← Book details Kasaita Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 2 OF 17

Sashe 2

Kasaita Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Falon Hajiya Kilishi muka fara shiga,a inda na ga hakan ba ƙaramin daɗi ya yi mata ba. Har ƙasa muka sunkuya muka gaishe ta, cikin daɗi ta amsa, har da kamo ni da tayi ta rungume,wai ga ɗiyarta ta dawo. Cikin zolaya irin ta manya ta fara magana.

"Amma dai nan za ta ƙwana, saboda gajiya,ai dole ne ta ɗan samu hutu."

Shi dai Yarima sai dai kawai ya yi murmushi, "Baka ce komai ba?"

"Hajiya ai yarki ce,ga ta nan."

Amma fa ya kasa ɗago kansa. Hakan yasa ni kuma na ƙara zolayarsa.

"Dama kuwa Hajiya duk na gaji, ga zaman jirgi,Gara na huta yanzu,ko sati biyu na É—an yi."

Ya É—ago ta gefen ido ya harare Ni, Hajiya tasa dariya.

"Daina hararar ta,ku tashi ku je tunda ka yi mini rowar ta."

Ya miƙe yana kiran, "Hajiya ba da ke nake ba, da ita nake,. Manya na magana tana saka musu baki."

Aka saka Æ´ar dariya, muka fito.

Manyan mata kenan, iyayen gidan Mai Martaba,su Mama. Zaune take kamar yanda muka samu Hajiya Kilishi, cikin sakan É—aya suka yi gaisuwa duk suka fice É—aya bayan É—aya, suna fita ta taso ta rungume ni jikinta.

"Your are welcome my daughter."

"Nifa mama?" Ya faɗa cikin ƴar shagwaɓar da yake yi mini. Kamar dai yanda na ga ya yi mata farkon zuwana gidan.

"Ina ruwana da kai ni kuma, sai ka koma can wajen Hajiya."

"Kai shi kenan,kun haÉ—e mini kai. Ita ma Hajiya cewa ta yi ta samu Æ´a."

"Sai ka koma wajen Mai Martaba,ƙila shi yana so."

"Kai Mama."

Muka ɗan yi dariya, sannan na ga ya zauna ƙasa yana gaishe ta. Hakan yasa ita ma ta zauna tare da ni a kusa da ita.

Ƴan nasihohi ta yi mana na mu zauna lafiya, kada ta kuskura ta ji wata matsala ta taso a tsakaninmu. Nan ta ce mini idan har na ga tana shirin tasowa na bugawa Hajiya Kilishi waya ko na nemi shawarar jakadiya. Nan take ta ba mu labarin cewa, bayan tafiyarmu an ƴanta bayin gidanmu, amma da sunan za su cigaba da aiki, amma a dinga biyansu albashi. Na gidana kuwa,an ce su nemo miji a yi masu aure, wacce mijinta ya bar ta ta cigaba da zuwa, wacce ya hana ta ta yi zaman auranta,ko yanzu haka ake ciki.

Ƴan gidan yari kuwa, Mai Martaba cewa ya yi sai kin dawo za'a sallame su, shi ne zasu bi layi a karanta miki laifin kowa, wanda ki ka ga ya dace ki sallame shi,ki sallame shi, wanda bai dace ba ki san ya zakiyi da shi. Na ji daɗi kuwa ƙwarai da gaske,a inda murnata ta ɗan fito fili.

A lokacin dai har Mai Martaba sai da muka ƙara keɓewa da shi na musamman, muka gaishe shi a fadar cikin gida. A lokacin ne ma na samu na yi godiyar abubuwan da ya yi mini, waɗanda na buƙata.

A nan shi ma ya yi mana nasihohi irin nasu na manya. Sannan ya ce Yarima ya yi taka tsantsan da rayuwa, saboda Abdulrahman ya zo da baya nan, har ya dinga rabon kuɗi a can gidan namu, ya ce a ɓangaren gidan Ahmad ya zauna. Sai da na ɗan nisa sosai, sannan na tunano wanda Sarki ke nufi, wanda Mama ta bani labari cewa ɗan Sarki ne, amma baya sonsa, baya son ma a ce ƴaƴansa ne, kenan ɗan Hajiya Asabe.

