← Book details Kawar Zuciya Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 23 OF 29

Sashe 23

Kawar Zuciya Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

tushe a kan Sophie. To ni bama tare ma, ina Lagos gidan Baba Murtala tana gida Abuja ita, muna wannan project din dana gaya miki zamu yi kwanaki nida Baba”. Sai kuma ya sassauta murya ya ce cikin lallashi. “Don Allah don Annabi Mama ki dinga kyautatama Sophie zato. Mama don Allah. Ba wanda ya isa ya hanani zuwa inda kike”. Mama cikin gundura da zancen tace “to naji, yaushe zaka dawo daga Lagos din?” Zayyan yace “ganinan dai Mama, amma Baba yace zan jima, akalla zamu kai sati biyu anan kafin kammala project dinnan”. Cikin subutar baki za’ace ko zarar bunu, Zayyan ya nisa ya ce cikin rage sauti kamar mai tsoron kada wani ya ji shi ya furtama Mama abinda ke ta yawo a ransa. “Mama yau sai na ga yarinyar gidannan, kanwata Azeezah, ta wajen Haj. Nana Aisha, ta girma fiyeda zatona, kawai naji ta kwanta min, har naketa cewa a raina “ba don ba don ba….???” Zayyan ya hadiyi miyau da kyar, sai yayi shiru kadan na wucin gadi, yua kasa karasawa. Mama tayi gyaran murya tace, “ehem, ina jinka Baffa, ba don ba don ba me?” Yayi ta maza yace “Na ce da sai na yi wa Baba Murtala zancenta, in ji ko bai yi mata miji ba?”. Mama Fatu ta yi kabbara a ranta har kabbarar tata fito fili bata sani ba, cikin kokarin hadiye dokinta da zumudinta ga zancen, kada ya gane girman excitedness dinta, ta ce, “Ina zuwa Baffa”. Sai ta katse wayar tasu, ta fadi gaban Ubangiji ta fuskanci gabas ta yi sujjadah akan goshinta ta ce. “Allah na gode maKa da Ka nuna min wannan ranar ina raye, ranar da alkadarin diyar Alaramma ya karye a zuciyar Baffa. Yau Baffa da kansa ya ce min ya ga wata mace daban yana so bayan diyar Alaramma ba tareda na saka shi kona tursasashi ba”. Mama har ta share hawayen farin ciki da gyalenta. Ta rasa ina zata tsoma ranta don dadi da farin ciki. Saida ta nutsu, sannan ta yi gyaran murya ta sake kiransa, with so much excitedness Mama ta ce, “Baffa har yanzu kana kan layi?” Ya ce, “Eh Mama”. Ta ce, “To ka saurareni da kyau kaji abinda zan gaya maka yanzu, maza kayi gaggawar sanar da Baban naku, ina tabbatar maka yanzu ne za ka yi aure mai suna aure idan aka dace, aure na gata da mutunci, auren babban gida daya dace da kai. Sauran al’amuran ka bar komai a hannuna, in dai ka gaya wa Alhajin naku ka gama naka, ko lefe ni zan hada maka komai kaji Baffa”. Ya yi mamakin yadda daga ‘yar magana ta subutar baki Mama ta dauki zancen da matukar muhimmanci irin haka. A daren da kyar Zayyan ya iya yayi barci saboda tunani, a karshe ya tabbatarwa kansa ya kuma gayawa kansa kara aure shi ne kadai solution na dukkan matsalolinsu shida Safiyyah ta kowanne bangare ya duba yaga hakan shine kadai maslaha. Amma daga bangaren ita Safiyyah shin hakan zai zamo solution a gareta? Kuma ta wace hanya zai bi ya gaya mata yau shi Zayyan ya ga wata mace daban a duniya bayan ita ya kalla sai biyu, kuma yana so zai aura ya hada da ita? Duk da cewa ba