Sashe 17
Kawar Zuciya Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Kudin project din wani Estate da yayiwa gwamnati ne ya fito a goman karshe na watan Ramadhan, ya samu kudi masu kauri a hannunsa, aljihunsa yayi nauyi sosai. Abinki da Da nagari, ba wanda ya fara tunawa as usual idan ya samu kudi masu kauri a lokacin sai mahaifiyarsa, Mama Fatu. Tuni ya manta da bacin ran da Mama ta saka shi a ciki watanni kadan baya da suka gabata, don shi duk wata nasararsa a rayuwa, yana fara dangantata ne da iyayensa. Don haka sune na farko da yake tunawa idan alkhairi irin wannan ya same shi. Yayi ma Baba Bello Sadaqah sannan yayiwa Mama Fatu hidima. Gashi ya jima bai je Katsina ba yayi kewar Mama. Don haka ya samu Safiyyah har daki yake gaya mata cikin farin ciki. “Sophie kina ina ne? Zo daga kusa ki ji?” Ta fito daga daki tana daura kallabinta, “gani nan Habiby, wani abu?” Suka game a karamin falonta, da rabi-rabin runguma, saboda ya taho da sassarfa ne itama ta fito da sauri, ya riko kugunta ya zagayeta da hannayensa biyu yana murmushi irin na namijin da aljihunsa ya cika da albarka a gaban iyalinsa. Yace ma Safiyyah. “Wannan sallahr so nake zan gwangwaje Mama da wani abu mai daraja, wane kaya ne na kwalliyar mata suka fi kowanne daraja?” Safiyyah na murmushi ta sakalo hannayenta a wuyansa itama, tace “Gold! (Zinare). Shine karshen kwalliyar mata mai daraja”. Yace “to Alhamdulillah. Zan sayama Mama sarka da dan kunne da zobe da warwaro na zinare don in gwangwajeta ba zatonta. Na san Mama da son kwalliya. Kudinnan dana gaya miki inata jira su fito na project din Bwari, yau sun fito cikin ikon Allah. Yace “bana taba manta wata sallah ina dan shekara goma. Baba yazo bashi da kudi isasshe a hannunsa, yace iyalinshi mu hakura da kayan sallah, saboda ya samu yayi wasu abubuwan muhimmai da ‘yan kudin hannunsa. Mama sai tace “ai ba komai Babansu, Allah ya dada rufa mana asiri Baban Baffa. Sai ta dauki sarkarta ta zinare ta siyar, tayi mana kayan sallah, ta baiwa Baba ragowar kudin tace, “kayi duk hidimarka da sauran kudinnan Babansu Baffa”. Tun lokacin abun ya tsaya min a rai. Don naga wani irin feeling na godiya da bazan taba mantawa ba a fuskar Baba ga Mama. Na kudurce nikuma sai na biya Mama ‘gold’ dinta duk sanda Allah ya bani gwaggwabar dama. Ya rubuta cheque na kudi masu yawa ya baiwa Safiyyah wadanda har saida suka bata tsoro, yace “Sophie, so nake Mama na tayi gayu da babban Zinare, ta fito kamar tauraruwa Zahra a cikin mata a wannan sallahr”. Safiyyah ta karba tana jinjinawa halarcin Zayyan akan son iyayensa, tace “amma Habiby, tare da kai zamuje mu zabo ko? Yace “a’ah ni mace ne? Ina nasan design mai kyau? Kawai kije ki zabo, sannan ki sayawa su Zahra suma duka kanana da bai kai na Mama girma ba. Da kuma amaryata Sabah da kanwata ta kaina, Rayyah”. Nan suka zauna bisa doguwar kujera three seater, yayi mata bayanin yadda yakeson na kowa ya kasance, da sauran mutanen da zasu yiwa kayan sallah a cikin kudin bayan sakon Mama, dama duk shekara ya saba hakan, ‘yan uwanshi kaf da nata, da iyayenta da nashi babu wanda baya yima kayan sallah na gani na fada. Kai hatta dan