← Book details Kasaita Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 11 OF 17

Sashe 11

Kasaita Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Allah ya ja da rai gata." Sannan ta miƙa mini.

Kafin inyi magana tuni na gane muryarsa, duk da ji ta ƙara zame mini baƙuwa,saboda ta koma ƴar ƙarama mai zaƙin gaske.

"Good morning, I hope you are recovering?"

"Darling what happening?"

"Oh, darling sorry, honey say hello to me please,ko na samu nutsuwa."

Ni na san dama ba zan iya amsa masa duk maganar da zai yi ba saboda abu biyu kunya da haushin tonan asirin da ya yi mini,saboda haka na kife kan wayar ba tare da nayi magana ba,bai fi minti ɗaya da ajiye wayar ba na ga Hajiya Kilishi ta yi sallama ta shigo. Subhanahi! Shi kenan ƙaryata ta ƙare, wannan tonan asirin na san ya je kunnan Sarki.

Hawaye ma na ji kawai sun tarar mini a cikin ƙwayoyin idanuwana,mata biyar ne biye da ita, da ganinsu ka san matan masu faɗa a ji ne, wato matan masu kuɗi, saboda biyu daga cikinsu na san su suna zuwa duba ni da na zauna zaman jinyar saran maciji a gidan Sarki.

Kaya ne lodi-lodi a hannunsu, irin farantan da jakadiya ta taɓa kawo mini kayan siyan baki,a ranar da aka bar ni ni ɗaya. Da ƙyar na samu na gaishe su saboda kunya. A nan jakadiya ta gayawa Hajiya na ƙi yarda a yi mini komai, da lallashi da ban magana ta shawo kaina, shi ma dan ina jin kunya da nauyinta, ga shi kuma tana da girma a idanuwana.

Ta tabbatar mini da cewa ita ma haka aka yi mata, sannan duk ɗan hakimi a kan haɗa masa ƴar ƙwarya-ƙwaryar irin wannan bikin idan dai har matarsa takai, to balle ni wai da nake matar ɗan Sarki gaba ɗaya. Dole dai ta sa na tsaya,nan fa naga hidima, ƙunshi mai zane, hannuwa da ƙafafuwa, wani irin naɗin kitso ƙwaya shida kacal, wanda na ga ya fi yi mini kama da kalba, amma bambancinsu shi naɗinsa kamar ana murɗa igiyar shanya.

*ƘASAITA BOOK 2*

*NA*

*MARYAM KABIR MASHI*

Page 9

Ni gyaran da ake yi mini ko ina amarya Ni ban same shi ba, saboda sai da Hajiya Kilishi ta sa na tsugunna ga turarurruka kala-kala shida, dukkansu kuma na garwashin wuta, sai a lokacin da suka gama ne ma aka buɗe kayan da suka shigo da su. Wata ƙwarya ce ta sha zanan baƙi ƴar ƙarama aka miƙo mini,wai in shanye abin da ke cikinta, ban yi gardama ba na kafa bakina sai naji kamar ruwan inibi da madara, kamar kuma madara da ruwan ƙwaƙwa, ni dai na shanye.

A taƙaice dai hidima ta tashi sabuwa tamkar ana wani ƙasaitaccen biki. Ƙarfe goma na safe kuwa ai gida ba inda zaka zauna, saboda jama'a. Hajiya Kilishi ta gaya mini cewa za'a tambaye ni me nake so, saboda mutane da kunya da wuya in iya magana, amma in rubuta a takarda,in an tambaya in bai wa jakadiya,kar in yarda wai a ga fuskata sosai,in zamo mai kunya.

Da za'a fita da ni inda zan zauna, sai da aka sa nayi tsaye na ware ƙafafuwana a saman wani kaskon wuta mai fitar da hayaƙin ƙamshi, shiga ta kuwa ba zan iya faɗar ko meye a jikina ba,ni dai kiran shi da yadi mai laushin gaske,ko kuwa les ne? Oho,ni dai na san sai dai kalar sa ce ruwan hoda, takalma da alkyabbar jikina kuwa ruwan madara ne, tare da mayafin da na zizara a saman kafaɗa ta.

