← Book details Kasaita Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 11 OF 17

Sashe 11

Kasaita Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Hankalin Mai Martaba ya dawo jikinsa sosai, saboda duk ya ruɗe wajen neman su Waziri. To aikin da ya ragewa Yarima kenan, neman dattawan da suka rufa mana asiri da yanzu an hallaka mu. Bayan komai ya lafa ne muka ɗauko hanyar dawowa Kaduna. A hanya ne na ji zazzaɓi ya saukar mini,ga shi ko mun isa gida Yarima ba zama zai yi ba, zai tafi yawon neman su Waziri. Wannan shi ne dalilin da yasa muna isowa Kaduna na ce mu biya asibiti in ga Likita, saboda zazzaɓin da ya rufe ni cikin ƙanƙanin lokaci, wanda ni na san hayaniya ce kawai ta yi mini yawa.

Ina zaune a mota da yara da mai rainonsu a baya. Ni kuwa ina mazaunin kusa da direba, ina jiran in ga inda Yarima zai fito, saboda ba zan iya zirga-zirgar cikin asibitin Arewa Clinic ba. Ganin shi ya taho yana washe baki kamar na yi masa albishir É—in daÉ—i, duk da na san yau farin ciki yake. Sai da ya iso ya buÉ—e mota sannan na ga ya É—aure fuskarshi.

Ni dai ban ce komai ba, amma ina mamakin ganinsa hannu biyu da wata ƴar farar takarda a hannunsa. Abin da ya sa ban yi magana ba, tunanin ko biyawa za mu yi ƙyamus a siyi magani, amma har muka wuce duk inda za'a samu magani ban ga ya tsaya ba.

Ɗaki na nufa kaina tsaye, saboda yanda nake rawar sanyin zazzaɓi. Ina ƙwance Yarima ya shigo ya zauna kusa da ni.

"Tashi ki karɓi takardunki." Gabana kam ya faɗi, amma na yi saurin tashi na karɓa saboda ganewa idanuwana abin da ke ciki.

Positive (Pregnancy test) . Na ga an rubuta a jikin takardar. Na yi saurin dafe cikina.

"Ciki! Haba." Ya harare ni.

"To me kike nufi?"

"Haba Yarima ciki fa?"

"Kina ko ƙwanto ne?"

"Haba gani na yi duka yaushe na haihu?"

"Ko kina nufin ciki ɗaya ya yi kaɗan? Da gaskiyar ki,ƙato kamar ni a ce ciki ɗaya na yi. Tsaya ki gani in dage in yi na biyu yanzu."

Ya taho da sauri zai hayeni, na yi É—an hanzarin sauka.

######
[2/25, 21:47] Ummi Tandama😇: *ƘASAITA BOOK 3*

*NA*

*MARYAM KABIR MASHI*

Page 9

"Na tuba wallahi,É—ayan ma ya isa."

"A'a da sauran Waziri da yake gadin ƙofa, tsaya dai ki ga,ke kin ɗauka abin da wasa ne."

Saboda rashin lafiyar da ke jikina yasa na kasa gudu sosai, har sai da ya kamo ni ya É—auko ni cak, ya É—ora saman gado.

"Yau Celebration (murna) É—in shiryawa da Mai Martaba zan yi."

Yana magana yana tuɓe rigar yana cillarwa. Ga shi saman cinyoyina zaune,ni kuwa sai dariyar kukan shagwaɓa nake yi, ina haɗa shi da Allah.

Ya yi saurin sumbatar bakina, ya tsotsa, sannan ya ɗago ni ya tattara gashina da ya baje saman gado, ya riƙe da hannu ɗaya.

"Yasmin na gode miki da ki ka taimaka mini da rayuwa mai ƙyau, ingantacciya. Ga shi kina haifa mini ingantattun yara. Na gode Allah da....."

Muryar Ammar ce ta nufo É—akin mu. Da ji da gudu yake yana kiran.

"Dady ka yi baƙi masu kayan soja, ga su can a get a tsaye."

Cikin gaggawa ya miƙe tsaye yana kokawar mayar da rigarshi jikinsa. Ni kuwa dariyar ƙeta kawai nake daga ƙwance, har Ammar ya shigo, amma riga ta ƙi sanyuwa,dan ma Allah ya taimaka da wandonsa a jikinshi. Ammar na shigowa sai na ji yana cewa.

