← Book details Kasaita Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 8 OF 17

Sashe 8

Kasaita Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Na yi murmushin zuci na miƙe, saboda tunanin me Yarima ya mayar da ni,yarinya ko me? Na iso na zauna gefe ɗan nesa da shi ya miƙo mini na karɓa ina mai mayar da hankali a kan ambulan ɗin.

"BuÉ—e mana."

Ban ce komai ba na buÉ—e ta, litattafai ne guda biyu wanda yanayin hotan da ke jikinsu da sunansu ya nuna mini cewa su Nobel (Novel) ne, na É—ora su a cinyata, saboda jin da sauran wani a ciki,alawoyin chakuleti na ji a ciki (Chocolate), ina zarowa na ga an rubuta Bounty a jiki.

Na É—ago na kalleshi wanda kallon yana nuna alamar tambaya.

"Taimaka mini za ki yi ki karanta mini su, amma yau mu fara da ɗayan duk da na san da wuya mu yi ƙwata a yau, amma ƙila ma yi sati muna karantashi, chakulet kuwa matata na siyawa, saboda na san zata taya ta hira."

Ya haye can ƙarshen gado ya ƙwanta irin ƙwanciyarsa da ya saba,wato rigingine, sannan ya yi filo da tafukan hannayensa, ya mayar da idanuwansa ya lumshe. Na girgiza kaina sannan nima na gyara sosai nasa fulalluka na tare bayana, sannan na soma karantawa.

Ni kaina na san muryata ta yi daɗi a wajen karatun, na san kuma duk mai sauraren karatun zai ji daɗinsa, saboda dallah-dallah nake yinsa, cikin cikakkiyar nutsuwa. A ƙalla ni na san na ɗauki mintuna talatin zuwa talatin da ƴan mintuna ina karantawa, sannan na ɗago kaina na kalli Yarima wanda na ji ya yi shiru,ni a tunanina ya yi bacci, amma sai na ga ya ɓalle maɓallin gaban rigarsa gaba ɗaya.

Ni kaina na san Yarima na da gashin da ya ƙwanta a ƙirjinsa, dalilin ganin kuwa,ɗakinsa da na taɓa shiga na same shi yana bacci, amma abin mamaki sai na ga na yau yafi na ranar yawa,baƙi,ƙwantacce tamkar sumar jariri. Na yi saurin mayar da kaina ga littafin da ke hannuna, amma kuma sai na ji na samu kaina da son kallonsa duk bayan ƴan mintuna. Ɗagowar da zan yi in kalleshi sai naga ya ware duk biyun gaba ɗayan rigar jikinsa ta sauka saman gado, cikinsa, cibiyarshi,ƙirjinsa da kafaɗunsa duk a waje suke, take na ji jikina na neman kama rawa,me ye wannan? Ni dai na san har yanzun ba na son Yarima, sai dai na san ina jin kunyarsa.

Na mayar da kaina ga karatuna, amma ni kaina sai na ji muryata ta canja,lumfashina kuwa ma nema yake ya tsaya,a zuciyata nake rayawa cewa in ajiye littafin in tafi gidana, madadin in ji ƙwarin gwiwa sai na ji tamkar an sare mini gwaiwoyina,cikin hakan da nake kawai sai na ji Yarima na kiran sunana a hankali.

Jin kiran sunana ma sai na ji ya ƙara sani na dake, na dawo dai-dai saboda tunanin ko Yarima ya fahimci na shiga wata matsala da na san ba zan iya faɗarta ba,kiran sunana ya kamata a ce ɗaya ne ko biyu, amma tun da Yarima ya fara shi ban ji ya tsaya ba, tun ina ci gaba da karatun har ya zama ina saukar littafin hannuna a hankali izuwa ƙirjina.