haramun zai aikata ba, kuma bai taba yi wa Safiyyah alkawarin ba zai kara aure ba, amma Hausawa suka ce, wai ido da kunya! Saboda nauyin idanun Safiyyah da ya fara ji tun yanzu, tun ma kafin ya sanar da Azeezah din ko mahaifinta, sai yayi maza ya kara kashe wayarsa, gani yake yana bude baki don yin magana da Safiyyah za ta ji abinda ke binne a zuciyarsa yau, wanda yake shirin aikata mata, wato sha’awarsa ta kara aure. Don haka kashe wayoyinsa shi yafi masa komai sauki. Washegari tunda sassafe wayar Mama ce ta tashe shi daga baccin da ya samu bayan ya yi sallar asubah. Kuma yana dagawa ko gama gaisawa ba su yi ba, ta ce, “Baffa mu gode wa Allah, mu kara gode maSa. Yanzun nan na gama magana da uwar gidan Alh. Murtala wato Hajiya Nana Aisha, na tambaye ta ko an yi wa Azeezah miji, ta ce tukunna, amma akwai yaron da take tare da shi a Cyprus kafin ta dawo. Saboda haka don Allah don Annabi Baffa kada ka yi da wasa cikin maganar nan, da zafi-zafi a kan bugi karfe”. Shi dokin Mama a kan maganar ya fara ba shi mamaki, kamar dama a jirace ta ke da ya kyasa wata ya gaya mata? Ya ce, “Mama ki bi a hankali, I haven’t decided yet”. Mama ta ce, “Zancen banza da wofi kenan, ni har na saka Zubaida a fara hada lefe na alfarma, don ni wurina yanzu ne zaka yi aure na mutunci a inda ya dace Baffa, kuma aure daidai class dinka da matsayinka”. Bai ce komai ba har Mama ta kashe wayarta. Ya ce, “Hummm! Mama kenan. Kowa in bai da kudi da reputation to ba mutum ba ne mai mutunci a idonta. Ba wannan dalilin ne ya sa ya furta abinda yake ransa a kan Azeezah kenan ba, a'a shi ra’ayi ne da sha’awa suka zarge wuyanshi. Daidai lokacin Baba Murtala ya kira shi a waya ya ce masa yana jiransa su karya kumallo. A gurguje ya yi wanka ya shirya cikin ash colour yadin filtex mara kauri, ya sanya hula kalar kayan jikinsa data ciza sosai. Nan Zayyan ya fito a Zayyan dinsa, tamkar saurayi dan ashirin da bakwai ba mijin mace daya ba. Ya gama feshe illahirin jikinsa da ultraviolet dinsa, sannan ya rufo dakinsa ya karanta addu'ar fita gida da neman sa’a sannan ya nufi cikin gidan. Har addu'a Zayyan yake a ransa, Allah ya sa Azeezah ba ta falon, ko bata tashi barci ba, domin emotions dinsa a kanta suna kasa boyuwa in ya ganta har gashi Baba Murtala jiya ya kusa ramfo shi, watakila shiyasa ya shiga ba shi labarin rayuwarta. Addu'arsa bata karbu ba, domin kuwa yana shiga falon Baban da ita ya fara yin tozali, tana zubawa Baba Murtala tea mai ganyen na’a-na’a. Azeezah ta sha kwalliyar safe har ta gode Allah cikin wani ubansu combination na swiss lace da atamfar super orange and black. Zuciyar Zayyan ta doka ta sake dokawa da wani sabon infatuation da sha’awar Azeezah, amma a hakan ya daure yasa tsahonsa ya shiga cikin falon da sallama dauke a bakinsa. Cikin dakewa da karfin halin kauda idanunsa daga gare ta. Baba Murtala ya ce, “Zo daga nan gefena Zayyan mu sha tea. Ke Azeezah hada masa shayin na’a-na’a ya wartsake makoshinsa”. Ya durkusa gefen Baba ya zauna yana gaisheshi da safiya. Azeezah ta mike zata bar wajen, Baba