"Tsaya Daddy kada ka sa rigar."

Yarima ya yi tsaye da riga a hannu.

"Daddy tsugunna ka gani."

Yarima ya tsugunna, Ammar ya taɓa damtsan cinyar hannun Yarima.

"Wai Daddy ka ajiye chuka,ka fita haka,kai ma sojojin su ji tsoron ka,ka bibbige mana su,nima in na girma zan chuka haka."

"Za kayi amma daga yau tsoka ake cewa."

Ya dafa wajen ƙirjinsa,in tuɓe riga in ga ina da wannan."

"Amma ba yanzu za kayi wannan ba, sai kana cin abinci ka girma,ka zama babba kamar ni."

"Mama wai haka?"

"Kai fita ka barwa mutane waje. Ba na hana ka shigowa É—aki ba sallama ba da irin wannan surutun naka. Fita mana."

Ya juya tare da cewa, "Ki yi haƙuri Mama." Yana fita na taso na ja kunnan Yarima.

"Kai ma ba na hana ka biyewa surutun Ammar ba? Wata rana sai ya baka kunya a gaban jama'a."

"Sorry Mamo." Na ƙara shan kunu na juya. Ya yi saurin fizgo ni jikinsa.

"Sorry Mamo, ina son in na dawo inga an yi mani fara'a."

"To je ka an yi haƙurin, kada a daɗe a zo a bani magani insha."

"Pracetamol ne kawai za ki sha. Bari in É—auko miki."

"Ni dai gaskiya mai ƙarfi wanda zai hana komai zama cikina."

"Kada ki damu, ba mantawa na yi ba. Kin ga ko Ammar ya ce zan iya faɗa da sojoji,kin ga kuwa ƙyau na ace ciki bibbiyu nake yi." Na ture shi.

"Ni dai je ka."

Ya yi dariya ya saka riga ya fice. Sai da sha É—aya na dare ta wuce, sannan ya dawo. Da ganinsa kuwa a gajiye yake. Ya zauna kusa da ni cikin cewa.

"Wash!"

"Sannu."

"Ke dai bari wallahi, na gaji sosai, ta so muje É—aki,dama dai ni ake jira, bari in É—an watsa ruwa in ji sanyi."

"Abincin fa?"

"Zan ci, bari dai in samu kaina tukunna."

Bayan ya fito ne yake ba ni labarin cewa wajen su Sarkin ƙarya Abdulrahman ya je, saboda yasa a tuhume shi inda ya kai su Waziri. Da ƙyar ya faɗa, shi ma gani ya yi za'a kashe shi a banza. Kin san inda ya kai su?" Na girgiza kai, tare da matsowa irin na mai ɗokin a gaya masa.

"Suna babban gidan yarin Legos,ƙiri-ƙiri Prison."

"To ya za'ayi yanzu?"

"Sai gobe zamu je mu taho da su. Kai Allah dai ya kusan raba mu da ƙajaga."

Haka dai muka dinga tattaunawa har muka ƙwanta.

N.T.A Kaduna, gidan talabijin na ƙasa, shi muke kallo. Inda muka ga su Yarima na saukowa daga jirgi da su Waziri a bayanshi, sun kai su talatin, dukkansu kamar za su kife ƙasa saboda rama, ga tsufa,ko kuwa in ce yunwa. Amma kaya ne masu ƙyau a jikinsu, ga shi sun sha aski. Jakadiya kuwa, sai kuka take yi,wai tunanin wahalar da ta sha take yi.

**** **** **** **

Wata ɗaya kenan da sati uku da dawowar su Waziri wanda ya yi daidai da yau aka yankewa su Abdulrahman da Yayarsa Hadiza da uwarsu Asabe da sauran muƙarrabansu hukunci a babbar kotu ta jaha, wacce ta yanke masu hukuncin ɗaurin rai da rai, saboda bincike ya nuna Abdulrahman da mabiyansa an kama su da laifin fyaɗe, aikata aikin alfasha da maza, shaye-shaye,kisan kai. Ga shi dama wai sana'ar shi fashi da makami.

