Sashe 14
Kasaita Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Na godewa Allah da ya wadata ni da miji mai jin shawarata, mai É—aukar duk kalamain da ya fito daga bakina,ko na iyayena. Wannan dalili ne ma yasa na sadaukar masa da nafila raka'a biyu domin ta zama kariya a gare shi, wacce nake zama musamman in yi masa ita shi É—aya, da addu'o'in da ke cikinta.
Dalilina kuwa, shi ne duk abin da muka tattauna da Yarima ya aikata shi, duk unguwa idan suka isa, tun daga gidan farko har ƙarshe sai an ajiye masu buhun-hunan abinci da jarin sana'a, wanda na tabbatar zai wadace su. Sannan sai a tambayi matsalar ka ta rashin lafiya ko haihuwa,ko bikin ɗiya,ko gyaran gida, sai a taimaka maka.
Wasu buhun-hunan abincin kuwa, don ajiya har sun lalace da hunhuna, sai waɗanda ƙwari suka cinye suka koma gari. Kai Alhamdulillahi, saboda yanzu ni na san nayi jihadi mai tsananin lada, tun da har Islamiyoyi aka buɗe, ban da makarantu masu ƙyau, ban da ɗaukar nauyin ƴaƴan da iyayensu ba su da halinsa su makaranta.
Sai kuma ni tawa gudunmawar, shi ne taimakawa mata ƴan'uwana da koyar da su ilimin zamani da na addini, yanda za su zauna da mazajensu lafiya da tarbiyyar ƴaƴansu, ga sana'o'i ana koya masu. Abin da ya so ya bamu wahala ni da Mai Martaba na biyu, shi ne Musluntar da arnan da suke zagaye da Jos, waɗanda wasun su ko kaya ba su iya sakawa ba,wasun su ma nama danye suke ci, amma mun samu da ƙyar mun taimaka masu.
Dabarar da muka yi kuwa, shi ne duk garin da suka isa, sai su ɗauko shugabansu su taho da shi cikin gari ya samu wata ɗaya,ko biyu yana ganin yanda jama'a ke rayuwarsu, ana koya masa duk wata al'ada mai ƙyau da Addininmu, to idan ya koma garinsu, shi zai dinga koyar da ƴan'uwansa,idan ya ga suna da sha'awa sai ya dawo gari ya gayawa Yarima, daga nan sai a tayar da mutane kamar ashirin cikin su da malamai da masu taimaka masu da abinci, ruwan sha,wanki. Yanzu haka duk an tura su a matsayin zasu shekara a can.
**** *** ****
Cikin jikina dai har ya shiga wata na sha É—aya a jikina babu zancen wata haihuwa, sai dai duk inda na zauna sai an taimaka mini nake tashi,don dai ma ni doguwar macece, da gajeriya ce da shi kenan sai an dinga saka ni a kujera ana turawa. Wannan abin yanzu shi ya damu duk wani masoyina.
Kai har da Mai Martaba Sarki ya aiko da cewa mu shirya zai turo likitocin da zasu duba ni. Shi kuwa Mai Martaba Yarima cewa yake gara mu bar ƙasar. Amma Sarki ya hana a je ko'ina ya ce saboda abin da tafiyar mu zata haifar, shi ne a shiga ruɗanin ya ya nake. Ni kuwa har mamaki suke ba ni, saboda ba na jin ciwon komai sai dai nauyin da cikin ya yi mini ya hana mini sakewa.
Likitoci turawa mata,su baƙwai suka iso gidanmu, ba wani ɗan rakiya sai Mai Martaba na ɗaya, yanda suka shigo falon ina tule waje ɗaya, shi ya bani kunya. Cikin matsananciyar kunya na samu na gaida su, daga nan kuwa suka umarce ni da in isa asibitin mu da ke cikin gidanmu.
Yarima kuwa kamar ya saka kuka, da ya ga likitocin nan, sai dai ganinsu tare da Mai Martaba yasa ya kasa yin magana.
Lallai na san an shiga ɗakin asibiti da ni, ɓangaren mu wato Emir's section.
