← Book details Kasaita Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 12 OF 17

Sashe 12

Kasaita Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Falon mu ya yi shiru har tsayin mintuna masu tsayi. Can Sarki ya nisa, "Yasmin, Hajiya Mariya, Hajiya Kilishi, aikin ku ne,kushawo kan É—anku. Ke kuma mijinki. Koma in ce aikin ki ne. Yasmin ki taimaka ki shawo mana kan mijinki, ya taimaki jama'ar da ba mu san iyakacinta ba."

Ba ni da damar yin gardama, sai dai na bishi da, "To Baba, za'ayi ƙoƙari."

Ni kuwa har hantar cikina sai da ta kaÉ—a. Daga nan kuwa aka cigaba da Æ´ar hira, jin falon ya kaure da surutu yasa Yarima ya shigo shi ma ya zauna aka ci gaba da yi dashi.

Sai da suka ci abincin ranar mu, sannan suka tafi,mu kuwa rakiya har mota. Yau an samu shiga, bayan mun dawo hirar mu kawai muka cigaba har ya tafi gona.

Bayan mun shiga ɗaki ne har ma mun yi niyyar ƙwanciya kenan an gama duk wata hira. Na ɗauko Novelle Gelly ina shafawa a jikina, domin jikina ya ɗau ƙamshi gaba ɗayan shi. Gefen gado na zauna, amma gabana ke ta wani irin mummunan faɗuwa, saboda maganar da nake son ta fito daga bakina. Ban kashe fitila ba na hayo gado na zauna kusa da shi tare da robar man ƙamshin jikin nan a hannuna,sai kuwa kaɗawa take yi, da alama jikina ke rawa.

Sai da na karanta addu'a sannan na ambaci sunan shi.

_Ya waliyyan ni'imati,wa mallazi inda kurbati,ij'alni matahu bardan wasalam alayya kama ja'altana barda wassalamun ala Ibrahim (Ƙafa baƙwai).

"Honey." Na kira shi a sanyaye.

"Ina jin ki Sweetyna." Ya faÉ—a, har da É—ora hannunsa a saman cinyata.

"Magana nake son mu yi da kai mai mahimmanci."

"Ina jin ki. In kuma so ake in ƙara wani cikin, to ban manta ba." Ya faɗa har da ɗan taɓa mini gefen cikina. Na yi murmushin da yake haɗe da fargaba.

"Honey maganar sarau...." Wata tsawa da ya daka mini. Bani ba,na yi imani maigadi ma ya tsorata. Ni kuwa har na kai bakin gado, saboda na yi zaton duka ne zai biyo baya. Tun kuwa da na sauka, na durƙushe nake jin ɗan cikina na mutsulniya, tamkar ɗan kifi a ruwa.

Bai ƙara cewa ƙala ba daga wannan, sai ma ya juya min baya. Gaskiya na san na yi awa ɗaya durƙushen nan, ina saƙa hanyoyin da zan bi. Ganin ba shi da wani alamun motsi ballantana in san hanyar da zan bi, sai na ce, "Wash! Wash!! Wash!!! Cikina." Ina faɗar cikina na ga ya yi saurin saukowa.

Tun daga can na ji yana cewa, "Me ya samu cikin? Da ke nake,me ya samu cikin?"

"Ciwo yake. Marata!"

"Tashi mu gani."

Ya yi saurin isowa ya kama ni. Na lanƙwashe.

"Ba zan iya ba, ina jin ɓari zan yi."

"What? To kin ga ni ga irin ta nan,kin sawa ranki abin da ba ruwanki, ga shi nan za ki janyo mana asarar ƴaƴana. Taso mana mu tafi asibiti." Ya sake ni, ya tafi ya buɗe durowa ya ƙwaso mana kaya. Ya zo ya kama ni.

"Tashi, sannu." Ya yi alamar ɗaga ni. Na riƙe hannunsa.

"Yarima!”

"Ba na ce bana son kina kirana da wannan sunan ba?"

