← Book details Kasaita Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 15 OF 17

Sashe 15

Kasaita Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Ki yi shiru Yasmin,ke dai kawai ki taimaka mini da murna, da addu'ar godiya ga Allah da ya bar mini ke."

Hawaye ya tsiyayo a kumatunsa. "Ba zan taɓa iya ƙwatanta miki yanda na ji rayuwata ta koma ba a cikin ƙanƙanin lokaci."

"To ba sai..."

Jakadiya ce ta yi sallama, muka saki juna, sannan na ce ta shigo. Ta shigo tana rawar jiki da yaro rungume a hannunta. Har a lokacin ban fahimci me ta shigo yi ba, sai da ta durƙusa gabanmu tare da gaisuwar ta ta miƙo mini yaron hannunta. Sannan na tuna ashe fa haihuwa na yi,ni na ma yi tunanin abin da na haifa ya mutu, shi yasa ban ma neme shi ba.

Yarima ya miƙa hannu ya karɓa, ya ce da jakadiya, "Su Mai Martaba suna nan?"

Ta amsa da, "Suna fada,su Mama ne dai suka tafi."

Ya miƙo mini jaririn hannunsa ya miƙe.

"Tsaya ki kula da ita,in je in dawo"

Jakadiya ta ce, "To." Shi kuma ya sunkuyo ya sumbaci goshina sannan ya tafi.

Sai da na ga fitarsa sannan na dawo da kallona ga abin da ke hannuna, "Mace ce ko namiji?" Na tambayi jakadiya.

Ta amsa da "Namiji ne."

"Ina Suhailat?"

"Mama ta tafi da su ita da Ammar."

"Me yasa ba su zo yi mini sallama ba?"

"Saboda Yarima. Kai Gimbiya ki godewa Allah, Allah Yarima yana son ki,sumansa biyar da aka ce masa kin mutu. Ki duba taurin rai irin na Allah ya ja da rai, amma sai ga shi yana kuka a gaban kowa."

Na yi murmushi irin na wanda ya tashi daga ciwo, sannan na lalubi mama na sawa jariri a baki. Sai da ya kama maman, sannan na samu damar kallonsa sosai, abin ka da jariri sai na kasa gane da wa ya yi kama. Ina cikin ƙoƙarin gano hakan Aunty Salwa ta shigo.

**** **** ****

Rana ta zagayo aka sawa yaro suna Abdul Nasir,amma ba a yi wani taro ba, saboda jikina ya ƙara warwarewa, saboda haka Mai Martaba Sarki ya ce a barshi sai wani satin. Wannan yasa aka ƙara sa masu kulawa da ni su matso kusa da ni domin kulawa da ni sosai.

Su Ammar kuwa sun zama Æ´an gidan Mama, saboda sai dai su zo da yawo su koma.

Bayan ƙwana uku da raɗin suna sai aka shigo falo na uku wanda nake zama domin hutawa, aka ce na yi baƙi. Ban tsaya neman ba'asi ba na ce su shigo. Sauran kaɗan in saki Abdul-Nasir ƙasa, saboda mamakin ganin baƙin su huɗu da na yi. Maza biyu, mata biyu,ba zancen koƙwanto na gane su, duk da sun canja kamaninsu. Cikin al'ajabi na kira sunan ɗaya daga cikin su.

"Mansura! Daga ina ku ke haka?"

Madadin su yi magana, sai kawai na ga Mansura tasa kuka, Æ´ar'uwarta Musulum na taya ta ko kuwa in ce suna taya juna.

"Su waye waÉ—annan?" Na tambaye su.

"Mazanmu ne, wannan mijin Mansura, wannan kuwa nawa."

"Daga ina ku ke haka? Ya aka yi ku ka san muna nan? Wa ya nuna muku gidan?"

"Mu ma labari muka samu, shi ne muka ce bari mu zo. Yanzu kuma muna ƙauyen Fembeguwa a zaune, saboda tsoron zama cikin birni gudun kada a sa a kamo mu."

Na kalli wacce ke kusa da ni, "A tafi da su wajen Sarkin gida ki ce baƙina ne a basu ɗakuna biyu, kowacce da mijinta. Ke kuma ki sa a basu komai da komai,ki tabbatar sun ci abinci.”