Hajiya Asabe uwarsu kuwa an kamata da laifin yin zina kafin ta yi aure, da ta yi kuma tana shigo da wani namiji a cikin gida. Tuhumar ƙarshe kuma ta tabbatar cewa su Abdulrahman ba ƴaƴan Sarki ba ne, sakamakon faɗi da tayi da bakinta cewa ƴaƴan faranta ne.

Hadiza kuwa zaman kanta take yi yanzu haka, ban da gidanta ne matattarar ƴan duniya, ban da bin bokaye da take yi, wanda ya bayar da tabbacin har maƙabarta an taɓa kama ta tana tono wani sashi na jikin matacce. Wa'iyazubillah. Allah ka cikamu da imanin mu,masu yi Allah ya shirye su. Na faɗa a zuciyata.

An yi an gama, sai rigima ta dawo kan Yarima, wanda aka zaɓa a matsayin shi zai hau kujerar sarauta, amma ya ƙiya, ya ce shi da Jos har abada. Wannan al'amari ba ƙaramin tayar da hankalin jama'a ya yi ba. Har ya zama garin Kaduna ƴan garin sun zo, tunda kullum ma samu baƙi ƴan baiwa Yarima haƙuri, da ba shi baki akan ya koma gida. Amma maganar shi ɗaya ce Kaduna ta yi masa, shi hankalin shi a ƙwance yake.

Yau kuwa manyan baƙi ne, wato ƙungiyar su Waziri, amma Yarima ya ƙiya. Da na je gaishe su suka dinga roƙona a kan in ja hankalinsa in nuna masa muhimmancin mutanen da zasu zauna a ƙarƙashinsa. Na bisu da to. Amma na san ba zan iya tunkarar Yarima da wannan maganar ba.

Su Daddyna sun zo tare da Mamee, amma sai ya ce masu insha Allahu zai yi,su bashi lokacin ya yi tunani. Haka suka tafi suna murna. Amma suna tafiya ya ce ai shi sam,kunyar su tasa ya amsa masu. To ni kuwa dama da na É—auko hanyar yi masa maganar, kallo É—aya yake yi mani in yi shiru. Wani lokacin ma har in samu la'adar cewa ba ni da hankali.

Sarki Jafar Sada ne yau da kanshi da Iyalansa gaba É—aya a gidan mu,Mama, Hajiya Kilishi, Ahmad,Yaya Salimat,Sauda, da Idris,Sarki ya yi gyaran muryar da dukkanmu sai da muka nutsu, sannan ya soma magana.

"Faysal my lovely son. Da farko zan fara da roƙon Allah ya raya maka zuri'arka, ya yi maka sakayya da aljannar fiddausi.

Faysal,sanin kanka ne ba mai raba ni da kai sai Allah, amma akasi ya faru tsakaninmu ta sanadiyyar yaudara da aka fara yi ta hanyar gaya mana aibunka da illolinka. Ban yarda ba da farko, sai da aka kawo mini shaida ta zahiri."

Ya buɗe wata ambulan ya miƙawa Yarima kaset da wasu hotuna.

"Duba!" Ya ajiye.

Ban kawowa raina komai ba. Ta haka ta fara yaudara ta. Ganin raina ya ɓaci matuƙa har na ɗan yi fushin ƙwanaki da kai,ai sai wannan hanyar ta ba shi damar shigo da abubuwan da na san sun daɗe yana tanadar su. Magana dai ni ke son ta wuce,a taƙaice ina neman a yi haƙuri a kan duk abubuwan da suka wuce,a taryi gaba,a kiyaye. Ko kana da magana?"

"Baba ni ban ce kayi mini laifi ba,ni ban riƙe kowa ba,ni dai nayi kokawar ƙwato maku ƴanci ne don kuna iyayena, amma ba don na hau gadon mulki ba. Na gode ƙwarai da ƙyautar da ka yi mini da nuna ƙauna, amma na barwa ɗaya daga cikin ƙannena,ai su ma sun girma. Amma ni Kaduna zan cigaba da zama, saboda hanyoyin cin....."

Ya miƙe ya je ya tsugunna ya kai gaisuwa. "Amma idan na ɓata muku rai ku gafarce ni." Ya miƙe ya shiga ciki.
Chapter 11 · 0% Book details