Sashe 13
Kasaita Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ƙarfe tara na dare shi ne ƙa'idar tashin Yarima daga fada, saboda ya samu lokacin hira da iyalinsa. Yau ma kuwa haka ya shigo gida, ya sameni ƙwance a ƙasan kafet ɗin da kusan launinsu ɗaya da katifa. Suhailat na ƙwance a gabana ta yi bacci. Yanayin yanda fuskarsa ta nuna shine yana tausaya mini. Yana isowa ya sunkuya ya ɗauki Suhailat ya kai ta ɗakinsu, sannan ya dawo ya durƙusa a gabana. Ya sunkuya ya sumbaci kumatuna.
"Sannu." Na É—an yi fari da idanuwana
"Wallahi Yasmin ina tausaya miki."
*Ni kuma kai nake tausayawa, saboda aikin da ke gabanka na jagorantar mu. Ga ni da ƴaƴanka,iyayenka da nawa,ga jama'ar garin. Ga jama'ar garin nan ba ki ɗaya duk fa a ƙarƙashin ka muke. Yanzu in mutuwa ta kama ka ka ce da Allah me?"
"Wallahi kuwa,ai shi yasa nake son in ga kin haihu lafiya sai mu zauna mu yi shawarar ya zamu yi balle dama duk inda muka je an ɗaukar min shi a kaset, sai mu sa a tsanake mu ƙara gani."
"Honey,tunda haihuwar ta ƙi zuwa me zai hana a fara, tun da idona da bakina za su yi aikin ba cikina ba. Yanzu da ka ce a bari sai na haihu,to in na mutu wajen haihuwar fa..."
"Haba Yasmin ki daina irin wannan mummunar maganar ta ƙananan yara,me ki ke so na koma idan na rasa ki?"
"Baka zama komai."
"Na ji nidai ba na son ki dinga yi mini irin waÉ—annan maganganun marasa daÉ—i da É—aci."
Ya juya har da ɓata rai sosai. Hannu na sa na juyo fuskarsa.
"Sorry, ba zan kuma ba na daina." Na faÉ—a cikin muryar nadama.
Ya ɗago fuskata ya ƙura mini ido, sai kawai na ga ya kai bakinsa ga nawa. Mun yi minti huɗu ya ɗago.
"Yasmin ni fa har yanzu son ki bai taɓa raguwa a zuciyata ba,kin san Allah duk every day, every time, every minute,every second,sai na ji sonki yana ƙaruwa a zuciyata. Ki daina gaya mini maganar da raina zai ɓaci,ki tayarwa da mijinki hankali,kin ji?" Na ɗaga kai alamar eh.
"To bari na É—auko kaset É—aya mu fara da shi."
Na yunƙura zan tashi ya yi saurin kama ni, na miƙe.
"Ina za ki?"
"Da abin hira zan É—auko maka,in samu kuma in cire maka kayan jikinka."
Ya ja kunnena, har sai da na yi ƴar ƙara.
"Ke É—in nan ba ki jin magana,sau nawa ina gaya miki cewa idan ina cikin gida kusa da ke na zama É—an aiken ki.?"
Na narke na yi irin alamar kukan shagwaɓa, tare da maganar shagwaɓa.
"Ni Allah ban yarda ba,ni sai in dinga baka wahala."
"Wallahi na cije bakinki idan ya ƙara yi mini gardama."
"Ni! Ni! Dai...." Ya zare takalman ƙafarsa zai ƙwala mini cikin haushi. Na yi gaba da ɗan guduna, ina kiran.
"Na daina, na daina, Allah....."
Ya kamo ni saboda irin yanayin gudun mai ciki. Ya É—aga takalman, na runtse idanuwana alamar tsoro, sai na ji ya zagayo ta bayana ya rungume ni yana dariya.
"Ga tsoro ga jan faÉ—a."
Dama yanda yake rungume ni kenan idan ina da tsohon cikin da zai hana masa sakewa ya rungume ni ta gaba. Ya sumbaci wuyana.
"To mu je in taya ki É—aukowa."
"To tsaya in cire maka alkyabbar ko?"
