← Book details Kawar Zuciya Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 24 OF 29

Sashe 24

Kawar Zuciya Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

kanka. Ya taba ce min, yana son baudaddiyar halayyarka, abin da kowa bai so ko ake ganin disadvantage dinsa, sau tari kai shi kake so. Abinda baya burge kowa kai shi yake burgeka. Ya ce auren da ka yi shi kadai ya mara maka baya saboda daga Hajiya Fatu har ‘yan uwanka mata babu mai son auren saboda diyar Alaramma ce kuma stammerer. Da wannan nake cewa, ni kuma na baka Azeezah, ka nemi yardarta, in Allah ya sa ta amince da zarar mun gama wannan project din, sai mu durfafi daurin aurenku”. Shayin da basu sha ba kenan a yau, haka suka fita suka barshi a wurin ya huce. Baba Murtala farin ciki ya hana shi sukuni, suna tafe a hanya direban Baban na sharara gudu da su a bayan Hyundai din Alhaji Murtala, sai ya ji Baba na waya da Azeezah din. “Azeezah kina gida ne?” “Mun fita ni da Mama Agege, amma muna hanyar komawa gida yanzu haka”. Ya ce, “To ki shirya tarbar bako yau da daddare, wajen karfe takwas in na dawo gida”. A dukunkune da fuska ta ajiye wayar don ta yi tsammanin ya dauko mata malamin da ya ce zai dauko ya dinga koya mata karatun addini a gida ne. Ita a wurinta ta wuce zama gaban Malamin islamiyya yanzu. Baba Murtala kuma ya ce, ko izfi goma ya san bata hada ba. Don haka ko da suka dawo gida ita da Mama, bata yi wani kyakkyawan minti goma a falo ba, ta gudu dakinta tasa sakata. Zayyan sai goshin magriba suka dawo gidan shi da Baba, don haka masallaci suka wuce kai tsaye, wanda ke like da gidan Alhaji Murtala. Can suka zauna suka bi jam'i har bayan da aka idar da sallar isha. Ko a masallacin Addu’a yake cikin ransa, idan nemansa da Azeezah alkhairi ne a gare su, shi da Safiyyah, Allah ya bashi kwarin gwiwar iya tsayawa a gaban wata macen da sunan neman soyayya ba Safiyyah Dandume ba. Da suka fito daga masallaci Baba ya ce su wuce cikin gida su yi dinner, sai ya ce ma Baba yana zuwa. Ya koma masaukinsa ya sake wanka, yau Zayyan kananun kaya ya saka, shirt da wandon jeans baki Tommy Hilfiger. Zai fesa turare kawai idanun Sophie suka fado cikin nashi idanun, sai ya fasa. Don ji ya yi tamkar hakan ya zama cin fuska a gare ta. “To na nawa kuma Malam Zayyan? Tunda gaka ka dauki wankan zuwa zance gun budurwa?” Wata zuciyar ta tambaya ta kuma kara masa da ce masa, “You are no longer a trusted husband to Sophie, you are now a “man” like other men, who are guided by their heart desires and emotions”. Ma'ana; kai yanzu ba dan amanar Safiyyah bane. Ba mijin da zata bugi kirji ta yarda dashi bane. A yanzun daya kake da sauran maza babu banbanci, wadanda ke tafiya akan muradin zuciyarsu da shaukin dake zukatansu". Wannan tunanin ne ya sa jikinsa yin sanyi kalau, ya maida turaren muhallinsa ya ajiye. Ya fasa fesawa. Amma sai wata zuciyar ta tabbatar masa da cewa, kara aure ba cin amana bane ga maza, ba kuma cin fuska ne ga Sophie ba. Karewa ma, yana ganin zai nemi wannan auren ne don ya samar mata maslaha a zama da shi, sannan ya nemo mata nutsuwa da kwanciyar hankalin data rasa a cikin rayuwarsu. Muhimmi shine zai yi auren nan ne ma don ta samu Da daga gareshi. Wanda ya yi alkawarin nata ne da duk macen da ya haifa, kuma hakan maslahar ta ce a rayuwa da Mama, duk wata tsangwama, duk wani zargi na ta mallake shi zai kau daga idanun Mama yanzu. Da wannan tunanin ya dan samu karsashin nufar cikin gida. Wai shi Zayyan ne yau zai je zance gun budurwa ba Safiyyah ba. Yana taku a hankali kamar ya fasa zuwa zancen, musamman da yake jin tamkar idanun Safiyyah na kallonsa. Amma da ya tuno surar Azeezah da iya kwalliyarta sai nan da nan wata zuciyar ta ce, "Zayyan kada ka bada maza mana, polygamy ba kanka farau ba". Ya samu Baba yana waya, tuni an shirya musu abincin dare. Ya yafito shi da hannun damansa don ya zauna gefensa as usual. Sai da ya gama wayar sannan suka fara cin abincin Baba na masa hira. Duk da Baba Murtala ya fahimci yau ya kasa sakin jikinsa da shi, shi ya sa ma yake kara jan hirar tasu don ba ya so surukuta ta shiga tsakaninsa da Dan nasa Zayyan tun yanzu. Yafiso su ci gabada gudanar da rayuwarsu normal ta uba da Da yadda suke yinta. Sai da suka kammala Baba Murtala ya ce, ya shiga daga falon Hajiya Nana za ta turo masa Azeezah. Bai jima da zama ba Hajiya Nana ta turo ta falon. Azeezah ta shigo fuska a turbune don ta dauka ko Malamin islamiyyar ne ya fara zuwa, don daga Mama har Alhajinsu ba wanda ya gaya mata cewa Zayyan ne. Don haka da ta ganshi a falon ta kusan sakin fitsari daga