← Book details Kasaita Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 2 OF 17

Sashe 2

Kasaita Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Tun ban É—aukar abin da Yarima ke mini da sunan so, har zuciyata ta amince lallai ya kamu da ciwon sona, ciwon da na lura ya riga ya yi masa katanga a zuciya,ni dai bana cewa ina son Yarima, amma tsanar da nake nuna masa a baya, yanzun bana iya yi masa ita.

Da la'asar wacce ta cika ƙwana huɗun sai ga Mama, bayan gaisawarmu ne, na ga sun fita falon sama da yake labulan shara-shara ne tsakanin ƙofata da falon, shi ya bani damar ganin abin da ke faruwa a tsakanin Yarima da Mama.

Shi ne na ga ya durƙusa ƙasa yana yi mata magana, amma bana jin maganar, sun ɗan ɗauki mintuna sha biyar sannan ya shigo.

"Yasmin can gida zan tafi da ke domin yi miki magani sosai,kin ga can an fi samun magani,a yanzun haka ma Sarki ya tura a ɗauko wani mai magani a ƙauyen Bukuru."

Na washe baki alamar na ji daɗin maganar da ta faɗa, amma sai na ji jikina kamar bai amince ba, sai dai kuma ba zancen gardama a tsakaninmu,ɗaga kaina da nayi na hango Yarima jingine a jikin bangon shigowa ɗakina, shi yasa na ji tausayinsa ya kama ni. Ya iso wajen Mama jiki a sanyaye, ya durƙusa ƙasa ya kama hannuwanta.

"Mama, wallahi ina kulawa da ita,ki tambaye ta ki ji, Yasmin ba ina kulawa da ke ba? Mama a nan fa nake ƙwana a wajenta, Mama ki bar ta wallahi zan kula da ita sosai, zan fi dama."

"Wai kai meye na damun kanka ne a kanta, kai ka ce mini baka son...."

"Mama kada ki faɗa, wannan a da ne,shin ba cewa na yi ƙwata-ƙwata ba."

"Ka ga an gama magana, sai dai ka yi haƙuri."

Ta juya ta kalleni.

"Zan tafi da ke yanzun,su wa za'a kira su shirya miki kayanki?"

"Mansura." Na bata amsa.

Ta kalleshi, "Kirawo Mansura a falo babba." Ya ce to, ya miƙe ya tafi.

Saman kujera doguwa yake zaune a babban falo, ya ƙwanta jikinta sosai, da gani ka san cikin damuwa yake, ya ɗago ya kalleni a daidai lokacin da ake saukowa da ni sai na ga ya yi murmushi.

"Ina nan zuwa anjima." Haka kawai ya faÉ—a,mu kuwa muka wuce.

**** **** ***"

Lallai kam na ga gata, na tabbatar da cewa iyayen mijina na ƙaunar ɗan su, shi yasa ƙaunar ta shafe ni,a nan na ƙara yarda da cewa sarauta abin ƙauna ce, ga wanda bai shige ta ba ne yake ganin tamkar aikin bauta ake a cikinta.

Yanzun kam ni da kaina zuciyata da sauran jikina suna ƙaunar sarauta, saboda ganin yanda take tafiya cikin tsari da nunawa jama'a ƙauna ta gaske. A wannan zaman ne ma na san wa ye Yarima da iyayensa.

**** **** ****

Yarima fari ne,ƙyakƙyawan gaske wanda dirin jikinsa na cikakken namijin da ya amsa sunansa, wanda gashin bakin fuskarsa ya ƙara ƙawata fuskar tasa, amma shi farin shi ja ne, tamkar na Turawa, idanuwansa kuwa sun ɗan yi girma kaɗan, tamkar na Salman Khan ɗan ƙasar Indiya.

Sai dai shi zamu iya kiran ƙirar jikinsa irin ta Turawa, da ganinsa dai ka ga (Handsome). Tabbas ya cancanci sunansa, wato FAYSAL.

