Sashe 8
Mahaukacin So Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
." Tasa kai Batula tai saurin riko rigar Rahma, hakan yasa Rahma ta dakata tana kallon ta cikin zafin rai "Uban me zan miki kika riken riga kazama kawai." Ba tare da Batula ta damu dajin wannan maganar ta Rahma ba ta fara cewa... *MAHAUKACIN SO* Autar Marubuta _______________________________________ Babu editing Page 19 & 20 "Kar ki fadawa Daddy, Musa kowa yasan ba ilmi ne dashi ba ." Rahma tasa hannu ta doke hannun Batula, taja tsaki sannan ta wuce Kawai hawaye Batula taji ya zubo mata Anan kuwa Alaji Sani ne yake yin waya ,yadda ranshi yake a turbune bai canza ba ya fara cewa. "Haba Akilu, to ita wannan yarinyar yar gidan waye, da zaka ce an nemeta a garin nan an rasa, bayan na fada maka ina tafiya a titin babbar unguwa ta taalakawa na ga yarinyar, sai da nai ta jira ko zanga inda ta shiga amman ban gani ba , gaskiya ka sake kokari Akilu ka zo min da labari mai dadi ." Yana gamawa ya aje ajiyar zuciya tare da cewa. "Gaskiya wannan yarinyar tamin , lokaci guda san ta ya kamani, tomm Hajjiya kishiya na tafe a gidan nan." Ya yi maganar shi kadai yana tunano yadda yadda ya ga wannan yarinyar, sai abin yake faranta masa rai . Sakamakon yau asabar babu inda Uncle yaje , tun wajejen hantsi yake a falo , har zuwa wannan lokacin da rana ta kusan faduwa. Idan har kasan Yaya Nasir, to yanzu idan ka ganshi zaka iya cewa ba shi bane. Duk da cewa shi ba mitum bane mai kiba , amman yana da matukar kyan gani Lokaci guda kuma yanzu duk yabi ya lalace , tunda Mama ta fara maganar auren Laila. Wayarshi tana gefe kusa dashi , yayin da shi kuwa yake kwance a kujera. Laila ce ta fito daga dakinta sanye da hijab ta karaso gabanshi "Uncle dan Allah me yake damunka , ko abinci har yanzu baka ci ba ." Uncle ya kauda kai gefe kamar bai ji maganar tata ba . "Uncle magana nake ." Kallonta ya yi cikin wani yanayi na isa yana cewa. "Tashi ki bani guri ." Ta kalleshi tana sunkuyar da kai da ajiyar zuciya Mikewa tai ta juya zata koma inda ta fito Taji muryar Uncle Nasir yana cewa. "Babu abin da yake damuna Laila." Hakan yasa ta juyo ta koma ta sake zama , Shima Yaya Nasir ganin ta zaune ne ya tashi zaune. "Uncle bani da kamarka a duniya, haifata ne kawai baka yi ba , idan nagan ka cikin wani yanayi bana jin dadi ko kadan , dan Allah Uncle idan a kan aure na ne ka dena damuwa, bazan auri kowa ba , sai wanda ka zaba mini koda bana san shi ." Nasir ya yi murmurshi mai ciwo , sann an ya ce . "Karki damu Laila, ina miki kaunar da bana son kowa ya rabe ki , amman akwai alamun lokaci zai raba mu ." Mama ce ita ma ta fito rike da carbi a hannunta ta samu guri ta zauna. Laila ta kalli Uncle cikin zumudi tana cewa "Yawwa Uncle, shi ne baka taba fadan komai a kan Batula ba ko." Wani dasss Yaya Nasir yaji ya dakar masa zuciya Ya kalli Mama da sauri Ba tare da Laila ta dubi yanayin da yake ciki ba , ta cigaba da cewa . "Gaskiya Uncle tana san ka , naji kuma an ce ko saurararta baka yi ." "Marainiya ce fa Uncle, wallahi tana shan wahala." Ajiyar zuciya Yaya Nasir ya sauke tare da cewa. "Nima ai maraya ne , sannan ke ma haka , babu wani soyyaya a tsakani da wannan yarinyar Batula, kin ga Laila ki dena maganar ta ." Kafin Laila ta bude baki tai magana Khairat ta turo kofa ta shigo tana sallama Abin da ya basu mamaki ganin Batula biye a bayanta "Wow Uncle, ka ga Aunty Batula 'yar halak." Laila ta fada ta tashi da gudu tana rungume Batula Yaya Nasir ajiyar zuciya yayi yana kauda kai gefe Mama cikin far a ta kallesu tana cewa "Auu wannan ne Batulan."? Mama ta aje maganar daidai da inda Batula ta zube gaban Mama tana gashsheta Nan Mama ta gaisa da Batula cikin sakin fuska, wanda hakan ya yiwa Batula dadi "Yaya Nasir ina wuni ."