Sashe 5
Kasaita Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ta yi murmushi, "Yana shugaba? Ai shugaba bai ga ta zama ba, ke dai kiyi ƙoƙari ki koyi dabarun taimakawa mijinki da shawarwarin da zai sa jama'arsa ta bi shi, ta kuma ƙara ƙaunarsa."
"Kin san su ne ke? Saboda ni kin ga ba Æ´ar sarauta ba ce ba,haye min tayi da rana tsakiya. Kin ga kuwa ba zan san komai ba game da ita."
Jakadiya ta yi murmushi, ta ƙara gyara zama. Tun da ta fara magana nake tallaɓe da kumatuna, saboda al'ajabin abubuwan da take faɗa. Wannan ne yasa a take na ɗauki waya na daddana, domin neman Yarima, saboda fara gudanar da dabarar ta farko cikin dabarun da jakadiya ta koyar da ni. Amma ina! Hayaniya ta yi yawa,ko ƙarar ta ma ba ya ji. Wannan yasa na yi haƙuri sai ya dawo gida, na umarci jakadiya da ta je tasa a sa fanka a kori duk warin turaren da suka saka a gidana. Na bata room Freshner gidan Yarima na ce a sa mini ita.
Yariman bai samu shigowa ba sai ƙarfe tara da rabi na dare. Cikin nutsuwa ya zo ya zauna gefen gadon da nake ƙwance, ya sunkuyo ya sumbaci laɓɓana.
"Sannu da dawowa."
"Ke zan yi wa sannu, ke da na barki ba lafiya, na so shigowa in ga jikinki,amma ina, na so in gaishe ki ko da a waya ne, amma duk hakan ba ta samu ba, sai yanzu ma na ga kiran ki a wayata, missed call,ki yi haƙuri ban ji ba."
"Ba komai. Yaya komai dai ya tafi lafiya?"
"Eh, to hakan nake tsammani."
"Wai me ye ya faru?"
"Wani mutum ne ke neman tayar mana da fitina, shi ne na sa aka kama shi har da yaransa, wajen goma, bayan an kama su ne na turawa Mai Martaba Sarki da aiken cewa ga masu son tayar da zaune tsaye an kama. Kafin Mai Martaba ya iso shi ne nasa aka tara jama'a na basu haƙuri da dai bayanan da zai kwantar masu da hankali." Ya koma ya ƙwanta rigingine,saman jikina.
"Kin san ko waye mai son haÉ—a mana rigimar nan?"
Na ce "A'a." Cikin sanyin murya.
"Wanda na gaya miki ne wai shi Abdulrahman,wai É—a ne ga Mai Martaba, amma baya son ma a na faÉ—a, saboda ko a yanzu ma bai bayyana ba,ba kowane ya ji ba. Ni ma waziri ne ke gaya mini."
Ya yi ɗan shiru. "Dama ni Mama ta taɓa ba ni labari cewa akwai su,su biyu ne ma har da Yayarsa. Yanzu dai Mai Martaba ya ja masa kunnansa cewa idan ya ƙara jin labarin ya zo garin nan sai yasa an kashe shi."
Na shafa gashin kansa, "Ka ƙwantar da hankalinka, ba ka tambaye shi cewa me yake so ba.?"
"Sarauta." Na É—an yi saurin alamun tashi haÉ—e da tambayar.
"Sarauta ta me?"
"Ta Mai Martaba."
"To kai fa?" Ya yi murmushi, "kina son sarauta ne? Aƙwai wahala fa." Na ɓata fuska sosai.
Ya ƙara yin murmushi, "Yasmin kenan,ki ƙwantar da hankalinki,komai ya wuce, ina nan a matsayina na Yarima mai jiran gado, har da Babyna."
Ya faÉ—a yana lakatar mini hanci. Kunya ta kama ni. Na yi saurin tura kaina filo, shi kuwa ya kama Æ´ar dariya irin tasu ta sarakuna. Ya turo kansa cikin filon.
"Yauwa." Na yi saurin fito da kaina daga ƙarƙashin filon na yi alamar tashi da saurina.
