← Book details Kasaita Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 7 OF 17

Sashe 7

Kasaita Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Na san kin gane na samu kaina cikin son ganin ki,shi yasa ki ke wahalar da ni." Shi ma tamkar ba shi da lafiya yake mayar mini da amsa.

"Sorry."

"Ina jiran ki."

Bai jira na mayar da amsa ba na ji ya kashe. Na ƙurawa kan wayar ido, tamkar zan ga hoton Yarima a ciki, na yi murmushin da ya ratsa jijiyoyin jikina, sannan na miƙe.

Ƙarfe tara daidai ina gaban madubina ina kallon jikina, riga da siket ne na atamfar Super Holland, ɗinkin wanda ya bi jikina ne, shi ne mai (shape) babu wani ƙwalliya a gaban ɗinkin sai dai buɗaɗɗan wuya ne mai zagaye. Sai kawai dogon zib tun daga saman wuya har izuwa bakin ƙugu, wanda makamin zuge shi,zamu iya cewa ya yi kama da ɗan ƙaramin zobe, shi kuwa siket ɗin irin ɗinkin nan wanda ƙarshensa buɗaɗɗe ne sosai.

Takalman dana saka, basu da wani tsini sosai, mayafin jikina kuwa kalar takalman ne, wanda suka yi shige da ɗaya daga cikin ƙwalliyar atamfar wato ja, turaren (Glorious Lonkoom) shi na feshe jikina da shi, wanda wayar G.S.M ce mai kalar ja a hannuna. Na yi murmushi sannan na tambayi kaina, shin me yasa nake jin farin ciki a zuciyata? Na lumshe idanuwana haɗe da tunanin wai ga Yarima nan zai rungume ni ta bayana.

Na buɗe ido da ɗan saurina har da ƴar ƙara haɗe da ɗan tsallena, tamkar da gaske, na yi dariyar da na ji tamkar yau ne ranar da aka yi mini wahayi da farin ciki, sannan na nufi gidan Yarima.

Falon ƙasa na yi sallama na shiga, kafin in rufe baki mutane sun kai baƙwai suka zube a gabana suna kirari da gaisuwa a gare ni, na amsa masu cikin nuna nima fa ƴar mulki ce, kafin in ƙarasa wajensa,tuni an malala mini wata lallausar darduma a wata kujerar da ke kusa da shi da alama ta mulkinsa ce.

Yarima kuwa yana ƙwance a gadon mulkinsa mai kama da katifa,ko in ce kujera mai hannuwa, amma mai faɗin gaske, ban da fitilu da ke zagaye da ita, ita kanta katifar mulkin sai ka tattaka hawa biyu sannan ka same shi ana uku ƙwance,ke nan kamar kana hawan matattakalar bene.

Yanda yake a ƙwanciyar rigingine nan wayoyin hannu da na gida sun zagaye shi sun kai baƙwai, amma kai da ganinsa ka san hankalinsa ba ya a wajen mutanen da ke zagaye da shi, suna ta fadancinsu,su ma za su kai taƙwas, daga ƙwancen da yake kawai ya waigo da kansa ya kalleni.

Hararar lumshe idanuwa ya yi mini,wacce zan iya cewa ta bayar da ma'anoni da dama, gaisuwa,kin mini laifi,ƙauna,son ganin ki nake,na ji daɗin zuwan ki.

Cikin nuna ban fahimci mai yake ciki ba na ɗan ɓata fuska alamar na ji haushi,nan take na ga yana girgiza kansa, sannan ya juyo ya kalli mutanen da suka kasu gida biyu. Wasu a wajensa suna yi masa firfita da gyara shi, ban da kirari da suke yi masa. Wasu kuwa suna a kaina ni ma ana yi mini nawa,kallonsu kawai ya yi sai na ji suna cewa.

"Mun bar ku lafiya, Æ´aÆ´an mulki, waÉ—anda suka gaje shi, godiya muke."

Kafin su ce sun yi gaisuwar nan da suke,ko in ce sallama,tuni wani dogari ya iso gabana da faranti a hannunsa lulluɓe da farin yanki,a take na fahimci komai wai in ina so inyi musu ƙyauta.