Kallona sai ya koma ga yarima da yake kirana, wanda idona ya hango ƙirjinsa na fitar da numfashi da sauri da sauri, wani mashi ne na ji ya dirar mini ta tsakiyar kaina, jikina na ji har ya ɗauki rawa cikin sakan ɗaya, saboda kiran da Yarima yake mini ya fi ƙarfin a tsaya ƙirgawa.

Littafin saman ƙirjina wanda hannuwana suka taimaka masa ya zauna a ƙirjin nawa, sai na ji ya faɗo saman cinyata saboda hannuwan nawa sun kasa ɗaukarsa,jiri ne ya ɗauke ni ko kuwa suman sakan biyu na yi? Ni dai ji na nayi na sulale na ƙwanta saman gado sosai a riginginan da nake da ƙyar na ja filo ɗaya ya tallaɓe mini kaina.

Amma duk wannan bai hana Yarima kiran sunana ba, idanuwana, kaina,jikina sun yi mini nauyin da ba za su iya motsawa ba, balle har ƙwayar idona ta samu ganin halin da Yarima yake ciki,ko ni kaina,shin me ye wannan? Ni na san ƙwaƙwalwata ta daina aiki balle in tunano amsar abubuwan da suka tarar mini a cikin mintunan da ba su wuce uku ba.

Mai nake ji a jikina? Kamar numfashin mutum a hancina, ƙwaƙwalwata na ji na karanto mini Yarima na bin jikina, hannayena da ke ware ya bi da hannayensa a hankali har izuwa tafukan hannayena ya haɗa da nashi ya runtse gam, sumbatar wuyana na ji ya yi, ya dawo hancina,bakina,buɗaɗɗan gaban ƙirjina da riga ba ta ƙarasa rufe shi ba.

Ni na san ina ji, amma ba zan iya motsa ɗan yatsana ba, balle har ya kai ni ga iya magana,ko ƙwatar jikina ba, sai dai na san numfashina yana fita sama-sama, ina jin shi kanshi ya ruɗe ya rasa ina zai kai sumbatar nasa,ko ina ya yi ina jin sa yasa haƙoransa ya zuge zib ɗin da ke gaban riga ta, wai nan na yi ƙarfin hali zan yi magana, amma madadin bakin da na samu da ƙyar na buɗe in yi magana sai gani na tsaya da wani irin numfashin da ya kasa wucewa cikina, ya tsaya mini cak a maƙoshina,saboda jin harshen Yarima na lasar fatar cikina, sai a lokacin na ji kamar na tunano ban sa shimi ba,rigar mama ce kawai na saka da zan taho.

Jin ya nutsa hannayensa a gashin kaina yasa na samu da ƙyar lumfashina ya isa cikin cikina tare da faɗar "Hasbunallahu wani'imal wakil" sai na ji kamar ɗan jinin jikina ya dawo, na samu na yi ɗan ƙoƙarin miƙewa zaune, amma ina sam na kasa, saboda Yarima da ya samu ƙaramin taɓin hankali a jikina.

Da ƙyar na buɗe idanuwana sannan na ɗaga kan Yarima na tallabo kumatunsa na girgiza kaina, wanda fuskata ke fitar da hawaye da ban fahimci ta ina suke fitowa ba, yasa hannuwansa duk biyun ya ɗago kaina ya girgiza kanshi shi ma, sai a nan na lura da hawayen da suka wanke fuskarshi shi ma, da ƙyar na ji ya ce, "Yasmin!"

Yana mayar da numfashi ɗaya bayan ɗaya. Na girgiza kaina da ƙarfi, sannan na samu na miƙe na zauna, ya koma gefe ya ƙwanta rigingine yana wani irin numfashi. Na miƙe tsaye, tafiya na fara nayi luuu zan faɗi, na yi saurin zaunawa, na nutsa hannuwana a gashin kaina, jin ya rarrafo ya zo ya rungume ni yasa na ɗan samu ƙarfin cire hannuwansa daga jikina na miƙe.