? Khairat ta fada bayan sun gaisa da Mama Ita kuwa Laila Sam bakinta ya kasa rufuwa , ta tsaya a kansu ta kasa zama "Ina wuni Yaya Nasir." Batula ta fada cikin sunkuyar da kai "Lafiya." Ya fada a takaice "Gaskiya Uncle kun dace sosai da juna .". Laila ke nan ta fada yayin da Yaya Nasir ya hade ransa Mama dariya ta yi kana ta mike tsaye tare da shiga ciki Kujerar da Mama ta tashi Laila ta zauna a hannunta tana magana cikin shauki "Ke khairat taso mu bar musu falon." Kafin khairat ta tashi Uncle ya mike zai fita "Uncle baku gaisa ba fa." Laila ta fada Dariya ya yi kamar me jin kunya kafin yace komai Khairat da Laila suka fita Kamar abin arziki Uncle ya koma ya zauna Hakan yasa Batula ta d'ago kai tana cewa. "Kayi hakuri Yaya Nasir , na zo ban sanar da kai ba , wallai ina cikin damuwa kala-kala , ganin ka ne zaisa naji sauki , shi yasa nazo tunda baka iya zuwa inda nake ." Wani takaici Yaya Nasir yaji ya turke masa zuciya Ya kalleta cikin zafi yana cewa "Ki dena yaudarar kan ki Batula, babu wani soyyaya tsakanin mu , babu yarinyar da nake so , hasalima bansan ya ake jin soyyaya ba , ya kamata ki sani bana san ki , kar kuma ki kuma zuwa inda nake babu abin da zaisa na soki har na aure ki ." Ya tashi ya fita Ajiyar zuciya mai zafi Batula ta sauke Gaff da kuka , zuciyar ta na mata zafi Lokacin Khairat da Laila suka shigo Wani murmurshi na yake sosai Batula ta jefa musu "Har an gama soyyayar Aunty."? Cewar Laila cikin tsokana Baki khairat ta tabe tana cewa. "Ki dubi wannan fuskar tata kice wani an sha soyayya. Laila Yaya Nasir fa baya san Batula maganar gaskiya ke nan ." Murmurshi Batula tai duk da bata ji dadin maganar ba "Inji waye , shi kuwa yake sona , ina kaunar Yaya Nasir Laila, kaunar da bansan daga ina take zubowa ba." Ta aje maganar tana rike hannun Laila fuska da hawaye Zafi Laila taji a zuciyar ta , ta kankame hannun Batula tana cewa. "Uncle mijinki ne Aunty Batula kar ki damu dan Allah." Murmurshi Batula tai tana cewa. "Allah ya sa ." Matukar tausayin Batula ya sake rufe Laila "Kira Mama mi sallama mu tafi." Khairat ta fada tana mikewa tsaye. Fatima ce ta fito daga wanka , gama sa kayanta ke nan , Fa'iza ta shigo tana cewa. "Wai dan Allah tun yanzu zaki tafi , ki bari sai anjuma mana ." Harara Fatima ta jefa mata yayin da take sanya man lebe ta ce da Fa'iza. "Ai dole ki fadi haka , tunda kwanan da nayi ma bai miki ba ,ke fa Fa'iza sau daya kika taba kwana a gidanmu." Ajiyar zuciya Fa'iza tai kafin ta ce . "To ai naga nan da can din duk daya ne , amman ina nan zan zo na kwana karki damu ." Fatima tai shiru yayin da take kallon babban madubin dakin tana kallon irin yadda tai kyau Yadda Fa'iza ta lura da ita ne yasa tai murmurshi tana cewa. "Wayyo kyau , ka ga amaryar Abdallah, gaskiya baby kin yi kyau ." Dariya Fatima ta sake yi tana cewa. "Wato dan ki wayantar da zancen da muke ko , ai shikenan." Fa'iza mikewa tsaye tai tana rike hannun Fatima cikin kauna ta fara cewa. "A"a Rabin Raina Fatima, babu abin da yake damuna, to idan ina tare dake mene zai dame ni , bari ma gashi kullum kina samun lafiya, ai wannan kadai ya isa ." Murmurshi Fatima tai tana fad'in "Alhamdulillah, to tunda haka ne gaskiya kawai ki shirya Abdallah ya aure mu tare domin ban shirya rashin ki ba ." Cikin sauri da firgita Fa'iza ta saki hannun Fatima lokaci guda kuma ta fara dariyar da Fatima bata gane ba . "Haba dai , ai ni Abdallah ya min kauyenci , sai dai ke shalelen babanta." Cikin tsokana ta aje maganar Dariya kawai Fatima tai , ba tare da tace komai ba ta dauki Jakarta ta rataya.. Dariya Fatima ta juyo tana yi , "Jiya na tashi sallah da dare ina ta tashin ki baki tashi ba ." Fatima tai maganar tana sanya agogo a hannunta "Hmmm , wallahi Fatima kawai bacci ne yaja ni , kuma kaina sai ciwo ." Fa'iza ta mayar mata Da sauri fateema ta fara cewa. "Daman haka zancen yake ai, kullum ciwon kai , saboda kina da damuwa baza ki fadan ba ." Fa'iza ta ce . "Hmmm". *MAHAUKACIN SO* Autar Marubuta ________________________________________ Babu editing Page 21 & 22 Baiwar Allah kamar kullum, yanzu ma wanke wanke take yi , Allah Allah take ta gama ta yi shirin zuwa islamiyya Jin muryar Rahma tai a bayanta tana cewa. "Ke kizo daddy yana kira." Ta juya ta koma ciki Da sauri Batula ta mike tana share hannunta ta nufi inda suke zaune suna kallo Sallama ta fara yi kafin ta shiga ciki Duk da babu wanda ya amsa ta nufi kusa da mahaifin Rahma ta zauna tana sunkuyar da kai . Kamar saukar aradu ta ji yana cewa. "Wannan yaron Musa, ya zo neman auren ki , kuma daman yanzu Rahma take fadan kina san shi ." Da sauri da tashin hankali Batula ta d'ago kai tana kallon shi "Daddy ba haka bane , kasan Musa ko asalinsa ba a sani ba kuma .." "Ke rufe min baki ." Baban Rahma ya fada "Ke da zaki farin ciki kin samu miji , kina ganin ko ita Rahma bata sami irin shi ba ." Kuka Batula ta fashe dashi tana fad'in "Wallahi Daddy bana san shi ." "Tashi ki tafi ki bani guri , ni nasan abin da ya dace ." Baban Rahma ya fada ,