Na ɗan sunkuyo kaɗan na ɗauki bandir uku na miƙawa na kusa da ni da hannu na yi masu inkiya da su raba. Ai kuwa na sha godiya da kirari irin na ƙwararrun dogarawa. Cikin mintuna uku falon ya koma shiru, daga ni sai Yarima da ke ƙwance, kamar mai jiran motar asibiti (Ambulance),ta zo ɗaukar shi.

Mun samu mintuna biyu a haka, sannan na yi murmushi na ce a zuciyata, mulki sai mai shi, sai kuwa ɗan da ya gaje shi. ƘASAITA, sai Sarki, sai kuwa jinin da ya fito ta sarauta. Na girgiza kaina sannan na yi murmushi na miƙe tsaye na nufi inda yake ƙwance.

*ƘASAITA BOOK 2*

*NA*

*MARYAM KABIR MASHI*

Page 6

Dole,in zamo ƙasanshi, ta wani ɓangaren kamar yanda Aunty ta faɗa, matattakala biyu na hau, sannan na zauna gefe ɗaya.

"Sorry." Na faÉ—a cikin sanyin murya. Ya juyo da fuska ya kalleni,kunyarsa tasa na sunkuyar da kaina, ina jin motsawarsa ashe matsowa ya yi ya kama yatsun hannuna É—aya.

"Yasmin kin firgita ni sosai,kin tayar mini da hankali,kin saka mini rashin walwala a jikina."

Ya sumbaci tafin hannuna na É—an yi saurin janyewa nuna alamar kunya, na É—an juya kansa jin a daidai nan yana magana.

"Yunwa nake ji, ki taimaka mini da abinci."

Na sa tafin hannuna na É—an ture shi.

"Ba ƙya so?"

"Tashi mu je ka ci abincin." Na faɗa cikin muryar sassarƙewa.

Ina jinsa ya koma da baya ya ƙwanta da ƙarfi tare da ajiyar zuciya, na juya na kalleshi yana mayar da numfashi a hankali, ya juyo muka haɗa ido na yi saurin miƙewa, sai na ga ya yi murmushin kunya ta kama shi, shi ma sai ya miƙe.

Alkyabbar da ke jikinsa ya ƙara gyarawa, sannan muka nufi wajen cin abinci, sai da muka isa sannan ya cire alkyabbar ya miƙo mini,na karɓa sannan na tafi ga ɗan ƙarfen da ake ajiyewa na rataye ta, ina juyowa na gan shi tsaye sai kallona yake,muna haɗa ido muka yi murmushi gaba ɗayanmu.

"Zan tafi idan kana yawan kallona."

"Dole ne in kalle ki Yasmin,saboda kin canja mini rayuwata gaba É—aya,kin mayar da ni tamkar ba ni da jini a jikina."

"Ka gani...."

"Ki yi haƙuri ba zan daina ba fa."

Na juya alamar zan tafi.

"Zo, na daina." Ya É—auke fuska ya zauna sosai na iso na tsugunna a gabansa domin in zuba masa abinci.

Tuwon niƙaƙƙiyar shinkafa ne,miyar dagwargwajajjan naman kaza, wacce aka yi ta da agushi, ya yi kalar kore-kore da gani ya sha kori (curry),shi kuwa tuwon ya sha naɗi a leda tamkar a hotel, na zuba masa, sannan na buɗe ɗaya ƙwanon, farfesun dagwargwajajjiyar hanta ne, shi kuwa ɗayan farfesun kifi ne, wanda hausawa kan ce masa ragon ruwa, ga shi ya sha albasa mai lawashi a cikinsa, da gani an saka shi a injin ɗin zare ƙayar kifi,ko kuwa in ce injin ɗin sa ƙaya ta yi laushi.

"Ke fa?"

"Ni naci a gidana."

Ya yi murmushi.

"Sam ban amince ba,ni dai na san kunyata ki ke ji, amma tsaya ki ga yanda za'ayi."

Ya miƙe tsaye a inda ni kuma dama a tsayen nake ya isa makunnan fitila ya kashe ta, dawowar da zai yi sai ya rungume ni a jikinsa, ya yi ajiyar zuciya.