Sai bayan da aka idar da sallar la'asar, sannan muka yi sallama da su. Ban tashi gane ina mota ta tsaya ba sai da aka buɗe mana ƙofa,kawai sai na ganni gidanmu. Na yi saurin kallon Yarima, sai na ga ya sha kunu, alamar babu wasa,ya ma yi gaba abinsa. Kafin ya kai ga ƴar matattakalar da ke ƙofar shiga gidanmu sai ga su Mamee sun fito, ita da Dad suna fara'ar murna.

Kunya ta yi saurin dirar mini,tare da murnar ganin iyayena da na yi, wata uku har da ƙwanaki da dama ban gansu ba, balle ma Dad ɗin da ba na iya ƙwana uku a da ban ganshi ba,ko tafiya ya yi saboda ni baya daɗewa, ya san har kuka nake yi masa a waya.

Yarima na isa na ga ya tsugunna ƙasa yana gaishe su. Shi kuwa Daddy sai naga ya ɗaga shi ya rungume, irin dai gaisuwar nan ta larabawa.

Dad cewa yake, "Oh! My Son, welcome back,I am happy to see you."

Ni kuwa ina isowa na faɗa jikin Mamee wacce kai tsaye tana dariyar murna. Ta ɗan riƙe ni tana dariya, daga baya kuma sai da ta taɓa ɗan wasan da ta saba.

######
[2/18, 09:13] Ummi Tandama😇: *ƘASAITA BOOK 3*

*NA*

*MARYAM KABIR MASHI*

Page 2

"Ke tashi daga jikina,ko Æ´ata ba ta zo ta haye mini jiki ba sai ke."

"Kai!" Na faɗa cikin yanayin jin kunya da shagwaɓa."

"Ke zo nan ƙyale ta dama ita haka take."

Cikin jin kunya, na isa wajen Daddy, Amma sai ga ni na tsugunne a ƙasa, saboda kunya da ta kama ni. Ya sunkuyo ya ɗago ni ya rungume a jikinsa. Ƙamshin turaren sa na ji ya dakar mini hanci. A take na ji kaina ya sara. Cikin sakan ɗaya na ji ina juyawa tamkar wacce ta yi hajijiya ta gaji (Katantanwa), wani amai na ji mai zafin gaske yana taho mini. Tun ina ɗaurewa har na ji gashi nan ya gangaro a bakina. Na zame jikina daga rungumar da Dad ya yi mini,na ruga a guje ga famfon da ake bawa fulawowi ruwa, na tsugunna. Wani irin mugun amai na dinga ƙwaranyawa. Ni dai na ji an riƙe ni, amma ban iya ɗaga kai ba ballantana in ga waye mariƙin nawa.

Tun ina yi daga tsugunne,sai ga ni na durƙushe sosai, shi kuwa aman nan ya ƙi tsayawa ko shan iska ma in yi. Na ƙwashe tsayin minti goma ina ƙwaranya amai. Sai ya yi kamar zai tsaya, sai kuma in ji wani sabo ya taso. Muryoyin sannu kuwa,ta ko'ina a kunnuwana, mai dafani kuwa, sai na ji ya tsugunna ya rungume ni a jikinsa.

Jin aman ya tsaya, yasa na samu na miƙe na isa na buɗe famfon na kuskure bakina, tare da wanke fuskata, saboda hawayen aman da suka tsattsafo ga idanuwan nawa. Sai da na juyo na ga mutane tsaye a kaina kusan mutum goma sha,ƴan aiki, masu gadi.

Mamee ce rungume da ni. Dad kuwa yana tsaye yana kallon ikon Allah, dukkansu suka yi mini sannu. Daga nan Mamee na ɗan riƙe da ni har cikin falon Dad ɗina. Na ɗan kishingiɗa kaɗan a kujera,Dad ke tambayata me ya ke yi mini ciwo? Na ce ba komai, sai dai kaina kawai. Cikin rawar jiki Daddy ya ɗauko magani ya miƙa mini. Mamee ta karɓa.

