Sashe 15
Kawar Zuciya Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Safiyyah ta fara wata irin naquda mai matukar wahala ranar wata Litinin, Zayyan baya gida yaje supervising ginin wani sabon Estate da yake ginawa a unguwar Jahi. Kasancewar tunda watan haihuwar Sophie ya kama baya yarda yayi nisa da tsakiyar Abuja. Sabah ta kira shi a waya ta gaya masa yazo su tafi asibiti Aunty Safiyyah fa ta fara nakuda. Nan da nan daa inda yake ya kira asibitinta suka tura motarsu ta daukosu daga gida, shikuma ya bar komai da yake yi a Jahi, ya karya kan motarsa yayi kwana zuwa asibitin. Suka iso kusan a tare da motar asibitin data dauko su Safiyyah. Har da shi aka hadu aka gungura gadon Safiyyah zuwa dakin haihuwa. A cikin awannin da basu gaza uku ba Safiyyah ta haifo santalelen yaron ta namiji mai kama da shi sak. Akan idanunsa, kanta bisa cinyoyinsa, yana mai tayata nishin haihuwar cike da tausayi kamar tare da shi suke labour, yana karanto addu’a yana tofa mata. ganin halin da Sophie ke ciki a wannan lokacin ya kara masa son Mamansa Haj. Fatu, yau ya yarda haihuwa ba karamin al’amari bace ga mata, gashin kanta ya wargaje akan cinyoyinsa yana supporting dinta da kalamai na karfafawa, bai gushe ba yana mata addu’a har ta haifo masa Danliti, kuma photocopy dinsa, bulelen yaro lafiyayye mai kama dashi sak. Amma me? Likitoci sun yi sun yi yaron yayi kuka bayan isowarsa abu ya faskara, stillbirth! ***** **** **** Zayyan sai ya rintse idanunsa a hankali, daidai sanda tunaninsa ya zo nan, yana mai tuno kyakkyawar fuskar jaririn da ya gani a ranar, dan su shi da Sophie, sai ya ji komai na memories din wancan lokacin ya dawo masa sabo. Wato lokacin rayuwarsu daga shi sai Safiyyah a gefensa. Amma a hakan ya daure ya cigaba da tunano al’amuran da suka gabata din, a kokarinsa na nemo maslaha da warwara, wadanda duk ba masu dadin tunawa bane a gareshi. Abin kunya da bakin cikin da yafi kowanne girma a gareshi shine, daga Mama har yaranta duka aka rasa wanda zai zo ya duba Safiyyah a asibiti, balle su jajanta ko yi musu ta’aziyyah na yaron da suka rasa, alhalin sunfi kowa sanin halin da suka shiga da wahalar da suka sha akan cikin wadda bazata lissafu ba kafin samunsa, da wadda suka sha bayan samuwarshi, in ka cire Yaya Zubaina da ta kira su a waya, tayi ta lallashinsu, ta kuma tunasar dasu muhimmancin yarda da kaddara da tawakkali akan jarrabawar Ubangiji kowacce iri ce. Saboda Baban Muntaqa baya barinta tafiye-tafiye sosai, amma kwarai taso zuwa har Abuja din, har lokacin Zubaina a garin Kano take aure. Kullum sai ta doko musu waya ta bata lokaci ta lallashesu, tana tunatar da su muhimmancin yin hakuri, da tagomashin da Allah ya tanadarwa wadanda suka rasa ‘ya’yansu suna kanana, tace kada susa damuwar hakan a ransu. Allah da ya basu wannan din, a lokacin da suka riga suka fidda rai da samun haihuwa, shi zai kuma basu wani kota IVF dinne cikin kudura da buwayarsa. Daga shi har Safiyyah a wannan dan tsukun kusan zautuwa sukayi a zuci da zahiri, saboda duk wata soyayyarsu da burinsu da kawar zuciyoyinsu ya koma ga zuwan Babyn nan duniya, sun gama tanadin irin tattalinsa da zasuyi cike da soyayya