← Book details Mahaukacin So Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 2 OF 13

Sashe 2

Mahaukacin So Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

ya karbi Laila a hannun Ummi, yayin da wasu hawaye suka zubo masa . Har dare yayi Nasir yana cikin takaicin gobe ta yi . Domin duk wata mafita ya duba domin ganin an bar masu Laila a gidan amman ya rasa yadda zai yi . Haka da dare ya yi Ummi da Mama suka shige daki da Laila suka kwanta , shi kuwa Nasir yana falo zaune ko abinci ya kasa ci . Washe gari da safe Wajejen hantsi Inna na zaune tana hutawa tana tunanin yau za a kawo mata jikarta Anan kuwa Ummi tunda Allah ya sa ta kula cewa Laila bata nan hankalinta ya tashi , ta duba duk gidan amman bata ga Laila da Nasir ba Hakan ya sa ta tashi Mama a bacci take fada mata Nan ita ma hankalinta ya tashi matuka "To kira shi a waya mana , ko ya tafi kai musu ita ." Mama ta fada Ummi ta ce . "Wallahi Mama wayarshi a kashe tun d'azu." Mama tai ajiyar zuciya tare da fadin "Oh ni Nasir ina ka shiga ." Ta fita ta nufi dakinsa, koda Mama ta kula da yanayin dakin sai ta ga kamar Nasir ya debe kayansa Da sauri ta koma dakin su ta duba kayan Laila, ta ga riga guda biyu ce kawai a cikin akwatitinta "Innalillahi Ummi ba dai Nasir guduwa ya yi da yarinyar nan ba ." Ummi taji gabanta ya fadi , ta kalli Mama da cewa ."kamar ya Mama me kika gani wai ." Cikin tashin hankalin nan Mama ta kara mata da cewa . "Na duba dakinsa kayanshi basa nan , kuma dubi kayan Laila." Cikin faduwar gaba Ummi ta sa hannu cikin akwatin ta ga rigunan Laila guda biyu sai wata takarda da akai rubutu da fensir a ciki . Da sauri ta dauki takardar tana zaro ido tana kallon Mama "Shi ne ya aje takardar ko , karanta muji ." Ummi cikin jin tsoron abin dake cikin takardar ta zura mata ido da nufin fara karanta wa . "Mama ku yafe ni , ni na tafi da Laila, sai wata rana karku neme ni , kar kuma ku d'aga hankalinku , idan da rabo zamu gana watarana babata . Sako daga Nasir." Abin da Ummi ta karantowa Mama ke nan Mama hannayenta guda biyu ta dora a kai cikin tashin hankali tana cewa. "Innalillahi wa inna'laihir raji un. Yanzu abin da Nasir zai mana ke nan , wannan wanne irin mahaukacin yaro ne . Innalillahi wa inna'laihir raji un." Mama ta sauke hannayen kasa tare da zama a bakin gado cikin wani yanayi Dogon numfashi Ummi taja , sannan ta aje shi cikin matukar takaici da tunanin irin abin da Nasir ya aikata musu "Yanzu ni me zance zanin aro ya bata ." Mama ta fada tare da fara kuka Ummi ta durkusar da gwiwowinta kasa a gaban Mama , sannan ta dafa kafar mahaifiyar tasu cikin rarrashi ta fara magana. "Dan Allah Mama ki dena wannan kukan , in sha Allah duk inda Yaya Nasir ya je da Laila zasu dawo." Cikin sabon kukan takaici Mama ta ce . "Yi shiru Ummi kar zuciya ta buga , yanzu ina zansa rai na idan wannan zancen ya fita." Ummi ta durkusar da kai kasa , yayin da wasu hawaye suka gangaro mata , domin tasan tabbas abin da Nasir ya yi ba abin da kuda zai bi bane , dole Mama ta shiga tashin hankali. Har wajejen 12 na rana , su Mama suna cikin wannan tashin hankali, duk sun kira wasu daga cikin 'yan uwa , da suke tunanin Nasir zai je amman babu labari. Anan ita ma Inna sai mita take yi, har Bahijja ta gaji da ji "To yanzu dan Allah Inna yaushe garin ya waye , ai tunda suka ce zasu kawota , zasu zo ai ." Inna ta maida mata da cewa . "Shiru kike ji makad'i ya fad'a rijiya ai , gaskiya abin ya ishe ni haka ." Bahijja tai ajiyar zuciya tare da gyara zaman yaron dake kafarta mai kimanin shekaru biyar da haihuwa A lokacin wata 'yar Innan ita ma ta shigo gidan me suna Rabi . Yaron mai suna Mahmud ya tashi daga kafar Ummi da gudu ya nufi Rabi , ita kuma tasa hannu ta dauke dan nata sama . Murmurshi Bahijja tai tana cewa. "Lallai Mahmud ka kyauta ." Mahaifiyar Mahmud ta ce . "To kinga lefinshi , dan gatan babanshi .". Ta karasa maganar tana kallon Inna da cewa . "Inna har yanzu basu zo ba ne ."? Inna ta dauke kanta , dariya ce taso kama Bahijja, domin wani abin idan Inna tai yana matukar bata dariya . Kallon Inna tai tana cewa. "Inna ke fa kina da jikoki , da zaki bar musu Laila, kinga Mama bata dasu ." Kawai Inna ta fashe da kuka tare da face majina da gefen zaninta tana cewa. "Allah ya jikanki Batula , Allah ya miki rahma , saboda ita nake son rike wannan jaririyar. Allah ya jikanki Batula." Duk sai jikinsu ya yi sanyi , yadda suka tuna 'yar uwar su . Bayan sallar magari ba Mama ta dukufa da addu'a , Domin har yanzu babu labarin Nasir Bayan Mama ta idar da adduarta, ta kalli Ummi da ke gefe ta yi tagumi ta ce . "Kira kanin mahaifin ku Alaji Bashir, kiji wanne hali ake ciki ." Cikin mutuwar jiki Ummi ta nufi daki domin dauko waya . Washe gari "Zancen banza , zancen wofi , kamar ya Nasir ya bata tare da Laila."