"Na sani,ka yi haƙuri, amma yau ne na ƙarshe, tunda ka nuna mini ba ni da amfanin komai a wajen ka. Yau zan haƙura da auranka,gara ka auro wacce take da muhimmanci da amfani a wajenka." Sannan nasa kuka.

Ina jin sa ya tsugunno. "Yasmin me ya faru? Me na yi miki? Ba ki taɓa gaya mini magana mai ɗaci ba sai yau."

"Yau ma kamawa ta yi." Ya É—ago kumatuna.

"Haba Yasmin, ya zaki tayar da hankalin mijinki...."

"Ba ka son a tayar da hankalin ka, amma kai zaka tayar da na mahaifinka?"

"Ba ruwan ki da maganar mu."

"Kenan ba ruwan ka da ni? Don Allah in tambaye ka?"

"Ina jin ki."

"Yanzu me ye nan cikina?"

"ÆŠana ne."

"Kana son shi ko baka so?"

######
[2/28, 08:27] Ummi Tandama😇: *ƘASAITA BOOK 3*

*NA*

*MARYAM KABIR MASHI*

Page 10

"Wacce irin magana ce wannan Yasmin?"

"Ka ce mini eh ko a'a."

"Ina son shi mana."

"In ya zube za ka ji ciwo."

"Ƙwarai kuwa."

"To ka yi tunanin irin ciwon da za ka ji,ka ƙwatanta shi ga in ka rasa ɗan da ya girma za ka ji ciwo. To mahaifinka abin da yake ji a zuciyarshi ya linka naka dubu, kuma tunda ba ka jin ban haƙurin shi, to ni ma ba zan ji ban haƙurin ka ba, zan bar maka gidanka da ƴaƴanka, amma zan tafi da cikin jikina,in je Likita ya cire mini...."

"Ki rufa mini asiri Yasmin,duk wata taƙamata taki ce,kin zauna da ni a lokacin da na shiga babban tashin hankali, sai kuma yanzu a kan ƙanƙanin abu ki ce ba zaki zauna da ni ba."

"Kai ka ɗauke shi ƙarami."

"Yasmin ke nake ji, ina son ki,ina son zama da ke, muddin na karɓi sarautar nan sai ya zamo na yi miki amarya."

Ɗan cikina ya sake wajen ƙwanciya da saurin gaske, saboda tashin hankalin da maganar Yarima ta haifar. Jinyar sakan biyar na yi sannan na yi magana.

"Na amince ka yi idan dai har za ka bi maganar iyayenka."

"Yasmin kin kuwa ji abin da na faÉ—a?"

"Na ji, cewa ka yi zakayi min amarya,ko ba haka ka faÉ—a ba?"

"Haka na faÉ—a,kin amince?"

"Eh, amma kai ma in ka amince gobe da safe za mu je Jos,ka gayawa Sarki ka amince da abin da yake so, sannan za ka koma Jos da zama,in ba haka ba,yau ba zan ƙwana gidan ka ba."

"Wannan ma bata taso ba,dama na ga wata yarinya ɗazun da na dawo daga lambu, sai kallona take yi,kin ga shi kenan sai in koma in gani. "Ƴar gayu ce."

Na yi murmushi, "Ƙyan Namiji dama ya auri mace wacce ya gani da idonsa ya ji ta ƙwanta masa a zuciya, ba wai wani ya gane masa ba."

"Yasmin kenan, ba ki san cewa matar daraja da ɗaukaka ta bi bayan zaɓin Iyaye....."

"Ya isa,mu je mu ƙwanta."

"Cikin fa?"

"Ya lafa, zan iya kai wa safe." Ya kama ni muka je muka ƙwanta.

**** **** **** **

Taro kan ya haɗo jama'a, ta ko'ina, sai isowa suke yi. Manyan sarakuna na ƙasa, gwamnoni,kai har da shugabannin kasashe, duk sun iso filin jirgi na garin Jos. Mu kuwa muna gefen mata, wajen su Mama, amma ni ma da tawa gayyar a bayana.

Yarima na can daga sashen su Mai Martaba ya sha alkyabbar alfarma. Abin ka ga farin mutum, ya yi ƙyau, wanda ba ya misaltuwa. Ni kuwa ni da Aunty Salwa daga ni sai ita muna hirar jama'ar da ke wucewa.

