Sashe 10
Mahaukacin So Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
rame kuwa Nasir,duk ka lalace jijiyoyi ta koina haba Nasir meke damunka ne ." Yaya Nasir ya yi murmurshi sannan ya ce ."Mama ta ke nan , babu abin dake damuna, bari naje na dauki Umar mu tafi office." Yasa kai yana murmurshi Bayan Yaya Nasir ya isa gidan Umar, Umar ya fito suka tafi , sakamakon motarshi na wajen gyara . Suna tafiya cikin mota , Umar bai iya cewa da Nasir komai ba , domin kawai tunanin irin maganar da yaji yayi yake yi , "Shin wai gaske ne ko dai bai ji daidai ba , ta ya Nasir zaka ce kana son Laila." Umar yake maganar cikin ransa yayin da take kallon Nasir ta gefe . "Umar kana lafiya kuwa. Tunda muka fito kayi shiru ."? Yaya Nasir ya fada yana kallon shi . Murmurshi kawai Umar yayi , kafin ya ce . "Ai kai za a tambaya Nasir, duk ka rame ka lalace, kamar wanda cuta ke cinsa ." Duk yanayin fuskar Uncle ta canza , ya kalli Umar, sannan ya maida hankali ga tuki yana cewa. "Lokaci ya yi da zaku san Laila rayuwa ta ce , duk da cewa kaji na fada shekaran jiya, kar kai tunanin ba na cikin hayyacina." Umar ya ji gabanshi ya sake faduwa da sake jin maimaicin wannan babbar zugar maganar daga Nasir. "Wai dan Allah Nasir kan ka daya kuwa , magana ake ta Laila kai ne ubanta , babu aure a tsakaninku, dan girman Allah kai shiru da wannan maganar, idan kuma wasa kake ka dena kar zuciya ta , ta buga . Wannan zancen kasan girmansa kuwa."? Da babban tashin hankali Umar ya masa maganar. Yaya Nasir ya aje ajiyar zuciya sannan ya ce . "Babu aure ka ce tsakani da Laila, tabbas ina son Laila Umar, Kuma wannan zancen dole ya fita waje, domin Laila tare zamu kasance." Hadiyar yawu Umar ya yi yana cewa. "Innalillahi wa inna'laihir raji un. " Tafiyar dactor ke nan ya gama duba lafiyar Fatima, sakamakon yadda bata jin dadi , Alaji Usman duk yabi ya tashi hankalinsa Fatima na zaune tare da mahaifin ta , sai ga Fa'iza ta fito daga dakin Fatima sanye da Jakarta a hannu . "Ba dai tafiya zaki ba , bayan mun yi dake anan zaki kwana , Kuma kin sanar a gida ." Fatima tai maganar tana kallon ta . Kawai Fa'iza tai dariya tare da juyawa tana cewa. "Daman so nake naji bakinki." Dariya Alaji yayi sannan Fatima ta tai saurin dakatar da Fa'iza da cewa . "Fa'iza ko zaki shiryawa Abdallah wani abin , ya ce mini zai zo yau ." Fa'iza ta juyo tare da cewa. "To ranki ya dade." Fatima tai murmurshi. Fa'iza na komawa dakin ta aje jakar tare da murmurshi tana cewa. "Fatima ke nan . Abdallah manya Allah ya kawo ka ." Matukar tashin hankali Umar yake ciki ,domin samm ya kasa fahimtar wannan zancen na Nasir baki daya , Idan yayi tunanin abin da yasa Nasir yake ramewa ke nan , Kuma yaki bawa Laila kowa ta aura, sai ya ga kamar gaske son Laila ya ke kuwa Amman Umar sai yayi tunani sosai , sannan ya koma ya tuba , domin lamarin tabbas ya yi muni sosai . *MAHAUKACIN SO* Autar Marubuta ________________________________________ Babu editing Page 25 & 26 Khairat