**** *** ****
_Innalillahi wa'inna ilaihir'raji'un!†haka Mai Martaba yake faɗa yayin da yake riƙe da ɗansa Yarima, wanda ke zaune dirshan a ƙasa yana kukan mutuwar matarsa Yasmin. Wanda hakan ya faru ne ta sanadiyyar haihuwa da ta zo mata da gardama.
Babanta Alhaji Sani Sa'id shi ne ke da ƙarfin halin yiwa mijinta nasiha.
"Haba Yarima,ka yi haƙuri mana,ka yi tunani da Allah ne ya baka Yasmin,don ya ɗauke abin shi kuwa,ai ba a ƙi gode masa ba. Mu ma nan fa jiran tamu mutuwar mukeyi, saboda faɗar Allah Subhanahu wata'ala ce da yake cewa KULLI NAFSIN ZA'IKATUL MAUTI (Dukkan mai rai mamaci ne). Saboda haka ƙyau a ce godiya ga Allah ka yi, tare da yi mata addu'a.
Wannan nasiha ita ta ƙarasa rikita Yarima, sai dai aka ganshi zube a ƙasa sumamme,gudun kada hankalin jama'a ya tashi, yasa ba'a yi wata hayaniya da ƙarfi ba, sai dai ɗauke shi aka yi aka kai shi asibiti, wanda likitoci suka bi bayansa.
Maganar da na yi ita ta dawo da hankalin jama'a gareni, wanda ɗakin cike yake da mata ƴan'uwana. Cikin su kuwa har da Mamee, Aunty Salwa,ga Mama,da Hajiya Kilishi, ban da jakadiya da ke rakuɓe a gefe, duk na karanci hakan kafin na kai ga yin magana.
Maganar kuwa ta yi daidai da firgita duk wanda ke zaune, ganin yanda suka nuna.
"Mamee lafiya na ga kuna kuka?"
Tambayar da na yi masu kenan. Gaba É—ayansu sun firgita, wanda dukkansu sun yo kaina, kowa so yake ya rungume ni. Jin jakadiya ta fita da gudu tana kira, "Mai girma Yarima Gimbiya ba ta mutu ba,dogon suma ne."
Maganar ta ta iso a kunnena, ita ta gaya mini da jira ake gari ya waye a kaini kabarina.
Na yiwa Allah godiya da ya taimaka mini na farka kafin gari ya waye. Na yunƙura zan tashi, amma na ji jikina kamar an karya mini ƙafafuna. Sai dai ji na yi Hajiya Kilishi na cewa.
"Jira a taimaka miki. Ke kuwa ai dole jikinki ya yi tsami,a haihu tun safe amma ba wanka." Sai a lokacin na faÉ—a tunanin abin da ya faru da safiyar yau.
Zuwan likitoci da Mai Martaba Sarki, wanda suka yi mini wasu allurori sun kai biyar. Yarima har faÉ—a yake masu, shi kuwa yana tallabe da kaina a cinyar shi yana yi mini sannu, balle da na ji wani bala'in ciwo na jijjiga mini tsokar naman jikina. Ban fi mintuna arba'in ba a haka sai na ji kamar an zare numfashin jikina.
Daga nan ne ban ƙara sanin yanda aka yi ba, sai yanzu, amma na ji Yarima na yi masu faɗa. A can cikin tsakiyar kaina ina jin matsanancin ciwon da nake ji, sai na ji suna ce masa wai allurar naƙuda suka yi mini. Haka kurum ruwan da suka sanya mini a hannuna ma na naƙuda ne.
Jin Hajiya Kilishi ta kama ni yasa na dawo hankalina izuwa kallonta, sannu ta dinga ce mini haka ma duk waɗanda ke wajen. Amma Aunty Salwa sai ma sabon kuka da ta saka ana ba ta haƙuri. Mamee kuwa ko motsi ba ta yi ba daga inda take zaune.