? Inna tai maganar cikin masifa , Bahijja dai tai shiru , hakan ya sake ingiza Inna tana cewa. "Ai zancen duniya ba ya buya , tun jiya abin ya faru amman baza su iya sanar damu ba , Allah wadaran sirikai irin wannan wallahi Aikin banza aikin wofi ." Ta sake kallon Bahijja da ita ma abin ke dukanta tana cewa. "To yanzu wanne hali ake ciki , shi kanin baban nasu Bashir me ya yi akai ."? *MAHAUKACIN SO* Na Autar Marubuta *AUTAR MARUBUTA CE* __________ _________ __________ _________ _Faduwar wani tashin wani_ _Yau ake yi, gobe sai labarin_ _Burina Rayuwata, rubutuna dan masoyana_ _Cikawa da imani fatana_ <><>< ><><><> <><><> <><><><> <><><><><> ________________________________________ Babu editing Page 5 & 6 A daren yau ma kuka Mama take ta yi , carbinta na hannunta Ummi ce take rarrashin ta da cewa . "Mama ki yi hakuri dan Allah, kinji abin da malamai suka ce , suna cikin koshin lafiya , kuma kin san Baba Bashir zai cigaba da kokarin ganin Nasir ya dawo , ki dena kuka ." Mama cikin wannan kukan ta ce . "Ki bari kawai Ummi , Nasir ya yi abin kunya , kiji irin maganganun da mutane suke yi , ba kuma sa duba cewa Nasir kanin mahaifin Laila ne , amman wasu har cewa suke yankan kai zai shiga da ita , wannan wacce irin masifa ce ." Ta sake fashewa da kuka . Bayan wata daya Anan cikin wani babban gida kuwa , Alhaji Usman ne zaune a falonsa yana wasa da wata yarinya me kimanin shekaru biyu, yarinyar kuwa sai dariya take ta yi abinta A lokacin matarshi ta shigo tana murmurshi da cewa. "Alaji ke nan fatiman ce dai sai wasa ake da ita , kamar baza ka fita office ba ." Dariya ya yi yana daukar yarinyar bisa kafarsa yana cewa. "Wato Hajjiya wannan yarinyar tamu Fatima , tafi min komai , idan ina tare da ita duk wata damuwa mancewa nake da ita ." Hajjiya ta ce . "Hmm Alaji ke nan ." Alaji Usman ya sake fadin . "Allah dai ya raya mana ita , ta taso cikin daula da rikon amana da sanin ya kamata." Ta ce . "Ameen ya Allah, kamar dai halin babanta." Alaji ya yi dariya. Inna ce nan zaune a cikin daki , Bahijja ce ta shigo sanye da kayan makaranta . Zama ta yi kusa da Inna tana cewa . "Wash Allah na gaji Inna." Inna ta kalleta da cewa . "Ai ana rana , amman yau kun taso da wuri ." Bahijja ta ce . "Wai Inna mancewa ki kai muna jarabawar fita ne ." Inna tai dariya ta ce . "Au haka ne fa , to Allah ya taimako." Bahijja ta ce . "Ameen Innarmu , daman yau ina son naje gidan Aunty Rabi ." "To ai shikenan Allah ya kaimu." Cewar Inna Sannan ta kara da fad'in "Ohhh ni duniya, har yanzu babu labarin Nasir ko."? Bahijja ta ce . "Ummmm Inna ke nan ." Inna ta rufe da cewa . "To Allah ya kyauta, abin ya wuce yadda muke tunani.". Bayan shekaru biyu biyu Mama ce a zaune a tsakar gida tare da carbi a hannunta, ta kalli Ummi dake gefenta ke danna waya tana cewa. "Wallahi babu abin da zancewa kanin mahaifin ku Alaji Bashir, sai fatan alheri. Ki dubi irin wannan kayan dakin da ya yi miki , wallahi sai dai godiya , ai da wani ne bazai yi ba ." Ummi ta kalli Mama ta ce . "Uhmmm! Haka ne Mama. Ya rike mu da gaske , sai dai mi fatan Allah ya bamu ikon biyanshi ." Mama ta ce . "Haka ne , Allah ya bada lada , sauran kwana goma fa , kamar yau aka sa bikin nan ." Ummi ta sunkuyar da kai tana murmurshi, yayin da Mama take sake cewa . "Ga Bahijja yanzu ta kusan shekara a dakin mijinta ." Ummi ta ce . "Haka ne ." Anan gidan Alaji Usman kuwa Shi ne tsaye a cikin falo , yana bude murya yana cewa da matarshi . "Wai haryanzu baki shirya fatiman ba ne , na ga alamun kina son na makara ." A lokacin matarshi ta fito rike da hannun Fatima wacce aka shirya tsaf da kayan makaranta tana cewa. "A yi hakuri mana Alhaji, ai gamu mun fito ." Ya rike hannun yarinyar tasu ya yi waje , yayin da yarinyar ke kallon mahaifiyar tata tana cewa. "Bye-bye mommy.".. ...... Bayan wasu shekaru Kasaitacciyar budurwa ce kwance kan gadonta tana hutawa, domin ko alamun bacci babu a tare da ita .
Chapter 2 · 0% Book details