Ya juya baya na zare masa alkyabbar jikinsa na ajiye saman kujera, sannan muka isa kicin.
Ba wani abu ba ne mai wahala ba abin hirar tamu. Tuwan abarba ne da inibi,an markaɗe su da ɗan kauri, tare da dabino wanda za'a jiƙa shi ya yi laushi, sai a ajiye ruwan gefe ɗaya, sannan a samu ƙwaƙwa ta ciki a goga ta da abin goga kuɓewa, bayan duk an wanke su kenan, sai a kawo ruwan abarbar da dabino da inibi a zuba a cikin ƙwaƙwar, sai a kawo madarar ruwa a zuba a ciki, ya danganta da yawansa, yawan madarar ga mai son suga ya zuba, ga mai son zaƙi sosai zai ji ya yi daidai. Amma ko ba inibi za'a iya yi, ana iya yi da madarar gari ma.
Cikin ɗan kofunan shan fruit salad ake shan shi, tare da ɗan ƙaramin cokali ana kiranshi da suna Appitizier (Coconut).
Mun kalli kasusuwan da dama a cikin ƙwara tara,babu abin da na lura a ciki wanda yake takurawa talakawa illa abubuwa baƙwai. Abin da muka zauna a yau juma'a muna tattaunawa da Yarima kenan.
"To ke yanzu me kika lura ya damu talakawana?"
"Ai ba talakawanka kaɗai ba, duk ƴan ƙasar Nijeriya."
To yanzu kamar me ye da meye ki ka lura da su?"
"Ruwa, rashin abin ƙonawa, itace ko kalanzir,ko gas,ga masu aiki da shi, ba wai babu ba, tsada ce ta yi masa yawa, suna buƙatar magudanan ruwa,takin noma, magunguna a asibitoci, hanyoyin mota, ballantana a cikin ƙauyuka, wutar lantarki,makarantun boko, Islamiyya tare da ilimintatun malamai,uwa-uba fetirin sawa motoci ko abin hawa ƙanana.
"Gaskiya na yarda. Ke kin ga wani ƙauye da muka je,kin ga ruwan da suke sha kuwa tamkar ruwan ƙwatami? To wai me ki ka ga ya janyo haka?"
"Rashin kulawa da sa ido, da zame hannu da ku sarakuna ku ka yi,ku ka bar wa gwamnati komai, ita zatayi. Ka yi tunani lokacin da sarakuna ke mulkin garuruwansu ka gani,ka san ya sha bamban da yanzu. A da Sarki ke da ikon komai kuma yana samun hanyoyin jin labarin abin da talakawansa ke ciki ta hanyar fadawansa da kuma Æ´an garin kansu. Ka tuna a da ko haihuwa aka yi a gari sai Sarki ya sani,ko hakimi,ko Dagaci,ko Mai unguwa, amma yanzu fa? Kai za ka baiwa kanka amsa."
"To yanzu wacce shawara za ki bani?"
"Ni dai shawarata biyar ce. Ta farko itace sarakunan mu su yi haƙuri don girman Allah su dawo da yanayin mulkin su na da, da adalci,su tuna su zasu fi sanin gwamna ko shugaban ƙasa, abin da talakawa ke ciki, saboda sun fi su hulɗa da jama'a,su manta da duk wani abin da aka yi masu,su ji tsoron Allah,su kawar da komai da ke zuciyarsu,su ci gaba da aikata ayyukansu na alheri, kamar yanda ake yi a baya.
######
[3/1, 19:48] Ummi Tandama😇: *ƘASAITA BOOK 3*
*NA*
*MARYAM KABIR MASHI*
Page 11
Su yi tunani da cewa Allah Subhanahu wata'ala ya damƙa ragamar mu a hannunsu, duk da na san yanzu haka in baku sarakuna ba yanda za'ayi gwamnati ta tafiya, duk da na san a kan san rai ne da ɗan nuna maku isa, amma kamata ya yi ku dage da ƙwarjinin da Allah ya ba ku ku nunawa Gwamnati dole sai daku za ta iya tafiya. Lallai wannan babban jihadi ne ga rayuwar duk wani mai faɗa aji a duniyar mu ta musulunci.
