← Book details Kasaita Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 3 OF 17

Sashe 3

Kasaita Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Na matso na faɗa ƙirjinsa na ƙwanta tamkar ba ni ba, ina jin shi ya sumbaci goshina. "I love You Yasmin,I can't explain how much I love you. Amma ke kina ɓoye mini me ke cikin zuciyarki.

Yasmin kin san ba zan iya yin komai ba sai kina kusa da ni. Me yasa za ki takura mini in bar ki gida? Wallahi ba zan iya ba,in ba so ki ke inyi ƙwanan ƙofar gidanku ba, amma na lura ranki ya ɓaci don na hana ki. Yasmin ki yi tunani, ba ki da lafiya fa, ya zan iya ƙwatanta ƙwanan da zan yi a yau in na tuna haka?"

Jin maganganun za su yi yawa na san halin Yarima, yanzu zai iya shiga matsananciyar damuwa idan na yi masa shiru. Na É—ago nasa tsinin hancina a daidai bakinsa.

"Ka yi haƙuri ba zan ƙara ba. Wallahi nafi son ganin farin cikin ka fiye da nawa. Na fi kowa baƙin ciki idan na ga kana cikin shi. Ka yi mini afuwa,ɓata maka ran da na yi ba zan ƙara maimaitawa ba...."

Ya É—ago ni, "kin ci abinci?" Na É—aga masa kai.

"Are You sure?" Na É—aga kaina.

"Ai na yi wa likita waya, har ma na gayawa Mama na ce ta shaidawa Mai Martaba cewa ba ki lafiya za mu koma gobe."

"What? Haba Yarima, daga É—an amai kuma sai ka damu haka."

Na sassauta murya, "Ka yi ƙoƙarin ɓoye sona a zuciyarka,fitowa da shi fili zai iya janyowa mutane su tsane ni."

Ya É—ago ni sosai, "Su tsane ki,su waye mutanen? Wa ya fara canja maki fuska? Gaya mini,kina so in sa duk a kashe su?" Na yi saurin rufe bakinsa cikin tashin hankali, kamar yanda na ga har ya rikiÉ—e mini ya koma Yariman farko.

Na yi sauri na sulale ƙasan mota tare da riƙe hannuwansa.

"Za ka yarda da duk abin da na faÉ—a?"

Ya É—aga kansa.

"Wallahi ba wanda ya taɓa canja mini fuska, kowa na sona kamar yadda ka ke sona. Ina son cewa da kai ka rinƙa ɓoye na ka ne ka bar ni in dinga fito da nawa a fili."

Sai naga yayi ajiyar zuciya, amma kuma ya kasa magana, sai da ya É—ago ni ya rungume gam, tsayin minti biyu, sai na ji yana magana cikin sanyin murya.

"Yasmin ba ki san yanda nake jin ki ba a zuciyata. Kin É—auka wasa nake ko?"

"A'a na san..."

Ta yi daidai da buɗe motar da aka yi, ya yi sauri ya rufe cikin ƙiftawar ido, jikinsa kuwa tun a lokacin ya kama rawa. Na gyara sannan na ji ya ɗan ƙwanƙwasa gilashin motar, cikin gaggawa aka buɗe mana ta ɗaya ɓangaren, na fito, shi kuwa ta ɓangaren da yake. Sai a lokacin na fahimci gidan Aunty muka zo,gudun kada in ruga in baiwa kaina kunya da uban gidana yasa na tsaya tafiyar wahainiyar da muke ni da Yarima.

Falo kawai muka isa na dinga kwala mata kira. A firgice ta fito daga ɗaki, na ƙarasa da saurin guduna na rungume ta. Ita kuwa sai dariya take yi,tana cewa in sake ta taryi baƙon ta.

Mun samu sama da mintuna ashirin a gidan Aunty Salwa,sannan muka yi sallama da ita, wanda har alƙawari ya yi mini a gabanta zai kawo ni in yini in mun huta. Na dinga murna. Ganin jikin Yarima a sanyaye yasa har na fara shiga damuwa, na matsa na kama hannunsa tare da durƙusawa a ƙasan mota.