da Batula ne a zaune, bayan Batula ta gama zayyanawa khairat tarin damuwa da yadda sukai da Alaji mahaifin Rahma. "Amman gaskiya Batula wannan lamarin babba ne , yanzu ta ya har Uncle zai yadda da aureki , cikin kwana uku har yazo gidan ku , Tabb." Khairat ta fada cikin gano matukar wahalar abin . Batula ta amsa da cewa. "Haka ne khairat, wallahi sai yanzu nima hankali na ya tashi, amman ya zanyi idan Musa shi ne kaddara ta ." Ta aje maganar tana kuka , duk sai zuciyar khairat ita ma tai sanyi , amman haka ta fara rarrashin ta , duk da ita ma khairat bata da wani kwarin gwiwa. "Assalamualaikum." Laila ta shigo dakin kharait tare da sallama Ita ta amsa sallamar ciki murya mara wadatuwar kuzari "Ahh me zan gani haka , Aunty Batula mene ya faru kike kuka kuma." Laila tai maganar tana durkusawa a gabansu. "Mutuwa aka yi ne khairat."? Laila ta sake fada. Sai da khairat tai murmurshi sannan ta ce . "Babu wata mutuwa, maganar auren ta ne, yayan babanta yace ta fito da miji kwana uku ko ya aura mata Musa, kuma kinsan Yaya Nasir take so . Sai kuma sauran matsaloli da baza a rasa ba ." Cikin rarrashi Laila ta fara cewa. "Haba Aunty Batula, dan Allah ki dena kuka , kuma in sha Allah da ikon Allah zaki auri Uncle dina , wallahi Aunty Batula zan yi duk yadda zan domin ki aure shi ." Murmurshin farin ciki Batula tai tana cewa. "Wallahi da burina ya cika Laila, da kuwa dukkan bakin cikina ya yaye." Laila ta ce . "Karki damu anuty." Murmurshin jin dadi ita ma khairat tai sannan ta fara cewa. "Ka ga yar gidan Uncle, daga ina haka ." Laila ta ce . "Hmmm daga gidan su Sadiya , kinsan yau ne Usman zai zo muje gidansu." Dariya khairat tai tana cewa. "Eh wannan gaskiya ne kuwa , ka ga amaryar Usman, sirikar Alaji Sani Shanshani." Duk suka kwashe da dariya. Sannan khairat ta sake kallon Batula tare da cewa. "To ya maganar jarin ya baki baban Rahman." Baki Batula ta tabe tana cewa. "Tab! Ni na ce ma ko a kudin gadona ne ya bani , amman yaki, bazai banba , bai bani da cikakken hankali, kuma wallahi ina son bude shagon atamfofi da takalma ko salun ne ma." Khairat tai murmurshi, yayin da Laila ta kara da "Ummm Auntyna Batula." Fa'iza ta gama shirin tarbar Abdallah tsaf,domin babu dadewa Sai ga Abdallah ya zo , sai da ya kwashi gaisuwa wajen Alaji da hajjiya sannan tare da yi musu ya mai jiki, sannan ya samu damar isa inda Fatima da Fa'iza suke . Tafiya suke cikin mota , babu wanda ya ce da kowa komai , sai dai kowa sake-saken shi yake a zuciyar shi. Fargabar Umar kar Nasir yaje gida ya bayyana Mama wannan zancen, domin tabbas yadda ta tsufa sai ya kasheta kasheta lokaci guda, tunanukan da Umar ya ringayi ke nan , Ganin Nasir ya kusan kawoshi gida yasa shi fadin . "Mu wuce gidan naku domin madam bata nan ." Ba tare da Yaya Nasir ya bashi amsa ba ya cigaba da tafiya a mota, yayin da yake kara gudu . Cikin kankanin lokaci suka isa gidan, Umar kamar yadda tun tuni ya saba ya fada cikin gidan yana sallama. Sannan bayan