← Book details Kawar Zuciya Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 12 OF 29

Sashe 12

Kawar Zuciya Part 2 Complete Hausa Novel · about 5 min read

A wannan dan tsakanin Zayyan da Safiyyah bakidaya suka fada wani hali na soyayyar samun DA ta kowacce hanya, duk iya tunaninsa ya rasa mafita akan yadda zasu samu haihuwa, ga Mama Fatu ta kara bude wuta da matsa mata lamba a dan tsukinnan da ‘ya’yanta mata suke ta ajiye ‘ya’ya, don kuwa hatta su Zahra sun haife mata jikoki saura shi, sun sake haifewa kowacce karo na bibbiyu, su da akayi aurensu bayan-bayan na Safiyyah. Maganarta dashi yanzu babu hira mai dadi irinta baya kullum sai korafi da shagube akan rashin haihuwar Safiyyah har fargabar zuwa gaida Mama yake yi. Bata wata hirar arziki dashi kamar da sai slogan dinta na gates cewa bakarariyar matarsa har yanzu dai babu labari. Tace bata ga riba cikin aurensu ba sai faduwa da asarar ciyarwa da bautar da yake yiwa mace.
Wannan magana da Mama Fatu tayi ta razana Zayyan da Safiyyah, wanda shi ya kara rura dimautarta da dokinta ga son haihuwa helter-skelter, abinda ya kaisu ga yin bincike na ilmi akan yadda ake samun haihuwa da gaggawa ga mai matsalar lalurar PCOS.
A garin binciken nasu ne a teburin likitoci daban-daban, kowanne likita saidai ya kawo shawarar cewa suyi (IVF) wato (In vitro Fertilization) da aka fi sani (dashen haihuwa) da harshen Hausa.
Safiyyah duk da dokin abun ya cikata wato IVF din, don wannan ne karo na farko data ji ‘hope’ na zata haihu, in dai Dan kanta ne da ya fito daga jikinta kuma na Zayyan to ko ta wace hanya ce tana maraba da samuwarshi, indai addinin musulunci bai haramta ba, duk da haka basu yi saurin amsawa likitocin ba, sannan basu gayawa kowa ba, saida sukayi nasu binciken na addini ta hanyar neman fatawa daga daga malamai daban daban, sannan sukayi bincike sosai a yanar gizo suka tabbatar IVF baida illa daga fuskar addini, da kuma tabbacin da suka samu daga likitoci na cewa kashi 25-30% na attempt din farko ana samun nasara.
Duk irin bayanin da yayiwa Mama Fatu, na cewa sun je asibiti shida Sophie, kuma suna kan zuwa har gobe, da bayanan da likitoci suka yi akan matsalar rashin haihuwar tasu, amma ya boye sirrin matarsa inda yace ance matsalar su (unexplained ifertility) ne shi da ita duk lafiya suke, hakan bai sa Mama ta tausaya ko ta tausasa kalamanta akan kaddarar Safiyyah ba. Tace.
“Fadi gaskiya kawai ka auro “juya” Baffana, ba wani ‘unexplained infertility’, tunda dai a shekaru kusan takwas da aure ta gagara haifa maka Da ko guda daya, ai JUYA ce kenan, musamman da babu bari ba batan wata mai nuna alamar haihuwa.
Wannan makauniyar soyayyar da kake yiwa diyar Alarammannan tayi yawa Baffa, na fadi na kara fadi meye ribarta? Ribar kowanne aure ai haihuwa ce, tunda bata da mahaifar haihuwa kuwa, aurenta babu riba a cikinsa sai asara”.
