Sashe 7
Mahaukacin So Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
. "Haka ne." Anan ma Alaji Sani Shanshani ne zaune cikin wani furgitaccen had'ad'd'en falo. A gaskiya ciki da wajen wannan gida ya matukar haduwa ba a magana. Gefe guda kuma ga wata Hajjiya can da gani babu tambaya matarshi ce Sannan wasu 'yan mata su biyu masu kama da juna , suma zaune a kujera kowacce tana danna wayarta Sallamar dansu ce ta sa suka kalli kofar shigowa falon Yayin da hajjiyan ta amsa sallamar "Usman ina aka je ne."? Mahaifiyar shi Hajjiya ta masa tambayar Yana sosa keya ya karaso ya zauna yana fuskantar mahaifin sa Murmurshi mahaifin nasa ya yi yana fad'in. " Lafiya kuwa, meke tafe da kai ."? Satar kallon Hajjiya Usman ya yi sannan ya dukar da kai kasa lokaci guda kuma yana sosa keya "Daddy a kan maganar Laila ne." Murmurshi gami da dariya Alaji Sani Shanshani ya yi Sannan ya kalli matarshi yana fad'in. "Ai ni nasan akwai magana." Sannan ya koma ya kalli Usman yana fad'in. "Ai Usman a matsayin ku na 'ya'yana , bazan gaza muku a kan komai ba, tun daga lokacin da kowannen ku ya fara numfashinsa na farko a wannan duniyar, idan akwai wanda ya nemi abu daga gare ni ya rasa ya sanar dani." Ya kalli sauran yayan nasa Sannan ya cigaba da cewa . "In sha Allah zaka aure ta , bari daman ita ce sanadin shiryuwar ka , ai alhamdulillah." Su kai dariya Yayin da hajjiya ke cewa. "Sai a kawo mana ita mu ganta , domin kullum kiran sunan ta ake tun kana America." Usman ya yi dariya da cewa. "Za ta zo kuwa mommy." Anan gurin aikin Nasir kuwa. Tashinsa ke nan ya shiga mota da nufin tafiya gida Muryar kanin mahaifin sa Alhaji Bashir yaji tana kiran sunan shi Da sauri ya fito daga cikin motar zuwa waje , yayin da ya durkusa yana gaida Alaji Bashir. "Wai meke damunka ne Nasir, duk ka rame haka , ko akwai wata damuwar a gida ne ban sani ba."? Alhaji Bashir ya yi maganar cikin saurin baki kamar yadda ya saba . *MAHAUKACIN SO* Autar Marubuta ________________________________________ Babu editing Page 17 & 18 Murmurshi Yaya Nasir ya yi , kana cikin girmamawa ya fara cewa. "Wallahi babu komai , komai lafiya lau." Alaji Bashir ya ce . "To ai shi ke nan Allah ya rufa asiri , ka gaida Maman." Yana gama maganar ya juya cikin bugaggiyar shaddarshi da malum-malum ya koma ciki Yayin da Yaya Nasir yake cewa. "Zata ji in sha Allah." Sannan Yaya Nasir ya sami damar shigewa mota . Anan kuwa Mama ce zaune ita da Laila, gama cin abincin su ke nan , domin ko kwanukan basu kwashe ba , wani ma da sauran abinci a ciki Laila wayarta ta aje gefe , ta kalli Mama tana cewa. "Mama Uncle ya taba baki labarin Batula."? Mama ta maida mata da cewa. "Wace kuma Batula." Laila tai murmurshi sannan ta ce . "Mama budurwar Uncle ce , tana son Uncle sosai , wallahi Mama rayuwar ta abin tausayi sosai , iyayenta duk sun rasu tana shan wahala." Mama ta maida mata da fad'i. "Allah sarki." A lokacin Nasir ya bankado labulai ya shigo tare da sallama Kusa da Mama yaje ya zauna a kujera yana ajiyar zuciya Ido suka hada da Laila, hakan yasa ta ce dashi . "Sannu da zuwa Uncle." Ya ce . "Sannunki ke ma ." Ido suka sake hadawa a karo na biyu, Laila tai murmurshi tana sunkuyar da kai "Uncle kana lafiya kuwa."? Laila ta tambaya "Duk ka rame sosai ." Murmurshin ciwo Uncle ya yi , sannan ya ce . "Alaji Sani Shanshani jiya da kanshi ya zo a kan maganar auren ku da Usman." Laila ta zaro idanu cikin mamaki Kafin ta ce komai Uncle ya cigaba da cewa. "Amman bazan bari ki auri Usman ba bai dace dake ba Laila." Laila ta sunkuyar da kai Mama ce ta mike tsaye cikin bacin rai tana cewa. "Nasir wannan abin ya ishe ni , lokaci ya yi da zaka bawa Laila miji ko ka barta ta zaba, tunda ka nuna mana kafi kowa iko da ita . Domin bazan zuba ido yadda kaki aure ba , ka zaunar da Laila ita ma a cikin gida, abin ya isa haka ." Wani furgitaccen zafi Yaya Nasir yaji a zuciyarshi , domin ya lura da batun Mama babu wasa a ciki "Ko Usman ko Mahmud, duk wanda Laila take so , ka aura mata, wannan abin ya isa haka tom." Ta shige daki Cikin yanayin damuwa Laila ta kalli Nasir, babban tashin hankalin data gani yasa duk tunanin ta ya rude Hawaye ta gani bisa idanun Uncle sun zaru suna shirin zubo . Kawai ya mike ya fita kafin a kai ga wannan lokacin Ajiyar zuciya ita ma Laila ta sauke me zafi tana kallon kofar da Uncle din nata ya fice , duk ta rasa me yasa ta damu yanzu haka , kuma tausayin Uncle duk ya kamata. Yaya Nasir ya na fita gidan Umar ya nufa kai tsaye . Shima Umar ya yi mamakin ganin Uncle a wannan lokacin da bai saba zuwa ba Babu korafi Umar ya masa iso har falo suka zauna. Shi kan shi Umar ya fuskanci Yaya Nasir yana cikin damuwa "Abokina lafiya, tunda ka zauna kai shiru , ko wani abun yana faruwa ne ."