Wannan al'ada ina amfaninta, na faÉ—a a zuciyata. A lokacin da na isa kujerar zamana inda muka zauna ina amarya,yau ma anan muke,ni da Yarima, sai dai kujerun da shimfiÉ—un kafet É—in sun sha bamban da na baya,sam ban sani ba, ashe kowa ya hallara ni kawai ake jira, hatta da sarki ya iso yana nashi rukunin, ango Yarima kuwa nan na sameshi a zaune.

Ba zan iya gane ko su wa da su waye ba ne a bayana, saboda gilashin da ke manne a idanuwana, ban da wani mayani da Hajiya Kilishi tasa ta ɗan lulluɓe min rabin fuskata, filin kasan ƙasan kuwa daga can gefe ɗaya raguna ne kawai ake gasawa a ƙarƙashin wuta, tamkar dai waɗanda zasu yi fati.

Aka buɗe fili da addu'a da sauran bayanan manyan mutane, wanda a ƙarshe Sarki ne da kansa ya miƙe yana bayani da godiya ga waɗanda suka zo,ni kuwa da ɗansa Yarima mun sha albarka, a lokacin ne naji Yarima ya zuro hannu ta alkyabbarsa ya kama hannuna.

Ban da dama tun da na zauna yake ta zunguran mini ƙafa da tashi ƙafar, ta ƙarƙashin kujerarmu,ni na san ba mai gani, tunda alkyabbun jikinmu sun rufe har ƙafafunmu, na ji kalma ɗaya da ya faɗa ita ce, "You Are cheerful Yasmin."

Na samu na sulale hannuna ba tare da na kalleshi ba. Ƙyaututtuka kam na sha su, shi kansa Sarki ƙyautar gidan gonarsa na ƙauyan Bukuru ya ba ni, ya kuma ce zan ziyarci ƙasa huɗu, sai wacce na zaɓa, sannan ya baiwa iyayena sababbin motoci guda biyu, ban da wani dunƙulin abu a cikin jar jaka da naga ya ce tasu ce, sai dai ban san komai ke ciki ba.

Waziri ya bani bayi huɗu da dokuna uku,doki biyu goɗiya, ɗaya namiji, da sabuwar mota ƙirar KIA (Optima). Ni wata ƙyautar ma in an faɗeta sai inji kamar ma ƙarya sukeyi, magana kuwa cikin nutsuwa yanda ba mai ji, Yarima ya dinga yi mini ita sau ɗaya na yi murmushi, na ji ya ce, "Thank God."

Kaina na ji ya sara tare da juyawa wani amai mai zafin gaske da na ji ya taso mini,wannan kuwa ya sameni a daidai lokacin da na ga wasu fadawa biyu sun miƙe tsaye da wani farin abu a hannunsu,sam da ban gane ko meye ba, sai lokacin da naji sun ce, "wannan farin zanin da kuke gani, shi ne zanin shaidar cewa ƴarmu ta kai ɗakinta, wato Gimbiya Yasmin."

A take na gane zanin gadon ɗakina ne wanda na baiwa jakadiya amanarshi, shi ne fa hankalina ya yi matuƙar tashi, a take na tallabe ƙirjina alamar amai, Yarima ya yi saurin dafa ni.

"Yasmin meye?"

Wata tambayar raini ma na faɗa a zuciyata, kafin ya ƙara yin wata magana sai dai na hango an ware zanin gadon nan kowa ya kama gefe ɗaya, kenan dai an yi masa buɗewar zanin da za'a shanya.

Cikin sakan biyu sai dai na ji amai ya wanke mini jiki dama ni gani ban iya ganin abin tashin hankali ba, sai inji ni ina ta amai, kamar wata mai yaron ciki,ko kunya ma Yarima bai ji ba naga ya miƙe da sauri ya kama ni,kafin sakan uku sai dai na ga wani koran labule ya sauka a gabanmu da bayanmu dama gefenmu ba kowa kujerunmu ne kawai.

