← Book details Kasaita Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 10 OF 17

Sashe 10

Kasaita Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Ai Gimbiya Allah ya yi da ragowar shan ruwana gaba, da tuni da sai dai in kun tunano ni ku ce Allah ya ji ƙaina. Yanzu mu ai mulkin kama karya ake yi mana a Jos, saboda azzalumin Sarkin da aka baiwa sarauta."

"Wa aka ba sarautar?" Yarima ya yi tambayar.

"Wani ne wai shi Abdulrahman, wai É—an Sarki ne, shi ne yanzu duk abin da ake yi sama da shekara uku duk baku da labari?"

"Ba mu da labari, wajen wa zamu ji?"

"Wajen Mama."

"In ta zo mu bata gaya mana komai. Ni kuma ko na je Jos ba na zuwa ko'ina sai gidanmu,ni kuwa ban taɓa ji ba,mun san dai ance an yi naɗin sarauta a Jos, amma ba mu san me aka naɗa ba."

"Ai abin ba daÉ—in faÉ—a,kin gan mu nan jiya muka gudo daga gidan yari. Wahala ta duniya ba wacce ba mu gani ba...." Tasa kuka.

"Ke har da fyaÉ—e an yi mini, tsofai-tsofai da ni. Ke yanzu dai Allah ya yaye mana masifa kawai."

"Ina su Mansura." Na tambaya cikin sigar tashin hankali.

"Sun gudu su duka waɗanda ki ka sani, maza da mata, saboda kamo su kawai aka dinga yi ana yi masu fyaɗe kullum. Maza kuma a kaiwa shugaban nasu, shi kuma aikinsa kenan amfani da maza. Gimbiya ƙartin mutane ya zo da su sune dogarawansa, sun kai ɗari biyu, ban da ƴan iskan ƴan mata." Ta sake fashewa da kuka.

"Dole ne in neme ku in sanar daku yanda ƙasarku ta koma. Ku yi mana arziƙi ku je ku taimakawa al'ummarku."

"Ina Mai Martaba yake ne ake yin irin wannan abubuwan kafirci?" Yarima ya tambaya.

"Yana nan,ai ya riga ya tsafe shi, sai yanda ya ga damar yi da shi. Waziri da manyan mabiyansa fa an neme su an rasa."

"Innalillahi wa'inna ilaihir'raji'un!” muka haɗa baki.

"Yanzu su waye kusa da Sarki?"

"Wasu ne ya kawo ya zuba masa. Kai bacin su Ahmad fa da ƙila ma an gama da su Mama, to su ke tsaye a kan iyayensu, duk sun ajiye karatunsu, sun zama masu gadin iyayensu."

"Yanzu ke ya aka yi kika gane nan gidan?"

"Gidan su Gimbiya na je na samu maigadinsu, shi ne ya yi min ƙwatancen nan gidan. Shi ya gaya mini ma kuna nan garin, da duk abin da ya faru a baya, saboda mu bamu sani ba. An dai taɓa jin labarin kuna ƴar takun saƙa da Sarki, har na cewa Gimbiya ta tashi tsaye,sa hannu aka yi maku kai da mahaifinka."

"Me ye sa hannu kuma?"

"A je mugayen matsafa su shiga tsakanin masoya biyu."

"Allah ya kiyaye. Yanzu ki tashi kiyi tafiyarki,ni yanzu hankalina a ƙwance ya ke ni da iyalina, saboda haka ba na fatan abin da zai zo ya dagula mini lissafi. Sarauta kuma Allah ya tayashi riƙonta. Amma ni yanzu ko ma sha'awarta ba ma yi, ballantana inji ina sonta."

"Amma Allah ya ja da rai kayi kuskure babba, saboda iyayen ka na cikin bala'i, amma sai ka ce ba ruwanka, yanzu haka fa Sarki ya auri matar nan uwarsu shi wanda aka naɗa, sai fa yanda ta yi da shi. Mama kuwa in zata fita sai dai fa ta fita ta ƙofar nan ɓoyayyiya ta je duk inda zata ta dawo."