"Honey,me ye ya tayar maka da hankali? Wa ye kuma? Nima fa zaka jefa ni cikin damuwa?"

Ya ɗago ni ya zaunar da ni a saman cinyoyinsa, sai da ya sumbaci laɓɓana, sannan ya cire gilashin fuskarsa.

"Ke ce Yasmin, hankalina ya tashi matuƙa a kan ba ki da lafiya, amma ki ka ƙi gaya mini. Yanzu me iyayen ki zasu ce? Bana kulawa da ke?"

"Wallahi ni kaina ban san dalilin yin amaina ba,ni dai na san lafiyata ƙalau. Ni dai zan iya cewa ƙamshin turaren Daddy ne ya saka ni amai, kuma yanzu ni lafiyata ƙalau, zan iya yin komai, zan iya cin komai."

Na koma na ƙwanta a ƙirjinsa, "Kada ka ƙara damun kanka a kaina."

Sai na ga ya É—ago ni ko kasa me zai yi mini ya yi, sai kawai na ga ya dungure mini goshina.

"Kada ki ƙara faɗa mini haka."

A take ma sai na ji ya ba ni dariya. Na sa dariya irin ta nutsuwa, ya rungume ni, shi ma ya yi tasa dariyar irin ta su ta mulki.

A hankali na ga gilashin motar mu na sauka, wannan yasa na yi saurin sauka daga cinyar mijina na gyara zamana sosai. Subhanallah! Jama'a ne tamkar su ɓall gidanmu, tun daga get ɗin gidajen har izuwa harabar gidan mu. Jinjina ake yi, gaisuwa, amma yau Yarima ya burge ni, saboda ɗaga masu hannu da yake yi har da murmushinsa, mutumin da ba ya ko motsi idan ya shiga motar nan, to balle ma an canja wata motar wacce za ta iya ƙara masa girman kai, amma abin mamaki yau har da murmushinsa.

Motar mu na tsayawa na hango wani mutum a tsaye,shi kam tamkar wani saboda yanda na ga an zagaye shi. Sakan É—aya da tsayawarta aka buÉ—e mana,kirari irin wanda ake wa Sarakuna, shi aka dinga yi wa Yarima. Gaisuwa da sauran hidimomi irin na sarakuna.

Wani abin da ya fi burgeni, shi ne wannan mutumin da ke tsaye tsakiyar nasa dogarawan, shi na ga an yi saurin kawo aƙwatin kuɗi a gabansa, aka buɗe masa irin na matafiya,brief case. Yana ɗaukar bandir sai dai ya ɓalle ƴar takardar ya watsa su. Amma mutanen mu ko matsawa ba su yi ba, ballantana su san ana zuba kuɗi a gabansu. Sai dai ma dogari ɗaya da yake gabanmu yana share su gefe,gudun kada mu taka. Wannan kuma ina jin dokar Yarima ce,sai ma a lokacin na lura cewa ƴan ɗari bibbiyu ne ake wa wannan watsin da su.

A nan na saki da sha'anin Yarima, wato har dogarawansa ma ya san yanda yake tafiyar da su. Wani abin mamaki Yarima bai tsaya wajen mutumin nan ba, ya yi wucewarsa, sai me? Ai tun daga barandar gidana na ga gidana ya canja. Ƴan matan gidana kuwa, duk sun taru a barandar, suna hango ni sai murna. Ni kaina duk sai na ji na ƙara ƙaunarsu. Mansura kuwa har da gudunta, ta iso ta durƙusa gabana ta kama hannuna. Na yi murmushi na ɗago ta, sai tasa kuka. Na yi murmushi na kama hannunta muka tafi.

#####
[2/19, 22:29] Ummi Tandama😇: *ƘASAITA BOOK 3*

*NA*

*MARYAM KABIR MASHI*

Page 3

Lallai Yarima " Na faɗa a zuciyata,ganin duk ya ƙyale mutanen da ke bin bayansa ya biyo ni gidana. Sai dai na ga ya yi wa wani dogari nuni da hannunsa. A take na ji dogarin na cewa.

