← Book details Kasaita Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 5 OF 17

Sashe 5

Kasaita Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Me zan ce ai kin gama faÉ—a, Æ´aÆ´anki ne fa, shawarata É—aya in har da ragowar zamansu tare,to ki kira É—anki ki ja masa kunne, saboda laifin na wajensa,ai ya ba ni labarin duk abin da ya haÉ—a su tun farko."

"Allah ya huci zuciyar Sarki,a ƙara dai duba wannan magana." Inji Hajiya Kilishi.

Ya miƙe, "Zan je in huta kafin tafiya masallaci, zan duba maganar insha Allahu."

"Godiya muke,a huta lafiya, sai ka fito." Inji su gaba É—aya.

**** **** ****

Sarki Jafar Sada ne zaune a doguwar kujerar mulkinsa, amma ta fadar cikin gida, kenan ɗakin shaƙatawar da yake ganawa da iyalinsa. Ni da Yarima kuma muna zaune a tsakiyar fadar,kowannan mu kanshi a sunkuye a ƙasa,ko ban faɗa ba kuwa na san daga ni har Yarima gabanmu faɗuwa yake yi, saboda na kalle shi ta wutsiyar ido ko motsi ma baya iya yi, saboda sanyi da jikinsa ya yi.

Cikin ɗan satar kallo ta wutsiyar ido na kallo fuskar Sarki, gumi ne ya fara tsiyayo mini a fuskata,tun kafin in dawo da kallon gabana, saboda ganin fuskarsa da na yi ba wani annuri cikinta, ballantana alamar wasa. Na ƙara mayar da satar wutsiyar idon nawa ga yarima, na gan shi yana mayar da ajiyar zuciya, duk bayan sakan biyu, ban da gumin da na hango yana yi wa kansa magangara a jikinsa.

Take kawai sai na ji tamkar in sa haɓar mayafina in dinga goge masa, wannan ne ma yasa na ji kamar zuciyata na ɗan kiɗan da ba sauti, balle ta samu ƴan rawa, hakan kuwa shi ya tunano mini daran jiya yanda muka ƙwana.

A daran jiya ni na yi imanin babu wanda ya samu runtsawa ni da Yarima, dalilin da yasa na gane hakan kuwa shi ne,ganin saman ɗakinsa da fitila duk da ba mai haske ba ce ba,a tunanina ta gefen gado ce ma ya bari a kunne. Na gane hakan ne a sakamakon leƙen da na kusan ƙwana ina yi ta labulayen taga ta,wai ko na ga Yarima a ƴar barandarsa, yanda ya saba. Amma har na gaji na haye gadona ban ga ko da ƙyallin kayansa ba, wannan ya ba ni tabbacin bai samu yin bacci ba,ƙila gara ma ni tunda na samu na shiga bargona na yi lamo. Inji Malam bahaushe ya ce, "wacce ta fi barci daɗi." To ni dai jiya, wacce ta fi barci ciwo na yi.

Saboda har yatsun hannuna sai da suka yi mini ciwo, saboda jan carbi,wai ko ya suɓuce daga hannuna in samu bacci ya ɗan ɗauke ni, amma sai dai na gaji na ajiye na cigaba da lazimin cikin zuciya, sai dai wani abin al'ajabi zan ce ko abin haushi? Wai har a wannan lokacin sai na ji zuciyata har gangar jikina sun ƙi amincewa da suna iya zama da Yarima Faysal, mutumin da yake taƙama da mulkin ƘASAITA,shin ko dai ni ce ban san son ba, ban kuma san makarai da makangan so ba? Tambayar tawa babu mai amsa mini ita.

Ganin har ƙarfe uku na dare ta yi yasa na miƙe na yi alwala domin in ragewa kaina da zuciyata zafin da suka ɗauka, sannan in roƙi Allah da ya zaɓa mini abokin zama wanda yake mafi alheri a gareni, Anwar ko Yarima, saboda ni na kasa gane wa nake so a cikinsu.

