← Book details Kawar Zuciya Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 5 OF 29

Sashe 5

Kawar Zuciya Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

haihuwa ba karya ne, maza sun fi mata son ‘ya’ya. Ta kara jefa Sophie a tagumi da damuwa mai tsanani. Tace “da yawan alfarmomin da take samu yanzu a wurin mijinta (wanda babban dan siyasa ne a jihar Kano) a baya data kasa haihuwa bata samesu ko guda ba”. Tace mata “saboda matsalar rashin haihuwa taga bala’in dangin miji kala-kala, dana uban miji, don mahaifiyarsa ta jima da rasuwa. Tace bata samu daidaito da martaba a idon su ba sai bayan data yi musu haihuwar fari, Da namiji, tace uban mijinta ya kafa mata karan tsana, har ya taba yin umarnin da aka saketa saki daya, tace da Safiyyah “a karshe dana ga ba sarki sai Allah sai na bazama, na hada da (dan kaucewa) sannan na samu biyan bukata. Wadda a halin yanzu ta sayomin kwanciyar hankali a gidana, da zama lafiya da miji na da ubansa da ‘yan uwansa. Nice tauraruwarsu, tunda na aje masu ‘ya’ya kuma maza”. Safiyyah wadda a cikin kowanne harafi na labarin da Ammara ke bata soyayyarta da da burinta da haihuwa na karuwa (to an extent), haka tsoron ta da rashin samunta shima yana ta kara ninkuwa. Har taji a ranta ko dai itama ta bi hanyar data bulle da Ammaran, komai tsananinta? Wadda har yanzu dai bata kai ga yi mata bayaninta baro-baro ba, aka kira Safiyyah ganin likita, Ammara tace zata jirata ta fito itama ta shiga ta fito, sai su karasa maganar. **** **** **** Safiyyah a teburin Dr. Galadanci. Bayan ta gaya mata matsalarta na cewa shekarun ta 8 da aure babu haihuwa babu alamarta, likitar tayi mata ‘yan tambayoyi na cewa ko ta taba ganin likita akan matsalar? Ta ce eh, sun je ABUTH da mijinta ba jimawa sun ga gynaecologist, sai Dr Galadanci ta nemi ganin result din ABUTH din. Sakamakon Safiyyah na ABUTH shi likitar ta karba ta fara budewa, sai taga cewa ba wani banbanci da duka gwajegwajen da itama zatayi mata. Duk da haka Dr. Galadanchi tayi nata binciken yadda ya kamata ta kuma ce Safiyyah ta koma reception ta dan jira fitowar sakamako. Wannan gap din na jiran sakamako ya baiwa Ammara da Safiyyah damar sake hadewa a waiting lounge suka dora daga inda suka tsaya kafin sakamakon Safiyyah ya kammala. Safiyyah ta kasa maida kwadayinta kan haihuwa da labarin Ammara, har tace da ita don Allah ta gaya mata kowacce irin hanya ce hanyar data bi ta samu haihuwa, Ammara tace “da dan wuya fa, amma in har kin yarda yafi komai sauki, tunda dai ba a garinnan na Kano kike ba zuwa kikayi kuma a yau zaki koma inda kike, mafi kyau shine a yau muje na raka ki, da zafi-zafi akan bugi karfe ‘yar uwa, daga can zaki samu motar Zaria tunda kan titin Zaria ne kauyen yake dama, ba sai kin dawo ta Kano ba zaki samu mota daga can har Zaria. Tafiyar mintuna talatin ce kacal daga Kano zuwa kauyen na Daka-Tsalle. “Kauye kuma?” Safiyyah ta tambayi Ammara, ta ce “Eh a can ne malamin yake. Koyaushe aka je kuma ana samun shi saidai layi”. A can kasan ran Sophie taji dan tsoro, ta ji fargaba da darsuwar wani abu, saboda dai ta fahimci komai yanzu, wato ta hanyar bin malamai ake samun haihuwa. Amma data tuno gore-goren Mama Fatu da ‘ya’yanta, ta kuma tuna