Sashe 5
Mahaukacin So Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
kuka . "Kuka ki kai Fa'iza, mene ya faru ."? Fatima tai maganar tana fuskantar Fa'iza "A'a ba kuma nai ba Fatima." Fa'iza ta maida mata da amsa Murmurshi tare da ajiyar zuciya Fatima ta yi tana kuma cewa. "Wai ba kuka ki kai ba , dubi idanunki fa ." Fa'iza ta sunkuyar da kai kamar wata yarinya tana murmurshi. "Dan Allah me yake damunki Fa'iza, akwai abin da kike boye mini." Fatima ta fada tana rike hannun Fa'iza. Hakan ya karyawa Fa'iza zuciya, kawai ta fada kafadar Fatima tana kuka mai gwanin ban tausayi. "Ya Allah." Abin da Fatima ta fada ke nan cikin mutuwar jiki Cikin wannan kuka Fa'iza ta fara cewa. "Babu abin da yake damuna Fatima, kawai dai kwana biyu na kan yi kewar mommy, ta tafi ta barmu cikin damuwa, duk duniya bata min dadi Fatima, rashin mahaifiya babban abu ne." Fa'iza ta aje maganar tana shekar kuka. Murmurshi Fatima ta yi tare da d'ago Fa'iza daga kafarta tana cewa. "Haba kawata , rasuwar mommy ta girgiza mu , amman a halin yanzu adduar mu kawai take bukata. Dan Allah ki yi hakuri ki dena wannan kukan , Allah ya gafartawa mommy." Ta karasa maganar tana sharewa Fa'iza hawaye da hankicin dake hannunta Murmurshi Fa'iza tai tana cewa. "Haka ne Fatima na gode ." Fatima ta mika mata makullin motar dake hannunta tana cewa. "Yau ke zaki tuka mu , karbi ." Fa'iza ta amsa tana dariya. Nasir ne a tsaye bakin mota tare da Batula Batula tai murmurshi tana kallon masoyin nata tana cewa. "A gaskiya na yi matukar farin cikin ganinka a kofar gidan mu ." Yaya Nasir ya yi murmurshi yana cewa. "Batula ke nan , to idan banzo gunki ba , gurin wa zan zo , ke ce fa wacce nake burin aure , uwar yayana farin ciki na , kaf mata banga ta biyunki ba , wallahi Batula ina san ki ,so na gaskiya babu yaudara." Wani farin ciki ne ya lullube zuciyar Batula, wai yau Yaya Nasir ne ke mata wannan zance Cikin zabura Batula ta farka a baccin da take , sakamakon ruwan sanyi da taji an watsa mata . Tana ajiyar zuciya Batula ta farka , lokaci guda kuma tana kallon wacce ta watsa mata ruwan Ba wata babba bace domin Batulan ma ta girmeta . "Asararriya , har yanzu baki tashi kin yi wanke-wanke ba , to uban waye zai miki , wallahi kika bari na fadawa Daddy sai ranki ya baci ." Tana gama maganar ta fice Ajiyar zuciya Batula tai tana murmurshi da cewa. "Daman mafarki nake Nasir bai zo ba ." Tai ajiyar zuciya A lokacin Khairat ta shigo dakin tare da sallama Batula na ganin kawartata tai murmurshi ta ce . "Khairat ke ce."? Khairat tai murmurshi tana cewa. "Eh wallahi , zan biya gidansu Laila shi ne nace bari nazo mu gaisa." Ta karasa maganar tana kallon yadda duk jikinta ya jike da ruwa "Rahma ce ta watsa miki ruwa ko , ai naga fitarta da kofi." Batula tai murmurshi mai ciwo tana cewa. "Wata rana sai labari ai khairat, yanzu ina iyayena suke , haka kowa zai bar duniyar ai ." Tsaki khairat ta ja tana cewa. "Kullum haka ki ke cewa Batula, yanzu a ce kanin mahaifin ki wai bazai iya rike ki da mutunci ba , matarshi ta wulakanta ki yarshi ma haka , sannan shima bai barki ba ." Murmurshin nan me ciwo Batula ta sake yi kana ta kalli Khairat tana cewa. "Ai da babu abin da zan dana biki naje naga Nasir ko zan ji dadi ." Khairat tai dariya tana cewa. "Ke fa sai a hankali, yanzu ko islamiyya bakya zuwa , Yaya Nasir kuma Allah ya waiwayo da hankalinshi gare ki ." Batula ke nan yarinya me kalli da nutsuwa, duk da ba sa'arsu khairat ba ce , amman suna tare da juna cikin aminci, sakamakon haduwarsu a islamiyya Batula ta dade tana wahala a rayuwa, domin tunda Allah ya yi wa iyayenta rasuwa ta fara fuskantar rayuwa a gidan kanin mahaifin ta . Wanda komai wulakancin da suka debo kan ta suke zubeshi. Sai dai Allah ya jarafci Batula da san Yaya Nasir, domin babu abin dake faranta mata rai face ganin hotonsa ko wani jinin shi . Duk da cewa har yau yaki bata fuskar da zata nuna masa soyyayar da take masa . Ni ko nace Yaya Nasir a duba maraicin Batula mana Anan kuwa Yaya Nasir yanzu ya dawo daga aiki Tun kafin ya shiga gidan ya tabbatar wa da kansa tabbas sun yi baki , cikin far'a da sakin fuska ya nufi ciki, Duk da bai san wanne suka zo ba "Assalamualaikum." Nasir ya yi sallama cikin falon ya yin da yake raba idanu Rabi ya gani mahaifiyar Mahmud zaune a doguwar kujera, kana Laila tana kusa da ita , sai kuma Mahmud din a kusa da Laila wato dai duk kujera guda. Sannan Mama a gefe fuska cike da far'a "Wa'alaiku mussalam Nasir." Rabi ta amsa ita ma cikin far 'a Murmurshin yake Yaya Nasir ya yi , sannan ya samu kusa da Mama ya zauna yana cewa da Rabi . "Yau ku ne a gidan namu , sannunku da zuwa." Ya karasa maganar yana murmurshin da bai kai zuci ba "Ina wuni Yaya Nasir." Mahmud ya fada Sai da Yaya Nasir ya d'aga kai ya kalleshi sannan ya amsa masa Sannan ita ma Laila ta kalleshi tana cewa. "Sannu da dawowa Yaya." Ya d'aga mata kai , alamun ya amsa "Ina wuni Aunty Rabi." Nasir ke nan Rabi ta maida masa da fad'i. "Lafiya lau Nasir, ya gida ya aiki . Ya wajensu Ummi." "Lafiya lau suke ." Aunty Rabi ta maida masa da cewa . "To Masha Allah, ai Mahmud ne ya dameni , in zo in ga Laila, sai kace ban taba ganin ta ba ." Ta karasa maganar tana kallon Mahmud da cewa. "To mun zo hankali ya kwanta ." Dariya Mahmud ya yi tare da kallon Laila dake kusa dashi cikin matukar yanayin shaukin soyyaya. Duk a kan idon Yaya Nasir da ke murmurshin yake mai ciwo . "Ai in sha Allah Mahmud, Laila matarka ce." Yaya Nasir yaji maganar har cikin kansa yayin da Aunty Rabi ke fada "To Allah ya tabbatar da alheri, tuwo na mai na ke nan ." Mama ta fada cikin murna . Kawai da saurin gaske Yaya Nasir ya mike ya shige dakinsa Nan su kuwa suka cigaba da hirasu , yayin da Yaya Nasir ya kan iya jiyo su daga daki . Bayan Mahmud ya dau mahaifiyar tashi sun tafi.. Sannan Yaya Nasir ya fito falon ya zauna cikin matukar mutuwar jiki. "Uncle baka ci abinci ba har yanzu ." Laila ta fada tana kallon shi Kawai kau da kanshi yayi gefe ba tare da ya ce komai ba Laila ta kalli Mama, Mama kuwa bama tasan abin da ake ba , domin ta shagala da jan carbin dake hannunta "Uncle lafiya kuwa."