Ya yi saurin mayar da ni ya zaunar, tare da riƙe min kunne.
"Kin manta ne ki ke tashi da sauri haka?" Ya ɗaga rigata ya sunkuya ya sumbaci fatar cikina, ya ɗago ya tallabi kumatuna tare da ƙura mini ido.
"Yasmin! Yasmin!!" Ya girgiza kansa.
"Ba zan taɓa iya ƙwatanta yanda nake jin ki ba a raina,son da nake miki yafi ƙarfin duk wani ƙaramin misali."
Na rausayar da idanuwana, waÉ—anda na ji sun aiko da hawaye. Mayar da su É—in da na yi na runtse ya yi daidai da gangarowar su saman kumatuna,ni kaina ban san dalilin zubowar su ba, sai dai na ji zuciyata ta yi mini sakayau, ba nauyi. Na san ba abin da take so sai Yarima, mutumin da nake jin ya gauraye jinin jikina gaba É—aya.
Hawayena kuwa sun tsiyayo ne ta dalilin wani abu da na ji yana yi mini yawo a tsakiyar kaina. Cikin sakan ɗaya na ga ya ruɗe,ruɗewar da take tayar mini da hankali. Gudun kada ya yi saurin fassara hawayena yasa na koma a hankali na ƙwanta a ƙirjinsa, zuciyata na son gaya masa cewa son da na ke masa yanzu ba zai taɓa misaltuwa ba, amma kunyarsa da nauyinsa sun hana ni sai dai na kurɗa kaina a wuyansa, na ce.
"I love You." Cikin sigar raÉ—a.
Ina jin shi ya ƙara matse ni a jikinsa,sam ban yi zaton ya ji ni ba, sai na ji ya ce "I love You too." Kunya ta sa na mayar da idanuwana na lumshe. Bai fi mintuna biyu ba na yi ƴar dabara na ƙwace jikina, saboda na san halin Yarima, sai mu ƙwana a haka. Na yi ɗan hanzari.
"Jira ina zuwa, na yi mantuwa." Na sauko daga gadona. Har na yi taku uku ya kira sunana, juyowar da zan yi sai na ji ya ce "I Fancy you."
Na yi murmushi na yi gaba. Faranti ne na shigo da shi É—auke da abinci, har na ajiye farantin ban ga Yarima ya motsa ba, na yi sanÉ—a na iso inda yake, ya yi kwanciyar nan tasa, tausayin shi ya kama ni. Ganin kafin in je in dawo har ya yi bacci, na sunkuyo na sumbaci goshinsa, ya buÉ—e idanuwansa a hankali ya yi murmushi.
"Na gaji."
"I know,sannu ga abinci nan na kawo maka."
Na riƙe hannunsa duka biyun.
"Ta so ka ci." Ya miƙe tsaye a inda na yi gaggawar taimaka masa ya cire alkyabbar jikinsa.
**** **** ****
Lallai kam ni na zama ƴar gata gaba da baya, balle da cikin nan na jikina ya tsufa. Sarki, Mama, Hajiya, Daddyna, Mamee duk ba sa son abin da zai taɓa ni, wanda kullum sai Sarki ya aiko waziri ko jakadiyar sa tazo ta ga lafiya ta. Mamee kuwa, sai dai waya. Dad kuwa ya zo gidana ya kai sau uku, ba wai don ya ganni ba,idan ya ga Yarima sai ya koma. Shi kansa Yarima ya kasa gane kan Daddyna, saboda ko an ce ya shiga ba ya shiga, sai dai ya ce gaishe mu ya zo yi.
Shalelena kuwa, kullum ana manne da ni,ko fada ma sai na yi da gaske yake sauka, Kaɗan-kadan kuwa ya hayo sama balle in ina ɓangaren gidansa,in kuwa na gidana ne, idanuwana na ga barandar gaba wacce ta koma hanyar zuwa ɗakinsa.