cewa ‘ya’ya fa zata samu itama kamar kowa, sannan wadanda su kadai ne zasu dorar da soyayyarta da Zayyan dinta, da kara mata matsayi a zuciyarsa data mahaifiyarsa ta daina kyararta, kuma sune kadai (‘ya’yan) zasu tsaya tare tare da ita a ranar da kowa ya gujeta ko ya juya mata baya ko ranar da bata da karfi ko ta tsufa, amfanin haihuwa da ‘ya’ya yanada yawan da bazai kidayu ba, sune zasu kula da ita idan bata da lafiya, sune….sune…sune komai na uwarsu kamar yadda suka zama sanyin idaniya ga Ammi, aminanta abokan shawararta, itada Sabah, Rayyah da Rayha. Amfanin haihuwa yanada yawan da bazai lissafu ba, kuma damuwar rashin ta yana da girman da zaisa ka gane dalilin halin yanayin dokantuwa da desperation din da ita Safiyyah ta samu kanta a ciki. Har sai ranar daya faru gareka, wato ranar daka budi ido shekarunka kusan goma da aure babu ko barin ciki balle batan wata a tare da kai sannan zaka gane irin yanayin data ke ciki. Sakamakon binciken Dr. Galadanchi dai ya nuna kusan abu daya dai dana Dr. Muwadda Shinkafi ta ABUTH. Bakinsu yazo daya cewa; polycystic ovary syndrome (pcos) shi ya hana Safiyya ovulating. Fasihiyar Likitar tace “amma ki kwantar da hankalinki ke da mijinki duk kuna da kwan haihuwa, nashi kwan lafiya kalau yake. Amma naki kwan baida kwaliti (inganci) a dalilin cutar ‘polycystic ovary syndrome’. PCOS cuta ce wadda ‘cyst’ wato ‘maruru’ yake fitowa a cikin ‘ovary’ din mace (wajen kwan haihuwa) wanda yake hana mace ‘ovulation’ har hakan ya haifar da rashin haihuwa. Akwai mata da yawa dake fama da lalurar pcos wadanda basu san sunada shi ba, haka akwai da yawa da alamun pcos ko daya baya nunawa a jikinsu, misali daga cikin alamominsa akwai fitowar gashi a kirji kona kasan fuska da sauransu. Kinada pcos wanda alamominsa basu nuna a jikinki ba. Kuma babu alamun cewa naki na gado ne. Pcos an fi gadonsa, amma akwai wadanda keda shi ba tareda sun gada ba. Ana kuma iya maganceshi a hankali. Ta taimaka mata da shawarwarin da suka kamata ta bata, ta rubuta mata magunguna masu kyau da tsada da zasu taimaka mata ta dauki ciki da taimakon Ubangiji dana treatment data dorata akai. Ta kuma bata lambar wayarta don su dinga communicating kai tsaye ta waya ba sai tazo ba, akan duk wani cigaba da aka samu ko akasinsa, tace ta yarje mata kiranta kai tsaye. Dr. Galadanchi tace ita tana ganin matsaloli na pcos iri-iri daga mata wanda ke hana su haihuwa. Tace “a yanzu dai babu likitan da zai ce miki ga hakikanin lokacin da zaki iya samun haihuwa sai dace, maigidanki na bibiyi nashi results din daga binciken ABUTH ya nuna lafiyarshi kalau, don haka kada ki fidda rai, da taimakon Allah zaki iya haihuwa a sanda Allah ya nufa with treatment, ki dage da shan magungunan nan dana rubuta miki”. Wannan bayani ya kara jefa Safiyyah cikin damuwa maimakon ya sanyaya mata, har fiyeda damuwar da result din ABUTH ya saka ta. Wannan ya sa ta kara amanna da maganganun kawarta ta Standard, wato Ammara, tun kafin ta baro gaban teburin likitar. Na cewa ba abinda likitoci zasu iya kullawa wanda baya haihuwa, sai dai su saka ka kayi ta asarar kudinka wajen sayen kwayoyin banza, da surutun wofi mara tabbas wadanda bazasu taimaka maka da komai ba. A iya hange da