← Book details Kawar Zuciya Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 11 OF 29

Sashe 11

Kawar Zuciya Part 2 Complete Hausa Novel · about 2 min read

ne haka? Har da zanyi magana ta karshe akai kice ta yi miki wahalar bi? Lallai shaidan yana son taka rawa a tsakaninmu akan maganar haihuwa, kuma sai akayi yaya bayan nan? Sai Tsimbirbira din ya ja ki dakinsa zai miki cikin haihuwa ki haihu, tunda ni mijinki ban iya ba…, ko saboda ni na kasa saka miki kwan haihuwa ko….?” Safiyyah ta kusa samun dan karamin hauka a lokacin, da wannan furucin nasa, da hanzari ta kai yatsu ta toshe kunnuwanta, kuka har da sheshsheka da majina tace. “Maganganunka sun yi min tsauri Zayyan. Ni dai na rasa me ya sameni a ranar, amma na yarda shaidan ne, na rantse da wanda raina yake hannunsa bai taba ni ba, ban shiga dakin da yace in shigo ba na samu kaina da gudowa. Habibi ko Ubangiji ana masa laifi a bashi hakuri, ya yafe, (why not you Habiby?) Ka yi hakuri ka yi min uzuri, koda da uzrin bacewar basira ta wucin gadi ne kadai”. Zayyan ya dago ya kalleta, Safiyyah ta kara fashewa da kuka tace “ka yarda wallahi komai nakeyi don mu haihu ne Habiby. Ina son ‘ya’yanka, ina son samun ‘ya’ya daga gareka koda guda daya ne, shiyasa na zama “desperate”, amma na tuba daga yau na hakura, na bi Allah na bi ka. Bazan kara zuwa ko’ina ba sai da izninka. Ta makalkaleshi kamar kyanwa, tana yamutsa shi kamar Baby a jikin uwarsa. Gabadaya Safiyyah ta jefa shi cikin wani tunani hade da tausayinta. Ya kuma gane da gasken gaske son haihuwar kawai take a ranta, in kuma bai taimaka mata ta samu ba, watarana zata jefa kanta a halakar da ba zata iya fita ba shima ta jefa shi, tunda an fara da bin kawaye gidan boka. Tun daga lokacin ne, ya shiga tunanin neman solution ga wannan matsalar tasu, don hankalin Safiyyah ya kwanta, shima ya huta da kwarzabar da yake sha a wajen Mama Fatu, akan zancen rashin haihuwarta. Ba don rashin haihuwar Safiyyah ya dameshi ba, ko ya zame masa matsala a cikin son da yake yi mata, ko ya zama nakasu a cikin rayuwar aurensu ba. Sai don kawai ya samo musu kwanciyar hankali bakidayansu. Dole ya sauka daga fushin nasa, yasa hannu ya dagota ya tallafota zuwa jikinsa, amma bakinsa da ya tafi yake sumbatarta kusufa-kusufa, bai yi shiru da yi mata nasiha ba, akan ta barwa Allah maganar haihuwa. Don shima ta fara saka shi a damuwa da son haihuwar tun abin baya damunsa sam.
Chapter 11 · 0% Book details