← Book details Kawar Zuciya Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 19 OF 29

Sashe 19

Kawar Zuciya Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

kai ya koma baiwa Mama hakuri, don yaga ta hassala sosai irin yadda bai taba gani ba. Da kyar ya samu ya lallasheta amma tace masa daga yau in ya kara zuwa ya tuhumeta akan an batawa matarsa rai, sai ta yi masa bacin ran da zai dade bai manta ba. Zayyan yau da kyar ya samu Mama ta hakura da fadan suka koma hirar sallama da juna, don gobe in sha Allah da safe zasu kama hanyar komawa Abuja shi da Safiyyah, kuma ya san zai jima bai zo Katsina ba. ***** ***** **** Tunda suka dawo Abuja yake tattalin Safiyyah da farin cikinta. Duk abinda ya san yana faranta mata shi yake yi, duk abinda ya san yana bata mata rai ya nesantata da shi. Har wani dan outing ya tsirar musu fita yanzu kullum da daddare suje eateries ko shawarma joint daban-daban, girki kuwa Safiyyah iya cikinsu take yi su biyu ma’aikatan gidan su suke yin nasu. Ni dai mai rubutu! Nan kusa ban ga mace ‘yar gatan miji wadda miji ya gatanta ya ke tattali don ya mantar da ita matsalar rashin haihuwa, sannan ya girmama matsayinta a zuciyarshi duk da haka, wato duk da rashin haihuwar, irin Mrs. Safiyyah Rafindadi ba. Yammacin wata Lahadi ya dawo gidansa bayan motarsa shaqare da cefane da provision dinsu yadda ya saba duk karshen wata, Safiyyah ya samu tayi daidai da takardun zanenshi akan gado wai tana zane, ko sallamarshi kanta a duke ta amsa ba tareda ta dago ba, wai kada tayi kuskure cikin zanen da take yi, don a lokacin idea din zanen ke tuttudowa a cikin kanta. Ya cire bakar babbar rigarshi ta bakin yadin voile din filtex ya ajiye a gefenta, yayi mata duban rahma yace. “Lallai ma Sophie, wato zane kike shiyasa ko kallo ban isheki ba, balle in saka ran zaki mike kiyi welcoming dina?” Still bata dago ba sai ‘yar dariya data yi, ta cigaba da Zanenta bilhaqqi, don IDEA da hikimar zane sun cika kwakwalwarta a daidai wannan lokacin, so kawai take ta juyesu akan takarda don kada su gudu. “Afuwan Habiby, Afuwan kaji? Amma don Allah kada ka katseni”. Zayyan ya rasa me take zanawa haka da har ta kasa bashi attention dinta ko yaya, ya karaso gabanta ya tsugunna yana leka zanen, ya dora hannu saman bayanta cikin wata irin siga ta kulawar miji zuwa ga matar da yake matukar so. “To ko zan iya sanin me kike zanawa haka? Arch. Safiyyah Rafindadi? Na ga kamar ba gida ba, ba kuma Estate ba”. Sa a lokacin ta dago da murmushi tana kallon sassanyar fuskarshi, da kwantaccen sajensa ya kara ma fuskar kwarjini, fuskar da bata taba gajiya da kalla da sajenda bata gajiya da shafowa da hannunta koyaushe. Yanzunma haka ta kai hannu ta shafi sajen nasa with so much love, tace. “Habiby yau tsegumi kakeso? To ba wani abu bane nake zanawa irin naka ba, ko irin wanda ka sani, ni yau “Ultra-Modern Market” ce nake zanawa irin ta turawa. Ka tuna sanda muka yi tafiyar nan zuwa conference din “Ranar Masu Zane ta Duniya (World Architecture Day) da aka gayyace ka a birnin Berlin?” Muka ga kasuwar nan ta zamani harka ce min ta burge ka? Da zaka iya da ka zana ta? To tun lokacin abun na raina, ina