Na juya ga su Mansura, "Ku je a baku masauki zan neme ku in kun huta."

"Mun gode. Amma za mu koma mu É—auko yaranmu."

"Kun haihu ne?*

"Eh, yaranmu bibbiyu."

"To shi kenan, amma da mazan nan naku su je su É—auko su."

"To Gimbiya, haka za'ayi." In ji mazan.

Daga nan suka miƙe,. Har sun kai ƙofa na kira Sa'a.

"Ki ce wani ya kai su su ƙwaso har kayansu."

"Tanko direba ko Brown?"

"Duk wanda aka samu."

Suka juya suka tafi suna ta godiya.

**** *** ****

Yau garin Jos ya ruɗe saboda hidimomin bakukuwa ga taron sunana da nake yi, wanda gaba ɗaya taron gidan mu ake yin sa. Duk girman gida irin namu, wanda zai kai kilo mita uku, amma cike yake da mutane. Get uku ne a ƙofar shiga, kenan wacce ke kallon kudu a kowanne zagayen get gidaje goma ne na fadawa.

Get É—in farko yaran gida ke zaune a cikinsa, kenan masu yi mana hidimomi da yi wa dawaki, fulawoyi. Kai aikin gidan gaba É—aya. Get na biyu kuwa Æ´aÆ´an dogarawa, wasu daga cikinsu, wanda shi ma gida goma ne. Get na uku ne ke da gida ashirin na dogarawa.

Idan an shiga daga ɓangaren gabas,ƙaton falo ne ƙwaya ɗaya, sai ɗaki ɗaya ƙaton gaske,an yi shi ne domin saukar Mai Martaba Sarki na ɗaya, sai ɓangaren yamma kuma barandun sama ne aka yi guda huɗu. Kenan kowanne ɓangare da aƙwai baranda sai ƙaton fili daga tsakiya,an tanade shi ne saboda wani gagarumin taro kamar na yau. Filin dai kamar filin wasan ƙwallon ƙafa (Football).

Ɓangaren Arewa ƙaton masallaci ne a cikin shi,aƙwai Islamiyyar yara da ta manya, wanda mata su yi da safe, da yamma maza su yi da daddare. A nesa da masallaci aka yi gidaje biyar. Limamin masallacin ke da ɗaya, ragowar huɗun malaman Islamiyya kowanne da matarsa da ƴaƴansa.

Idan aka iso ƙofar shiga gidan daga yamma kaɗan,ƙaton asibiti ne mai ƙunshe da ɗakuna taƙwas na jama'a kenan, sai ɓangaren manya aka yi wa likitoci hudu kacal. Dukkan gidajen ɗakuna biyu ne da falo a cikin shi, sai kuwa ɗakin samari a bayan gida, wanda yake tare da banɗakinsa.

Manyan falo taƙwas ne a gidan, uku na shi, uku nawa, dukkansu na karbar baƙi ne, amma ƙofa biyu ce ta shiga gidan da ƙofar shiga falona, sannan da ta shiga nashi falon.

Ɗaya cikin ɗaya ne, sai in da muke son zama. Ganin baƙin idan aka fita daga falukan namu da aƙwai wani fili a tsakiyar falukan, wanda ya ƙunshi ƙofofi biyu. Ɗaya ta shiga falon sa, koma in ce sashen shi, ɗaya kuwa ta shiga nawa sashen, amma idan ka shiga falo ne kowa a farko shine falukan mu mu da yaranmu. Kenan personal falon mu,amma kuma daga cikin falon kowa zaka iya shiga na ɗaya, kenan haɗe muke waje ɗaya, sai dai kowa da ɓangarensa.

Ɓangarena ɗakuna baƙwai ne, amma ɗaya ne nawa, sai na yara ɗaya, na ƙwamfuta ɗaya. Haka nan yake ba kowa a ciki,an yi shi ne kawai saboda baƙin a na kusa. Biyu kuwa na masu kula da ni da gidana da ƴaƴana, wanda su nasu kamar an yi su ne daga gefe ɗaya tare da banɗakinsu har da ƴar barandar su ta shan iska.