Ƙarfe goma na safiyar yau juma'a sai ga ɗan aike daga fadar Sarki,magatakarda ya kawo mini saƙon zungureriyar takardar da ta ƙara tayar mini da hankalina,dama daga wanka na fito, cikin nauyin jiki don ma na samu na ɗan gyara fuskata, da ɗan mutstsuka mai ina shirin saka kayana saƙo ya iso mini.

Tun da na zauna a gefen kujerar tsakiyar ɗakina ban iya ma buɗe takardar ba, saboda ji nayi kamar kaina ba a wuyana yake ba,ni kaina ban san iya mintunan da na ɗauka ba a nan zaune, sai da Mansura ta shigo sannan na ji tana tambaya ta wai lafiya? Duk maganar da take mini a farko na ɗauka mafarki nake, sai da na ji an dafa mini yatsun ƙafafuna, sannan na ɗaga na gan ta a durƙushe gabana.

Ban san hawaye nake fitarwa ba sai da na dawo hankalina ga shi duk tafiyar nan da na yi ban ji na je kowacce duniyar tunani ba,ni dai cewa na yi ko kuwa don haukan minti biyar É—in da aka ce duk É—an adam na yin shi duk rana kenan dai shi na yi a zaune.

Miƙawa Mansura takardar na yi na ce karanta mini da ƙarfi. Da ta karanta sai na ji ba wata takardar tafiya gida ba ce,ko ince takardar rabuwa da Yarima ba, ashe ta saƙon in je Sarki na kirana ce,in an sauko daga masallaci,tana gamawa na ce mata je ki waje ga ni nan zuwa, to ina za ni? Wa zan gayawa? Tunanin da na cigaba da yi kenan.

Cikin mintuna baƙwai sai na ji Aunty Salwa ta faɗo mini a raina, na yi sauri na miƙe na ɗauko wayata na daddana nambobin, minti ɗaya aka ɗauka, ina fara gaya mata abin da ke faruwa. Ya isa haka ta ce mini,in je tana son ganina,ba zancen waya ba ne ba, saboda haka in tambayi Yarima in fito da wuri,in biya ta gidanta.

Wannan fa ya bani ƙwarin gwiwar in shirya in isa gidan Yarima,a yanzun ɗin nan. Baƙar shadda ce Galila, wacce aka yi wa aikin hannu, duk ta sha ɗigon farin aiki, ƙasan zanin kuwa aiki ne mai yanka-yanka, iya kusurwar cinya yake, sai hannu iya rariyar hannuna, duk ya sha tsagun irin na jikin zanan.

Turare na ɗauka hannuna ina shirin fesa shi a jikina, sai na ji murɗawar ƙofar ɗakina a hankali, ban yi tunanin juyawa in ga kowa ke shigowa ba, saboda ganin ina tsaye a jikin madubi kenan ko wa ye zan gan shi ta cikin madubina. Gabana na ji ya yi wani abu wanda ya ratsa mini naman jikina ya bi ta cikin jinina har ya fito ga saman fatata. In da gashin da ke saman fatar duk ya miƙe tsaye, wannan ne na ji ana cewa tsigar jiki.

"Me ya kawo mini? Ganin Yarima da na yi ta cikin madubina ya shigo da doguwar rigar bacci jikinsa mai wani irin aikin sarauta, amma iyakacinsa bakin ƙofa, ya jingina da ƙofar ya mayar da hannayensa ya goya a saman ƙirjinsa ya harɗe ƙafafunsa da juna, tare da mayar da kai ya jingina shi a jikin bakin ƙofa sannan ya ɗan ɗaga kansa sama da turaran a hannuna na ɗan wayance na iso wajen da yake a tsaye.

"Yarima barka da asuba."

Ya juyo da kanshi ya kalleni, sannan ya amsa da laɓɓansa ne kawai na ga sun motsa, har da lumshe idanuwa da buɗewa.

"Lafiya?"

Ya juyo ya kalleni,a take na ga idanuwansa sun yi jajir.

