Sashe 7
Kasaita Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ban yi wani motsi da ƙarfi ba har na samu na buɗe barandar ta wacce zata kaini dakin Yarima, domin in sanar masa abin da ke faruwa. Ina buɗe ƙofarshi da makulli ba abin da na ci karo da shi sai ɗan sayon sayon safar jaririna ɗaya. Na sunkuya na ɗauka, sannan na ƙarasa cikin ɗakin.
Fitilar wayata dai na yi amfani da ita ina duddubawa, na yi murmushin da ya ratsa har zuciyata, saboda jin daɗi. Na lallaba na isa inda suke ƙwance. Ƙwance yake a rigingine ya ɗora yaron a ƙirjinsa, fararen kayan sanyi ne ya sakawa yaron,zaman da na yi a gefensu wannan yasa na kunna fitilar gefen gadon da suke ƙwance. Ƙyau Yarima ya ƙara yi mini. Na sunkuya na sumbaci goshinsa, tare da shafa gashin kansa.
Gani na yi ya buÉ—e idanuwansa a hankali, "Ka firgita ni fa."
Ya yi ƴar miƙar nan ta masu bacci, sannan ya tallabe yaron, ya miƙe zaune tare da sa ɗaya yana murtsikar idanuwansa alamar tashi daga bacci, har da ƴar guntuwar hammarsa. Zolaya ta sa nayi alamar tashi in tafi, sai a lokacin ne ma ya yi magana.
"Ina za ki kuma?"
"ÆŠakina."
"Da me ya kawo ki?"
"Neman yarona."
"Shi kaÉ—ai ya dame ki,ni fa? Ko yanzu ba'a yi da ni?"
"Na isa."
"Zo nan."
Ya nuna kusa da shi da hannu É—aya. Na iso na zauna.
"Dama na É—auko shi ne saboda ina son yin magana da ke,kin ga da wuya gobe mu samu ganin junanmu da zamu iya tsayawa mu yi magana, saboda jama'a.
Dama game da sunan yaron nan ne. Mai martaba ya mayar masa da sunansa, shi ne na ce bari na tambaye ki in ya yi miki,kin san shawara tana da daÉ—i."
"Yarima ba ka gajiya,in ba ya ga zolaya irin wacce ka saba yi mini,ya ma zaayi in buÉ—e baki in ce bana son sunan da Sarki ya sa. Kai dai ka faÉ—i maganar da ke damun ka, ba dai wannan ba."
"Ita ce mana, sai kuwa maganar zuwa gida wanka, gidan mu fa ake kaiwa, ma'ana wajen Mama za'a kai ki, gidan Sarki, amma za'a tambaye ki ra'ayin ki."
Ya kama hannuna É—aya, "Don Allah ki ce nan za ki zauna,a kawo miki masu kulawa da ke kawai,kin san Allah ko jakadiya kawai sai ta kula da ke, ballantana daga gobe kin gama wankan ganyen, magunguna zaki cigaba da sha."
Na yi shiru, tunanin ya za'ayi in ce bana zuwa. Na girgiza kaina.
"Ba zan iya ba, kunya nake ji."
"Kunyar me, ba gidan mijinki ba ne ba."
"Saboda me kai kuma ka ke son in Zauna nan gidan."
"Saboda ni."
"Ba ka da lafiya ne?"
"A'a,in dinga ganin ku."
"Ai can ma zaka dinga ganin mu ko?"
"Yasmin, Please understand me."
Na miƙe tsaye, "bari in tafi kada wani cikinsu ya farka bai gan ni ba, kaga kunya zan ji."
Bai ce mini komai ba, ya koma ya ƙwanta. Ni kuwa na juya na nufi ɗakina, amma sai na ji duk jikina ya yi mini nauyi.
Da na ƙwanta kuwa har gari ya waye ban yi bacci ba, saboda tunanin maganar Yarima ina son in ga jakadiya in gaya mata, saboda ko tana da dabarar yi, amma jama'a sun yi yawa.