Amma wani abu ƙwaya ɗaya da yake damun zuciyata, shi ne yanda gaba ɗaya suka raja'a da cewa namiji zan haifa, ba sa maganar mace ƙwata-kwata , wannan abu na tayar mini da hankali, ballantana idan na ga Yarima ya ɗaga cikin nawa yana sumbatarsa,yana faɗin ɗan shi ya kusa isowa duniya. A take sai na ji hankalina ya tashi, wannan ne ma yasa wasu lokuta na kan yi shiru tamkar na fita daga hankalina na ƴan mintuna.
Buɗe ƙofa da na ji yanzu ma ita ta dawo mini da hankalina, na gyara kishingiɗar da na yi a saman kujerar falon samana, na juya na kalli Yarima wanda ya fito daga ƙofar ƙuryar ɗakina,su Mansura suka yi saurin russunawa suka yi gaisuwa, sannan suka miƙe domin sauka ƙasa.
Ya iso ya tsugunna gwiwarsa ta hannu a saman cinyoyina, "Honey,na bar ki ko?" Ya É—an yi tsaki.
"Wallahi Mai Martaba ya ƙi yarda, da yanzu muna can, tare da ke kullum."
Ya sunkuyo sosai, "My boy,how are you today?" Yasa hannu ya buɗe cikin kamar yanda ya saba, ya sumbace shi ya mayar da kansa ya ƙwantar a jikina.
Na sunkuyo na sumbace shi, gashin kaina duk ya rufe mu gaba É—aya. Na É—aga kaina sannan na É—ago shi.
"Yarima in tambaye ka mana?"
"Ƙwarai kuwa."
"Me yasa ba ka son a haifar maka mace?"
"Me ki ka gani?"
"Ban taɓa jin ka ambaci mace ba,ko ba ƙwa son a haifar muku mata?" Na yi shiru kaɗan.
"Yanzu in na haifi mace ba zaka zauna da ni ba?"
Sai kawai idanuwana suka ciko da hawaye. Ya miƙe tsaye ya zo ya zauna kusa da ni, wanda hakan yasa na saukar da ƙafafuwan ƙasa. Ya kamo hannuna ɗaya ya riƙe da hannayen shi duk biyun ya fara wasa da ƴan yatsun hannuna,a daidai lokacin da ya fara magana.
"Yasmin kin san dai mutum ba ya haihuwar wata halitta wacce ba mutum ba ko? Sai dai ya haifo nakasasshe ko marar lafiyar jiki,ko wanda halittarsa ba ta cika ba,ko kuwa ma ya mutu a ciki ko?" Na É—aga kaina.
"To wallahi Yasmin a ce ki haifo wata halitta ta daban,ko ɗaya daga cikin abin da na lissafa, wallahi ni na san ma na so shi na gama,ko da kuwa jama'a za su ƙi ni a kansa, saboda kawai ya fito ta jikinki, ta balle mace mutum. Yasmin ya zan yi naƙi mace, alhalin kin san mu mata rahama ne a gare mu.
Ki tuna ke mace ke kika canja mini rayuwata, ta zame mini abin so da ƙauna, abin sha'awa ga kowa. Ke mace ke kika ƙwantar mini da hankalina lokacin da ya tashi, ke mace ke ce kika rungume ni a jikinki a daidai lokacin da na wuce mahaifiyata ta rungume ni a jikinta.
Ki tuna ke mace, ke ce wacce za ta haifa mini Æ´aÆ´ana,ki tuna ke ce tsanin rayuwata gaba É—aya,in kin ga dama ki ruguza min rayuwata, wanda duk duniya babu mai baiwa É—a namiji daÉ—in rayuwa sai Allah da matarsa tagari,in kin so kuma ki gyara mini ita.
Yasmin ki ƙwantar da hankalinki a kaina,ki dinga haifa mini yarana,ko da kuwa duk mata ne, ina so. Wallahi ina so,ni na san dalilin ki,wai sarauta? Ba dole ba ne a ce dama ɗana ya yi sarauta,ko da kuwa duk maza na haifa har guda ɗari,in Allah ya so sai ya ba ƴaƴan ƙannena,ƙila ma wanda ba'a ɗakinmu ɗaya ba da mahaifinsa.