"Da ki kaga me?"

Ya faÉ—a cikin maganar raÉ—a-raÉ—a.

"Idanuwanka na ga sun yi ja.”

Sai na ga ya yi murmushin da ya dinga fitar da sauti, sai na ga ya wuce ni ya shiga cikin ɗakin ya samu kujerar da ke tsakar ɗakin ya zauna, sannan ya ɗago hannu ya yafito ni, ya nuna kusa da shi, ma'ana in zo in Zauna. Ban wani nuna damuwa ta ba na iso amma sai na ji na kasa zama saman kujerar na koma gefe ɗaya na zauna a ƙasa, madadin ya yi magana shi ma sai na ga ya zamo ƙasa ya zauna kusa da ni, na yi alamar zan matsa, gaba ɗayan shi ma ya juyo gare ni tare da kaikansa wuyana. Cikin maganar raɗa na ji ya yi magana.

"You hate me.”

Ya ƙara yin sama da kan shi zuwa daidai kumatuna.

"Sarki ya aiko in je."

Na yi saurin faÉ—a ina mai alamar tashi, yasa hannuwansa duk biyu ya rungumo ni jikinsa ta gefena.

"Yarima."

"Yasmin, Yasmin, Yasmin,jiya na ƙwana ina roƙon Allah ya cire mini ke daga zuciyata but still... Na lura ke har yanzu zuciyarki ba ta son zama da ni." Ya yi murmushi.

"Nayi tunanin in zo in yi sallama da ke, Idan har na fahimci ke har yanzu you don't want to stay with me,saboda ni na san halin Sarki, ba ya sauraran komai idan ya riga ya faɗi magana.”

Duk wannan maganar da yake yi a cikin raɗa yake yin ta, irin ta marar lafiya, sannan ga shi ya matse ni a jikinsa, sai shinshinar min wuya yake,yana ƙara tura kansa cikin wuyana,ni kuwa idanuwana a lumshe suke ban da numfashina da ke neman ɗaukewa.

"Ba zan iya tsallake duk hukuncin da Sarki ya yanke min ba, amma zan ɗan yi iya ƙoƙarina in ga ko na samu nasara.”

Ya yi shiru a daidai lokacin da ya juyo da fuskata a tasa.

"Amma na yanke hukuncin barin ƙasar.”

"Saboda me?" Na faÉ—a a sanyaye nima.

"Saboda ke.”

"Kai da baka so...” yasa yatsunsa biyu a laɓɓana yana zagaya su, wannan yasa ban iya ƙarasa magana ta ba.

Na yi ɗan hanzari kaɗan na miƙe, saboda jikina da na ji ya fara rawa.

"Wai me ye haka Yarima?”

Na yi irin maganar nan wacce da ji na da ƙyar na ƙwato ta daga bakina, ya mayar da numfashi ya kai sau baƙwai, sannan ya miƙe tsaye.

"Sorry.” ya juya ya tafi, har ya kai ƙofa na tuno da maganar zuwa gidan Aunty Salwa,na yi masa magana.

"Yarima,ni zan je gidan Aunty Salwa yanzu, bayan masallaci nima zan wuce Sarki ya aiko in je."

"Ki gaishe ta.” Kawai ya ce ya juya ya fita,a inda nake tsaye a nan na durƙushe na yi wajen minti talatin sannan na samu da ƙyar na miƙe na ƙarasa shiryawa.

Ban ƙara ganin Yarima ba sai da na shiga ɗakin Hajiya a nan ne take ce min Yarima na cikin ƙuryar ɗakinta a ƙwance, ban iya tambayarta ba ko lafiya sai na ji zuciyata tana son ta ganshi, na san kuwa ba zan taɓa iya wuce Hajiya in nufi ƙofar dakinta ba, har na zauna na ji ta ce, "Shiga ciki mana ki zauna man baƙi sun yi yawa, balle ma yau juma'a." Na ce to, tare da saurin tashina.
Chapter 5 · 0% Book details