← Book details Mahaukacin So Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 11 OF 13

Sashe 11

Mahaukacin So Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

gidan , ni banma san dalilin da yasa wani sai taje gidan ku ba ." Ya yi tsaki ya dau mukullin motarsa ya fita . Aiko haka aka tafi, motar Usman a gaba sannan Uncle da Laila a tasu motar Haka suka isa gidan wannan shahararren mutum me kudi. Tabbas Uncle sun ga karamci sosai, haka kowa na gidan suka gaisa da Laila cikin farin ciki. Sai dai babban tashin hankalin da Alaji Sani Shanshani ya sami kanshi Laila ita ce yarinyar da ya ke ta neman ko yar gidan waye, domin tunda Allah yasa ya ganta kwanaki hankalinsa ya kasa kwanciya , tabbas son Laila yake bada wasa ba , sai dai kaf a cikin su babu wanda ya kula da irin yadda mahaifin Usman wato Alaji Sani hankalinsa ya tashi, bayan yaga Usman dansa ita ce yarinyar da yake burin aura. Tabbas zamu ga yadda za ai da wannan MAHAUKACIN so. A wannan tsakiyar daren Alaji Muktar ya tashi yana ta rusa kuka . Haka har ya tashi matarshi Hajjiya ma'anatu. "Lafiya lafiya kuwa Alaji."? Ta masa tambayar tana share idanunta na bacci . Cikin wannan kukan ya fara cewa. "Tabbas Allah abin tsoro ne Ma'anatu, yanzu bani da komai sai tarin dukiya kawai, bani da farin ciki bani da sukuni , haka Allah ya yi wa Hajjiya rasuwa tana shirin ganar dani hanya me kyau, na zama butuulu abin gudu abin kyama, rayuwa ta babu wani kyau a cikinta." Ya sake rushewa da sabon kuka Duk sai tausayinshi ya kama Hajjiya, karon farko data fara ganin kukan sa . Kafin ta ce dashi komai ya cigaba da cewa. "Allah ya jikanki uwata, Allah ya jikanki Hajjiya, kullum gobe na kike son ta gyaru, gashi yanzu na girma, tsufa ya fara cimmin Hajjiya innalillahi wa inna'laihir raji un "Tabbas lokaci ya yi da zan gyara kuskure na, ya Allah na tuba , ya Allah na tuba ." Ya kwanta kafar Hajjiya Ma'anatu yana sake rangada kukanshi Farkawar Fatima ke nan , ta tashi da niyyar yin sallar darenta kamar kullum yadda ta saba , Haske ta kunna cikin dakin tana kallon Fa'iza dake ta sharbar bacci . Murmurshi Fatima tai tana cewa. "Bari na yo alwaala kema tashin ki zan Fa'iza." Ta karasa maganar yayin da kanta yayi wata sarawa Hakan yasa ta koma bakin gadon ta zauna,tana dafa kanta , Ta bata wajen minti biyar sannan ta mike tsaye tare da shiga bandakinta dake cikin daki Babu bata lokaci ta dauro alwala, sannan ta shinfida sallaya , Kana ta nufi bakin gado tana lissafin baza ta iya wannan sallar a tsaye ba "Fa'iza." Fatima ta fada da niyyar tashin Fa'iza a bacci . Kafin ta sake bude baki ta kira sunan Fa'iza , taji muryar Fa'iza ba tare data farkaba tana cewa. "Shi ke nan Abdallah, son ka ne kaddarata, amman kafi dacewa da Fatima, babu yadda zan yi ." Cikin tashin hankali Fateema ta durkusa gaban Fa'iza dake bacci Bisa idanunta ta ga hawaye jeri-jeri . Ajiyar zuciya mai zafi Fatima ta sauke tare da fad'in. "Abdallah kuma." MAHAUKACIN SO* Na Autar Marubuta. ________________________________________ Babu editing Page 27&28 Haka Yaya