"Yarima ya ce a jira shi ya huta. Yarima na gaishe ku. Nan da awa biyu zai fito."

Me zai faru? Ina kunna kai a gidana, na ji wani ƙamshin turaren wuta na tashi. Nan take kaina ya fara juyawa. Cikin ɗan sauri-sauri muka gaisa da jakadiya da jama'arta. Haka shi ma Yarima na ga yana gaisawa da su. Ko lura ya yi,ai muna hawa sama a guje na ƙarasa banɗaki. Yarima na bina shi ma tun kafin in kai ɗan wajen alwala,bath amai ya kubce mini. Alkyabbar jikina kuwa sai dai wata.

Yarima riƙe da ni na dinga ƙwaranya amai kamar dai yanda na yi a gidanmu. Nan take na ji Yarima na waya cikin mutanen shi na ji ya yi wa ɗaya magana. Wai ina likitan da ya ce ya zo gida ya jira shi?

Nan take na ji yana cewa,nan da minti biyar ya hayo sama da sauri yana son ganinsa. Ni kuwa har amai ya kai sai dai ruwa-ruwa, saboda abincin ya ƙare.

Ina gamawa Yarima ya kama ni wanda jikinsa har rawa yake, ya cire mini alkyabbar jikina, ya wanke min fuska. Ban da sannu da yake yi mini, ya ɗago ni idanuwansa sun yi ja, ban da hawayen da suka cika su, ya dinga shafar fuskata. Lallai na amince Yarima son gaskiya ne a jikinsa, saboda ya rasa me zai ce mini. Ya kama ni muka fito ɗakina, ina fitowa wani sabon aman ya taso. Na koma ciki da guduna. Ya biyoni ya yi tsaye a kaina, ina ta faman yunƙurin aman da ba komai a cikina.

"Mama Yasmin zata mutu ta bar ni. Ki zo Mama."

Wannan maganar da ya yi ita ta tabbatar min waya ce ya yi, duk da ban iya É—aga kaina na kalleshi ba.

"Ka hawo kawai." Wannan ya tabbatar mini da likita yake. Da sauri na ga ya fita, sai na ji yana cewa, "Shigo nan ka ganta. Sau uku kenan tana yin shi a yau,kaga har ya zamanto ba komai a cikinta, kalli yanda take?"

Likita ya sunkuyo, "Sannu Madam." Na É—aga kaina kawai."

"Me ke saka ki amai?"

Na ɗaga masa hannu alamar ya jira, suna tsaye,Yarima na ta safa da marwa a banɗaki. Har tsayin mintuna goma, sannan na ɗago, wanda a take na ji jikina na rawar zazzaɓi. Ban da jiri da nake gani.

Yarima ya riƙe ni muka fito ɗaki. Muna fitowa na yi saurin komawa banɗaki.

"Yarima bana son warin turaren wutar nan, kaina juyawa yake yi."

Nan da nan ya kuma ruÉ—ewa, "Doctor, ya za'ayi?"

"Yallaɓai ko a tafi da ita sashenka mu gani."

"Haka za'ayi."

Da sauri na ga ya buɗe ƙofar, bayan wacce za'a fita barandar baya, wacce ke kallon ta gidan Yarima, sai da ya buɗe, sannan ya kamo ni. Muna fita madadin in ga fili kamar da, sai na ga an gine ta, ta yi wani zagaye kamar ƙaton fayif na ruwa, ga fulawoyi na gaske nannaɗe da jikinsa.

Ban iya tsayawa na lura da yanda aka yi ta ba sosai, ni dai na ga muna tafiya har mun ɓulla ƙofar barandar Yarima. A take na ga ya buɗe mun shiga, sai na ga ɗakin Yarima. Yana isa ya ƙwantar da ni a gadon shi, ya janyo bargo ya lulluɓa mini,sannan ya koma ga kaina ya zauna, inda likita ya matso ya tsugunna gabana.
Chapter 3 · 0% Book details