurawa Laila ba , Kuma wallahi da zarar an yi maganar auren Laila sai duk hankalina ya tashi ." Alaji Bashir ya mike tsaye tare da cewa. "Na dai baka lokaci, da zarar ya kare ni zan aurar da ita ga Mahmud." Ya nufi hanyar fita tare da sallama da Mama. Zumbur shima Nasir ya mike tsaye, duk su Mama ya basu tsoro Hanyar fita ya bi kai tsaye gidan Umar ya nufa babu ko takalmi a kafarshi. Dake babu nisa tsakaninsu sosai , cikin babban tashin hankali Yaya Nasir ya nufi gidan Umar. Umar na kokarin shiga gida, ya hangoshi yana tahowa, sai da ya zo gaff da Umar, Umar ya fara murmurshi tare da cewa. "Ka ga angon Batula." Lokaci guda yana kallon kafarshi da ya lura babu takalmi Kafin Umar ya sake maganar Yaya Nasir har ya juya ya sake nufar hanyar gidansu. "Kai lafiya kuwa, ko dai wani abin ne yake faruwa a gidan ."? Umar ya tambayi kanshi yayin da yake hangen Yaya Nasir dake komawa gida cikin dafewar kai Da sauri Umar ya shiga gida, da nufin ya dauko wayarshi ya bi bayansa. Laila ta mike ta koma kusa da Mama cikin matukar tausayin Uncle dinta ta fara magana. "Mama me yake faruwa da Uncle ne, yanzu fa ko takalmi babu ya fita , kullum sai ramewa yake ." Mama ajiyar zuciya ta sauke , sannan ta ce da Laila. "To nima ta ya zan sani Laila." Rufe bakin Mama ke nan Uncle ya shigo , kai tsaye kuma ya nufi dakinsa. Shima sai ga Umar ya shigo tare da sallama "Auu Mama nayi zatan wani abin ne yake faruwa, na ga Nasir cikin wani yanayi , shi yasa na biyo bayanshi ." Mama ta ce "Ummm ! Kai ma dai ka fada Umar, gashi nan daga maganar auren Laila ya koma haka ." "Bari na shiga dakin nashi ." Umar ya fada tare da nufar kofar dakin Koda Umar ya shiga , Yaya Nasir yana zaune bakin gadonshi ya dafa kanshi . Haka ya amsa sallamar Umar ba tare da ya d'ago ba . "Me yake faruwa ne Nasir."? Umar ya yi masa tambayar yana zama a gefenshi Hakan bai canza komai ba daga Yaya Nasir Sai bayan wasu sakanni sannan ya d'ago kai yana cewa "Ni ne fa na raini Laila Umar, ni ne fa ." Sai wasu hawaye sharrrr suka zubo masa "Tabbas ya kamata Laila tai aure , amman akwai ciwo a zuciya ta , bana son rabuwa da Laila , Umar in takaice maka zance ina MAHAUKACIN Son Laila , so na aure , da zamu rayu tare da juna har abada.".. Umar cikin tashin hankali ya damke masa baki , domin kar su Mama suji wannan kazamin zance . Lokaci guda gumi ya ketowa Umar *MAHAUKACIN SO* Autar Marubuta ________________________________________ Babu editing Page 23 & 24 Yaya Nasir ya wurgar da hannun Umar gefe, Cikin buguwa kamar dan maye ya koma ya kwanta. Wani das das das zuciyar Umar take bayarwa , ya kalli Nasir dake kwance cikin rashi yana cewa. "Wai daidai naji kuwa? Ko dai Nasir ya haukace ne , an ya kuwa abin da ya fada haka naji."? Ya aje ajiyar zuciya me zafi, kana da ya lura yayi bacci Ya nufi hanyar fita. "Ahh Umar tafiya zaka yi ne." Umar ya ce . "Eh Mama." Sannan shima ya fice kamar furgitacce Laila ta kalli Mama tana cewa. "Wai Mama baki ga Yaya Umar gumi yake ba , bayan sanyin da ake yi Ko dai fada sukai da Uncle."