Sashe 6
Mahaukacin So Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
ya dore da dariya. Anan kuma Laila ce ita da wani had'ad'd'en saurayi a cikin falonsu . Bayan sun gama gaisawa da Mama, kana Mama ta shiga ciki ta barsu "Wato Laila tunda naje America, duk rayuwata babu dadi na yi matukar kewarki sosai fatan dai alkawarin mu na nan ." Saurayin mai suna Usman ya yi maganar A daidai lokacin Yaya Nasir ya nufo cikin falon Hakan yasa ya dakata sakamakon muryar Laila da yaji tana cewa. "Nima na yi kewarka sosai , amman har gashi kayi shekaru da yawa a America, gaskiya ban yadda ka damu dani ba , ko nema na baka taba yi ba ." Laila tai maganar cikin shagwaba Zuciyar Yaya Nasir ce ta sake karyewa a take a wannan wajen Cikin rashin ya ke cewa . "Usman ne ya dawo ."? Ya yiwa kanshi tambayar "To Laila auren mu shi ne zai tabbatar da irin kaunar da nake miki, amman ko rana daya babyna bata wucewa ba tare dana tuna ki ba ." Usman ya sake fada cikin soyayya Murmurshi mai jan hankali Laila ta yi sannan ta bude baki da niyyar cewa wani abu. "Assalamualaikum." Yaya Nasir ya shigo da sallama ya tari numfashinta. Sallamar ta amsa masa cikin far'a Kana Usman ya zamo daga kujera yana gaida Yaya Nasir Babu wani salo ko shauki Yaya Nasir ya amsa gaisuwar Sannan ya shige ciki. "Laila ko dai har yanzu Yaya Nasir yana fishi dani ne , ai yanzu na shiryu na gyara halayena Laila." Laila tai ajiyar zuciya domin ganin Uncle din nata a haka duk bata ji dadi ba Shi kam Uncle dakinshi ya shige ya zauna , Domin tabbas sam bai ji dadin ganin Usman ma . A lokacin baya Usman ya shigo rayuwar su da matukar son Laila , duk da cewa uncle baya son kowa ya kusanci Laila komin mutuncinsa kuwa. Sai Uncle yayi amfani da yadda Usman yake takadiri kuma mara ganin girman mutane ya raba shi da Laila. Soyyayar Laila ita ce ta gyara Usman har ya shiryu ya zama mutum , domin a halin yanzu shi yake rike kasuwancin mahaifin sa Alhaji Shehu shanshani , mutum ne mai matukar dukiya. A halin yanzu sam Uncle ba ya jin dadin dawowar Usman. To za mu ji yadda zata kaya tsakanin wannan mutane. Shin ko Mahmud ne zai auri Laila ko Usman ko wani daban . Muje mu tambayi Uncle kawai, Laila 'yar gwal ce . Domin kuwa duk wani saurayin Laila Uncle baya son shi Yanzu mene ai bun Usman da Mahmud Uncle? Tom ba dai musan me Uncle yake nufi ba , mu dai mu sha bikin shalele Ga kuma bangaren Fa'iza da Fatima Ga kuma Batula To dai alkalamin Autar Marubuta ne. *MAHAUKACIN SO* Autar Marubuta ________________________________________ Babu editing Page 15 & 16 "Haba dan Allah khairat, wai sai Uncle ya min fada ne , wallahi mun yi yawo sosai , duk na gaji." Laila ta fada cikin mita "Ke wallahi Laila munguwar matsala ce dake , Uncle Nasir da ba ya bari kina fita , shi ne yau kin fito amman sai mitar jaraba, ai gara ai miki auren ma , ki zaman gidan da hujja ." Dariya Laila ta kwashe da ita yayin da suke hada kafad'a da kafada suna tafiya Laila ta ce . "Aure manya , ai saina aurar da Uncle tukun." Da sauri khairat ta kalli Laila tana cewa. "Allah sarki harkin tuna mini Batula, wallahi Laila tana son Uncle sosai ." "Wai wace wannan Batulan kina yawan fada mini ita , kuma Uncle yana santa ."