? Laila ta sake masa shishshigi Agogon hannunshi ya kallah kana ya yi ajiyar zuciya. Kamar kuma bazai kalli Laila ba , sannan ya juyo gareta yana cewa. "Kina son yaron nan Mahmud." *MAHAUKACIN SO* Autar Marubuta ________________________________________ Babu editing Page 13 & 14 Ajiyar zuciya Laila ta yi , kana ta kalli Uncle din nata tana cewa. "Yaya ni ban za bawa kai na kowa ba , duk wanda ya dace dani daga gareka nake jiranshi." Murmurshi Yaya Nasir ya yi, sakamakon yadda yaji abin da bai yi zatonsa ba Kawai ya mayarmata da cewa. "Jeki kawon abincin." Anan kuwa Abdallah da Fatima ne cikin mota , suke tafe a hanyar zuwa gidansu Fa'iza "Gaskiya fa kina son Fa'iza da yawah." Abdallah ya yi maganar ga Fatima yana murmurshi Ita ma Fatima murmurshi tai tana cewa. "Eh wallahi, haka nima take sona Dear, wallahi rayuwar Fa'iza abin tausayi ne , zan yi komai dan farin cikinta." Murmurshi Abdallah yay yana sake cewa. "Hmm ai na gani , gashi zamu shopping kin ce a biya a daukota. Nima ai ina san abin da kike so ." Murmurshi Fatima tai tana kallon masoyin nata Yayin data duba fuskar wayarta tana duba wani sako da ya shigo mata . "Karki manta yau muna da ganin likita." Hawaye ne suka ciko mata idanu , ta kalli Abdallah tana cewa. "Ina matukar kaunar ka Abdallah." Abdallah ya juyo yana murmurshi yayin da take ganin wannan hawaye. Bai iya cewa da ita komai ba , domin ji yay baki da ya ta karya masa zuciya. Fatima tai murmurshi ta fice sa'ilin da ya yi parking daidai kofar gidansu Fa'iza Kallo ya yi ta binta dashi har ta shige ciki Kana yayi murmurshi da ajiyar zuciya yana cewa "Allah sarki baiwar Allah Fatima ta, kyakykyawa mai hankali, ya Allah ka bani ita a kaddarata." "Fa'iza tashi , tashi." Fatima tai maganar tana janye malullubin da Fa'iza ta lulluba . Ta tashi zaune tana cewa. "Kai Fatima na tashi to mene." Dariya Fatima tai tana cewa. "Ki fito , ina ta kiran wayarki, Abdallah ne a waje zai kaimu shopping." Wani faduwar gaba Fa'iza taji ya ziyarce ta dajin sunan Abdallah "Abdallah kuma." Fa'iza ta nanata "Ehh tashi-tashi-tashi." Ta fada tana jawota , kana tasa kai waje tana cewa. "Ki sauri ki fito muna waje." Yadda Fa'iza take a wannan tsayen kawai ajiyar zuciya tai , ba tare data motsa ba "Aminiyata ce Fatima, bani da kowa bayan ke , tabbas bazan rusa mana alaka ba Fatima ko zuciyata zata fashe." Ta karasa maganar tana jawo wata doguwar rigarta mai launin marun gami da yellow Cikin sauri ta fara shiryawa Domin zuwa ta same su a waje . Tana fita kofar gida ta fara hangensu daga cikin gilas din motar , sai farin ciki suke abinsu Murmurshi tai sannan cikin nutsuwa ta fara takawa wajensu Murfin motar baya dake a bude nan ta shiga tana cewa. "Soyyaya ruwan zuma." Abdallah ne ya juyo yana mata murmurshi kafin ya ce komai Fa'iza ta sake fad'i. "To ina zamu ne ." "Zamu je Abdallah ya siyo mana abayoyi ne Fa'iza." Fatima ta bata amsa murmurshi Abdallah ya yi kana daga karshe kawai