Sashe 4
Mahaukacin So Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
tunda ka shigo, ka je kaci abinci ma ya gagara." Nasir ya yi ajiyar zuciya tare da murmurshi yana cewa. "Mama ke nan." Laila ce ta kalleshi da cewa. "Uncle N na kawo maka abinci ne." Shima ya kalleta ya maida mata da cewa. "Karki kuma ce min Uncle ko Uncle N, Yaya Nasir kawai." Yadda Laila ta ga alamun da gaske yake ya sa ta cewa. "Tom." Sannan Mama tai dariya tana cewa. "Ai ni lamarin ku dariya yake ban , ai kuma Baba ya kamata ki rika ce masa ." Dariya Nasir ya yi yana cewa. "A'a Baba kuma Mama, kina ganin had'ad'd'en saurayi." "To ai irin yadda kai wahala da Laila tana karama, idan tace baba ai batai laifi ba." Nasir ya ce . "Haba Mama mene na tone-tone kuma." Dariya Mama da Laila su kai , Mama tana cewa. "To mene Laila bata sani ba ,ai an bata labarin komai ." Duk ka suka kwashe da dariya Nasir na cewa. "Allah sarki duniya." Anan cikin gidan Inna kuwa , bayan shekaru masu yawa, tana nan yadda take , idan ka cire wata yarinya jikarta Farida da aka kawo mata suke zaune tare Inna na zaune taji sallama, tun ba a shigo ba hakan ya faranta mata rai ta fara nuna farin cikin ta , domin ta dau murya. Wani had'ad'd'en saurayi ne sanye da kananun kaya , rike da mukullin mota ya shigo . "Sannu da zuwa Mahmud, angon Laila in sha Allah." Inna ta yi maganar cikin farin ciki, yayin dashi kuma dukkan hakoransa suka bayyana yayin da yake dariya. *MAHAUKACIN SO* Autar Marubuta ________________________________________ Babu editing Page 9 & 10 Guri Inna ta sama masa ya zauna yayin da suka gaisa cikin raha da girmamawa take tambayar mahaifin nashi da mahaifiyarshi Rabi Nan ya tabbatar mata duk suna lafiya "To Inna ina Faridan ta shiga ne ."? Mahmud ya tambaya Inna cikin sakin fuska ta ba shi amsa da cewa. "Tana islamiyya , ba a ta so ba ." Mahmud ya ce . "To Masha Allah." Su kai shiru na wasu sakanni, hakan yasa Inna cewa. "To ko daga wajen Lailan kake ." Sarkin dariya, ya yi dariya yana cewa. "A"a daga gida nake , gurin ki na zo kawai ." Inna ta ce . "To ai ka kyauta, amman ya kamata ka biya gidansu Lailan." "To ai Inna Baban nata ne kamar ba ya son zuwa na fa ." Inna ta ce . "Kamar ya , wai Nasir, duk tsiya Laila jininka ce ai bai isa ya hanaka zuwa ba , gara a samu a tura kawai , idan ma wani yake son bawa ya fasa." Mahmud ya yi murmurshi yana cewa. "Haka ne Inna, amman kina ganin ban yi wuri ba ." "Babu wani wuri da ya yi , tunda dai ta gama makaranta tun -tuni , to me ake jira kuma." Mahmud ya ce . "Haka ne ." Haka su kai ta hirarsu , lokacin da ya tashi tafiya ya debo kudi ya bata , sannan ya hau motarshi ya koma . Suna cikin tafiya a mota , Laila ta kalli Nasir yayin da suka hada ido sukai wa juna murmurshi Ajiyar zuciya Laila ta sauke , kana ta kalli Nasir tana cewa. "Uncle ina da.." Ba tare da ya bar ta ta fadi abin da take so ba ,ya katseta da cewa. "Laila bana ce ki dena cemin Uncle ba ." Murmurshi tai tare da hadawa da dariya tana cewa. "Ni Uncle gaskiya na saba , ka barni a hakan ." Shima yayi dariya yayin da yake murza kan mota ya ce . "To shi ke nan." Murmurshi ta kuma masa tana cewa. "To Uncle yaushe za kai auren hankalin Mama ya kwanta." Zuciyar shi yaji wani bugu yana fita da ya kasa gane dalilin sa Ba tare da ya kalli fuskar Laila ba ya fara cewa da ita. "Laila ba ko yaushe ake samun so na gaskiya ba.so abu ne mai wahalar da zuciya da kuma rayuwa, zan yi aure Laila karki damu ." Kallonshi tai cikin sakin fuska tana cewa. "To Uncle wace zaka aura , zan so ganin wannan ranar ." Murmurshi ya mata , a sa'ilin da yake shan kwanar gidan Ummi yana cewa. "Ki samo mini wacce ta dace Laila." Cikin far a ta sake cewa dashi . "A kwai kyawawan mata da zasu dace da kai Uncle." Kallonta ya yi tare da katseta da cewa. "A'a bana son kyakykyawa Laila, wacce take da kyan zuciya kamar ke, take da hankali da tausayi kamar ke Laila." Sunkuyar da kai ta yi tana murmurshi, kana daga bisani ta dago tana cewa. "Uncle dina ke nan , duk kasa naji kunya ma , ni bansan so ba Uncle, amman ina gani ina kuma ji a littattafan hausa, so guba ne me karya zuciya Mai hana sukuni idan ba kai dace ba , sannan kaddara ne da ba a sanin lokacin da yake bibiyar mutane." Dariya Nasir ya yi tare da cewa. "Wato haka kika san so ke nan , karki mamaki idan kika ga komai ya faru a sanadin so ." A lokacin