almajirin gidansu Safiyyah wani yaron dake zama gidansu yana zuwarma Ammi aike mai suna Saminu, ya shaida soyayyar Zayyan ga ahalin Safiyyah, don duk shekara bandirin shaddah baya wuceshi shima, duk sallah karama Zayyan bai mantawa dashi. Balle kuma kannenta uku, wato Sabah da Rayyah da Rayha, koda ba’a hannunsu zasu yi sallah ba ya maida yi musu kayan sallah cikin obligations dinsa (hakkinsa), tun bayan dawowarsu Abuja. Sosai Safiyyah ta yi masa addu’ar karin budi da nasara cikin al’amuransa, tayi godiya yadda ya dace macen kwarai ta godema mijinta in yayi hidima ta bajinta irin wannan, ta kuma kara alfahari da Habiby dinta domin ya cika dan halas din da kowacce Uwa zata yi fatan haifar mai kaunarta da yi mata halarci kamarshi. Baya taba iya yin dogon fushi da Mama Fatu (no matter how) yadda zata bakanta masa da halinta. A kullum fatanta shine na samun ‘ya’yan da zasu yo gadon wadannan nagartattun halayen nasa, Zayyan Bello ya cika dan halas, uwa da ubanshi babu sama dasu a komai, tana addu’ar Allah ya bata ‘ya’ya daga gareshi su gado komai nasa, itama su ji kanta a tsufanta, ko ba don bata da shi ba. A washegarin ranar suka je wani dankareren shagon zinare suka zabi latest design na set din wani white gold saukar jiya-jiya daga Dubai. Ya lashe miliyoyin kudin da Zayyan ya warewa Mama har da dori. Ta kuma sayawa sauran kannensa dan kunne kowacce yadda yace tayi. Sannan suka zarce kasuwar Wuse market tayi siyayyar komai da ya lissafa mata na kayan sallar jama’arsu, karkashin rakiyar kannenta su Rayyah, kaya ta zabowa su Zaitoon na gani na fada, masu tsada da quality, ta hada ma Mama da saitin turarukan (Aventus for Her) da ya taba gaya mata cewa dashi kadai Mama Fatu take amfani a matsayin nata neman albarkar, ta sayi wani tsadaddden akwati dan karami mai kyau, ta zauna ta jera turarukan nan da saitin (white gold) din a cikin akwatin gwanin ban sha’awa sukayi kyau a cikinsa. Kai kace wata yarinya budurwa za’a kaiwa toshin sallah. Sannan ta siyowa dukkan kannenshi da kannenta kaya kamar yadda ya tsara. Da Zayyan ya dawo gida ta nuna masa sayayyar duka tayi masa bayanin na kowa, yayi murna sosai da ganin sakon Mama da kannenshi, ya jinjina ma fasaharta da iya zaben design din zinare. Amma yana bude na su Sabah ya dauki atamfar yana juyawa a hannun shi, ko daga kalarta da rashin nauyinta ya san bata fi atamfar dubu takwas ba, ya dubi Sophie sama da kasa ya hade rai yace. “Safiyya menene haka? Me kike nufi da hakan?” Hankalinta ya tashi, ta dauka wani abu ne tayi masa ba daidai ba, sai taji yace yanzu don me zaki siyowa su Sabah kaya masu arha, su Hatoon ki siyo Swiss laces masu tsada, shin akwai bambamci tsakaninsu ne a gurina? Ban ji dadin abinnan da kika yi ba ko kadan, baki kyauta min ba”. Sai ta soma bashi hakuri, tace “ba haka bane Habiby, kudin ne sunyi kasa sosai, sai naga cewa su Zahra yafi dacewa da wannan, su din kannenka ne da kuke ciki daya, hakkinka ne ka yi musu komai yanzu, musamman da hakkinsu kamar a wuyanka yake, su Sabah kuwa Ihsani ne tsakaninku wanda bai zame maka dole ba”. Cikin takaicin kalamanta yace “sannu Mrs. Right, Gwanin na iya sarkin iyawa, toh