"Sorry, ban lura da ke ba." Ya faÉ—a cikin raÉ—a, sannan ni kuma na zame na zauna.

Zaunawar da na yi tayi daidai da kamawar wata Æ´ar fitila mai duhuwa wacce haskenta kawai za ka gani, amma ba zakaga mutum ba sosai, yanda nake zaune nan haka ya zo ya zauna kusa da ni a hankali ya dinga lalubo bakina yana saka mini tuwon nan, shi ma a haka ya ci nasa.

Idan na girgiza kaina, shi ma sai ya ce ya ƙoshi,ni kuwa na san Yarima yana tare da yunwa sosai, saboda tashin hankalin da ya saka kansa, na ganin zai rasa ni. Cin abincin da ya kamata ayi shi cikin mintuna sha biyar, sai ga mu mun ƙwashi awa ɗaya. Na gane haka ne a lokacin da na iso kicin domin ajiye ƙwanukan abincin da muka ci,ni kuwa na yi tsaye a kicin ɗin na rasa me ke damun jikina, saboda wasu abubuwa da nake jin suna yi mini yawo tamkar kiyashi na bi mini jiki,shin ko son kenan? Shin ko na kamu da ciwon son Yarima ne nima? Kamar yanda na ga duk ya yi laushi a kan ciwon da ya kama zuciyarsa da gangar jikinsa,wai shi ciwon so na.

Motsin da naji yasa na yi saurin ci gaba da harhaɗa ƙwanuka tamkar dama aiki nake tun da na shigo.

"Sannu da aiki."

Na juyo na kalle shi ya jingina da gefen ƙofa, ya rungume hannayensa a ƙirjinsa, murmushi kawai na yi masa,a zuciyata na ce lallai Yarima yana son ƙananan kaya, saboda riga mai dogon hannu da take jikinsa wacce ya ɓallewa maɓallan gaba na rigar.

"Ki bar shi, da akwai masu gyarawa."

Na sunkuya wajen famfo na wanke hannuwana, sannan na iso inda yake tsaye ni ma na tsaya saboda ba hanyar wucewa, maimakon ya gafara in wuce sai na ga ya rakuɓe gefen ƙofa sosai, ma'ana in zo in wuce, wanda ya yi mini alamar da hannunsa ɗaya, duk da dama idanuwansa tsaye suke a kaina suna yi mini kallon kamun barewar damisa a jeji, ma'ana tamkar idanuwansa za su lumshe gaba ɗaya.

A hankali na zo na raɓa zan wuce, sai da na shiga tsakiyarsa sai ya sa hannuwansa ya kare ni, wato ya saka ni tsakiya sai da ya lumshe ido ya buɗe ya ɗan girgiza kai alamar kana son faɗar wata magana, sannan ya yi magana.

"Ina za ki?"

"Kina da gidan da ya wuce nan?"

"Eh."

"Wanne kenan?"

"Wanda iyayena suka saka ni a ciki."

Ya É—an juyar da kansa ya kai sau huÉ—u, sannan ya dawo da kallonsa gare ni.

"Ina son da kiyi mini wani aiki."

"Na me kuma?"

"Mu je sama ki gan shi."

"Dare fa ya yi, goma ta wuce."

"Ƙuya kenan fa."

Nayi murmushin kunya.

"Na isa,mu je in yi maka ko na tafi kada inyi dare."

"Matata na ce mini za tayi dare a wajena,Yasmin kenan." Ya faÉ—a a daidai lokacin da ya sauke hannuwansa na wuce.

Sama na isa, wanda shi dama yana biye a bayana, kujerar da ke kusa da gado ita na zauna shi kuwa a zagayen gadon da ke tsakiyar É—akinsa, ina kallo ya janyo durowar kusa da gadonsa ya É—auko wata babbar ambulan mai fulawoyi ja, wanda ita kuma bulu ce mai haske (light blue), ya É—ago ya kalleni,ni kuwa dama shi nake kallo.

"Zo ki gani."
Chapter 7 · 0% Book details