tsaye. Duk ta rude, domin kwarai Zayyan mijin Safiyyah ke da kwarjini a idanun ‘yammata. Rasa me za ta ce ta yi, tunda dai ai ta san babu wata manufa da Baba zai turo mata shi in ba ta neman aure ko dalili makamancinsa ba. “Zauna mana Azeezah”. Zayyan ya fadi cikin tsare ta da idanunsa da suka kara ruda ta. Haka ta dosana ta zauna a nesa da shi akan hannun kujera. Ya gyara zama ya ce, “Kun dawo kenan?” Ta amsa da “Eh”. Tana wasa da ‘yan yatsunta. Sai ya yi gyaran murya ya ce, “toh dai Azeezah, ba sai mun ja ta da nisa ba, tunda dukkanmu ba yau muka san juna ba. Kuma diyan Baba ne mu duka ba bakin juna bane. Sannan ni ba yaro bane kamarki, na kusa shiga shekaru arba’in, kin ga kenan babu bukatar yin kwane-kwane ko bata wa junanmu lokaci. Azeezah na ganki a gidanku, gaban iyayenki kuma na yaba, in short I admire you, zan so kara ki cikin iyalina idan kin amince. Sunana Zayyan Bello, kamar yadda kika riga kika sani, ni dan marigayi aminin Baba ne. Ina da mace daya mai suna Safiyya, wadda tunda muka yi aure sama da shekaru goma ba mu taba samun matsalar da muka kasa warwarewa a tsakaninmu ba”. Ya dan nisa kafin ya sassauta murya ya cigaba da cewa. “Azeezah ni da matata muna da fahimtar juna, ina son kara aure ba don ta rage ni da komai ba, ina kuma barar shigowarki cikinmu, don kara dankon zumuncin gidanmu da gidanku. Idan har kin amince bana so abin ya dauki lokaci, don ni da ke babu bukatar sanin asalin juna, sai amincewarki kadai nake nema”. Duk wata kalma guda daya da yake yi a kan matarshi kular da Azeezah ta ke yi, har ta ce a ranta, wai shi wannan a wurinsa haka ake zuwa neman soyayyar budurwa? Da alama farin shiga ne gun zuwa zance wajen budurwa ‘yar zamani kamarta. Ba zai maida hankali wajen gaya mata irin kamun da soyayyarta ta yi masa ba, sai wani yan-yan-yan akan tsakaninsa da matarsa? Kamar ta yi kuka saboda ba wannan take son ji ba, ta ce cikin gatse. “Kuna da irin wannan fahimtar juna da soyayyar kai da matarka, to meye naka na son kara aure, kuma me ka zo nema a gare ni tunda ba so ba ne ya kawoka? In zumunci ne ai da abinku na ganku kaida Baba, so ko dani ko babu ni zaku cigaba da abinku yadda na riskeshi”. Tana fadin hakan ta sha mur sosai, ta dora kafa daya kan daya, don ta tsani rainin hankali irinna maza. Kwarai tambayar tata ta shammace shi, har ya rasa amsar da zai bata, hakan yasa ya baiwa kansa assignment na ‘yan sakanni. Don ya samu amsa kwakkwara da zai bata. Yana ganinta yarinya, mai tarin wauta, ashe-ashe tasan abinda take yi? Meye dalilin son kara aurensa? In har yanada komai da yake bukata a gidansa? Shine assignment dinda shima ya baiwa kansa a yanzu. Dalilai da yawa masu muhimmanci sun yi mujazar wannan son karin auren, domin yana ganin shine kadai maslaha a gare su shida Safiyyah, don yana sha’awar mace irin Azeezah a gidansa da rayuwarsa, yana son mace ‘yar gayu, mai wayewar kai, domin likely mace mai body shape dinta da irin dirarrun dugadugan kafar Azeezah itace daidai shi. Ustazancin Sophie yayi masa yawa, tsayin shekarun da sukayi tare da zata canza da tuni canza to ba’a sakewa mutum nature dinsa, wanda shi yake hana ta sakin jiki su yi irin soyayyar da shi yake so, for over a decade da aurenshi da Sophie yana ganin bai samu sakewarta da shi a gadon aurensu irin yadda yake so ya kai sau goma ba, saboda kunyarta da kawaicinta akan hakan, amma ba don bata sonshi ba. Azeezah za ta yi bridging wannan gap din, ga dukkan alamu, duk da tarin negativities dinta da mahaifinta ke kuka dasu, shi ba zai zame masa matsala ba in dai zai samu yadda yake so da ita, yake kuma kwadayin samu a gidan aurensa, ko da kuwa Safiyyah ta haihu, hakan ba zai hana shi wannan auren ba. Sannan idan Allah ya nufa ya samu haihuwa da Azeezah kafin Safiyyah dan ko ‘yar na farko da yardar ubangiji zai zamanto tukwicin kauna ta gaskiya ne da zai yiwa Safiyyah. A takaice sexual dysfunction din Safiyyah da neman mata yaro daga gareshi, su ne dalili kuma silar son kara aurensa. Azeezah ta kafe shi da idanunta tana jiran amsa, tana kuma ankare da yadda tambayarta ta jefa shi a gumi da tunani. Zayyan ya dago a hankali suka hada ido, sai ya yi mata murmushin da ya kara narka zuciyarta a kansa. Ya ce, “kisa a ranki babu namijin da zai zo neman aure a inda babu burbushin soyayya a ransa. I like you Azeezah, amma don Allah kalmar SO dinnan ki yimin jinkirinta, har sai na tantance ta a raina, kada in fade ta a lokacin da bai dace ba. Na yi miki alkawarin adalci da farin ciki a gidana, don ke kanwata ce da ba zan iya cutarwa ba, ina
Chapter 24 · 0% Book details