Su biyar ne kaɗai ƴaƴan Sarki. Yarima shi ne babba, sai ƙannansa huɗu, amma mace ke bi masa Salimat, ita ce matar ɗan Sarkin Wasai, wato ƙaramar hukuma ce a Jos,sunan mai bi mata Idris,saurayi ne yana karatu a London, sai Sauda wacce take aure a Mina,sai autansu Ahmad. Yarima za a iya kiransa ɗan shekara talatin da biyar, ya yi karatunsa ne a Greece tun yana ɗan Sakandire aka kai shi ya karanci hulɗa da jama'a Public Relations.

Ba wai domin ya yi aiki ba, a'a don dai ya iya zama da jama'a da riƙe gari, idan ya zamana ya hau mulki.

Matan Sarki biyu ne, amma mahaifiyarsu Yarima Hajiya Mariya, ita ta haifesu su uku, shi da ƙannansa, da Idris da Salimat, amma Sauda ƴar ɗakin Hajiya Khilishi ce ita da Ahmad wanda yanzu yake makarantar gaba da Primary.

*ƘASAITA BOOK 2*

*NA*

*MARYAM KABIR MASHI*

Page 2

Ko a ido ka ga yanda ake wa Yarima,ka san ana ji da shi, sannan kuma sam ba ka gane cewa ba ɗakinsu ɗaya da ragowar ƙannansa ba,ni kaina sai da na zauna gidan sannan na gane da kaina.

Amma Mama ta ce mini, Yarima ba shi ne ɗan Sarki na farko ba,yana da yayyansa biyu mace ce babbar gidan ƙwata-ƙwata Hajiya Asabe, sai ƙannanta Abdul Rahman, amma tun kafin sarki ya hau sarauta ya auri uwarsu Hajiya Hadiza, sun rabu tun shekaru da dama.

Yanda ta ba ni labari ba ta san abin da ya haÉ—a su ba, amma Sarki baya son ko sunan yaran a ambata, ba ma uwarsu ba, wannan dalili ne ma yasa jama'a da dama sun yi zaton Yarima ne babban É—an Sarki Jafar.

Uwarsu Abdul Rahman tafiya ta yi da su hannunta tun suna ƙanana, sai dai in sun ga dama suna zuwa gaishe shi, shi ma sai a yi shekaru basu zo ba, yanda ta bani labarin, yanzun haka Hajiya Asabe tana Ibadan tana auran wani mai kuɗi Alhaji Alabi.

Shi kuwa Abdul Rahman yana Scotland zaune da matarsa baturiya (Vivian), yanda Mama take nuna mini kamar Sarki ya yafe su ƙwata-ƙwata, kenan ya barwa uwarsu su, sai dai ta ce ya kan aika masu da kuɗin makaranta da na abinci da suna yara, yanzun kuwa ko maganarsu ma baya son a tayar.

Asalinsu Mama kuma iyayenta ƴan barikin Ladi ta nan Jahar Plateau,tun da daɗewa a garin Jos,ƴan ƙauyukan garin ke zuwa karatu, wato Makarantar ƙwana ta gaba da Primary,anan suka haɗe da Sarki a lokacin bai ma hau gadon sarauta ba, daga baya ne ma da ya hau mulki ya ƙara auran Hajiya Kilishi.

Yanzun haka iyayen Mama suna nan da ransu a garin Aboko, da sauran danginta. Yarima kuwa shi ne ɗan ta na farko, sai Salimat, sannan Idris, daga su kuwa ba ta ƙara ba. Hajiya Kilishi kuwa anan Jos ya aure ta,ɗiyar hakimin Bukuro ce ta nan ƙaramar hukumar Plateau.

Saboda rashin ganin hanya a ranar da muka zo gaishe da iyayen Yarima, shi yasa ban gane cikin gari suke zaune ba,a unguwar Dogon Agogo,wai wannan rukunin da nake gani har wajen baƙwai a gidan Yarima,wai na farko fada ce in Sarki ya zo kenan dai gidansa ne na hutawa,ko kawo baƙi na musamman.

Sai masallaci a liƙe da shi, ragowar rukunin kuwa kamar namu ne,gidana da na Yarima, sai na su Idris da Ahmad,wai in sun yi aure, amma kowanne da kalar yanda aka tsara nasa ginin, amma tsananin kowanne gida zuwa wani gida, sai an shiga mota,in ba motsa jini za'a yi ba, saboda ko da Asuba ko ragowar sallolin nan an kai Yarima a mota.