Nasir ya aje mota , shima ya shigo . Zama sukai a falon , lokaci guda kuma suna hada ido da juna . Umar ya yi saurin kauda kai gefe, wanda yayi daidai da fitowar Mama daga dakinta. "Auu kun dawo ke nan , Umar sannunku da zuwa." Umar ya amsa da . "Sannu Mama da gida." "To bari a kawo muku abinci ai kunsha rana ." Ta shige da nufin kawo musu Ajiyar zuciya Yaya Nasir ya sauke me zafi, kamar me shirin fara magana , amman ya yi shiru. "Nasir me zai hana ka dau hutu , kaje kaduna dangin Mama ai zaka huta ko." Umar ya yi maganar kamar mejin tsoron Nasir. "Ni yanzu babu wani hutu da zan je , anan ma ina hutawa ne ." Lokacin Mama ta gama aje musu abincin sannan ta samu guri ta zauna. "Mama ina Laila ne, tunda na shigo banji motsinta ba ." Uncle ya tambaya Mama ta kalli kofar dakin Laila kana ta ce . "Tana can tana shiryawa , ko ka manta yau Usman zai zo ya kaita gidansu." Da sauri Nasir ya mike tsaye, shima Umar yayi saurin mikewa. "Lafiya kuwa, kaji min yara ."? Mama ke nan Umar ya yi murmurshin yake tare da komawa ya zauna. Lokacin Laila ta shigo sanye da babban dogon hijabi , "Yau kika ce Usman zai zo Laila."? Ta kalli Nasir da fad'in. "Eh Uncle yama taho." Ya koma ya zauna kamar wanda aka cirewa laka. Ba tare da Laila ta dubi hakan ba ta fara cewa. "Uncle dina dan Allah ina neman alfarma a gunka , dan Allah." Ta karasa maganar tana durkusawa "Tashi -tashi , hau kujera ki zauna.kin fi karfin haka lailata, ke rayuwa ta ce kuma babu abin da zaki nema ki rasa." Ta mike ta zauna, Mama ta ce . "Iko sai Allah, shakuwar Laila da Nasir." Ba tare da Laila ta sake jiran komai ba ta ce . "Uncle dan Allah ka dubi rayuwar Batula, ka share mata hawaye, ta nuna ka matsayin wanda zata aura, Uncle dan Allah ka aurota ta zamto matarka, tana cikin wani hali." Idanunta cike da ruwa ta karasa maganar Mama taja dogon numfashi, Umar kam lokaci guda ya rasa tunanin sa , domin ganin Nasir ya tsaya yayi jimmm yake tunanin irin amsar dazai bayar Murmurshi mai cike da karfin hali Umar ya yi . "Sannan ya ce . "Masha Allah." Nasir ya kalleshi Wayar Laila ce ta fara ringin Babu ko shakka Usman ne , hakan yasa ta mike cikin mutuwar jiki, Mama ta tashi ta nufi dakinta Ganin Laila ta fita ne , yasa Umar fad'in. "Dan Allah Nasir ka nutsu, kasan abin da zakana fade, ni wallahi idan ka bude baki zakai magana ba karamin tsoro nake ji ba , karkaji yadda zuciya ta ke zafi, gaskiya wannan ba Nasir din dana sani ba ne." "Umar kanajin abin da Laila tace kuwa, Batula fa, bayan ba wanda nake son rayuwa da ita sai Laila, gaskiya lokaci yayi da ya kamata kowa ya sani." Tsakiyar kan Umar ya sara , sakamakon jin maimaicin wannan zancen "Shin dan Allah Nasir ina ilminka, dole ne na kaika wajen malam ya sake tabbatar maka babu aure a tsakaninku, haba Nasir." Cikin kasa-kasa da murya ya yi maganar Lokacin Laila da Usman suka shigo nan Usman ya gaidasu Nasir ya mike tsaye tare da fad'in. "Tare zamu tafi, kaima Umar idan zaka je ka taho, zan kai Laila