Saboda la'akari da abin da malamai suke faɗa cewa, ranar ƙiyama ana fara hisabi ta jini ne, sannan kuma manyan malamai, masu kuɗi, shugabanni, sarakuna, saboda haka wannan ma ya ishe mu ishara ta mu dage mu ga yanda ƴan ƙasa mu suke tafiyar da rayuwarsu, saboda shi Allah ba ruwansa gaba ɗaya zai haɗa mu ya tambaye mu yanda muka tafiyar da mulkinsu, ba ruwanshi da cewa shugaban ƙasa ko gwamna, mulki duk mulki ne.
Ko mace a gidan mijinta ita ma mulki take, haka namiji a tsakiyar iyalinsa duk mulki yake. Za'a kuma yi masa hisabi a ranar gobe ta yaya ya tafiyar da iyalin nan nasa kamar yanda muka sani, ga hadisin Manzon Allah (S.A.W) da wasu daga cikin ayoyin Alkur'ani mai girma.
Lallai waɗannan hadisai ana iya duba su ga litattafan Buhari da sauran sahihan litattafai. Ku sani talakawa na cikin masifa kala-kala, waɗanda suke neman taimakon Allah, tare da shuwagabanninmu. Lallai Allah yana sane da duk wanda ya taimaki wani, ya ƙyautata rayuwarsu ta zamo ingantacciya. Allah ya taimaka maku, shiyasa nake tausaya maka.
A saboda haka fushi da sa ido ga shuwagabanninmu ba na sarakuna ba ne, ba haƙuri da tausayawa talakawansu shi ne nasu, da hanyoyin da za su bi su ga sun gyara, sun dawo mana da jin daɗin da ya wuce, wanda muke tunanin ba zai taɓa dawowa ba,su yi mana bazata su dawo mana da shi. Allah ya taimake ku, ya sada ku da gidan Aljannar fiddausi madauwamiya, Allah ya raya maku zuri'arku, ya ƙara taimaka muku da haƙuri da mu,Amin."
"To yanzu wacce shawara za ki ba ni?"
"Shawarata a nan ita ce,ka fara yin amfani da abin da ke hannunka, ikon mallakar ka."
"Kamar me?"
"Kamar ɓangaren abinci. Ka ga yanzu haka a gidan nan zuwa gidan da muka baro, zuwa gidan Mai Martaba na ɗaya,aƙwai ɗakunan ajiyar abinci sun kai talatin (Stores), kowanne da kala-kalar abin da ke ciki,na yi imani in zamu shekara ɗari ba zamu nemi abinci ba, amma ka sani shi abinci ne ba zai kai shekara ɗari ba, da kuma mu da koyaushe Allah zai iya ɗaukar ran mu, sannan ko da yaushe abincin nan na iya lalacewa.
To me zai hana a taimakawa talakawa da shi, sannan kuma Allah ya hore maka maƙudan kuɗi, ba Mai Martaba na ɗaya ba, ba kai ba,ni kaina da nazo gidanka daga baya, na san na mallaki duniyoyin da zan iya taimakawa da su daidai gwargwado."
"Ai kuwa na gode, Allah ya yi miki albarka, ya baki ƴaƴa masu ƙaunar ki kamar yanda ki ke ƙaunar ubansu. Da kin haihu kuma zan fara."
"A'a ba ruwanka da haihuwata,ka cigaba kawai."
"Ai saboda matsalar mata sai ke."
"Ga jakadiya nan na amince da ita,ka yi tunanin ƙaunar da take yi mana, iyaka ni zan dinga tsara mata abin da ya kamata ta yi, ba ma sai na fita ba."
"Ni dama ai ba na son ki fita a gane mini ke,kin manta ke One in town ce?"
"Wallah Honey ka bar koÉ—a ni zanyi maka kuka."
"Na daina,ai ba na son inyi asarar hawayen nan naki masu É—igon tawwadar ilimantarwa."
"Ka ƙarayi."
"Sorry My Beby na."
Na yi dariyar jin daɗi, tare da juya bayana na ƙwanta a ƙirjinsa, ya rungume ni.