← Book details Mahaukacin So Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 12 OF 13

Sashe 12

Mahaukacin So Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

ya dosa . Ita ma Hajjiya mikewa tai tsaye , ba tare da tace komai ba , ta zubawa sarautar Allah ido. "Daddy me yasa ? Daga ina wannan maganar kuma."? Alaji Sani ya sake hadewa yana mayarwa da dan nasa amsa. "Kamar yadda kaji , baza ka aure ta ba ." Yana gama fade ya sa kai ya nufi dakinsa. Cikin wannan tashin hankali Usman ya kalli mahaifiyar shi. Maganar na dakire masa , idanu da hawaye ya ce . "Mommy kin ji . Mene ne yake faruwa ne ." Ya karasa maganar hawayen na zubo masa Ajiyar zuciya ta yi sannan ta ce dashi. "Ka kwantar da hankalinka , zan yi magana dashi, komai zai zo da sauki ." Usman ba tare da maganar mahaifiyar tashi ta kwantar masa da hankali ba ya zauna yana tunanin irin wannan lamarin da Alaji Sani ya zo dashi ." Autar Marubuta. *MAHAUKACIN SO* Autar Marubuta ________________________________________ Babu editing Page 29& 30 Lecture ta farko suka gama , duk kowa ya fita , kamar yadda suka saba Fa'iza duk sai taji babu dadi yau da babu Fatima Guri taje ta samu ita kadai ta zauna, Cikin muryar ta me sauti ta ce . "Abdallah." Kana tai murmurshi Wayarta ta bude kai tsaye ta nufi wajen hotuna. Cikin sauri ta nemo wani hoton Abdallah da suka yi tare da Fatima Murmurshi tai kafin ta zuko hoton tana kallo "Abdallah bawan Allah." Tai maganar yayin da lokaci guda hawaye ke zubo mata . Niko na ce karku ga lefinta, so ne Kamar wasa kuka shabe-shabe tana sharewa, tana kuma kallon hoton tana magana. "Wallahi Abdallah ina kaunar ka shin ta ya zan mallake ka , zuciya ta tana mini zafi sosai kamar zata fito, ina maka san da bansan dalilinshi ba , son da bansan daga ina yake zuwa ba innalillahi wa inna'laihir raji un So sam bai mini adalci ba , na kamu da mahaukacin son ka ." Ta share hawayen nata , yayin da wasu ke sake gangarowa suna sauka bisa wayar da ta kafawa idanu. "Wallahi sai dai ciwon zuciya ya kashe ni dana bayyana wannan abin kunyar , Fatima ki rayu cikin farin ciki yafi mini komai , babu abin da zan iya sai dai hakuri." Ta sake rurucewa da kuka tana kifar da wayar bisa jikinta, tare da damke fuskar ta da hannayenta tana wani irin kuka mai gwanin ban tausayi . Yaya Nasir ne kwance a falo , domin har yanzu bai samu sauki ba Babu yadda Mama da Laila basi dashi ba kan yaje asubiti amman yaki Kuma ba komai ne ke damunshi ba , face yadda Laila ta bijiro masa da auren Batula, sannan ga Usman yana son auren Laila maganar har taje gaban iyayenshi . Wayar Laila ce ta fara ringin , hakan ya sa ba tare da bata lokaci ba nufi wayar . Usman ta gani yana kira , hakan yasa ta dauki wayar ba tare data matsa koina b Yayin da ita ma Mama ta shigo falon. "Hello Laila." Usman ya fada cikin rauni sosai . "Na 'am ya dai naji ka a haka ." Cikin matukar ciwo Usman ya fara mata maganganu. Ba tare da ya tsaya fada mata irin tashin hankali da yake ciki ba . "Wallahi Laila ina san ki, so wanda