jiran ranar da zan samu nutsuwa in kwaikwayeta in zana. To tsarin ta na dauka yanzu nake nawa zanen a kansa”. Da admiration sosai yake kallon zanen nata yana mamaki, kodayake in dai Sophiensa ce ai bai kamata yayi mamaki ba, in dai akan hikimar zane ne, in bata fishi ba, to zasu yi kunnen Doki, duk da yana gaba da ita a kwalin karatu. Ya shiga tattara takardun wuri guda yana turesu gefe yana fadin. “Ko kina sane da cewa kuma yau ce ranar cin abincin Zayyan ta duniya? It’s my lunch time! Yanzu dai ayi hakuri da zanennan a kawomin abinci, yunwa sosai nake ji a duniya, in na gama kuma a dumama min shimfida irin dumamawar da aka dade ba’a yi min ba. Baby, na rasa gane kan ki tun last week kike avoiding dina cikin dabara”. Murmushi tayi, don ta gane me yake nufi, ta dauki kayan zanen da takardun ta kai daya dakin ta adana su ta dawo. Kuma daga lokacin ta manta da zancen sabgar zanen kasuwa ta shiga hidimar hadawa Habibinta abinci, mai rai da lafiya wanda ta tabbatar zai gamsar da shi. Lafiya kalau suka ci abincin dare tare, tana shiga toilet da zummar tayi wanka, sai taga isowar bakon watanta. Tsaki tayi, daga haka ta soma kuncin rai ita kadai, sau tari hakan ce take kasancewa da ita duk sanda taga isowar period dinta, ta shiga kunci kenan, tunda alama ce ta cewa ciki dai bai samu ba har yanzu. Haka tayi wankan cikin dacin rai da bacin rai mai tsanani, domin ta saka rai, dama kuma in period dinta ya kusa, sau da dama behaviour dinta ya kan dan canza, ta zama ‘moody’. Shi bai san dalili ba amma a satinnan ya lura ta rage shige masa, kuma tana kakkauce ma haduwarsu a shimfida. Ashe dalilin duk wannan ne, period ne ya kusa yin sallama. Ta fito daga wankan kenan ta ganshi kwance a gadonsu daga shi sai shorts, yayi dai-dai a tsakiyar gado irinna jiran isowar uwargida yana waya, sai kawai taji ranta n abaci, aikin Habiby kenan soyayya da iya romance amma bai damu da haihuwa ba, Safiyyah ta fada a ranta. Daga yadda yake wayar (with respect) ta fahimci shi da Baba Murtala ne. Sai ta zauna akan stool din mudubi tana shafa lotion a jikinta a hankali, cikin son bata masa lokaci da rashin kuzari a tare da ita. Me ke damun Sophie ne? Idonsa ya kai ga saman kirjinta wanda ya ciko sosai saboda haihuwar data yi duk jikinta ya zama danye (fresh) dashi. Sha’awar matar tashi da baya taba gundura da ita (duk da baya samun yadda yakeso daga gareta saboda alkunyarta) nan take tazo mashi. Gashi yanada tafiya Lagos a washegari, kan wani muhimmin project na ginin flyover da Baba Murtala ya samo masa kwangilar yinsa. Hasali Baba Murtala aka baiwa kwangilar, amma ya barwa dan nasa, yace shi yayi madadinsa, don yana son ya shigar dashi harkar ginin bridges da flyovers bayan harkarsu da yafi sabawa da ita ta ‘Real Estate’. Ya gama wayar ya ajiyeta a gefensa, a lokacin ita kuma Safiyyah ta gama laqailaqan shafa man nata, ta sanya kayan barcinta masu dan kauri, tazo ta haye can kuryar gado ta kwanta, ta ja lallausar duvet ta rufe rabin jikinta. Zayyan ba haka yaken son ganinta ba, don alamu ne na bazata marabceshi ba, shikuma gaskiya yau din wata sabuwar samartaka ce ta bakunceshi, jin kansa yake at the zenith