Ta kai ta kawo a yanzu Safiyyah ko gidansu Zayyan ya gagareta zuwa, bata iya shiga sha’aninsu na biki kona haihuwa, bama sa gayyatarta, abun nasu babu kawaici babu tausayi da alkunya, kai sai ka rantse da Allah ita zata halicci dan a mahaifarta. Idan kuwa tayi kuskuren zuwa wani sha’ani na iyalin Mama, kamar sunan haihuwar ‘ya’yanta Zaitoon da Hatoon da akayi recently, yadda kasan mujiya haka take komawa a cikin su, saboda wulakanci da kaskancin da suke mata, ga yada mata mummunar magana cikin habaici a gaban kowa, akan rashin haihuwa kai sai ka rantse a kasuwa ake sayar da haihuwa.
A kodayaushe sukayi waya da Ammi kuka take tana labarta mata irin mawuyacin halin da take ciki da uwar mijinta da ‘yan uwansa, Ammi ba abinda zata iya a kai banda ta kwantar mata da hankali, kullum tausarta kawai takeyi, tace ta kara hakuri kan wanda take yi, matsalar rashin haihuwa ba a kanta aka fara ba, ba kuma kanta za’a kare ba, kada kuma ta fidda rai. Saboda yadda Safiyyah ke gaya ma Ammi Hafsatu halin damuwar da take ciki da dangin mijinta, har auren Safiyyah ya soma fita daga ran Ammi, don ta kan ce a ranta sam Uwar Zayyan uwar banza ce, bata da Ikhlasi. Kamar bata haifi ‘ya’ya mata ba itama.
Amma a matsayinta na uwa bata nunama Safiyyah hakan ba, amma a ranta ta fara tsanar auren yanzu, don kwatakwata Safiyyah ta rasa nutsuwa da farin ciki a cikinsa, tsakaninta da mijinta lafiya kalau amma zuciyarta babu dadi, duk da ganin zaman daular da take ciki da kowa dake nesa da ita yake yi mata baya sata zama cikin nnutsuwa. Yes, da gaske Safiyyah tana cikin daular miji domin Zayyan kullum kara buda masa nasibi cikin harkokinsa Allah yake yi, har wata ‘yar kiba ya aje ta musamman irin ta kasaitattun mazan Abuja, masu murza naira da jin dadinta son rai. Ita kuma Safiyyah kullum ka ganta kamar marar lafiya kamar kudin guzuri, bata da karsashi da walwala a cikin tsararrakinta.
Ya nutsa sosai ga tunanin mafita a garesu. Har zuwa lokacin da Safiyyah ta kara bijiro masa da zancen baya, wato bukatarta na suje wani asibitin kudi a Kaduna, bisa shawarar da likitoci suka bata akan suyi (In vitro Fertilization).
Sai ya shiga tunanin ko hakan za’a yi kawai don Safiyyah ta samu kwanciyar hankali ta rike Da a hannunta? Su kuma huta da gori da fitinar Mama Fatu?
A daren suna waya shida Mama, yake yi ma Mama maganar cikin damuwa,
“Mama yanzu saboda Allah kinji dadin hakan? Mama uzzurawarki ga son Sophie ta haihu kota halin kaka, yasa Safiyyah fara tunanin muyi IVF kawai”.
Mama ta tambayeshi cikin halin ka’in kula ko meye IVF din?
Nan ya yi mata bayanin cewa “Dashen Da a mahaifa”.
Mama ta zabura, tace “to ba dai cikin zuri’ata ba, amma in kun ga shi zai fishsheku to kuje ku yi tayi.
Indai mutum yace ra’ayin Bature zai biyewa shi ya jiwo, shi dama kowa yasan halakakke ne, ku zai halakar ba ni Fatima ba”.
Mama bata hana ba, amma ta nuna matsalarsu ce yin IVF ba tata ba. Don haka shi da kansa ya yarda suje Kaduna a yi musu Dashen, don itace kadai last hope din su.
Basu kara bi ta kan Mama akan zancen ba, suka shirya suka tafi Kaduna da niyyar ayi musu dashen haihuwa.
A wani babban asibitin kudi a Kaduna wai shi (Nisa Fertility and Gynae Center Kaduna) akayi ma Safiyyah da Zayyan dashen Da (IVF), sosai suka tsaya suka naqalci ilmin abun, ta yadda suka gane komai akansa, kafin su yarda aka yi mata.
**** **** ****
Chapter 12 · 0% Book details