Murtala ya ce, “Shin ke wace irin sakarya ce da kullum sai an ce ki gaida mutane sannan zaki gaishe su? Kuma shin baki ji nace ki hada masa tea irin nawa ba?” A gaskiya Azeezah ta tsani yadda Baba ke dizga ta a gaban yaron nan, don ta lura wani matsayi yake da shi mai girma a gun Babansu, tunda dan Arch. Bello Rafindadi ne, wanda tun haihuwarta ta ke jinsa bakin Baba da girman abotarsu a bakin Babanta Arch. Murtala Babangida. To ya za ta yi? Haka ta juyo da zummar gaishe shi, yayin da idanunta suka fada a cikin nasa. Saura kadan zuciyar Azeezah ta narke kamar yadda kitse yake narkewa in ya shiga rana. Hatta kalmar gaisuwar makalewa ta yi a makoshin Azeezah Murtala, domin sai yau ne tayi ma Zayyan Bello kallo na hakika don jiya ko kallon fuskarsa bata yi ba. Duk wata jijiyar da ke cikin jikinta sai da ta saki, ta karbi kwantaccen sakon da ke cikin idanunsa zuwa gare ta, kafafunta ma rawa suka hau yi, ta shiga gaishe shi da shakakkiyar murya da dimaucewa. Baba Murtala ya kara bada ita da cewa, “To shayin ma wato sai na sake cewa ki hada masa karo na uku ko Azeezah?” Saura kadan Azeezah ta fashe da kuka, sabida bazata iya hada wannan shayin ba. Hannunta da jikinta duka rawa suke. Zayyan ya cece ta da cewa. “Kyaleta ta je Baba, ni ko Safiyyah bata hada mun shayi, da kaina nake hadawa, kyaleta zan hada da kaina Baba”. Tsaki Baba Murtala ya yi, yana ta korafi dai a kan halin sangartar diyar tasa, har yana cewa, yana jin tausayin duk mijin da zai kwashe ta. Domin kuwa ba haka uwarta take ba. Murmushi Zayyan ya yi, beautiful serene smiles dinsa, wani tsadadden miskilin murmushi da ba koyaushe yake yin irinsa ba, ya ce. “To Baba ni in rage maka dawainiya mana? Ni ina sonta a haka, ka ba ni ina so”. Sakatoto da baki Baba Murtala ya yi yana kallon dan nasa, kafin ya ce, “Tau? Ubanka nake dai ba Kakanka ba, balle ka maida ni abokin wasan ka, ni ba sa’an wasanka ba ne Zayyan da za ka tsokane ni. Barni in sha ‘tea’ dina cikin dadin rai, kada ka sa ya huce min da shiriritarku”. Ya daga kofin shayinsa ya kurba. Zayyan ya dinga murmushi yana cewa, “In dai za ka ba ni Baba, ba zan yi maka wasa ko shiririta ba nima, ai babu irin wannan wasan tsakaninmu nida kai Baba. Uba ne da tilon Dan sa”. Kawai sai ya ga Baba Murtala ya daddage ya fashe da kuka. Jikin Zayyan ya yi sanyi, don ya dauka zafin maganarsa Baba Murtala ya ji, amma sai Baba ya kama hannunsa ya rike yana kallonsa da kauna ido fal hawaye. Ya ce, “Bar ganin ina zubda hawaye, Bello na tuno. Ya taba cewa, ba don ka yi aure da wuri ba da zai fi so ka auri daya daga cikin ‘ya'yana mata don kara dankon zumuncinmu. A lokacin sai na ce masa, kada ya kara irin wannan maganar kada mu taba tunanin yi muku auren hadi, wanda a karshe bata zumunci yake zama. Yau da ka furta da bakinka cewa, kana son Azeezah, duk da yadda nake ta kushe ta a idanunka, tun zuwanka Zayyan ban yabi halin Azeezah ko daya a kunnenka ba, ko sau daya ban fadi alkhairi akanta ba, sai hakan ya tuna min da abinda Bello ya taba ce min a
Chapter 23 · 0% Book details