*** **** ****

Tsugunne muke gaban Sarki ni da Yarima a ƙaton falonsa, na cikin gida,kawunanmu kuwa a sunkuye suke da gani ka san gaban manya muke.

"Yau ne matarka za ta koma gidanta wacce ta samu tsayin ƙwanaki arba'in da biyu a hannunmu, dalilin da sakacin da ka yi da ita har ta faɗa haɗarin saran maciji.

Bayani ya same ni na irin zaman da ka yi da ita a baya, zaman ko in kula da banzatar da ita. Wannan dalili ne ma ya janyo mata faɗawa rayuwa ƙuntatacciya, na gode,ka yi mini daidai ashe ni ina taƙama da ina da ɗa mai biyayya, ashe ban sani ba,ƙarya zuciyata ke gaya mini.

Ka bani mamaki,a ce ita mace na je na nemo auranta ga iyayenta, suka amince suka ba ka ita, alhalin ba ta san ka ba, kuma suna da wanda ke jiransu su aura masa ƴarsu, ita ma tana da wanda zuciyarta ke so, amma ta haƙura ta yi biyayya ga iyayenta, kai kuwa ban isa ba."

"Baba...." Yarima ya faÉ—a cikin sanyin murya.

"Kada ka ce mini komai, kai ne da bakin ka ka gaya mini da ka amince in zaɓa maka wacce na ga ta dace da kai, tun daga ranar na baza mutane a kan su gano mini matar da ta dace da ɗana wanda nake mugun ƙauna a zuciyata, Allah ya ba ni ya kuma ba da sa'ar aka samu ƴar gidan manyan mutane masu mutunci.

Ka tuna,bakina da naka muka yi wannan maganar ba fa aike na yi maka ba,ka tuna,kiranka na yi ka faɗa mini wacce yarinya ka gani ta ƙwanta maka a yi maganar auranku,ka tuna, kai da bakinka ka ce mini babu.

Yanzun na yanke hukunci zan raba auranku, amma na baka tsayin ƙwanaki biyar ka zo mini da rubutacciyar takardar sakinta...."

"Baba...."

"Bana son jin komai daga gare ka,ka bani haushi,ka ɓata mini raina matuƙa."

Ya miƙe tsaye, "Ɗiyata ina ƙaunarki da ɗana, amma ki je kiyi haƙuri, sannan ki yafe ni da na sa aka raba ki da wanda ke son ki,saboda son kai irin nawa. Zan aiko a yi kiranki." Ya juya ya tafi.

Yana ƙulewa a inda har ya ƙule, Yarima na Baba,Baba cikin girmamawa, amma bai ko juyo ba,ni kuwa na waigo a sanyaye na kalli Yarima inda ya koma ya ƙarasa zama a ƙasa.

"Tashi mu tafi." Na faɗa cikin muryar da zata ƙara karyar da zuciya.

"Kin ji abin da Sarki ya ce fa Yasmin."

Na ɗan yi murmushin da ƙago shi kawai na yi.

"Kana da magani?" Ya girgiza kai. Na miƙe na bar shi a wajen zaune,gudun kada ya karyar mini da zuciyata.

Ina jiyo su daga falo,suna cikin É—akin Mama yana gaya mata, amsar da ta bashi ce nima ta É—an firgita ni.

"Gara haka,ai ni har naji daɗi, tun da baka son ƴar mutane a dinga ajiyarta a gidanka,ƙwanaki nawa kuka ɗauka da ita ba ka ji kana son ta ba,sai yanzu....?"

"Mama zan iya yi miki rantsuwa da Alƙur'ani akan ina son ta, Mama duk laifinta ne...."

"Laifintan wa? Kusan kullum sai mun yi waya in har baka zo ba,in dinga ƙwatanta maka cewa don tana mace,kai ya kamata ka dinga shishshige mata,yau da gobe za ta saki jiki da kai."

"Wallahi Mama, ina yi mata, ita da wanda take so,wai shi ANWAR."

"Shi kenan ka ga yanzu ka yi wa kanka, ita kuwa tana da wani."
Chapter 2 · 0% Book details