of his thirties. Ga tafiyar da zaiyi a washegari wadda zata daukeshi kusan sati biyu babu dumin Safiyyah a gefe. Yayi maza ya daga duvet din nata shima ya shige, ya mika hannu yayi musu light up. Amma da ya kai hannunshi gareta janyewa tayi kamar yasaka mata shocking, ta koma can karshen gado ta lafe abinta, tana faman kuncin rai. Da matukar lallashi a cikin sautinsa da taushin muryar da ba koyaushe yake mata amfani dashi ba, Zayyan yace “kada ki mun haka Sophie. I’m thirsty. Na lura fa tun shekaranjiya kike avoiding haduwarmu a gadon nan, kike min wannan ciccijewar dana kasa gane ta mecece. Ko meye dalilin wannan kuncin ran da kikeyi yanzu?” Murya can kasa Safiyyah tace, “Nifa babu komai”. Zayyan ya mirgina ya shige cikin jikin Safiyyah da azama, sosai yabi ya kanainayeta ta ko’ina ya like mata, ya ninketa bakidaya a cikin kirjinsa, yana gaya mata cikin radar jan hankalin masoyi da iya lallashin mace. “Idan kika juya min baya a daren yau, komai zai iya faruwa dani Sophie, kin san ke ce kadai maganin damuwar nan tawa, daga ke banida wata. Babu wani uzurinki da zan iya karba yau, sati guda kenan kina doje min, alhalin ban yi miki laifin komai ba”. Ya kai bakinsa saitin kunnenta yana cewa da ita cikin rada “hakurina ya kare Safiyyah, ki dubi girman Allah ki dubi darajar aure ki karbeni ko one round ne, haba Sophie me kike so inyi ne?” Maganarsa ta karshen nan har kunya ta bata. Amma Safiyyah ko gezau, don yau wani miskilanci ne ya sameta babu gaira babu dalili, tayi kememe tayi kemadagas ta ki yarda da shi da lallashinsa. Ta kuma kasa bude baki tayi masa bayanin cewa period dinta ya zo, ya canza mood dinta, don ta san kota fada din, in dai Zayyan ne ba hakura zai yi ba, bazai fasa cewa (she should try and find another way to comfort him) ba, ita kam ta fara gajiya da nacin Zayyan, tun bayan data haihu abin nasa karuwa yake, mutum ne very romantic sosai. Ita bata san cewa yanzu ne ta zama mace sosai a wurinsa ba, yafi samun nutsuwa da gamsuwa da ita a yanzu, fiyeda kafin ta haihu, tunda ta yada jego ya koma sabon ango shikuma, ya laqe mata kamar kaska, don tafi masa gardi da zaqi yanzun. Wannan ya biyo bayan kayan gyaran da Yaya Zubaina ta aiko mata na “Manzil Alwafir” dake Kaduna. (Duk wasu matsaloli na aphrodisiac ko gyaran aure “Manzil Alwafir” sunada maganinsu, including treatment na cutar PCOS da sauran matsalolin da suka shafi mata don gyara matantaka da inganta rayuwar aure. Manzil na aika kayansu ko’ina cikin Najeriya, za’a iya tuntubarsu ta wannan layin waya 09045065562). Safiyyah kam ta karba ne gun karamar uwarta Anti Dije bayan haihuwarta tayi amfani da kayan Manzil yadda ya kamata, bata ko san amfaninsu ba, bata kuma san abinda zasu jawo mata kenan ba. Yayi lallashin, yayi ban bakin, yayi ban hakurin in ma laifi yayi mata bai sani ba, amma Safiyyah ko a jikinta, ta ki bashi access din komai, koda kuwa na ya samu damar da zai sumbaceta ne. A karshe ma da ya fitineta da lallashin sai ta bara baki ta abinda ke cin ranta. “Ni kam wai don Allah Habiby, na dauka don samun haihuwa ake wahalar yin abinnan? To ni gara a daina kwata-kwata, tunda ba
Chapter 19 · 0% Book details