tsinkayen Sophie na lokacin sun amince ta yarda da shawarar wannan matar kawai, in dai hakanne kadai hanyar da zata samar da haihuwa gareta da gaggawa, akwai alamun gaskiya sosai a cikin maganganunta, saboda babu alamun karya ko damfara a tare da ita, ko wani alfanu takeson samu daga gareta, face taimako da haduwar jini, don da ganin ta tafi karfin neman komai a wajen wani. Allah shaidarta ne akan cewa tayi addu’a kuma tana kan yi, ta sha duk wasu tsadaddun magungunan da Dr. Shinkafi ta rubuta mata na tsayin lokaci, wadanda ta duba ta ga duk kusan irin wadanda Dr. Galadanci ta rubuta mata yanzu ne ba wani banbanci mai yawa. Amma Allah bai sa ta dace ba. Watakila mafitar kadai itace wannan da Ammara ta kawo. Watakila Allah ya nufeta da zuwa Standard Hospital ne yau don ta samu mai taimaka mata, don haka bari kawai tayi kundumbala ta bi shawarar Ammara, wannan dogon bayanin na likitoci ya isheta, bata ko son sake jinsa. Tana wannan tunanin sai ga Ammara dinma ta fito itama daga ofishin likitar, take gayawa Safiyyah cikin far’a, “an daure min bakin mahaifa (IUCD insertion), muna iya tafiya yanzu”. Suka fito tare, Ammara ta bude motarta wata kankanuwar (Peageout 507). Ta bude ta shiga ta kuma mika hannu ta budewa Safiyyah kofar gefenta tace, “in har kin yarda da shawarata kin kuma yarda bazan cuce ki ba, to kawai ki shigo mu wuce in kaiki Daka-Tsalle. Daga can zan saki a motar Zaria”. Without a second thought Safiyyah ta amincewa ranta bin Ammara gidan malami. Ta kama murfin mota ta bude tashiga ta zauna ta rufe kofar. Ammara ta fizgi motar da gudu suka harba kan titi. Suka bullo ta Tarauni suka hau kan Titin Naibawa Zaria Road, wanda titi ne da zai kai ka har garin Kura, ya kuma mike dakai babu shan kwana har Daka-Tsalle. Suna tafe a hanya Ammara na tuki tana kara yi mata famfo irin na matan masu kudi da suka saba da harka da malaman tsubbu. Take ce mata “ta saki ranta, ta ganta kamar ace “kyat!” ta zura da gudu. Tace ai da yawa yanzu mata wayayyu sunfi ganewa zuwa wajen malaman tsubbu akan duk wasu matsaloli da suka sha musu kai ba haihuwa kadai ba, ke har rashin lafiyar da aka rasa gane kansa da gindinsa malaman kauye sunada maganinsa, hakan yafi musu sauki fiye da su dauwama cikin bakin ciki da ciwon, bacin rai da inferiority complex, irin na rashin daukar ciki da haihuwa kamar na kowacce mace, da kuma bibiyar likitocin da bazasu kulla musu komai ba sai karerayi da surutan banza. Tace Allah na tuba duk da ana cewa zuwa wajen malaman tsubbu haramun ne, to ai Allah mai afuwa ne mai gafara, bayan bukatarka ta biya kawai sai kayi sahihin tuba, da niyyar bazaka sake aikatawa ba, ba shikenan ba?” Safiyyah sai ta soma shakkah, ta soma tunanin anya ita a matsayinta na Safiyyah diyar Malam Usman wanda ya koyar dasu Tauheedin cewa ba’a yiwa Allah wayo, kuma ba’a tursasashi, saidai ayi ta rokonsa, anya wannan hanyar ta dace da ita? Idan ta bulle da Ammara, itama zata bulle da ita ta samu haihuwa? Ba duka abinda yayi wa ‘A’ ne yake yiwa ‘B’ daidai ba. Anya ma wannan hanya ta kaucewa kamar yadda Ammara ta kirata ta arziki da Alheri ce a gareta? In Ammi da Malam da Zayyan suka ji ta taka kafafunta wajen bokaye neman
Chapter 5 · 0% Book details