Bayan Hajiya Kilishi ta taimaka mini na yi wanka da ruwa mai zafin gaske, wanda ta cika bahon wanka, ta ce in shiga. Bayan na shiga ita kuma ta zuba wani a wata tasa mai faÉ—in gaske (silba), ta dinga tsoma tawul a ciki tana gasa mini jikina. Ni kuwa kamar kada ta daina saboda daÉ—in da nake ji.
Ina fitowa aka ba ni kunnun goruba cike da ƙwano aka ce in shanye shi. Ban ƙi sha ba, amma ni na san ba zan iya shanye shi ba. Lallai dole na yi mamakin har yanzu a ce Yarima bai shigo ya gan ni ba. Shin ko dai tsorona yake ji? Ko kuwa ya daina sona yanzu?
Kasa ɗaurewa na yi da na kalli agogon bango na ga har baƙwai da rabi na safe ta wuce, amma Yarima ba wanda bai shigo ya yi mini sannu ba, har da Dad ɗina da yake nuna kawaici a kaina, sun shigo da shi da Mai Martaba Sarki. Ni dai kasa ɗaurewa na yi har na tambayi Hajiya Kilishi.
"Hajiya ina Yarima ne? Ko ya yi tafiya?"
"A'a yana nan, amma na ji Mai Martaba Sarki na cewa jikin nasa da sauƙi, yanzu haka suna wajen shi."
Hankalina na ji ya tashi matuƙa, da a ƙwance nake, amma sai gani na tashi zaune. Ya zan yi ni yanzu? Na tambayi zuciyata. Sai kawai na ji na miƙe tsaye. Hajiya ta yi saurin kama ni.
"Me ye?"
"Hajiya zan iya zuwa wajen Yarima?"
Eh,mu ma yanzu can zamu. Su Mamee ma na can tun ɗazu. Amma ganina da kinyi haƙuri sai Sarki ya tafi da mutanen shi,ki ƙwantar da hankalinki, ba abin da ya same shi, razana ce kawai ya yi."
#####
[3/1, 22:22] Ummi Tandama😇: *ƘASAITA BOOK 3*
*NA*
*MARYAM KABIR MASHI*
Page 12
Ya ya zanyi? Dole na bi maganar manyana. Haka dole na koma na ƙwanta, amma hankalina duk baya jikina. Gudun kada a ce mini Yariman ya mutu, amma kaɗan-kaɗan na tambayi duk wanda na ga ya shigo, cewa, "Ina Yarima?" Sai dai su bani amsa da yana nan lafiya.
Ƙarfe biyu saura minti goma sha ɗaya na ga Yarima ya shigo cikin sauri. Yana shigowa ina ƙwance, ganinsa yasa na yi saurin tashi tsaye. Ya iso ya kama cinyoyin hannuwana duk biyun, ya zame hannayensa suka sauko ga ƴan yatsuna. Ya dawo da hannayensa ya shafi wuyana da su, ya tallabe kumatuna ya kalleni. Sai a lokacin na ga ya yi murmushi, ya mayar da ni ya rungume gam a jikinsa, ya ɗagoni ya zaunar da ni a bakin gado, shi kuwa ya tsugunna a gabana, da gani ya rasa ya zai yi mini. Sai na ga yasa ɗan yatsana a bakinsa.
A tunanina wasa zai yi mini,sai kawai ya cije ni, na sa ƙara irin wacce ke dawo da hankalin Yarima a gareni, sai kawai na ga yasa dariya. Nima ban san lokacin da nasa tawa dariyar ba. Sai na ga ya hayo gadon shi ma yana mai cigaba da dariya, ya mayar da ni ya rungume a jikinsa. Sai kawai na ji lema na tsiyaya cikin rigata ta bayana, na ɗago kansa.
"Yarima me ye kuma na fitar da hawaye bayan ga ni?"
"Yasmin da kin mutu da ya zanyi da ra....."
"Haba Yarima, kamar ba Musulmi ba,za ka dinga kawowa kanka irin wannan tunanin, ba ka san Allah mai rahama mai jin ƙai ne ba. Yanda Allah ya ɗauke maka ni, haka zai musanya maka da wacce ta fi ni."