Nasa ɓangaren ɗakuna biyu ne kacal, ɗaya nasa, ɗaya na ƙwamfuta (Computer). Tsayawa lissafa abin da ke cikin gidan ma asarar baki ne, saboda ya dame gidanmu na farko sau ba iyaka. Idan kuwa an fita daga cikin ƙofar shigowar kuwa,nan kicin yake da sito, kenan ƙofar shigowa falona na cikin gida, amma na taryar baƙi, saboda ni biyu kenan cikin gida, ɗaya kuwa na cikin gida na karɓar baƙi, ɗaya ƴan gida ko mabuƙata.

In an zagaya bayan gida, barga ce, kenan ɗakuna ɗai ɗaya da banɗaki a jere guda taƙwas na ma'aikata ne masu yin abinci mata, da kicin ɗin su ƙaton gaske na yin abincin ƴan barga da duk wani baƙon da zai yi sallama, da wajen ajiye ajiyensu na kayan abinci.

Gefensu daga ɗan nesa kaɗan gidaje ne uku a kulle,su ma ɗaki biyu da falo ne, bayan gida duka kuwa ƙaton lambu ne cike da kayan marmari, waɗanda ba rani ba damina, duk kullum da ƴaƴan a jikinsu, amma tsakiyar lambun ruwa ne ke gudu ta ko'ina ka waiga za ka ga duwatsu, ballantana ma cikin lambun.

Yau ne aka ɗaurawa Ahmad aure shi da Idris ƙannan Yarima kenan, waɗanda suka auro ƴaƴan daga wajen garin nan. Ahmad ɗiyar Daraktan (Director) ce a Katsina, wanda suka haɗu da yarinyar a ƙasar Spain,inda ya yi karatunsa, wanda ita ma karatun ya kai ta. Duk da ita ba ta gama ba, saura shekara biyu, wannan yasa ma in an gama bikin can za su koma da zama har sai ta kammala, shi kuma zai yi wani karatun tattalin arzikin ƙasa a matsayin digirinsa na biyu.

Shi kuwa Idris ɗiyar Sarkin Dutse ce ta jihar Jigawa. Yara ƙyawawa, Fulanin asali ƴaƴan Sarkin adalci na ƙasa. Ana cikin hidimar biki ne na ga Mabaruka, muka gaisa. A nan ta ke bani labarin ta yi aure har ta haifi ɗan ta namiji yana gida ta baro shi. Nan ta yi mini barka da arziƙi.

**** *** ****

"Kai na gaji!”

Na ce daidai lokacin da na ƙwanta cinyar Yarima, wanda ke lallaɓa Nasir ya yi bacci. Ya waiga ya ja kunnena wai faɗan zan tashi Nasir. Na yi ƙara, haka kuwa ya sa ya tashi, da guduna na ruga saboda na san Honey zai iya cizona a kumatuna ko ma na sha mintsini.

Ya cije leɓe, "Zan rama ne."

Na yi masa gwalo. Ya ɗauko Abdul Nasir ya biyoni a guje. Abin ka da ƙaton ɗaki, sai na dinga zagaye a ciki. Kafin ya kamo ni jakadiya ta yi sallama. Na tsaya tare da kallon agogo. Ƙarfe sha ɗaya na dare,me jakadiya ta zo yi yanzu ɗakin mijina?.

Kafin in gama tunani Yarima har ya bata izinin shigowa. Tana shigowa ta yi saurin zama ƙasa.

"Allah ya ja da rai an iso da ita, tana ɗakinta.”

Ya yi shiru ta kai minti uku, sannan na ji ya yi magana.

"Ki ce ina yi masu sannu da zuwa. Bayan minti ashirin ki kawo ta nan ta gaishe da Yayarta,su san juna."

Na yi tsaye, amma ban fahimci komai ba, har jakadiya ta gama kirarinta ta tafi.

Inda na ke tsaye ya iso yana dariya, ya kama ni, "Na kama ta! Na kama ta!! Nasir mai za mu yi mata?"

Yasa hannu ya mintsini kunci na É—aya.

"Tsaya don Allah Yarima,wai wacece aka kawo? Ban fahimci maganar ku ba?”

"Za ki gan ta yanzu.”

"Wace ce?"

######
[3/2, 15:46] Ummi Tandama😇: *ƘASAITA BOOK 3*

*NA*

*MARYAM KABIR MASHI*

Page 13
Chapter 15 · 0% Book details