? Cewar Laila Khairat ta ja wo hannun Laila su kai wani lungu tana cewa. "Zo muje gidansu ki ganta , wallahi tana san Uncle." Wata gajiya ce ta sake rufe Laila da ganin yadda khairat tajata wannan waje . Hakan ya sa ta fincike hannunta tana cewa. "Wai duk ina kika san wannan wajejen, ni fa ba kowacce zan bari Uncle ya aura ba , sai wacce ta isa ." Khairat kawai taja mata tsaki Gidan Alaji Muktar Yana zaune ya yi tagumi , kawai yana tunanin irin yadda yayan da ya haifa suke ta mutuwa, a lokacin da yake bukatar su . Duk wacce danta ya mutu sai ya saketa , yana cikin wannan yanayin ne wata matarshi Hadiza ta shigo falon Zama tai kusa dashi tana cewa. "Alhaji lafiya kuwa." Ba tare da ya ce da ita komai ba ,kawai ya zaro wata takarda a aljihunsa ya mika mata . Faduwar gaba taji dasss Hannunta na rawa ta amsa tana budewa. "Innalillahi wa inna'laihir raji un Alaji ni zaka saki , innalillahi Kawai ta fara kuka , ya mike ya bar mata falon . Ana cikin haka sai ga uwar gidan nasa Hajjiya Ma'anatu ta shigo Tana kallon Hajjiya Hadiza da takarda a hannu tana kuka ta ce . "Innalillahi wa inna'laihir raji un Hajjiya Hadiza sakin ne ko, shi ke nan sauran ni , tunda daman Allah ya yiwa mahaifiyar shi Hajjiya rasuwa shi ke nan tamu ta kare ." Hajjiya Hadiza ta sake fashewa da kuka . Anan kuwa Batula ce zaune kan kujera tana wanke-wanke Ta yi nisa sosai kadan ya rage mata ta gama , sai ga sallamar su Laila Sai da Batula ta fara zuba musu wannan murmurshi nata kana ta amsa sallamar cikin farin ciki Suma cikin far'a suka karaso kusa da ita. Kafin wani ya bude baki ya ce komai , sai ji sukai wani "Shamm" Wasu uban kayan wanki wata mata mai zubin hajjiyoyi ta zube a kan Batula dake wanke-wanke. "Uban me kike har yanzu baki gama ba , to ga wanki nan , maza ki gama ki dora girki sannan ki fara ." Cikin biyayya Batula da amsa da "To Mommy." Kana wacce ta kira da mommy ta juya ta koma ciki Murmurshi Batula ta sake yi musu tana cewa. "Khairat ki dauko wa Laila abin zama mana." Ta karasa maganar tana kallon Laila da duk jikinta ya yi sanyi "A'a! Ke da kike aiki tafiya zami ." Laila ta fada cikin nufar hanyar fita . Bayan sun yi sallama khairat tabi bayanta Tunda suka fito Laila bata ce komai ba haka ma khairat, kowa yana sake-sake cikin ransa "Wai ita Batulan aiki take yi a nan gidan , kinji harta sanni ." Laila taiwa khairat maganar cikin sanyi Murmurshi khairat tai tana cewa. "Allah sarki Batula, yadda take son Uncle ba dole tasan ki , kin gan ta wallahi tana shan wahala , nan fa gidan yayan babanta ne , iyayenta sun rasu."