Nasir ya kwana da matukar zazzabi sosai, domin a wannan daren sai da aka sanya masa ruwa , Ba kuma komai ne ke damunsa ba , sai yadda Laila take neman ya auri Batula, bayan yana shirin sanar da kowa Laila son ta yake . Haka shima Alaji Sani , bayan tafiyar su Laila duk ya kasa samun sukuni. Yadda ya ga Laila a karon farko ya kamu da son ta , ba tare da yasan ita ce Usman yake son aure ba . Haka ya kwana da tunanin yadda zai bullowa wannan lamarin , amman abin ya gagara. Bayansu Fa'iza sun yi wanka , sun ci abinci. Sai Fa'iza tai shirin tafiya makaranta. "Ki bari Abdallah ya zo ya kai ki ." Fatima ta fada ba tare da murmurshi a fuskarta ba . Juyowa tai tana cewa "A'a karki kirashi, zan fara biyawa gida tukun basai kin kira shi ba ." Kawai Fatima ta dauki wayarta tare da kiran number Abdallah "Hello Rabin Raina." Abin da Abdallah ya fara fade ke nan bayan daga wayar Bai jira Fatima tai magana ba ya sake fad'in "Ya jikin naki abar kauna." Babu wadataccen farin ciki a tare da Fatima ta ba shi amsa da cewa. "Jiki da sauki baby, dan Allah ka zo ka kai Fa'iza makaranta kasan anan ta kwana, motana kuma ta lalace." Daga can bangaren Abdallah ya maida mata da cewa. "To shi ke nan ranki ya dade gani nan zuwa." Ya kashe wayar . Fatima ta kalli Fa'iza tare da cewa "Hmmmm" Hakan yasa Fa'iza cewa. "Da baki kirashi ba wallahi." Kawai Fatima tai dariya domin tama rasa mene zata ce Shiru sukayi na wasu sakanni kowa yana sake-saken sa "Daman duk halin da Fa'iza ta ke shiga saboda Abdallah ne ."? Fatima ta tambayi kanta a zuciya. "Tabbas ya kamata ace na gane hakan tuntuni, domin lokuta da yawa Fa'iza bata san maganar Abdallah ko ganin sa , amman ta ya akai ban gane ba , koda yake ban taba tunanin Fa'iza zata so shi ba ." Ta karasa maganar tana kallon Fa'iza dake zaune. Wayar Fatima ce ta fara ringin ganin Abdallah ke kira ta d'aga wayar , bayan ta gama ta kalli Fa'iza da cewa. "To Fa'iza Abdallah ya zo , sai kin dawo, nima anjuma dactor zai zo dubani." Ta karasa maganar tana kallon Fa'iza Cikin mutuwar jiki Fa'iza ta mike tana fad'in. "To Fatima Allah ya baki lafiya, bari nai sallama da mommy sai na wuce." Ta dauki Jakarta ta fita. Mai zafin gaske Fatima ta aje ajiyar zuciya, sannan ta koma ta kwanta . Bayan tayi sallamar da mommy kamar yadda ta ce . Sannan ta nufi wajen Abdallah, babu bata lokaci Suka gaisa da Abdallah cikin farin ciki. Sannan ya bude murfin motar yana cewa da ita "Bismillah." Tare da nuni da hannunsa Murmurshi tai , taji kanta ya wani fashe dan dadi kamar ita ce sarauniyar tasa . Ta shiga tare da cewa "Na gode Abdallah." Yayi murmurshi ya shigo kana suka fara tafiya. Tunda suke tafiya Fa'iza take kallon shi ba tare da ya sani ba , wani gawartaccen kuka ne ya biyota , amman ta daure ta hadiye shi . "Tabbas ina san ka Abdallah, amman abota bace ce haka ba , koda san ka zai kasheni bazan bayyana ba ." Tai maganar cikin ranta Haka Abdallah ya shigo da ita cikin harabar makaranta Kana Fa'iza ta fito tana murmurshi. "Na gode sosai Abdallah , amman fa naso na biya ta gida sai