Sashe 21
Kawar Zuciya Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Kasancewar gidan Arch. Murtala babban gida ne na zamani ginin (Bungalow) a shiyyar Ikoyi har da tankasheshen sassan baki, anan Baba Murtala yasa aka saukeshi. Saida yayi sallahr azuhur yayi wanka ya huta, sannan Baba Murtala ya turo Seyi, don yayi masa jagora zuwa cikin gida wajensa. Har falon da iyalin sa kadai ke shiga Baba Murtala yayi umarni ga Seyi ya kai shi. Baba Murtala dai kamar ya hadiye dan nasa saboda kulawa da maraba, ya rasa ina yaka saka ina yaka aje da shi, duk sanda yazo gidan haka yake nan-nan da shi, Zayyan na shirin zama akan kilishi Baba Murtala yace “zo zauna nan a gefena kaji Zayyan, Da na na kaina, kullum na ganka ji nake kamar da Bello nake tare. Ka jima ba ka zo gidan naku ba, yaushe rabon ma ka zo har na manta, bana jin duk kannenka ka san su gabadaya”. Ya dauki waya ya kira maidakinsa Haj. Nana Aisha, wadda ita kadai ce matarsa tun ta lalle, yace da ita “Da na Zayyan ya iso. Maza a Shiryo abincin rana a kawo mana nida shi, muna karamin falona”. Daga nan inda suke zaune Zayyan na iya jin muryar Haj. Nana tana kwalawa daya daga cikin ‘ya’yanta mata kira. “Azeezah! Azeezah!” Daga can nesa ya jiyo amsawar Azeezah din, da wata ‘yar gayun murya ta yanga da lalaci, tace. “Na’am, I am coming Mum”. (Ma’ana ina zuwa Mama). Ta fito daga dakinta ta iske Maman nasu a kitchen, tana shiga Haj. Nana ta hau fada “sai ki kule a daki da waya a hannu, ki barni da aikin abinci nikadai ko, na rasa mace irinki Azeezah, komai naki kamar bana mace ba, sai kwalliyar banza da iyayin wofi kika sani, amma harkar kitchen data hankali ko oho, ni Nana Aisha ina tausayawa mai tsautsayin mijin duk da ya kwashe ki”. Azeezah ta zumburo baki, kafin tayi dariya, bata dai ce komai ba. In da sabo ta saba da wannan gorin na Mum dinta. Abin haushin har Daddy haduwa suke suyi tayi mata gori. Cewa ita muna mata ce. Duk abu na matan kwarai baza’a sameta ciki ba sai chatting a waya da midnight call. Mum din tace, “ki dauki abincin da na shirya daga dining ki kaiwa Daddy da bakonsa a falonsa, na kai dining yace a kai musu falonsa”. Azeezah ta ce “toh” sannan ta juya don cika umarnin mahaifiyar tata tana cewa a ranta ko waye wannan bakon da Daddy ya kai har karamin falonsa wanda su kadai ke da access din shiga wajen. Tana tafiya cikin rangaji tamkar reshen bishiya ko hawainiyar da bata son taka kasa don yanga da iya takun tafiya. Tamkar budurwar Dawisu don class da iya ado. Haj. Nana tace kiyi sauri mana, kina wannan tafiyar taki kamar ta hawainiya, yace a kai da sauri. Shi da dan sa ne dan wajen marigayi Bello Rafindadi. Kiyi maza kai musu, kizo ki rakani saloon Agege”. A bakin kofar shiga falon ta tube takalminta dauke da katon tray ta shiga falon, saida ta shiga sannan ta tuna bata yi sallama ba, tayi maza ta koma tayi sallamar ciki muryarta ta ‘yan gayu, don tasan kadan da aikin Baba ya dizgata gaban bakonsa, akan rashin sallama. Ilai kuwa saida Baba Murtala ya ce “da baki koma kinyi sallamar nan ba Azeezah da tamu ce dani da ke”. Zayyan ya