"Subhanallahi!" Na faÉ—a a zuciyata, saboda ganin yanda jama'a suka yi yawa, har sun fi duk taron da aka yi. Cikin gidan kuwa jama'a mata da maza,cin abinci akeyi ban da kayan sha,kai abin ya yi mini yawa, har na zamo ba na iya gane komai.
Daɗina ma ɗaya ba yawo ake yi ba, zaune nake a saman kujerar mulkina a falon ƙasa, sai dai kowa ya zo ya kawo tashi gaisuwar,in kuwa na miƙe tsaye, to kaya zan je sakewa. Jariri Jafar Bn Jafar,yana hannun yayar Mamee Ruƙayya a riƙe, sai dai a leƙa a gansa, wanda kuwa yake da buƙatar ganinsa sosai sai dai ya kalli ƙaton hotonsa da ke manne a falona, wanda Mai Martaba ne ya aiko da shi.
Ƙarfe huɗu na yamma kuwa duk jama'ar da ke gidan mu ta dawo waje, ana gama sallah kowa ya nemi wajen zamansa, tamkar dai yanda suke yin kayansu, amma yanzu ya sha bamban da na baya, tunda na baya za ka ga jama'a bayan mu, yanzu kuwa daga ni sai Yarima, sai kuwa dogarawa guda bakwai da ke zagaye da mu.
#####
[2/21, 08:11] Ummi Tandama😇: *ƘASAITA BOOK 3*
*NA*
*MARYAM KABIR MASHI*
Page 6
Yaro Jafar Bin Jafar na hannun jakadiyar Sarki, tsaye wajensu Mama da Mamee da Hajiya Kilishi, ban da ragowar mutanen da ke bayan su. Dad É—ina kuwa ga kujerarsa ga ta Sarki.
Wasan ƙwallon dawaki aka fara yi (Polo), sai kuwa ɗan hawan Daba, sai wani wasa da shanu ke yi (Hawan Ƙaho), ban da wasanni da raye-raye da yare kala-kala suka yi. Saboda Yarima dai shi ne baya magana, amma ta hannu da ta ƙafa yake yi mini magana, shi ne yatsun hannuna ɗaya na riƙe da nashi yana ta wasa da su, ban da idan na gaji na ƙwace ya koma tsokanar ƙafa.
Duk bayan an gama wannan hidimomin ne wanda za mu iya cewa ƙarfe biyar da rabi ta yi, sai na ga wasu irin ƙartin mutane guda biyar sun shigo filin, kowanne ɗaure da bantai a jikinsa, ma'ana ba riga sai wata fata mai ruwan jinin kare ɗaure a ƙugunsu, ga shi iyakacinta cinyarsu.Waziri ne ya miƙe ya fara magana.
"Yau ne ranar da Allah ya kawo muka ga jikan Mai Martaba Sarki, rana ce ta farin cikin kowa. Duk wani wanda yake gidan nan ya san sunan yaron shi ne Jafar Bin Jafar, wanda ya gaji sunan Sarki kenan. Yanzu za mu ƙara tabbatar da cewa yaro namu ne, jinin mai girma Yarima ne, duk kuwa wanda ya tashi a gidan nan ya san ƙa'idarmu ce hakan, saboda haka jakadiya Bismillah."
Ni dai na sa ido in ga ikon Allah, na san kuwa ba ni kaÉ—ai ba, har danginmu gaba É—aya, shi ne Æ´an uwan Mamee da Daddyna.
Jakadiyar Sarki ta sauko daga sama riƙe da jariri a hannunta sanye da kayansa masu ƙyan gaske. Tana shigowa tsakiyar filin nan sai na ga ta miƙawa ɗaya daga cikin ƙartin nan ɗana. Na ɗan yi alamar zan miƙe, Yarima ya riƙe min hannu. Ban ko kalleshi ba, amma na san dai na koma na zauna.
Ina kallo aka tuɓe (cirewa) yarona kayansa gaba ɗaya, ya zamo tamkar yanda aka haife shi. Ganin ƙaton nan ya cilla jaririna sama yasa na yi saurin cakume cinyar Yarima da hannuna ɗaya. Sai a lokacin na ji Yarima ya yi magana, sai da ya jefa shi sama sau uku yana cafewa, sannan na ga ya miƙawa tsohon cikinsu.