kuma na manta." "Ahh to shigo na kai ki mana ai saina dawo dake , na tabbatar miki baza ki makaraba ." Ya karasa tare da nuna mata agogonsa Dariya tai tana gyara zaman Jakarta a kafada tana cewa. "A'a karka damu na gode sosai Abdallah." Ya yi saurin mayar mata da cewa. "Mene na godiya, ai Fatima ta ce min dake da ita duk daya ne to karki damu." Kawai ta masa murmurshi Ya zuro hannu yana mata bye-bye tare da zuke gilashin motar . Sannan ta ba shi guri ya wuce , tana bin motar tasa da kallo. Anan kuwa cikin babban gidan Alaji Sani Shi ne da kanshi zaune cikin falo , ya hada hannu da fuska, ga dukkan alamu yana cikin tunani . Matarshi ce mahaifiyar su Usman ta shigo falon Yayin da taci karo dashi Kana ta fara fad'in. "Oh ni Alaji dan Allah mene yake damunka , tun jiya duk ba yadda muka saba ganin ka ba , wallahi har ka rame Alaji, mene yake damunka."? Alaji Sani ya cire wannan tagumi dake bisa fuskar sa yana gyara zaman shi . Sai da ya yi kamar ba zai magana ba , sannan ya kalli Hajjiya yana cewa. "Sanin abin dake damuna ba shi da amfani, domin rayuwar yau da kullum sai dai Allah, abin da muke so ba shi muke samu ba." Hajjiya ta ce . "Wannan haka ne ." "Ina Usman."? Alaji ya tambayeta "Yana dakinshi ko a kira maka shi ne ." Ya jinjina mata kai alamun "Eh." Sannan ta tashi ta fita . Babu dogon bata lokaci sai ga Usman ya biyo bayan mahaifiyarshi fuska cike da far 'a "Daddy ina kwana ." Usman ya fada bayan ya zauna bisa kasan kafet "Lafiya lau Usman." Alaji Sani ya maida masa "Ai daddy tun jiya nake so mi magana, domin ka ga Laila dai ." Ya fada cikin farin ciki. Alaji Sani kai tsaye ya fara cewa. "Eh na ga Laila Usman, kuma ta yi min Masha Allah." Usman yaji zuciyarshi ta sake cika da farin ciki "Amman Usaman ina san kasan cewa, ita rayuwa kaddarata, kuma babu abin daka taba nema ka rasa a wannan duniya tunda ka fara numfashi." Usman ya jinjina kai tare da cewa. "Haka ne daddy." "Sannan wannan yarinyar yarinya ce me hankali , domin ni bazan manta ba sanadinta Allah ya shirya mana kai , to ina jin dadi sosai ." Usman ya sake jinjina kai cikin farin ciki. Alaji Sani ya cigaba da maganar yana cewa. "Wannan yarinyar Laila, tsatson su mai kyau ne da kowa zai so hada zuri'a dasu ." Alaji Sani ya sake jan numfashi mai tsayi sannan ya ce . "Amman Usman ina tabbatar maka , baza ka taba samun wannan yarinyar ba , abin nufi baza ka aure ta ba ." Dariya Usman ya kyalkyale da ita , lokaci guda kuma yana kallon mahaifinsa da cewa. "Haba daddy dan Allah, ka dena min wannan wasan , yanzu fa ka gama yabon Laila, daddyna kana da abin dariya." Wani bakin ciki ne ya sake tokare zuciyar Alaji Sani ganin yadda dan na sa ya dauki abin wasa . Hakan yasa Alaji Sani ya mike tsaye cikin bacin rai Ya fara magana. "Kaiiiiii Usman! Ni mahaifin ka ne , bana yin irin wannan wasan da kai , auren Laila a gareka ya zama mafarki, domin ina tabbatar maka har abada baza ka auri yarinyar nan ba ." Cikin matukar tashin hankali Usman ya mike tsaye tare da gaza gane inda mahaifin nasu
Chapter 11 · 0% Book details