← Book details Mahaukacin So Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 3 OF 13

Sashe 3

Mahaukacin So Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Wayarta ta jawo a gefe kai tsaye ta nufi wata number da kai saving da My fa Ta dannawa number kira , bugu daya , wata mace me dadin murya ta d'aga tana cewa. "Hello Fatima ya kike ya mommy."? Fatiman ajiyar zuciya tai tana cewa. "Wallahi Fa'iza lafiya lau , daman ina son mu hadu ne ." Daga can bangaren wacce aka kira da Fa'iza ta fara cewa . "Ba damuwa Fatima , zan zo in sha Allah." Ta karasar maganar da yaren masu jan kunne (turanci) Bayan sun kammala wayar , Fatima na saukewa wani kiran ya shigo mata , wanda ya matukar faranta mata rai , ba kowa bane face muradin aurenta Abdallah. Anan gidan Mama kuwa, bayan shekaru masu yawa babu abin da ya canza a wannan gidan , idan ka cire wasu shekaru a can baya da Mama ta kasa gane kanta sanadiyar shigowar Nasir cikin gidan babu zato babu tsammani A yanzu haka duk suna zaune a falo , a kan carpet suna karyawa . Nasir ne ya kalli Laila da duk hankalinta ke kan wayarta yana cewa da ita . "Laila bana hanaki danna waya ba , lokacin cin abinci."? Baki ta turo gaba kamar mai shirin kuka , sannan ta kalli Mama ta ajiye wayar a gefe ,kana ta maida hankalinta ga abincin dake gabanta "Uncle N , ina so naje gidan Aunty Ummi." Laila ta yi maganar tana kallon Nasir Shima kallonta yayi sannan ya maida mata da cewa . "Ki bari sai gobe zan kai ki ." Laila ta ce . "Tom Uncle." Mama dai bata ce dasu komai ba Wannan ke nan , shekarun baya da suka wuce Mama tana zaune da rana cikin gidanta , sai taji sallamar Nasir ya shigo , hakan ya matukar tada hankalinta sosai , domin tare da Laila ya shigo a hannunsa, lokacin tana da shekaru uku , Babu abin da Mama ta iya cewa a kan wannan lamarin , domin tunda Nasir yasa kafa ya fice da Laila tana jaririya, bai dawo da ita ba saida ta shekara uku . Mama kawai kuka ta fashe dashi mai matukar taba zuciya, mutanen gari kuwa kafin kace komai sai gari ya dauka ga Nasir can ya dawo shida Laila Haka Alaji Bashir Shima ya sami labari , bayan ya zo ya ganewa idanunsa ya matukar fitar da bacin ransa da takaicin sa ga Nasir, domin har wani zance yaso ya fitar da zaisa Nasir ciikin mugun yanayi, amman Mama ta hana shi . Tashin hankali aka yi sosai kafin komai ya dawo daidai , ita ma Inna da guntun bala'inta tazo , ta juyewa Nasir In takaice muku zance Mama harda hawan jini sai da ta watanni babu lafiya , kuma tai matukar fushi da Nasir Lokacin da Nasir ya so kare kanshi yake basu hakuri, tare da tabbatar musu ba ya son a dauke Laila a gidansu ya sa yayi wannan abin , domin sam baya son a raba shi da jaririyar yayan nashi . Sai dai babu wanda ya amshi uzurinsa , domin ba abin da za a kama bane Nan Inna ta sake tada jijiyoyin kai , a kan dole sai an bata Laila, Yadda Nasir ya ga Mama na matukar fushi dashi yasa bai ja dasu ba Sai dai bayan sun dauki Laila, abin bai musu dadi ba , domin kullum kuka babu wanda take kira sai sunar babanta Nasir, haka ta rame ta lalace babu wanda ta saba dashi sai Nasir. Hakan yasa dole suka dawowa da Nasir yar shi Bayan wannan ya faru sai komai ya fara lafawa , domin Nasir yayi matukar nadama , hakan yasa Mama ta yafe masa . Har yake bata labaranin yadda ya kula da Laila Nan ne aka sanyata makaranta, ta fara wayo Shi kuma Alaji Bashir bayan Shima ya huce , ya bawa Nasir aiki. Sai Mama taji duk farin cikinta ya dawo , domin a halin yanzu Laila ta gama makaranta. MAHAUKACIN SO Autar Marubuta ________________________________________ Babu editing Page. 7 & 8 Nasir ne zaune a cikin office dinshi , yayin da abokin shi Umar ya kawo masa ziyara Wayar Umar ta fara ringin, ya kalli wayar dake bisa teburin aikin Nasir da yakan iya ganin me kiran Sannan ya kalli Nasir yana cewa . "Mutuniyar ka fa ke kira. Dan Allah ka bawa yarinyar fuska , wallahi tana san ka ." Nasir kawai yaja tsaki tare da jan bakinsa yayi shiru Hakan baisa Umar jin haushi ba , ya sake cewa dashi . "Yanzu dan Allah to sai yaushe ne za kai aure, dukkan abokanmu sun yi aure , amman kai ko a jikinka , bayan ga yarinyar nan Batula na son ka kamar zata mutu." A lokacin Nasir ya maida masa da cewa . "Ni fa duk wani aure baya gabana , kuma babu yarinyar da nasa gaba , kawai sai na aurar da Laila tukun ." Umar kawai ya yi ajiyar zuciya. Anan