"Ban yarda ba, saboda da Mama ta gaya mini. Kin ga tashi ki tafi. Honey ba ta dubu goma ta sha ruwa a hanya, kada ki ƙara dawowa gidana,kina jina?"

"Allah ya ja da...." Ya daka mata tsawa. Nan take na ce, "ya isa. Tashi mu je waje,ki jira ni." Na shiga É—aki, ita kuma ta tafi waje.

Ina fita na ja ta zuwa bayan gida, na tara masu aikinmu na ja masu kunne a kan kada su sake su faɗa cewar akwai baƙuwa a gidan nan . Na ba ta ɗaki na ɗiba mata sabulu, sannan na bayar a sayo mata kayan sawa.

Satin jakadiya shida kenan a gidanmu, ta yi ƙyau, ta mayar da jikinta tamkar ba ita ba. Yanzu abin da ya rage ƙoƙarin shawo kan Yarima. Jakadiya ta ce mini babu wata hanyar da zamu bi mushawo kan shi illa mu jira zuwan Mama,idan har muka samu Mama ta gaya masa halin da ake ciki baki da baki,wata ƙila ya amince ya tashi tsaye ya nemawa al'ummar da ke ƙarƙashinsa yanci.

Ikon Allah! Yau kuwa safiyar Laraba sai ga Mama ta zo, ganin ta sake lafiya ƙalau kamar yanda take yi mana kenan, ta nuna ba a cikin wata matsala take ba. Dalili ne ma yasa na ɗan tambaye ta ina su Mansura da jakadiya, sai na ji Mama ta ce.

"Lafiyar su ƙalau." Kan ganin bata da niyyar cewa komai yasa na aiki ɗaya daga cikin masu aikina na ce a kira mini baƙuwar nan.

Shigowar jakadiya za ta yi daidai da É—aga gwangwanin lemon da Mama ta yi. A madadin ta ci gaba da sha, sai aka samu akasin hakan, saboda firgitar da ta yi.

Gaskiya dai ta bayyana daga bakin Mama, wanda Mama har da kukanta take faɗar wasu abubuwan. Hankalin Yarima kam ya tashi. Cikin sakan ɗaya jinin sarautar sa ya gudanyo jikinsa, saboda har wata rawar jiki na ga yana yi. Sai da ya nisa ya kai sau baƙwai, sannan ya miƙe yana cewa.

"Zan je sai na kashe su."

Mama ta yi saurin riƙe shi tare da zaunar da shi, ta koma ta zauna ita ma. Ya dube ta ya ce, "ina nan zuwa da bindigata, sai na kashe shi."

Mama ta yi murmushi, sannan ta yi kirarinsu na manya, shi ne "Ta yaro ƙyau take yi, amma ba ta ƙarko. Ai Yarima duk yanda ka ke tunanin mutanan nan sun riga sun wuce mu. Abin da ya kamata mu yi kawai shi ne mu ma mu dage da roƙon Allah ba dare ba rana. Na farko jakadiya kin fi mu sanin hanyoyin da za'a bi a karyawa Sarki abin da ke jikinsa."

Nan take na ji Yarima ya ce, "Aƙwai wasu addu'o'i da ayoyi ina da su na karya sammu ko wani mugun baki. Ban da ayoyin da Manzon Allah (S.A.W) ya ce mana, tare da koyar da mu yanda zamu aikata su."

Zan sa a yi saukar Alƙur'ani mai girma,sau sittin da baƙwai, wanda kowanne daga ciki za'a tofa a ruwa a yarfawa wanda ake tunanin an yi masa sammu, ba wata hanya da zamu bi illa wannan. Sannan mu duka mu dinga tashi cikin dare muna gabatar da wannan nafilar, da kuma wacce Allah ya hore mana. In zamu iya kuma mu ma muyi sauka da kanmu. Ga addu'o'in da sallar nafila.