canjin da kika dawo mun dashi me zanyi dashi? Idan har na isa dake ki koma kasuwar nan, abinda kikayi wa su Hatoon, shi nake so inga anyi wa su Sabah…”. Dolenta suka koma kasuwa washegari aka sake siyo kayansu Sabah, don ransa ya baci sosai a ranar, ya dauke mata wuta da wannan abinda tayi, har saida ta gyara kuskurenta, ta kawo ta nuna masa ta bashi hakuri. Sannan ya sauko, ta hadawa kowa nashi aka aika kayan Katsina. Infact duk kannensa da aka kai musu kayan sun yaba, kowa yayi murna ana ta bugo waya ana yima Yaya Baffa godiya don sun dauka shi da kansa yaje ya sayo masu. Mama kam kuka ta saka, tace wai yau Baffa ya tuna mata Baba Bello, komai Baba zai saya mata sai ya zabo na kerewa sa’a, don ya san ta da son special abu da basu cika gari ba, Mama tun asalinta mace ce mai son gayu da kashe kala, tana matukar son kayan ado na yayi, tana harka ta jiki sosai da manyan matan ‘yan bokon Katsina, saboda farin jinin Baba Bello. Da sallah tazo, Zayyan da Safiyyah dasu Sabah suka yi shiri suka wuce Katsina don halartar shagalin bikin sallah kamar yadda mafi akasarin mazauna birnin tarayyah ke yin sallah a garuruwansu na haihuwa. Gidan marigayi Prof. Bello Rafindadi gida ne da ake yin hidimar abinci ta alfarma duk ranar sallah, gate dinsu a bude yake. Wannan ya shiga wannan ya fita. Ana dafa abinci kala-kala ana bayarwa ga baki da makwabta. Haka ake yi duk sallah tun Baba Bello yana raye. To yau ma hakan ce ta kasance a gidan. Ya kasance a kowanne washegarin sallah Mama Fatu tana gayyatar matan abokan Baba da kawayenta, suzo gidanta a ci a sha da cimaka ta alfarma da snacks, su wuni sur har yamma suna hira, zaki gansu duka hamshakan mata ne kusan su goma a falon Mama, ana hira ana nishadi, to ko bayan rasuwarshi Haj. Fatu ta cigaba da al’adar tata, ta gayyato mutanenta ranar sallah. Wannan shekarar ma kamar ko wacce, kawayen Mama sun zo harda matar VC mai ci a yanzu na jami’ar Umaru Musa ‘Yar adua, Safiyyah tazo falon ita da kannenta zasu yiwa mutanen Mama gaisuwar sallah, Sophie ta sha ‘swiss lace’ dinta ‘purple’ me kyau, kannenta Sabah da Rayyah dake biye bayanta sun sako kayan da Zayyan ya siya musu na sallah iri daya sak da na yaran Mama wato su Hatoon, su Sabah sun yi kwalliyar sallah da kayan ne saboda Uncle Zayyan yana gidan, suna so su nuna mishi godiyarsu, ta hanyar saka kayan. Don yace dasu da yamma in sha Allah idan ya dawo daga cikin gari za’a yi (family picture) harda su kafin ya maidasu Dandume gobe kamar yadda ya alqawartawa Malam. Idan su Zahra da Zaitoon sun iso daga gidajensu. Shiyasa suka saka kayan ba tareda sun kawo tunanin komai a ran su ba. Suna shiga falon Mama tayi arba dasu, ta kalli kayan dake jikinsu, nan da nan annurin fuskarta ya dauke kaman an aiko mata da saqon mutuwa. Tana tozali da kayan jikinsu Sabah ta danna ashar a zuciyarta, tace a ranta lallai ma Safiyyah da take rainawa ta bari tayi kauri da yawa, ta samu Baffa da yawa, me Safiyyah ke nufi na sakawa kauyawan kannenta kaya irin nasu Hatoon? Haka suka karaso suka gaishe da Mama da kawayenta Mama na zabga musu harara daga su har Safiyyah din. Hajiya Yabi kawar Mama ta lura da irin kallon