dago kai daga kan wayarsa yana kallon ‘yar gayun yarinyar dake shigowa. Bata da tsayi can kamar Safiyyah amma tafi Sophie kakkauran jiki irinna ‘yan ajebo, ya sake kallon ta karo na biyu yana tuna sanda ya santa lokacin aurensa da Sophie da suka je Rafindadi tareda Mamanta Haj. Nana lokacin bata fi shekaru goma sha biyu ba, lokacin ko kirgen dangi bata fara ba, yayi mamaki da yaga itace yau tayi wannan girman haka na farat daya? Yanzu akalla zata yi shekaru ashirin da biyu, komai na budurci da hutu ya nuna a jikinta. Ta shigo da tankareren tray din da gidajen manyan masu kudi kawai zaka ga irinsa, ta ajiye akan center table din dake gabansu, ta gaida shi a gajarce ko amsawa Zayyan bai iya yayi ba, sakamakon wani tunani maras tushe da ya zo ya sarkeshi a nan take. Tunani ne yazo masa cewa. Ba don ba don ba, ai da ya gwada cewa Baba Murtala ya bashi auren ‘yarsa Azeezah ya kara da ita, in yaso ta haifa masa Da, ya dauka ya baima Sophie ta rike ta rainar masa a matsayin nata, a huta matsalar haihuwa dake damun Sophie. Abinki da namiji wanda ya fito daga gida cikin kishirwar mace, a take ransa ya kyasa masa Azeezah. Yayi ta kawata masa suffofinta. Ba Azeezah ba da take zukekiyar yarinya mai class, wanke hannu ka taba, da iya gayu da takun tafiya mai jan hankalin da namiji, a wannan lokacin ko wadda bata kaita komai bama Zayyan ya gani kyasawa zaiyi a ransa. Saboda wawakeken gibin da Safiyyah ta bari a ransa daren jiya da yau da safe kafin ya fito daga gida. Sanye take da fitted gown ta wani bakin lace mai adon ruwan gold, rigar ta bi dirin jikinta ta kwanta sosai, ta fidda duk wani tudu da kwari na jikinta, a kanta kananun kalba ne na karin gashi (attachment) wanda in ba gaya maka tayi ba bazaka taba gane cewa sakawa tayi ba, ta yi ado dashi ta dunkuleshi ta baya, wani kuma ta zubo dashi gefen fuskarta. Baba Murtala ya lura da kallon ‘yar shi Azeezah da Zayyan yake tayi a sace, har ta juya zata bar dakin, tana gaida shi amma tsabar yayi nisa a tunani bai ma ji gaisuwar tata ba. Tunani kawai yake yana sake cewa a ransa “ba don ba don ba! Ai kawai da ya gwada neman aurenta”. Baba Murtala yayi murmushi yace “kanwarka kenan, marar kan gadon gidan, “Azeezah!”. Duk cikinsu itace sai a hankali, komai sai an kwabeta na rasa mai yasa bata taso da kan gado ba, ita ba ta fari ba ita ba auta ba. Ko don ita kadai ce mace a cikinsu?” Azeezah ta ciji lebe tasan mawuyaci ne dama Baba bai dizgata ba shiyasa bata so Mum ta saka ta kawo masa abinci falo musamman idan yana tare da baki. Baba Murtala yayi murmushi yace “tana gaisheka” nan da nan ya shiga nutsuwarsa ya yi maza ya canza fuska ya mayar da ita ya dinke tsaf, ya amsa a gajarce kuma ciki-ciki. Azeezah bata damu ba, ta juya zuwa kofa, duk dakin ya bade da kamshin wani sassanyan turaren Humra na mata data shafa, mai sanyaya rai. Zayyan ya bita da kallo, kugunta kamar zai karye don shape, sai kadawa bom-boms keyi kamar da gayya take juya jikinta. “Yaa Subhanallah” inji Zayyan a zuciyarsa. Baba Murtala ya lura dan nasa ya tafi da yawa sai ya cetoshi da cewa, “bisimillah