*ƘASAITA BOOK 2*

*NA*

*MARYAM KABIR MASHI*

Page 7

Na mayar da zib ɗin rigata na zuge, na samu na ja mayafina da ke saman gado ba zancen tsayawa yafawa, sai da na je ƙofa, sannan na tsugunna na ɗauki takalmana a lokacin idanuwana suka sauya kallo izuwa saman gadon da Yarima ke durƙushe yana kallona ya ware hannayensa yana ɗan girgiza kansa kada in tafi.

Ganin ina kallon shi yasa na ji yana kiran, "Please Yasmin come to me." Wannan ma yasa na juya na tafi, sai kuwa da na je ƙofar fita, sannan na samu na yafa mayafina, amma takalma sai da na je ƙofar gida, sannan na iya sa su, ina buɗe ƙofa kuwa taku uku na yi na tuɓe su na riƙe a hannuna ina isa ɗakina na wurgar da su.

Fitilu kawai na kashe na faɗa saman gadona ban tsaya neman wata rigar bacci ba,fulalluka na haɗa na rungume a ƙirjina,ni kaina ban san me zan tunano ba saboda ƙwaƙwalwata ma ta daina aiki, sai dai numfashina kam ya dawo, amma da ɗan sauri nake fitar da shi tamkar na yi gudu na gaji.

Ban fi mintuna biyar ba na ji an murɗa ƙofata an shigo, da ƙyar na samu na lalubo wayar makunnan fitilar ɗakina ina kunnawa sai na ga Yarima a tsaye, yanda rigarsa take haka take ma yanzu, na lumshe idanuwana na mayar da kaina na ƙwantar alamar mamaki,jin an mayar da ƙofa an rufe yasa na ɗaga na kalleshi, ban yi wani ƙoƙarin tashi ba.

Ganin ya nufo gadona yasa na fara tunanin me zan yi yanzu ban tunano komai ba na ji ƙarar faɗuwa, kallon da zan yi sai na ga yarima a ƙasa na yi wata doguwar wuntsulawar da ban san ma ina da ƙarfin yin ta ba,ni dai gani na nayi kawai a gabansa na ɗago shi na girgiza shi, cikin wani yanayin muryar tashin hankali na kira sunansa.

Cikin sakan uku na ga ya buɗe idanuwansa yana murmushi,ni kuwa har na fara fita daga hayyacina a cikin ƴan sakannin nan, sai na ji kawai na yi ƴar dariya, shi ma sai ya ƙara yin murmushi, sannan ya tashi ya zauna ya kishingiɗa a cinyata da take durƙushe, sai a lokacin ne ma hankalinmu ya kai ga abin da ya kada shi. Takalmana ne da na yi jifa da su muka gani a gefe ɗaya, yasa hannu ya ɗaga takalman ya kalleni sai kuwa muka yi dariya gaba ɗaya, amma irin mai kama da murmushin dariya,yana cikin haka ne ya juyo ya haɗa goshina da nasa, sannan ya rataye hannayensa bayan wuyana. Cikin yanayin dariya ne ƴan hawayen da suka fito a lokacin da nake faman son in ga ya tashi suka gangaro, sai na ji ya saki takalmin ya ɗago fuskata yasa hannayensa duk biyun ya lalubo kumatuna, sannan yasa manyan ƴan yatsunsa yana goge mini hawayena tare da girgiza kansa alamar a'a.

Sai kuwa na jina lumshe idanuwana ina yin ƴar wata dariyar kuka-kuka, murna-murna, sannan na sunkuyar da kaina sosai na ci gaba da ɗan kukan murna,gashin kaina kuwa ya zubo ya rufe mana fuskokinmu. Ina jinsa ya sa hannayensa ya tattare gashina, sannan ya ɗago kaina da hannayensa, kallon da ya yi mini yasa a take na ji na nutsu, saboda haɗa ido huɗu da muka yi da shi,kafin in yi wani motsi tuni ya kai bakinsa ga nawa, kafin inyi wani tunani har ya lalubo harshena ya riƙe.
Chapter 8 · 0% Book details