Sashe 4
Kasaita Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"Madam kamar me ki ke ji yana yi miki ciwo.?"
"Zazzaɓi, ciwon kai, sai amai."
"Mara fa,ko ciki?"
"A'a."
"Yanzu za ki iya tuna ko ƙwana nawa rabon ki da al'ada?"
"Likita bana son irin waÉ—annan tambayoyin fa." In ji Yarima.
"To Yallaɓai an bar su, sai dai ina son fitsarinta, yanzu zan je in dawo. Awa ɗaya za ka bani."
"To ya za'ayi a É—ebi fitsarinta,in ba ya ga rashin hankali irin naka?"
"Allah ya ja da rai,ga ƴar ƙwalbar da za ta yi a ciki ta bani. Yanzu zan tafi da shi, zan yi wani ɗan aiki ne da shi. Wannan kuma jininta za'a ɗiba.
Ya fito da sirinjin ɗaga aƙwatin hannunsa, sannan ya ɗauko wani abu yasa a kunnanshi, sai na ga ya ɗaure mini hannu da wani abu kamar balt (belt).
"Ba hawan jini, Yallaɓai,a taimaka a bayar da jinin da fitsarin." Ya janyo sirinjin zai ɗauki jini. Yana sa allurar na ɗan yi ƴar ƙara.
"Ka bi a hankali fa,in har da ciwo ka barshi kawai."
"Ai an É—auka ma, sannu." Ya kama ni ya kai ni banÉ—aki, sai da muka isa ya tsayar da ni, ya tallabe kumatuna, ya dinga shafa su. Da gani ya rasa me zai ce sai kawai na ga ya haÉ—a bakina da nasa yana tsotsa, ya sake ni.
"Ya zan yi Yasmin?"
"Bana jin ciwon fa."
"Ga jikinki nan da zafi, ga shi har jikinki ya yi laushi." Ya sake ni ya fito kawa.
"Ina fitowa da ƴar ƙwalbar fitsarin a hannuna ya yi sauri ya tarye ni ya karba.
"Tashi likita." Ya kalli agogon hannunsa, ƙarfe huɗu da rabi.
"Nan da biyar da ashirin ina son in ganka cikin gidan nan."
Da rawar jiki likita ya karɓa ya tafi yana cewa, "Insha Allahu Yallaɓai, alheri ne."
Ni ke ƙwance, lulluɓe da bargo, shi kuwa tsugunne a bakin gado, yana ta faman shafa mini fuskata da bayan hannunsa, na mayar da idanuwana na lumshe, sai na ji yana cewa.
"Yasmin." Da sauri na buÉ—e ido, sai na ga ya yi ajiyar zuciya.
"How do you fell?
"Da sauƙi."
Ana haka Mama ta shigo har da Hajiya Kilishi da wasu su uku. Ya yi saurin taryarsu.
"Mama ga ta nan,zo taɓa jikinta ki ji."
"To mu je." Suka iso gabana.
"Yasmin ya ya jikin?"
"Taɓa jikinta ki ji Mama."
"Na gani ma ba sai an taɓa ba, likita ya zo?"
"Yanzu ya tafi, amma yanzu zai dawo."
"To shi kenan, bari mu jira dawowarsa, sannu Yasmin."
Na É—aga kai, dukkansu ma suka yi mini sannu, sannan na ji Mama ta ce bari su zauna a nan falo, shi kuwa cewa yake.
"Mama kada ku tafi fa, Mama mutuwa za tayi?.
"A'a."
"Za ta tashi."
"Eh." Ta juya suka tafi. Ko awa ɗaya ba a cika ba, sai ga likita ɗauke da wata ƴar talabijin ɗin ƙwamfuta da shi da wani ɗauke da wasu tarkace a hannunsa. Ya shigo, ya gama jonawa cikin mintunan daba su wuce biyar ba, sannan ya iso wajen Yarima da yake tsaye a kaina." Yallaɓai muna son za mu ɗauko hoton marar ta kawai."
"Bismillah."
"Tsaya ina zuwa." Ya iso ya janye rigata a hankali, tare da rigar ciki ta shimi. Cikin Æ´an mintuna ya ce ya gama.
"Me ye."
"Bari mu yi magana da Hajiya, tana falo."