ya bude kofar motar ya fita , kana Laila ta bishi da murmurshi tana fad'in "Allah sarki Uncle dina , Allah ka ba shi mace ta gari , ka faranta rayuwar shi , shi ne komai na , kunnuwa na maganar shi kawai suke ji ." Ta wajen gilashin motar ya matso kusa yana cewa da ita . "To zaki fito ne ko kuwa." Dariya ta yi kawai ta bude murfin motar ta fita , kana ya tasa ta gaba suka shiga gidan Ummi kanwarshi. Sallama Laila ta fara yi a cikin falon , yayin da taci karo da wani karamin yaro yana zaune yana wasa. "Sultan ina maman naka ." Laila tai maganar yayin da ta dauki yaron a hannunta. "Sannunku da zuwa." Ummi ta turo labulan falon tana fad'i "A she Aunty Ummi kina nan na yi zatan Sultan kika barwa gidan." Dariya ta yi sannan ta kalli Nasir tana cewa "Yaya Nasir ka zauna mana." Nasir zama ya yi kamar yadda kanwarshi ta bukata "Aunty Ummi khairat bata zo nan ba ke nan ." Laila ta tambaya Ummi ta kalleta tana cewa. "Ta zo tana ta zaman jiranki har ta tafi." Laila ta zumburo baki tana kallon Nasir da fad'in. "Wallahi duk uncle ne yaja , tun dazu nake cewa ya taso mu taho." Nasir ya yi dariya yayin da ya kara da cewa. "To ba sai na kai ki gidan nasu ba , ko ba wannan kawar taki kanwar soja ba . Kafin Laila ta ba shi amsa Aunty Ummi ta fara magana. "Wai ba ku ce min Mama kalau take ba , bamu gaisa ba , sai wani zance ake kuma ." Dariya Laila ta yi kana ta kalli Aunty Ummi, lokaci guda kuma tana gyara zaman Sultan dake hannunta yana wasa , tana cewa. "Mama tana lafiya kalau , ta ce a gashsheki sosai da sosai da jikokin nata ." "To Masha Allah." Abin da aunty Ummi ta fada ke nan Sannan Yaya Nasir ya maida mata da cewa. "To ina yartawa ne kuma Mama na." Aunty Ummi ta ce . "Au wai Mommy, tana makaranta." Laila ta ce . "Mai sunan Mama ai akwai son makaranta." Aunty Ummi ta kalli Laila tana cewa. "Na yi zatanfa da Mahmud ma zaku zo wallahi." Kawai Yaya Nasir duk ya canza ya koma wani yanayin daban Murmurshi Laila ta yi kana ta ce . "A'a Uncle ne ya kawo ni ." Kawai Yaya Nasir ya tashi tsaye , sannan ya karbi sultan a hannun Laila tare da mikawa Ummi shi , Fuska babu annuri ya ce . "Tashi mu tafi." Duk mamaki ne ya rufe su da ganin Nasir ya canza musu a wannan yanayi "Tashi mu tafi na ce ." Ya sake jefawa Laila maganar mai tafe da umarni "Hakan ya sa Laila ta mike jiki a sanyaye "Haba dai Yaya Nasir, daga zuwa kuma , ko gaisawa ba a gama ba , ko ruwa baku sha ba zaka ce zaku tafi." Aunty Ummi tai maganar tana nuna rashin jin dadinta a zahiri Ba tare da Nasir ya ce da ita komai ba , kawai ya nufi kofar fita kana yana fad'in. "Sai wani lokacin." Ya fice Da sauri Laila ita ma ta zura takalmi tana cewa da Aunty Ummi. "Zan dawo wani lokacin Aunty." Tabi bayanshi da gudu gudu Ajiyar zuciya Aunty Ummi tai tana cewa. "Ikon Allah, Yaya Nasir fa sai a hankali ." Anan kuwa bayan Fa'iza ta fito daga lecture ta sami guri ta zauna. Babu dadewa sai ga Fatima ita ma fito daga tata lecture din Kai tsaye in da tasan tabbas zata sami Fa'iza nan ta nufa Aiko tana karasa ita ma ta sami guri kusa da Aminiyar tata ta zauna tana cewa. "Washh Fa'iza, gaskiya yunwa nake ji ." Fa'iza ta kalli Fatima cikin murmurshi tana . "To sai muje muci abinci ai ." Kafin Fatima ta maida mata ne kiran waya ya shigo mata Wani murmurshi Fatima ta saki tana kallon Fa'iza. Hakan ya tabbatar wa da Fa'iza cewa Abdallah ne ke kira . "Hello Abdallah." Abin da Fatima ta fada ke nan ba yan ta kara wayar bisa kunnenta Fa'iza tai ajiyar zuciya tare da kauda kai gefe , amman hankalinta na kan wayar da Fatima ke yi Yanayin yadda taji Fatima na maganar soyyaya ya sa idanun Fa'iza suka kada sukai jajir lokaci guda kuma kanta ya fara ciwo. Mikewa tai tsaye tai nisa da inda Fatima take tana share hawaye. *MAHAUKACIN SO* Autar Marubuta *AUTAR MARUBUTA CE* __________ _________ __________ _________ _Faduwar wani tashin wani_ _Yau ake yi, gobe sai labarin_ _Burina Rayuwata, rubutuna dan masoyana_ _Cikawa da imani fatana_ <><>< ><><><> <><><> <><><><> <><><><><> ________________________________________ Babu editing Page 11 & 12 Bayan Fatima ta gama wayar ta hangi Fa'iza can nesa da ita , hakan yasa ta mike tsaye ta nufi wajen Fa'iza Fatima na karasa wajen ta , tai ajiyar zuciya tana cewa. "Wai nan kika taho."? Fa'iza juyowa tai da murmurshi mai ciwo tana cewa. "Eh ." Lokaci guda kuma tana kokarin boye idanunta na