da kauna na iyaye, da kuma tarbiyyar da zasu bashi duk sun gama tsarawa. Kai har makarantar da zasu kai yaron sun zaba tun bai zo duniya ba saboda tsabar dokinsu ga isowarsa. Kwarai su kadai suka san irin wahalar da suka sha kafin Allah ya basu shi ta hanyar ‘In-Vitro Fertilization’. Da irin spending din da sukayi akan samuwar cikin da rainonsa. Hakika tattalin arzikinsa ya girgiza akan haihuwar babyn nan da shirin tarbarsa. To ina ruwan Allah! Kana naka shima yana nashi. Kuma nasa shine gaskiya. Duk jarrabawar da yayi nufi ga bayinsa shi ya san ladan daya tanadar musu akanta, zai kuma baiwa bayinsa wannan ladan a duniya ko a kiyama, akan hakurin da suka yi, in har sun yi hakurin dominsa ne sun tsarkake shi. In kaga wadannan ma’auratan a wannan lokacin na makokin jaririnsu, sai sun yi matukar baka tausayin da nan da nan zai saka ka zubda musu hawaye. Domin sun rasa duk wani karsashi na jikin dan adam, da kuzarin su na cikin gida da waje. Can zaka hango su tsakiyar makeken gadon su manne cikin jikin juna, suna faman sauke ajiyar zuciya ba mai iya baiwa dan uwansa baki. Ba mijin ba, ba kuma matar ba, ba mai iya lallashin dan uwansa koda da kalmar “sannu” ta fatar baki ne. Wannan ya faru bayan an sallami Safiyyah daga gadon asibiti. Babban bacin ransa yadda Mama dasu Ya Zubaida duk suka yi shakulatin bangaro dasu. Abun yayi matukar bashi mamaki da tsoro, bai yi zaton kiyayyarsu da Sophie ta kai haka ba, tunda in akan haihuwa ne ai gashi ta haifa musu Allah ne bai barshi ba. Tun daga lokacin ya fahimci kiyayyarsu da Sophie maras dalili ce, amma ya zaiyi? Abun ya tsaye masa a rai kwarai. Ya san tun fil azal jinin Mama bai hadu dana Sophie ba, amma bai taba tunanin abun ya rikide zuwa tsana tsagwaro irin wannan ba har a gun kannensa da babbar Yayarsa, da har zata dau ciki watanni tara ta haife dan babu rai, amma su kasa ko jajanta mata su kasa zuwa su kuma kasa kiran waya wannan abun ya tsaye masa a rai fiyeda zatonsu. Abinda shi bai sani ba, tun daga lokacin da Safiyyah ta yanke shawarar yin Dashen haihuwa saboda gorinsu da tsangwamarsu, daga lokacinne kuma ta samu rashin son da suke yi mata ya rikide ya kara matsayi zuwa tsagwaron tsana, dama kuma sun sha alwashin koda ta haifi dan da rai tunda ta hanyar IVF ne ta samu cikinsa bazasu taba rika mata shi a matsayin Da kamar sauran ‘ya’yansu kuma jikokin Baba Bello ba. Saidai ta kai Dandume su Alaramma su goya mata. Bai manta da lokacin da ya kira Mama ba, tun suna asibitin da Safiyyah ta haihu kafin a sallameta, ya gaya mata Safiyyah ta sauka, amma yaron ko shurawa bai yi ba. Yasa hankaci ya tsane idanunsa ba tareda Mama ta san idonsa ruwa yake fiddawa ba, budar bakin Mama sai cewa tayi, “yo daman wannan dan nata irin sauran ‘ya’yan mutane ne da za’a zaci dole zai rayu? Dasa mata shi fa akayi ta karfi da yaji, to meye abun mamaki ko damuwa don ya zo babu rai? Shin in tambayeku; ku duka kaida Safiyyahr, wai ana yiwa Ubangiji dole ne akan abinda bai ga damar bayarwa ba? Matarnan taka Safiyyah ‘juya’ ce Baffa, na kara fadi gaskiya juya ce, ku yarda ko kada ku yarda kuma ya rage naku. Da zata haihu da tuni ta haihu kamar yadda kowacce mace ke haihuwa naturally. Idan ka sake yarda aka yi Dashen haihuwar Da da maniyyinka Baffa Allah ya isa ban yafe maka ba! Tunda dai mata masu haihuwar nan ta gaske ba karewa suka yi a duniya ba!”