Ya juya ya fita. Cikin mintuna biyar ya leƙo ya ce zai tafi,yana fita su Mama suka shigo.
"Yasmin mu mun tafi, Allah ya bayar da lafiya."
"Mama me ye wai.? Me likita ya ce muku?"
Ko nima sai na ji gabana na faɗuwa da sauri da sauri,cutar me gare ni kuma? Na tambayi kaina. Tambayar da Yarima ya ƙara yi wa Mama ita ta mayar da hankalina gare su.
"Mama don Allah ki gaya mini?"
"Wai me yasa baka tambayar Hajiya ga ta nan sai ni da ka raina? Ku mu je ku ƙyale su." Suka yi gaba abinsu, sai ya bi Hajiya.
"Hajiya me ye?" Sai da ta kusa isa ƙofar fita, sai na ga ta tsaya. Bana jin abin da suke faɗa, amma ni tuni har gefen filona ya jiƙe da hawaye, balle yanda na ji amsar da Mama ta bayar.
Ina kallon su shi da Hajiya, sai na ga ya dafe ƙirji duk hannu biyun,can kuma na ga ya durƙusa ƙasa da gwiwoyinsa duk biyu.
Amma sai na ga yana dariya, ya É—aga hannu sama, ita ma Hajiya ta yi waje tana dariya. Tana fita, na ga ya rugo a guje ya faÉ—a saman gadon, cewa yake.
"Allah kana ƙaunata, da za ka ƙara mayar da Yasmin ta zama tawa har abada."
Ya wuntsulo ƙasa ya tsugunna, sai na ga ya janye bargon jikina, ya ɗaga cikina ya shafa fatar shi, ya sunkuya ya sumbace shi. Ya ɗago ga fuskata, ya goge hawayen da yake ta ƙwarara a gare ta.
"Yasmin na rasa da wane baki zan yi miki godiya."
Ya sumbaci goshina, ya dawo ya shafa cikina.
"Yasmin abin farin ciki ya same mu ya ya zan yi miki bayanin shi?"
Ya ɗago ya ƙura mini idanuwan nan nasa masu firgita ƙaramin yaro. Ya ɗago cikina sosai ya rungume shi, tare da ƙwantawa a saman sa.
Ya ɗago, "Baby na ne a nan Yasmin. Na zama Daddy daga yau, kada ki ƙara kira na da Yarima, sai dai Baban Yarima." Ya kanga kunnensa.
"Lah! Yasmin,kin ji wai Æ´an biyu ne."
Nan take na gano me yake nufi. Kunya ta yi saurin dirar mini. A take na tambayi kaina, kenan ciki gare ni? To ni ya zan cewa Daddyna,in ya ganni da ciki?.
Ya matso ya ƙwantar da fuskarsa a tawa,na rufe fuskata, ya yi murmushi ya sumbaci kumatuna, tare da faɗar.
"I'm proud of you." Ma'ana "ina alfahari da ke."
Sannan na ji ya miƙe tsaye, ina kallonsa ta tsakankanin ƙofar yatsuna ya fita daga ɗakin. Tsayin mintuna biyu ya yi, sai ga shi ɗauke da ɗan faranti a hannunsa, ya zauna bakin gado tare da ajiye farantin da tree top ya ɗago ni, sai da ya matsa mini na sha, sannan ya ba ni magani ƙwaya ɗaya na sha, na koma na ƙwanta.
Ƙwanciyata ta yi daidai da wata ƙara mai ƙarfin gaske kamar ƙarar bindiga. Ban da ihu da muka ji mutane na yi. Ba Yarima da ke zaune ba,ko ni dake ƙwance ina fama da zazzaɓi, sai da na miƙe cikin sauri. Gaba ɗayanmu sai ga mu tsaye jikin taga, ban da ƙura da ta turnuƙe wajen.
Bayan kamar mintuna uku, sai muka ga ƙura na washewa a hankali. Ganin wani mutum muka yi a tsaye zagaye da shi, ana ta watsa kuɗi, jama'a na ta tsinta. Yarima ya juyo ya kamani.
"Zo ki ƙwanta, bari na sauka ƙasa na dawo."
"Ka turo mini jakadiya." Ya amsa da to. Ya yi waje.
