Sashe 16
Kawar Zuciya Part 2 Complete Hausa Novel · about 5 min read
data yada wanka wato ranar da ta kwana 40 da haihuwa ya shirya komawarsu gidan. Cikin ikon Allah a ranar sai ga mahaifinta Malam Usman da kansa a gidansu ranar da suke shirye-shiryen tashi. Haroun ya kawo shi har Abuja tun daga Dandume, a motar Haroun din. Nan suka shiga hidima da bakuntar babban bakonsu Malam, Zayyan da Safiyyah da su Sabah kowa hidima yake da zuwan Malam, su dora wannan tukunya su sauke wannan, ana wadata malam da cimaka ta alfarma. Ya wuni sur tare dasu cikin kauna da soyayyahr Uba mai girma, ya yi musu nasiha da wa’azi sosai akan muhimmancin karbar jarrabawar Ubangiji kowacce iri ce, komai dacin ta, da ribar dake cikin hakan watarana. Ya tunasar dasu tanadin da Ubangiji yayiwa iyayen da suka haifi da ya koma. Tare dashi aka tare ranar da yamma SUNSET ESTATE. Ya kwana tare dasu a sabon gidan a ‘guest wing’ Haroun kuma a hotel ya kwana, kusan kwanan zaune sukayi ranar suka raba dare a falon Safiyyah shida Zayyan da Safiyyah, yana mai basu sirrin addu’oin neman biyan bukata, abinda ya tadowa Zayyan kewar Baba Bello. Suka kasa tafiya suje su kwanta har asubah suna like da Mallam. Zayyan ya kara jin kansa maraya sosai da soyayyar da Malam kema Safiyyah, sai yanzu yafi jin kewar Baba Bello, ya san da Baba yana raye da abubwan dake faruwa da yawa basu faru ba, da tuni shi da Safiyyah sun ga gata a wannan haihuwar tasu, da kauna da tattali, a wannan lokacin da ba abunda suka fi bukata fiyeda kaunar iyaye da support dinsu. Tabbas da Baba Bello na raye, ba zai watsar masa da iyali yadda Mama tayi ba, alhalin tana ikirarin tana sonsa tana kuma kaunarsa, a matsayin tilon dan data haifa namiji ta kasa taya shi son iyalinsa. Sai yaji idanunsa sun kawo ruwa da hamma a lokaci guda, har Malam ya lura yace su tashi su je su kwanta haka. Da malam zai koma a washegari yace tunda Safiyyah ta yada wanka, ta kuma samu lafiya zai wuce da Sabah da Rayyah Dandume. Karon ta na farko da sake haduwa da Haroun kenan, tun bayan aurenta da yazo washegari daukar Malam zasu wuce. Gabadaya Haroun din Malam ya canza mata, ya zama babban mutum, Haroun ya samu cigaba sosai ta kowanne fanni na rayuwarsa, harkar danyen man fetur yake yi yanzu da ‘Dangote Refinery’, saboda abinda ya karanta kenan a jami’ar Maiduguri wato (Petro-chemical Engineering). Bayan gaisuwarta da Haroun ya amsa ya kuma yi mata ta’aziyyah bai bar wata kalma ta kara shiga tsakaninsu ba. Bai ko kalleta ba, abin ya tsaye mata don kuwa Haroun a can baya yafi kowa shiga sha’aninta ita ke basar dashi. Sanda akayi aurenta kuma ya koma Nsukka yana hada kwalin karatunsa na biyu kuma tun bayan aurenta in zata iya tunawa Haroun bai taba kiranta a waya ko sau daya ba. Al’amarinta da Yayanta Ridhwan (Yaya Shaikh) shi yafi komai bata mamaki akan na Haroun din Ammi, don in Haroun kishi yake tayi aure ta barshi, alhalin an san yana sonta tun tana karama, itama kuma ta san yana sonata koda bai taba furta mata ba. To Yaya Shaikh kuma fa? Kalmar so ko kwalli daya bata taba gittawa a tsakaninta dashi ba. Gara Haroun zata ce hatta Ammi ta sha gaya mata son ta yake yi, tun tana karama, amma yana kallon kansa a wanda bai isa ya aureta din ba, kasancewasa almajiri ga Mallam. A wannan zuwan da Malam yayi ne yake gaya mata cewa anyi auren Yaya Sheikh a Doha (Qatar), ya auri wata Shuwa Arab haifaffiyar Maiduguri da suka hadu a karatu mai suna Assafe. Da Malam yace zasu tafi tare dasu Sabah Zayyan ki yayi, don yaga yadda zaman nasu ya zamewa Safiyyah abin debe kewa, bata shiga damuwa da tunani saboda kullum suna gefenta suna kwasarta da hirar Ammi, sai ya shigo falon suke musu sallama su shiga dakinsu data basu. Don haka zamansu tare da ita ya taimaka ainun wajen dawowar walwalarta. Sai ya roki Malam alfarmar ya bar su Sabah su cigaba da zama tare dasu zuwa bayan sallah, don a lokacin an kusa shiga watan Ramadan saura sati guda wata mai alfarma ya kama. Da kyar Malam ya yarda ya barsu, amma yace sallah da kwana uku lallai-lallai ya gansu sun dawo Dandume. Malam da Haroun suka kama hanyar komawa Dandume washegari. Kulawar mijin kwarai irin Arch. Zayyan Bello Rafindadi, da addu’ar caring iyaye masu riko da addini irin nata, sun taimaka matuka gaya wajen dawowar nutsuwar Safiyyah, bayan rashin IVF babyn da suka yi. A kullum yana karfafata da cewa “data haihu, da bata haihu ba shifa yana sonta a haka, she will forever remain his ALTER EGO, sa’annan the only partner da yake son ya rayu da ita a duniyarsa da lahirarsa. Ba wani abu wai shi rashin haihuwa da zaisa ya juya mata baya. Yana rokon Allah ya taya shi akan hakan. Shi ita ya aura ba abinda zata haifa masa ba da baima sanshi ba. Cikin kalaman sa na koyaushe Zayyan ya kan ce mata “koda zasu mutu basu haihu ba, bazai taba amfani da hakan ya wulakantata ko ya goranta mata ba, ko ya juya mata baya ba wai dalilin rashin haihuwa. Ire-iren kalamansa masu dadi kenan da suka taru suka farfado da Safiyyah, ta soma komawa harkokin ta na yau da kullum, bayan rasa dan da suka haifa ta hanyar Dashe (IVF). A wannan gabar ne kuma bayan dawowarsu SUNSET ESTATE Zayyan ya bata gwaggawaban jari, yace ta soma business din duk da take so, duk don ta kwantar da hankalinta, da kokarinsa na faranta mata, a bisa wuyar data sha wajen samun ciki da haihuwar In Vitro Fertilized Baby dinsu, wanda ya kira da suna a cikin zuciyarsa “Areef”. ***** ***** ****