... Nan khairat duk ta bawa Laila labarin Batula na abin tausayi da yadda take son Uncle A karshe duk tausayin Batula ya rufe zuciyar Laila Fa'iza ce tsaye gaban mudubi sanye da rigar da Abdallah ya siyo musu ita da Fatima "A gaskiya rigar nan ta yi kyau Abdallah." Fa'iza ta fada a cikin zuciyar ta, yayin da take sake juya jikinta tana ganin rigar Wayarta dake ringin yasa tai saurin juyawa ga wayar Kana ta zauna bakin gado tare da daukar wayar tana karawa a kunne da cewa. "Hello Rabin Raina Fatima." Daga can bangaren taji muryar Fatima tana cewa "Wallahi bana son fada miki wannan zance a waya kizo dan Allah." Ajiyar zuciya Fa'iza tai kana ta maida mata da cewa. "Gaskiya 'a'a Fatima." Ba tare da Fatima taji haushin hakan ba , cikin sabon farin ciki ta sake cewa. "An yi mana baiko da Abdallah, ashe dadi sun tsai da magana." Yadda kasan an yi ruwa an dauke, duk Fa'iza sassan jikinta suka dena aiki Sai bugun zuciyarta da yake yi kamar zai fito "Uhm wai da gaske." Fa'iza ta fada yayin da wasu zafafan hawaye suka zubo mata Cikin farin cikin dai Fatima ta tabbatar mata da wannan lamarin mai dadin ji . Bayan sun gama wayar , kawai Fa'iza tai murmurshi tana fad'in. "Fatima Allah ya tabbatar da alheri, Allah ya baku zaman lafiya da Abdallah." Ta rushe da kuka mai gwanin ban tausayi Farin ciki ya cika zuciyar Fatima, tana zaune cikin falonsu da wannan farin cikin ne mahaifin ta ya shigo , Sakin fuskar shi ya yi sosai ga yartashi guda kamar rai Zama ya yi yana fad'in. "Me ake yi ne me sunan Mama, kin sha magani ko." Shalelen baban nata baki ta zumburo tana cewa. "Daddy wai shi likitan nan ya yi ta bani magunguna, ni ban sha ba na gaji." Zaro idanu ya yi yana fad'in. "A'a yi hakuri mana 'yata, ai lafiyarki ita ce kwanciyar hankalina dana mahaifiyar ki , daure mana ai kin kusa samin lafiya in sha Allah." Murmurshi Fatima tai tana cewa. "To Daddy na , amman kafin bikin mu da Abdallah daddy ina so ka kai ni Umara , daddy idan da hali hadda Fa'izata." A lokacin mahaifiyar Fatima ta shigo tana cewa. "To masu Daddy." Ta karaso ta zauna Murmurshi Alaji ya yi yana fad'in. "Shi ke nan Fatima, zaku je in sha Allah karki damu." Cikin farin ciki ta mike tsaye tare da cewa. "To Daddy bari naje nasha maganin." Ta wuce cikin farin ciki Murmurshin Hajjiya tasa tana cewa. "Fatima ke nan , Allah ka bawa wannan yarinyar lafiya." Ajiyar zuciya Alaji Usman ya yi kana ya fara da cewa. "Wallahi Hajjiya ciwon yarinyar nan yana damun rayuwata, zan so ace Allah ni ya sanyowa wannan ciwo na zuciya a maimakon Fatima, wallahi zuciyata kullum bata samun nutsuwa idan na tuna da halin da take ciki." Cikin rarrashi mahaifiyar Fatima ta fara cewa da mijin nata Alaji Usman. "Haba Alaji! Ai shi bawa kowa da irin tashi kaddarar, muma irin tamu ke nan , ya jarafce mu da yarinyar da muka fi so , to mu yi tawakkali kawai mu gode masa , tunda gashi dai tana samun lafiya. Kuma ka ga Abdallah da danginsa zasu kula da yarinyar nan , dan sun san halin da take ciki kuma suna santa ." Alhaji Usman ya dukar da kai kasa ya d'ago yana fad'in. "Haka ne , badaban Fatima na son yaron nan ba , kuma auren sa zai faranta mata, da gaskiya ni bana son tai nisa damu , amman farin cikin ta shi ne namu." Hajjiya ta ce