Nafila ce raka'a huɗu, kowacce nafila da Ayatul kursiyu ƙafa baƙwai 7, dukkansu bayan ka yi sujjadar ƙarshe sai ka karanta wannan addu'ar. _Wallahu galibun ala amrih,walakin na akasaran nasi la ya'alamun (7),_ Idan mun sallame sai mu karanta wannan addu'ar.

_Allahumma wahastu nafsi wa irdilaka_ sau baƙwai(7), sai mu karanta Laƙada ja'akum, ita ma sau baƙwai(7).

Manzonmu Annabi Muhammad (S.A.W), ya ce wanda yake karanta waÉ—annan kalmomi guda goma, Allah zai kare shi daga sharri biyar a duniya,biyar a lahira. Ga su nan kamar haka:---

_1) Hasbunallahu liddini_
_2) Hasbunallahu liman ahamman_
_3) Hasbunallahu liman hasadani_
_4) Hasbunallahu liman kadani bi su'in._
_5) Hasbunallahu indal masala fil ƙabar._
_6) Hasbunallahu indal mizan_
_7) Hasbunallahu indal masala fil ƙabar_
_8) Hasbunallahu la'ila ha'ildalaihi tawakkaltu wahuwa Rabbul Arshir azim._

Allah yasa mu dace.

Cikakken bayanin maganin sammu,wato yanda za'a bi a karya sihiri,ko wani mugun Aljani mai taurin kai,ko sanin me mutum ya kamata ya yi,mata ko maza. Ana iya neman littafin nan kantin Al'Ameen Bookshop GUZURIN MATA MUSULMAI IZUWA ƊAKIN AURE. Wanda Malam Bashir Aliyu (Bashir) ya wallafa. Za'a samu duk wani ƙarin bayani a ciki.

Cikin wata ɗaya da ƙwana biyu muka gama duk wani tsarin da muke son muyi. Ta hanyar Mama kuma muka samu ta baiwa Mai Martaba maganin da yarfa masa wannan ruwan sauka. Ban da masallatai da Yarima ya dinga bi yana cewa a tayamu roƙon Allah.

Ba na mantawa da duk zuwa Makka da zan yi,wato aikin Hajji,ko Umarah, sai na yi roƙon Allah ya daidaita tsakanin Yarima da Mai Martaba.

Yau ga shi zan iya cewa Allah ya amsa roƙona,dama kuwa faɗa ce ta malamai, cewa duk muminin ƙwarai ba zai ziyarci ɗakin Allah da buƙatunsa ba face Allah ya biya masa buƙatunsa. Sai dai zasu iya ɗaukar ƴan lokuta, wasu kuma sha yanzu magani yanzu ne. Ko dai ka dawo ka ga alherin abun,ko kuma ma kana can kana dawowa ka samu abin da ka roƙa ya faru.

Mu kanmu ba mu san lokacin da Yarima ya je ga hukumar ƙwantar da tarzoma ta ƙasa ba (Mobile) bayan ya samo taimakon gaggawa, sai dai yau muka wayi gari muka ji an kama Sarkin ƙarya Abdulrahman da mahaifiyarsa, da Yayarsa Hadiza da duk mabiyansu.

Allahu Akbar! Yau ba wanda bai yi wa Mai Martaba kuka ba, shi da É—an sa Yarima, wanda suka samu shekara ta biyar ba su ga juna ba.

Gaban bainar jama'a Mai Martaba Sarki Jafar ya rungume ɗansa, wanda ya ɗauki sama da mintuna goma, ya ɗagoshi ya kalle shi, sai kuma ya mayar da shi jikinsa ya ƙwantar. Daga baya ne yake tambayar ina jikansa Ammar. Yaro ɗan shekara biyar da wata huɗu ne kawai babu. Amma har ya zama ɗan saurayi saboda girman jiki da yake da shi.

Bayan ya ganshi ne aka miƙa masa Suhailat. Abin ka ga rashin sani, ta ƙi zuwa wajen Sarki. Da yake Allah yasa ta yi saurin tafiya da gudunta, ta iso wajena ta riƙe ni gam tana nuna mini Mai Martaba.
Chapter 10 · 0% Book details