ba shi da lissafi Daman an ce so kamar ruwan shayi ne mai tsafi, a karon farko zaka kasance mai begensa , kana daga karshe ya kona maka harshe Laila." Dakatar dashi tai tana cewa. "Wai me yake faruwa ne ." Yanayin yadda tai maganar yasa hankalin Mama da Yaya Nasir ya koma kanta . "Laila daddy ne yake fadan , bazan aure ki ba , babu dalili wallahi Laila da gaske yake , na rasa inda zansa kai na." Ajiyar zuciya mai tsafi Laila ta sauke , sannan tai wani shiru Kawai ta kashe wayar. Kallon Nasir da Mama ta yi, sannan ta zame ta zauna cikin wani yanayi "Me yake faruwa ne." "Kin gama waya kuma jiki ya mutu ." Mama ke nan Laila Uncle ta kallah tana cewa "Usman ne yake fadan , mahaifin sa ya ce bazai aure ni ba ." Da sauri Yaya Nasir ya tashi daga kwanciyar yana jingina bisa kujera. "Kamar ya , a kan me , mene ya sa ."? Mama ta jibgawa Laila tambayoyin. "Nima ban sani ba Mama." Laila ta bata amsa Yaya Nasir tsabar farin ciki ji yayi kamar ya kwashe da dariya. Amman ya yi shiru yana sauran maganar da Mama ta fara "Ikon Allah, Nasir ka bincika kaji daga ina wannan matsalar kuma , ai sai a sasanta ko mene yafe faruwa." Yaya Nasir mikewa ya yi sannan ya yaye bargon da ya lulluba dashi , kana ya zauna a kujera. "A'a Mama, babu wani bincikawa , Allah ya sa hakan ne yafi alheri." Nasir ya mayarwa da Mama amsa . Cikin sauri Mama ta sake fad'in. "Kamar ya kuma."? Nasir ya yi shiru, sannan ya yi ajiyar zuciya. "Mama dan Allah ki barsu , bafa neman kai muke da Laila ba , tunda sun fasa alhamdulillah kawai ." Ya mike ya fita , domin yaji matukar karfi . Mama ta kalli Laila tana cewa. "An ya kuwa wannan baban naki , ko a jikinsa." Laila kawai ta durkusar da kai Kai tsaye Yaya Nasir gidan Umar ya nufa . Umar yaji dadi yadda yaga Nasir har ya taso alamun jiki ya yi sauki. Har cikin gidan suka shiga kana suka zauna a falo . "Yanzu-yanzu Usman ya kira Laila yake cewa mahaifin sa ya ce bazai aure ta ba ." Yaya Nasir ya yi maganar yayin da ya zauna. "Innalillahi wa inna'laihir raji un , me yasa kuma ." Umar cikin rashin jin dadin labarin ya fada Dariya Yaya Nasir ya yi , yana cewa "Kai dallah , mene na wani tashin hankali , ni daman bason auren nake ba. Kuma daman ba lallai bane na ba shi Laila, amman tunda an yi hakan alhamdulillah, daman nace ma Laila tawa ce ni kadai ." Cikin matukar mutuwar jiki Umar ya jingina da kujera yana sake fad'in. "Innalillahi wa inna'laihir raji un, wai Nasir an ya kuwa aljanu basu shafeka ba , sau nawa nake fada maka babu aure tsakaninku da Laila." Umar ya rike haba ya dan yi wani jimm sannan ya mike ya rike hannun Uncle yana cewa. "Dan Allah ta so muje ." Yana janshi zuwa wajen Yaya Nasir na masa tambaya yana cewa. "Ina zamu je ne ."? Umar kawai ya cigaba da janshi suka sha wani lungu daga bayan gidan Umar, Ganin inda Umar ya nufa , yasa Yaya Nasir fisge hannunshi yana cewa. "Mene haka , me zafi gidan Malam Usaini."? Ya yi tambayar yayin da yake kallon tarin almajirai da suke ta karatu a zaune a kofar gidan .
Chapter 12 · 0% Book details