kuwa Fa'iza ce kwance kan gadon Fatima, yayin da Fatiman take gefe bisa gadon a zaune "Har yanzu dai kin ga Abdallah shiru ." Fatima tai maganar tana kallon Fa'iza, murmurshi na yake Fa'iza ta yi tare da kauda kanta gefe . A karo na biyu , Fatima ta sake bude baki cewa. "Ai na ce masa bani da wata kawar data wuce ki , domin kawancen mu ya koma 'yan uwan taka ." Murmurshi Fa'iza ta kuma yi , kafin ta ce . "To ni wallahi da baki kira ni ba , yaushe muka gaisa da Abdallan ? Ko sati biyu ba ai ba , da naje shopping na ganshi ." Fatima ta maida mata da cewa . "Amman shi ya ce kun dade baku hadu ba , yana son ku gaisa." Fa'iza ta ce . "Ai shi ke nan ." Lokacin ne wayar dake bisa hannun Fatima , ta fara ringin Hakan yasa ta yin murmurshi tana cewa. "Kin ga kiranshi , ya zo ke nan .". Tana karasa maganar ta dauki kiran . Bayan ta gama ne ta fita , yayin daba wani dadewa tai ba ta bugo wayar Fa'iza tare da sanar mata ..... Wani tsoro Fa'iza taji duk ya kamata , jikinta kuma duk ya mutu, haka ta tashi ta nufi babban harabar gidan su Fatima inda suke tare da Abdallah Dogo ne sosai kalar hutu, da gani yaron manya ne , duk da ba fari bane . Haka Fa'iza ta karasa gabansu tare da cewa. "Assalamualaikum masoyan juna ." Murmurshi Fatima ta yi , yayin da Abdallah ya amsa mata da cewa. "Wa'alaikis Salam aminiyar sarauniya ta." Ba tare da Fa'iza ta kalli fuskar Abdallah ba ta sake fad'in. "To ya kazo , ya kawar tawa." Wani murmurshi me kyau da jan hankalin Abdallah ya yi sannan ya maida mata da cewa. "Lafiya kalau Fa'iza, amman wato yadda alakarku take da fateema abin yana matukar burge ni , rayuwar ku abin birgewa." Dariya Fatima da Fa'iza sukai a tare da juna , kana Fatima ta maida masa da fadin. "Ai ni Fa'iza ta wuce komai a guri na , domin rikon amana da matukar mutunci, ta yadda ranta ya baci idan na wani zai yi fari , haka kuma ..." Fa'iza ce ta dakatar da ita da cewa. "A'a wannan ai kowa yasan halinki ne , ke mutuniyar kirki ce , ko rabin ki ban yi ba." Abdallah ya yi dariya cikin wani yanayi mai kyau , sannan ya kallesu yana fad'in. "Abin naku abin birgewa." Sannan Fa'iza ta kalli Fatima tana cewa. "Bari na shiga ciki, sai kin shigo , Abdallah sai anjuma." Su kai sallama sannan Fa'iza ta nufi cikin gidan. Allah-Allah Fa'iza take ta shiga ciki , domin ci take kamar kafafunta baza su dauketa ba , bayan ta karasa dakin Fatima, ta fada gado cikin wani yanayi ta rushe da kuka mai gwanin ban tausayi. Anan gidan Mama kam Tana zaune cikin falo suna kallo da Laila, Nasir ne rike da jakar office ya turo kofar falon. Bayan ya yi sallama ya sami daya daga cikin kujerun falon ya zauna. "Mama sannu da gida ." Nasir ya fada Mama ta maida masa da fad'in. "Sannu Nasir da hanya ." Kana Laila ta kalleshi tana cewa. "Uncle sannu da zuwa ." Ya maida mata da cewa. "Yawwa." Sannan ya maida hankali ga kallon da suke , lokaci guda kuma yana cewa. "Mama Allah ya sa dai ba tuwon kikai mana ba ." Mama ta ce . "Hmm." Ba tare data kara cewa dashi komai ba , bai damu da hakan ba ya kalli Laila yana cewa. "Yawwa ke Laila, wai mene hadinku da Mahmud ne , na ga kwana biyu abin bana gane masa ." Cikin mamaki Mama ta kalli Nasir tana cewa. "Kaji mini yaro , Kamar ya mene hadin su , ba d'an uwanta bane ." Kawai Laila ta kwashe da dariya mai cike da bayyana matukar kyanta Yadda Nasir ya ga tana dariyar ne yasa yaji farin cikin sa ya karu . Mama ce ta bude baki tare da cewa. "Ai kai ta zamanka , har Laila ta yi aure , kana nan a gida tunda abin ba ya damunka." "Hhhhhhhhhh. Mama ke nan ai bazan aure ba , sai na aurar da Laila, domin bazan bar rayuwar Laila ta shiga garari ba." Mama ta ce . "Ai shi ke nan , sai ka zauna har lokacin barina duniya ya yi , ban ga yayanka ba ." Dariya Nasir ya kuma yi yana fad'in. "A'a wallahi Mama babu inda zaki in sha Allah." Mama tai murmurshi tana cewa. "To zaka ci abincin ne ko zancen za kai ta yi." Nasir ya ce . "A'a Mama mu dai cigaba da zancen , domin tabbas sai me sa'a ce zata aure ni , kuma me sa'a ne zai auri Laila, Kuma idan na shigo gida na ganku tare da Laila sai naji duk damuwa ta ta tafi, shi ya sa Laila tunda ta ga ma secondary kawai ta zauna , domin bana so ta cigaba da karatu maza suna biyo mini kyakykyawa ta.".. "Dan Allah ka yi min shiru Nasir.". Mama ta fada Yayin da Laila ta kuma dariya . "Sai surutu kake yi
Chapter 3 · 0% Book details