? Mama kawai ta ce mata "Ummm." Fitowar su ke nan daga harabar makaranta, suna jiran Abdallah. "Fatima da kin zo mun hau nafef kawai mun tafi Abdallah ya bata lokaci." Fatima cikin wasu idanu ta kalli Fa'iza sannan ta ce . "Fa'iza akwai abin da ya rikeshi , kuma yanzu zaki ganshi , gashi kaina yana matukar ciwo sosai , zazzabi nake ji Fa'iza." Murmurshi Fa'iza tai tana rike hannun Fatima, yayin da motar Abdallah tasha gabansu . Tun dazu Batula take zaune a falo tana jiran fitowar yayan babanta da take kira da daddy Domin wajen minti 30, ke nan tana zaman jiranshi Sai da aka sake kwasar minti biyar sannan Alhajin ya fito tare da matarshi. "Au ke Batula kina nan ashe." Ya fada yayin da yake lunkuma wani naman kaza a bakinsa . Sannan sai ga ita ma Rahma ta shigo rike da wannan naman a cikin plet, Sai da ya cinye wannan naman na bakinshi tasss , sannan ya kalli Hajjiya yana cewa. "Ita kun bata naman ko."? Rahma da sauri ta maida masa da cewa "Daddy ai idan taci nama wai zuciyar ta ke tashi." Tai maganar tana mata gwalo Kawai Batula tai murmurshi "Kaji yar baiwa shi ke nan Musa ya huta da siyen nama." Alaji ya fada Wani bakin ciki Batula taji ya turnike mata zuciya, Yadda Rahma tai mata sharrin bata cin nama bai bata mata rai ba , kamar yadda Alaji yanzu ya ambato sunan Musa mai gyaran takalmi. Shanyewa tai kawai tai shiru , sannan Alaji ya fara da cewa . "Batula abin da yasa na kira ki , ke kamar yar cikina ce , domin ke yar kanina ne Abubakar , mutum ne mai biyayya, kuma daman an ce mutuncin ya mace gidan mijinta." Tunda Batula taji wannan batu tasan inda ya nufa Hakan yasa suffar ban tausayi ta sake kamata "Jiya magabatan Musa sun zo mini , kan neman aurenki ." "Amma na ce su jira ni zasu ji daga gare ni , fatan dai kin shirya auren yaron nan , domin mutumin kirki ne , zai rike ki da mutunci, sauran gadon mahaifin ki dake hannuna sai ai miki kayan daki dasu ." Murmurshin mai matukar ciwo Batula ta ajiye sosai , domin yadda wani bakin ciki ya tsaya mata a zuciya yasa ta dole tayi wannan murmurshi. Duk da haka ba tai kasa a gwiwa ba , ta kalli yayan babanta tana cewa. "Daddy akwai wanda nake so , amman wallahi ba Musa ba ne , ka bani dama domin ..." "Ke dallah yi shiru, yana magana kina magana ko ."? Mahaifiyar Rahma ta fada Rahma ita ma ta dora Da cewa . "Karya take yi ma daddy babu wani wanda yake santa ." Alaji ya cigaba da cewa "Ai baza ai haka ba Hajjiya ,." Ya koma ya kalli Batula yana cewa. "Na baki kwana uku , ki kawon shi yaron da kike so , idan har ya cancanta to zan aura miki shikenan." Zumbur Batula ta mike cikin farin ciki tana cewa. "Na gode daddy Allah ya saka da alheri." Ta mike ta fita . Rahma tana jan wani tsaki . Tsabar farin ciki Batula ta rasa yadda yadda tai , amman lokaci guda ta kame tare da tunanin yadda zata kawo Nasir gaban Alaji , to tabbas wannan babban lamari ne, Amman ta yanke shawarar shiryawa ta nufi gidansu khairat. Fitowar Nasir ke nan zai tafi wajen aiki , ya kalli Mama sannan ya ce . "Ina Laila ta shiga kuma Mama."? Mama ta maida masa da amsa tana cewa. "Taje gidan kawarta ne ." Sannan Mama ta sake kallonshi tana cewa. "Ka ga yadda ka
Chapter 9 · 0% Book details