Cikin ƙanƙanin lokaci Yarima ya ɗaga ni na miƙe tsaye,da amai ya yi tsalle sai jikin Yarima amma sai na ga ko a jikinsa shi dai buƙatarsa in taka,gyaran murya na ji ya yi sai dai na ga hannu ya zuro ta wata ƙofa ya miƙo masa wani yanki ja, mai kama da yankin bargon jariri, har ya fara goge mini,ganin ina layi yasa na ga ya ɗauke ni cak sai dai na ji ya yi gyaran murya.

A take na ga kawai yana tafiya labulan nan na binmu ba mai ganin kowa ba mai ganinmu, shi kuwa ɗan yankin nan ya shinfiɗa shi saman ƙirjina wanda amai ke ta zuba a jikinsa,ni dai dole ta sa na koma saman ƙirjin Yarima na ƙwanta, idanuwana kuwa tuni a lumshe suke.

Jin an ajiye ni wani abu mai laushi yasa na buɗe idanuwana,gani na a ɗakina saman lallausar katifar mulkin nan zan ce ko kujera? Wacce ta sha dardumai na alfarma, da rawar jiki na ga ya cire alkyabbar jikinsa da ta sha feshin amai, sannan ya duƙo wajena yana ƙoƙarin cire mini tawa,na ɗaya masa hannu alamar ya tsaya.

"Don't touch me." Na faÉ—a.

"Yasmin ki yi haƙuri in taimaka miki."

"Bana so,ni ka kira mini Aunty Salwa."
Na saka kuka, yayin da na ci gaba da cewa "ka cuceni,ka tona mini asiri,ka yaudare ni, Allah ya saka mini, yanzun kuma gidanmu zan tafi, ba zan ƙara zaman dabbanci ba a gidanka,ƙiri-ƙiri ku mayar da al'ada addini."

Yasmin ni kaina ba na so, ya zan yi dama na san sai kin zarge ni."

"Zargi ne ma?"

Ya zauna jikin gadon zai kama ni.

"Kada ka taɓa ni,wa ya sani ko yanzun ma ka fita ka faɗawa jama'a cewa ka rungume ni."

"Oh! My Darling....."

Dagewa na yi nasa kuka mai ƙarfi, sai na ji ya tashi ina jin takun fitarsa,bai fi minti biyar ba sai na ji an shigo. Aunty Salwa ce ta shigo da saurin ta.

"Aunty kin ga Yarima ko, ya cuceni, ya wulaƙanta ni a gaban jama'a." Na ƙara sa da kuka.

Ta iso ta zauna kusa da ni tare da dafa kafaÉ—ata.

"Haba Yasmin bai dace ba a ce kin zargi mijinki ba a kan abin da ya faru,in har za kiyi la'akari da taron da aka yi a yanzu, wannan zai nuna miki cewa tun kafin a san za'a haifi shi kanshi Sarkin haka akeyi, na fahimci al'ada ce su wacce take muhimmiya a wajensu. Saboda muhimmancinta fa Sarki da kansa yau tun da baƙwai na safe ya je ya gayawa Daddy,kin ga irin murnar da Sarki ke yi kuwa,ni a ɗan tunanina da na yi, wannan shi ne mataki na ƙarshe da za'a gane wa ye Sarki na gaba,in ka dace da mace tagari, to daga lokacin ma za'a iya kiranka Sarki mai jiran gado,in kuwa da sauƙi, to ko mutuwa sarki ya yi an san ɗansa wanda ya cancanci a baiwa sarauta.

Ki yi tunani ki gani,ni tunanin abin da za ki yi ƙoƙarin ki hana a nan gaba, shi ne yin taron,ko nunawa jama'a zanin gadon yanzun ki tashi ki canja kayan jikinki, kamata ya yi ma ki ɗan shiga ruwan ɗumi."
Chapter 11 · 0% Book details