Zayyan, mu ci abinci ko? Muna da wuraren zuwa da yawa a yau, da abubuwan da zamu fara gabatarwa fal. Don haka ka ci abinci ka koshi ka ji ko. Na gaya maka two weeks project ne, so probably zaka zauna anan Lagos har kwana goma sha hudu”. Zayyan ya gyada kai, ya nutsu ya maida hankalinsa ga Baban nasa, ya bude warmers din alfarma da Azeezah ta ajiye musu ya fara serving dinsu shi da Baba, kowa a faranti daban. Baba Murtala ya kasa shiru da canzawar yanayinsa. Don gabadaya walwalarsa ta dauke. “Zayyan are you okay? Azeezah ce fa, kanwarka ta gidannan naga kamar baka gane kanwar taka ba, last week ta kammala karatun digirinta a Cyprus ta dawo gida”. Zayyan yaji kunya tunda Baba ya gane kalar kallon da yakema diyarsa, a fili yace “umh” kawai, don jikinsa yayi sanyi kuma, a ransa yace “karewar hutu a kasar waje tayi karatu. To akul! Dina”. Suna cin abinci Baban ya shiga bashi labarin diyarsa Azeezah, a lokacin da tana kankanuwa, yace hasali duk cikin yaransa Azeezah daban ta zo, itace bata da kwakwalwar karatu sai ta giggiwa, kullum ta karshen aji take dauka a makaranta. Ya samu ta gama sakandire da kyar da sidin ludayi, sai tasa rigimar ya kaita waje tayi karatu don sakamakonta bai yi kyau ba, da kyar ya samu wata makarantar kudi (private university) ta dauketa a kasar Cyprus, shi yasa da ya kaita makarantar ya barta ta karanci abinda malaman jami’ar suka zaba mata (Make up Artistry) sabida kanta bai jan karatu sam. Kuma da yake tana da interest akan kwalliya din tun tana karama hobby dinta ce, ta tsaya ta maida hankali ta kawo masa dan shakwa-shakwan certificate na zama professional Make-up Artist. Yace komai Azeezah tayi sai an yi mata gyara, komai sai an saka ta a hanya, kuma bazata rike na yau ba gobe sai an maimaita, in ba haka ba sai an ga kuskure da wauta a ciki, ya tambayi Zayyan, shin ko ya taba ganin yarinya mai gurgun bahagon personality irin na ‘yarsa Azeezah?” Sai kuma yagirgiza kai, cikin alhini yace. Ba don kamar ta daya da ni ba, da tabbas nace canzawa Haj. Nana ita akayi a asibiti, don dakikiya ce ta gaske Azeezah”. Abun ya baiwa Zayyan matukar dariya, musamman ta sigar da Baba yake bashi labarin kamar da sa’ansa yake hira, har sai da Zayyan ya murmusa, ya ce “haba dai Baba!” Yace “Allah Zayyan Azeezah halinta sai ita, ni dai nan kusa ban taba ji ko ganin yarinya mai son rayuwar jin dadi na rashin kangado da son kyale kyalen duniya irin Azeezah ba. Itace ta biyun karshe a cikinsu, amma kamar diyar fari sabida tsabar wauta da rashin sanin ya kamata, duk cikin ‘ya’yansa yace babu mai son duniyarta, da son rayuwar hutu da jin dadi zallah na wuce kima irin Azeezah. Can Baba Murtala yace “a kullum in lamarinta ya dameni ina gaya mata bamu zo duniya don mu huta ba, babu wani jin dadi ga dan adam a wannan rayuwar sama da ya bautawa Allah ya nemi abin rufin asirinsa, hutu sai a aljannah, jin dadi zai dauwama ne kadai idan ka bautawa Ubangiji da lokacinka da lafiyar daya baka. Ka tsare sallolinka. Kullum nayi gabas, ita sai tayi yamma, in nayi kudu, sai tayi arewa. Kamar bani na haifeta