"A'a ba a shan magani ko sai an ga likita. Ka bari in sun tafi can su ga likita, sai ya rubuta musu magani."

Nan take na ji Dad ya fara faÉ—a, "Ya ma za'ayi a ce sai ta ga wani Likita,ai kowa ya san maganin ciwon kai."

"Ka zo ciki Alhaji." Ta yi ciki. Na san ɗakin Daddy suka nufa. Nan fa Yarima da ke zaune gefe ɗaya ya yi ɗan ƙaramin zaman makokin cutata, ya samu damar saurin isowa gare ni, ya kama ni ya rungume ni da rawar jikinsa.

"Ya ya me ke miki ciwo? Ki gaya mini kin ji Yasmin, talk to me please."

"Bana jin komai, sai dai kaina da ya yi mini nauyi kamar yana ciwo."

Ya sake ni ya durƙusa a gabana, ya rike hannayena duk biyun, "Please Yasmin, tell me the truth."

"Ba komai,ni bana jin komai."

"Yasmin look at me." Na É—ago na kalleshi.

"Kada ki ɓoye mini Yasmin,ki kalleni ki ga yanda na koma a yanzu kawai. Kina tunanin in ki ka ɓoye mini ya zan koma a nan gaba?"

Ya sumbaci hannuwana. Na zame hannu ɗaya na shafi gefen fuskarsa, tare da sunkuyowa na sumbaci laɓɓansa cikin kunya.

"Ba zan taɓa yi wa mijina ƙarya ba saboda ina son shi ba zan so in ga hankalinshi ya tashi ba. Ka amince da abin..."

Motsin da muka ji yasa ya yi saurin tashi ya koma inda yake zaune. Shi ne kujerar da ke nesa da ni.

Dad ne ya shigo, amma sai na ga damuwar fuskarsa ta gushe, wanda take kaɗan ya yin da Mamee ta biyo bayansa. A nan Mamee ta ce mu shiga ciki mu bar su nan. Na miƙe tare da satar kallon Yarima, saboda in karanto me ke fuskarsa. Cikin maganar raɗa ya ce, "Take care." Na lumshe ido alamar na amsa masa na wuce cikin gida.

Mamee ta zaunar da ni ta dinga yi mini Æ´an tambayoyi kamar su, "Ba komai dai zaman ki da mijinki? Ya ya yanzu kun daidaita ko? Ya gida? Sarautar ba dai matsala?"

Duk na amsa mata da eh kawai. Saboda na san ni yanzu ba ni da wata matsala dama matsalata É—aya ita ce Yarima, yanzu kuwa ni kaina na san ina son Yarima. To ballantana shi wanda na lura da zai iya rasa rayuwarsa idan har ya rasa ni.

Sai ƙarfe uku muka bar gidan, amma kafin in tafi tamkar ban taɓa yin komai ba, saboda sai da ma na ci abincin Mamee na ƙoshi. Lafiyata ƙalau muka yi sallama da su. Duk da sai da na nunawa Yarima ya bar ni gida tsayin ƙwana baƙwai,a lokacin muna falon Mamee. Wannan ne ma ya baiwa Yarima damar cije mini laɓɓana da harshensa kada ma na sake faɗar irin wannan mummunar maganar. Na ɗan narke masa tare da cewa.

"Gidan mu ne fa! Yanzu shi ne mummunar maganar?"

Bai ma ba ni amsa ba, sai dai ya É—an kama hancina ya ja ya tafi falon Daddy,wato manufarsa baya son maganar ma.

Muna shiga mota na ƙwanta daidai lokon motar.

"I am tied." Har da ɗan canja yanayin fuskata. Bai fi minti ɗaya ba na ji Yarima na kiran sunana. Na juya na kalleshi, sai na ga ya ware hannuwansa, alamar in isa gare shi. Na ɗan kaɗa idanuwana na gyara ƙwanciyata sosai, alamar dai ba na zuwa.

"Honey please come on. Ina son jin É—umin jikinki a kusa da ni."
Chapter 2 · 0% Book details