Me zan gani? Gani na yi ya saka mini yarona a cikin ruwan nan da ke cike da uban bahon ƙasar nan,ai ban san lokacin da na miƙe tsaye ba na ce "Yarima kalli ka gani, za'a kashe shi." Da sauri na ga Yarima ya fizgo hannuna ya zaunar da ni.
"Yasmin ki ƙwantar da hankalinki, kada ki ba ni kunya. Ni nayi imanin Jafar ɗana ne,ni ne mutumin da ya fara sanin Mamansa,ni na san...."
Ai kuwa wannan tsohon mutumin yasa yarona cikin ruwan nan ya barshi ciki bai É—auko shi ba. Yarima ya matsa hannuna sosai, "Kalle ni." Na juyo na kalleshi.
"Me ki ka gani?"
"Ba komai." Na juya na kalli inda aka jefa mini yarona.
"Ka gani ko,ka gani ko." Jin ya yi shiru ya ƙyale ni yasa na yi saurin kallonsa.
Fuskarshi ba wata walwala da ya juyo ya kalleni. Ni kuwa har firgita na yi don tsoro, wannan yasa na yi shiru na zauna sosai, sai kuma hawaye da na ci gaba da zubarwa. Ba wani mai ƙwaƙƙwaran motsi a cikin mutanen da ke wajen nan, wajen ya yi shiru kowa yana kallon ikon Allah, tamkar a ce wani shugaban ƙasa ya iso wajen taron,an tashi za'a yi taken ƙasar su.
Abin ka ga uwa, sai na ji na kasa haƙuri, sai da na ƙara kamo hannun Yarima,ko kallona ma bai yi ba, na juya na kalli Dad ɗina,amma ban ga alamar hankalinsa ya tashi ba, kowa na kalla sai in ga hankalinsu ƙwance yake, sai dai alamun su da ya nuna suna jiran ganin abin al'ajabi.
Sai da aka ɗauki tsayin mintuna wajen sha biyar, sannan na ga yasa hannu ya ɗauko shi. Yanda aka yi masa da farko, haka ya yi masa yanzu, shi ne cilla shi sama sau uku. Inda na ga kamar hankalin Yarima ya tashi, shi ne a inda aka cilla shi na farko, sai na ga Yariman ya ɗan yi alamar miƙewa tsaye, na biyu sai na ji yasa kuka irin nasu na jarirai, sai na ga Mai Martaba ya miƙe tsaye.
Gaba ɗaya mutane suka miƙe tsaye aka dinga ihu da tafi,sai a lokacin na ga Yarima yana dariya, ya juyo ya kalleni, kallon da ni da shi kawai muka san fassarar shi. Hankici ya miƙo mini, ma'anar shi na goge hawayen fuskata, tare da cewa.
"Na gode." Cikin sanyin murya.
"Wata al'ada sai mu masu ita."
A nan na ga jakadiyar mu ta gangara tsakiyar filin nan, jakadiyar Sarki na karɓar yaron sai na ga ta baiwa tamu jakadiyar. Murna kuwa da jakadiyar mu ke yi kamar zata kifa don sauri.
Daga nan dai jakadiya ta ɓace mana, sai kuwa Sarki da ya tashi ya yi wa jama'arsa godiya tare da ni kaina da iyayena.
Ana haka aka miƙo mini jariri Jafar,wai zan kai wa Sarki shi. Kamar na yi ihu don kunya. Ganin na kasa tafiya yasa Yarima ya karɓa, ina kallo ya miƙawa Mai Martaba, shi kuwa ya ɗan tsaya yana nunawa jama'a shi, sannan na ga ya miƙawa wazirinsa.
Jafar ya yi lamo cikin baƙaƙen kayan sanyi, waɗanda aka ɗorawa ƙaramar alkyabba a sama. Waziri ya miƙawa Hajiya Kilishi wacce suke rukunin mata Iyaye. Ina kallo ta baiwa Mamee. Mamee da ƙyar ta karɓa,ni dai na san kunya hana ta karɓa tun farko.