Bayan kamar awa biyu kowa ya gama zama aka ce Sarkin Malaman Sarakuna ya zo ya buÉ—e filin taro da addu'a (Adalin Sarki kenan,Sarkin Musulmai Dr. Usman Nagwaggo) Sarkin Katsina kenan. Dattijo fari tas, mai ruwan matasan yara, jikinsa ba ya tsufa. Shi ya fito ya fara jero addu'o'in buÉ—e taro tamkar wanda ya girma a tsakiyar Larabawa, saboda harshen da ya karya tamkar na matashin Balarabe.

Tsayawa bayanin abubuwan da aka yi ma mun san ɓatawa kanmu lokaci ne, balle lissafa manyan da suka halarta. Amma mun san Sarkin Sarakuna na Nijeriya, manya ba wani a gabanka, shi ya yi naɗin sarautar,wato Mai Martaba Alhaji.Dr. Ado Bayero, wanda jama'a ke so kenan.

**** **** ****

Wani irin mahaukacin gida ne aka bai wa Yarima, har sai da ya ba ni tsoro. Na kalli gidan, daga ni sai ƴaƴana biyu, sai cikin da ke jikina wanda bai wuce wata baƙwai ba. Masu yi mana hidima kuwa ba su ƙirguwa, amma Mama ta ce in dinga yi wa mijina abinci da kaina. Haka kuwa aka yi, duk na ware ɗaki ɗaya na mayar da shi kicin ɗin kaina, wanda ni kaɗai ke shigarsa, sai kuwa ƴaƴana, amma ko jakadiya shakkun shigarta ciki nake yi.

Tsarin kundin littafin mulkin aka damƙawa Yarima domin ya yi nazarinsa, duk da ba wai shi kenan Mai Martaba ya daina aiki ba, a'a mulkin na ga hannun Mai Martaba, Yarima kamar ɗalibi ne da malami, wato ya koyi yanda ake yi, tun kafin Mai Martaba ya rasu ko kuwa ya yi tsufan da ko ya yi magana ma jama'arsa ba za su saurare shi ba,ko kuwa a dinga cewa ruɗin tsufa ne, amma yanzu da hankalinsa, duk abin da aka yi ba daidai ba zai tsawatar.

Dama su tsarin mulkinsu kenan, shi ne a baiwa wanda ake ganin ya cancanta a baiwa sarauta, tun Sarki na da rai, ba don komai ba sai don ya ga yanda zai tafiyar da nashi tsarin mulkin, saboda in ya yi kuskure a nuna masa hanyar gyara.

Shi kuwa Yarima, sabon tsari muka zauna muka gyarawa littafin nan, saboda wani al'amarin da ake yi yakan ɗan taɓa talakawa, sannan shi Addininmu ya nuna za'a tambayi duk wani mai mulki haƙƙin yanda ya tafiyar da talakawansa.

*** *** *** ***

Tsarin da Mai Martaba na biyu ya yi, ya burge kowa, ya kuma ƙara masa farin jini a wajen talakawansa. Tsarin kuwa shi ne da kansa ya zagaya garin Jos da kewayenta domin sanin halin da talakawansa ke ciki. Wasu lokutan kuwa ma ba a shigowa a mota sai a ƙafa, wasu kuwa ƙwatami ya yi yawa, wasu ƙauyukan kuma da ƙafa ake zuwansu.

Wannan rangadi ya ɗauke shi tsayin wata biyu har da ƙwanaki goma sha baƙwai,yana yin shi. Wata rana Yarima ya dawo da fara'a, wata rana kuwa da kuka yake iso mini,saboda irin ganin da idonsa ya yi na halin da talakawansa ke ciki.

Ni kuwa ciki ya tsufa, amma har yanzu haihuwa ta ƙi zuwa, wanda zan iya cewa na shanye watan haihuwata, ma'ana na wuce watan haihuwata. Wannan kuwa ya tayar da hankalin Mai Martaba na biyu, Yarima kenan.
Chapter 12 · 0% Book details