. Wannan maganar ba karamin firgita shi da gigita shi ta yi ba, da sauri ya cire wayar a kunnensa ya duba yana tantamar anya Mamansa Haj. Fatu ce wannan? Kodai wrong number ya kira? Sai a lokacin ma ya tuna cewa ai ko sau daya Mama Fatu tun samun cikin Safiyyah haka siddan bata taba kiransu tace Allah ya inganta ba, ko Allah ya sauki Safiyyah lafiya, a lokacin da take goyon cikin. Ance ba’a fushi da iyaye, amma hakika Zayyan ransa ya sosu sosai da attitude din mahaifiyarsa, abunda Mama Fatu tayi ga iyalinsa bai taba zaton uwa zata yi shi ga dan data haifa ba. Har hakan yasa ya dan dauke kafa daga Katsina, na dan wani lokaci. Ya maida hankali ga taya su Sabah kula da lafiyar Sophie, su su kula da ita daga safe zuwa dare, shikuma ya yi nasa jegon daga dare zuwa safe. A lokacin da Sophie take jegonnan ne kuma ya fahimci wani abu a halittarsa, wato jikinsa baida jimirin hakuri da rashin matarsa na lokaci mai tsaho. Kusan kullum Safiyyah na barci irinna masu jego, shi kuma yana fama da shan ruwan kanwa, domin kwantar da sha’awarsa ta da namiji, kwarai ya kan gaza hakuri da ita cikin dare, baya kuma son ketare iyakar Ubangiji don har lokacin jinin biki Safiyyah take yi. Ga Safiyyah da kunya, ire-iren hanyoyin nan na kwantar da hankalin miji a yayin biki ko al’ada nauyinsu take ji, wani irin nauyi abun yake yi mata, sosai take jin kunya in ya nuna mata irin abubuwan da yake so tayi masa wadanda su kadai zasu iya kwantar da hankalinsa, duk kokarinsa na fahimtar da ita shida ita babu sauran kunya ta wannan fannin, shekara goma ba wasa ba, ta bude idonta suyi irin rayuwar data dace dasu amma Safiyyah kunya da nauyi da gidadanci basa barinta, irin dai upbringing na gidan manya data riga samu da kuma rashin good socialization da zai bata damar samun exposure akan kula da miji, ko irin ‘yan karance-karancennan na zamani da ake daukar ilmin rayuwar aure a cikinsu Safiyyah bata yi. Kaidai barta a karance-karancen da zai zurfafa ilmin ta na Architecture. Ganin karatun hikayoyin soyayyah take a matsayin bata lokaci ko rashin tarbiyyah. Not because she doesn’t love him. Amma ta gaza sanin hanyoyin kula da bukatunshi na aure yadda ya kamata, alhalin karshen duk wani so da soyayyarta ta diya mace a duniya tasan na mijinta Zayyan Rafindadi ne. A’ah ita dabi’arta na kunya, russunar da ido, da kana’a, nature dinta ne da Allah ya halicceta dasu tun fil azal, kunya da kawaici da rashin zaqewa akan sexual relationship dinsu. Komai shi yake yi a gadon aurensu. Ita saidai ya barta dasu rufe ido da ji masa kunya, da kiran sunansa. Wannan ba zai zamo abun mamaki ba, in aka yi la’akari da irin (decent upbringing) din da Safiyyah ta samu a gida. Har Sophie ta yada wanka Zayyan bai je Katsina ba, ya kuma gama shirya surprising dinta da tarewarsu a sabon gidansu dake cikin shahararren Estate dinsa da ya kammala, wanda sai yanzu Allah yayi kammaluwarshi, watau SUNSET ESTATE, Estate dinsu shida Safiyyah dake GUZAPE. A ranar