? Yaya Nasir ya kauda kai tare da ajiyar zuciya "Hmmm." Abin da Umar ya iya fada ke nan Hakan yasa Yaya Nasir ya kalli Umar ya fara cewa. "Mama ce ." "So take na aurar da Laila." Murmurshi Umar ya yi yana fad'in. "Laaa kaji wani zance me dadin ji , alhamdulillah Masha Allah, ai Mama wannan abin da tai shi ne daidai , domin baka da niyyar aurar da ita ." Cikin sauri da mamaki Yaya Nasir ya kalli Umar dake kusa dashi Cikin farin ciki Umar ya sake jaddada masa da cewa. "Wallahi wannan ya yi , a cikin Mahmud da Usman, nasan Laila zata so daya ." Da sauri Yaya Nasir ya mike tsaye tare da wata ajiyar zuciya Idanunsa suka canza kala "Wallahi Umar bana son aurar da Laila ga kowa, idan naji ko naga wani na binta da sunan soyayya sai naji duk na tsane shi , bana son rabuwa da Laila Umar, ban shiryawa hakan ba." Ya karasa maganar yana rike rigar Umar kamar mai shirin zarewa. Tsoro ne ya rufe Umar da ganin yadda Nasir yake . Kawai Nasir ya yi murmurshi ya sake shi sannan ya kama hanyar fita ba tare da yace komai ba "Ikon Allah." Umar ya fada yana bin sa da kallo Bayansu Fatima sun fito daga lecture, kawayenta sai matukar farin ciki suke da jin yadda aka sanya bikinsu da Abdallah Fa'iza tana cikin class a zaune, domin tunda aka fita bata fita ba , ko zuwa duba Fatima ba tai ba ko sun fito Durkusar da kai tayi bisa benci Babu kowa cikin ajin , daga ita sai wani dalubi da yake karatu a can bayan benci Wata me suna Maryam ce ta shigo ajin yayin da take kallon wannan dalubi da cewa. "Munaf. Sannu da kokari." Ya amsa mata da "sannu Maryam." Kai tsaye gun Fa'iza ta nufa , yayin da take kiran sunanta tana kuma kokarin d'ago mata kanta sama Cikin jajayen idanu Fa'iza ta d'ago "Maryam ya akai ." Maryam cikin rike haba ta fara fad'i. "Haba Fa'iza, wai meke damunki, duk sai ramewa kike yi , haba dan Allah mene ne ."? "Babu abin dake damuna Maryam." Fa'iza ta maida mata da amsa Ba tare da jira ba Maryam ta sake maida mata da cewa. "Gashi idanunki sun yi jah , alamun kin yi kuka , ai shi ke nan , idan tayi wari maji ." Dariyar da bata kai zuciya ba Fa'iza ta yi Sannan ta ce . "Ina Fatima."? "Fatima tana can tana ta nemanki fa , bata san baki fito ba ."..... Fatima ce zaune kan gado tana kallon hotonta dana Fa'iza Murmurshi tai tana shafa furkar Fa'iza, sannan ta fara cewa. "Ban san meke damunki ba , wani abu ya dade yana damunki amman kin ki sanar dani ." Zama ta gyara tana sake zumin din hoton ta cigaba da cewa. "Aminiyata har a aljanna, ina kaunarki Fa'iza, in sha Allah zan yi kokarin sanin meke damunki, tun da baza ki sanar dani ba ." Ta karasa maganar tana kallon saman dakinta kamar me yin wani Nazari . "Wannan wanne irin rashin mutunci ne da cin fuska , yanzu yarinyar nan Laila kina ji wai yaron gidan Alaji Sani Shanshani zasu bawa." Inna tai maganar bisa wayar dake hannunta ta kara a kunne "Mene ne Alhaji Sani yafi mijin Rabi ? Tsabar cin mutunci, to wallahi wannan lamarin ba a a yi shi ba ." Daga can bangaren Bahijja cikin muryar girmamawa ta fara cewa da mahaifiyar tata "Dan Allah Inna ki yi hakuri abi wannan lamarin a sannu , yanzu haka ma ba haka zancen yake ba ." Cikin wannan fada dai Inna ta sake fadin "Kamar ya ba haka zancen yake ba , wallahi naje gidan naci mutuncin Nasir din , tunda ba shi data ido ." Bahijja ta sake fad'in "Ni dai dan Allah Inna ki hakuri, karki je gun Nasir da wannan maganar." Inna ta ja dogon tsaki tare da kashe wayar tata Anan kuwa Batula ce ke girki ta kunna wayarta Tana sauraran wakar hamisu breaker mai taken "So Ne." "Banza jaka kin damu mutane da waka." Juyowa Batula tai tana kallon Rahma dake fada mata wannan maganar Batula kashe sautin ta yi kana ta cigaba da abin dake gabanta "Ai wallahi bari daddy ya dawo , zan fada masa Musa me gyaran takalmi yana son ki gara kawai a aura masa ke mu huta ." Da sauri da tashin hankali Batula ta kalli Rahma tana cewa. "A'a dan Allah Rahma, karki fadawa Daddy wannan maganar, Musa ba san shi nake ba , kuma daddy zai kama zancen ki ." Cikin maraici Batula ta karasa maganar "Hhhhhhhhhh to ai taimakon ki zai , banda shi waye yake son ki , can zaki talauci ya kashe ki banza