Cikin mintuna sha biyar sai ga jakadiya a nan nake tambayar ta me ke faruwa? Bayan gaisuwar da ta yi mini,a nan take ba ni labari wai wani ɗan Sarki ne ya zo, tun ba mu daɗe da tafiya ba. Ba yaudarar da ba ya yi a gidan nan, shi ne rabon kuɗi, abinci da sauran kayayyaki, duk wanda aka kaiwa ya ƙi karɓa, to zai faɗa ne. Take gaya mini ko ita an bata magani ta zubawa Yarima a abinci da sauran wurare.
"Kin karɓa?"
"Eh, saboda in ka ƙi karɓa sai dai a wayi gari ba kai."
"ÆŠan Sarkin wane gari ne?"
"An ce babban Yayan su Yarima ne,wai shi Abdulrahman."
Na yi shiru. A nan take na tunano labarin da Mama ta ba ni, ina cikin wannan tunani sai ga Yarima ya shigo da saurin shi.
"An kashe mutum uku a wajen can."
"Me ye dalilin kashe su?"
"Wai saboda sun ƙi ɗibar kuɗin da yake sa wa ana watsawa."
"Wa ye shi?"
Wai Yayan mu ne."
"Meye dalilinsa na yin haka?"
"Sarauta yake so."
Na yi shiru tare da faÉ—uwar gaba mai tsanani saboda tunanin kada a kashe mini mijina.
Canja alkyabbar jikinsa ya yi, ya ƙara sa turare a jikinsa.
"Ina za ka?"
"Wa je." Na miƙe da sauri.
"A'a kada ka fita ya harbe ka."
Ya yi murmushi.
"Ai mu ba'a kashe mu ta nan ɓangaren."
Ya nuna jakadiya da É—an yatsa.
"Kin ga wacce za ki danƙawa amanar mijinki nan. Sai kuwa masu dafa mini abinci, ta sanadiyyar su ake yi mini komai."
Ya iso inda nake tsaye, ya tallafi kumatuna, cikin nutsuwa ya fara magana.
Kada ki tayar da hankalinki,ki yi tunanin cewa kina da yaron ciki, zai iya zuɓewa ta kowanne hali,ki ƙwantar da hankalinki."
Hawaye suka ƙarasa gangarowa.
"Ni dai ban yarda ba."
Ya yi murmushi, "Yasmin kada ki karaya mana. Ki tuna gidan sarauta fa ki ke. Haba Honey."
Na ƙwantar da kaina a ƙirjinsa, sai kuka sosai. Ya ɗago ni ya ƙura mini ido ba tare da ya yi magana ba. Ɗan tsayin minti ɗaya, sai kawai na ga ya mayar da ni ya rungume ni sosai. Ya ɗago ni da saurinsa ya sumbaci goshina, ya dawo ya tsotsi bakina,bai ce komai ba ya ɗauke ni cak ya ɗora a gado. Ya ja bargo ya lulluɓe ni, ya sunkuyo yana gyara gashin kaina, wanda ya zubo a fuskata,ko in ce wanda ya hautsine saboda ƙwanciya.
#######
[2/20, 13:07] Ummi Tandama😇: *ƘASAITA BOOK 3*
*NA*
*MARYAM KABIR MASHI*
Page 4
Ya ƙara sumbatar goshina, kawai ya juya ya tafi. Bin shi na yi da kallo, shi yasa idanuwana suka gane mini ba jakadiya a ɗakin nawa. Yana fita tana shigowa na mayar da kaina na ƙwantar,sai na ji hawaye sun ƙi tsayawa. Jakadiya ta iso ta tsugunna gaban gadona.
Allah ya ja da rai,ai ke ce ya kamata a ce kin ƙara ƙarfafa masa gwiwa tare da shawarwari, ke ce mace,kin fi shi tausayi, ke ya kamata a ce kin tsaya kin lura da tambayar me yakamata a yi wa talakawa,shin hukuncin da bai cancanta ba a yi shi?"
Na tashi zaune. "To yanzu jakadiya,kina jin ya ce an kashe mutum uku, wacce kuma daraja gare shi,ai kin ga bai dace ba ya fita, sai ya tsaya ya ga ya zata kasance."